Showing 54001 words to 57000 words out of 114314 words

Chapter 19 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt

out Ruqayyah", Ruqayyah na sharɓe hawaye ta miƙe ta fita, Momy tace "Alhaji karka yanke hukunci cikin fishi, ka tsaya kayi nazari dan Allah, yaran yanxu sai a hankali idan ka biye musu sai ka bata musu rayuwa da baki ko kuma ka tagayyara su da wani action ɗin, Allah ya huci zuciyarka, plxx think twice kafin ka zartar da hukunci...". ajiyar zuciya yayi yace "toh aurar da ita zanyi daman har yanzu Dauda na ciki", Momy tace "Eh ba damuwa gara ayi mata auren" da haka ta tashi ta fita.


★Tinda aka mayar da Sa'adatu da Maimuna makaranta shegun suka samu babban lasisin tsula tsiyarsu, yau sati uku kenan sau ɗaya suka taɓa zuwa, a kullum zasu shirya cikin uniform harda jaka snn su fita, daga sun fita sai ko wacca ta kama hanyarta, Maimuna ta wuce yawonta daga wnn hotel ɗin zuwa wani, Sa'adatu kam gidansu Mabaruka take wucewarta su sheƙa ayarsu san ransu, daga lokacin tashi daga makaranta yayi sai su dawo gida, hakan ba ƙaramin daɗi yake musu ba, su a ganinsu da baƙi ƙirin gwara baƙi baƙi. A fanin Hajar kam babu abinda ya shalleta dasu, a kwandon shara ta wurga su, ita gani take ma kamar babu su a gidan, koda sun takaleta saidai ta yamutsa fuska tayi banza dasu ko kuma ta shige ɗaki. ta kwantar da hankalinta ta zubawa idonta toka bama ta gani ba bare ta tanka, ta tushe kunnenta bama ta ji ba bare ta tanka, ranar Alhamis da daddare Hajar na zaune a soro tare da Nura, firar su suke cike da shauƙi da kaunar juna, rufe fuskarta tayi da hijab tana tiƙar dariya sbd abin dariyar da ya fada, shima dariyar yake yace "insha Allah gobe zasu kawo min kuɗina wajen Baba..", ta bude fuskarta tace "kuɗin me?", yace "kuɗin da zan ɗauki hanyar mallakarki..", turo baki tayi tace "kaji ka ko, toh wai haka ake yi, nifa har yanzu ba sanka nake ba, kuma ni ƴar yarinya ce ban isa aure ba" ta murguɗa masa baki childishly, murmushi mai sauti yayi yace "Ohh really, ai naga alama shiyasa yau kika takura sai naxo kin ganni hakan ma ai duk cikin rashin so ne, snn kuma very soon zaki zama mother kinga ba maganar yarinta..", ta juya manyan idanunta tace "Au nice ma nace maka kaxo ko?", kafaɗa ya ɗaga yace "Eh mana, kin ga you inform your parent kinji", wani gwalo ido waje tayi tace "chabb ai kwa ba za a kawo kuɗin ba indai ni zan gaya musu", dariya ta basa sosai na expression dinta yace "toh meye aciki?", yana kwaikwayon muryarta yace "haka fa kawai zaki ce, Umma Baba gobe za a kawo kuɗin", turo baki tayi tace "ni gida zan shiga", ya kalli agogon wayarsa yace "Okay, sai munyi waya don ban gaji da jin muryarki ba", ledar da yazo da ita ya miƙa mata, ƙin amsa tayi tace "A'a nagode", haɗe gira yayi yace "amshi mana ko so kike mu ɓata", a hankali ta amsa tace "nagode", ya tashi ya nannaɗe darduman da ya zauna ya naɗe wacca Hajar ta zauna ma, amsar darduman tayi tace "nace maka fa ka ringa bar min zan naɗe fa", yace "naƙi ɗin..", ya ringa kallonta har saida ta gaji ta juya masa baya tana turo baki tace "Allah nace maka fa banaso", yace "toh me nayi miki", tace "saida safe" ta shige gida. tinda ta shigo Maama da Sa'adatu dake zaune bakin ƙofar ɗaki suke binta dana mujiya, Maama tayi tsaki tana kallon ledar hannunta, Sa'adatu tace "kullum sai a shigo da wata mitsiyaciyar leda, uhmm Maama za kiji zuwan da dawowar wllh, a banza ake zaman soro harda su leda, ai nasha ganin blue film na zahiri a soron nan...", Maama tace "barewa tayi gudu ɗanta yayi rarrafe, ai muna ganin jalala a wnn gidan...", Hajar dai ta wuce ɗaki abinta. washe gari Juma'a, bayan Sallahr la'asar aka kawo kuɗin Hajar, Baba ya shigo gida da uban kuɗin a hannunsa yana kabbara yace "alhmdllh", yaye labule Maama tayi tace "wnn kabbara haka malam sai kace wanda akay wa bushara da gidan aljanna..", yace "ki fito ki saka albarka kuɗin auren Hajara aka kawo", Maama ta buga wata shegiyar guɗa ta fito tace "Au haba, ƙwandala nawa aka kawo?", ƙanƙance ido yayi yace "wace irin ƙwandala kuma Rabii?, ke me yasa ba a abin arziƙi ne dake", tace "ai gani nai ƙwandalar ce ta dace da ita", Baba ya girgiza kai yace "kiyi fatan Allah ya bawa ƴaƴanki ko da rabin nata ne..", da sauri Sa'adatu da Maimuna suka matso jikin window suka kasa kunne suji nawa aka kawo, Nabilah kam taɓe baki tayi, Maama tace "nawa ne", Baba baice komai ba ya kunce ledar uwar kuɗin ya fito dasu, zaro ido Maama tayi ganin yawansu, tinda take bata taɓa ganin kuɗi masu kaurin haka ba, Baba ya mayar da kuɗin yace "ƙwandala goma ne" ya wuce ɗakinsa ya barta nan tsaye da sakakken baki, wani tuƙuƙin baƙin ciki da hassada ne ya turnuƙeta, tamkar kububu haka ta afka ɗakinta, ta dubi Maimuna da ke jikin window tace "wai mahaukaciya kuka mayar dani ko me?", Maimuna ta turɓune fuska cike da rashin ɗa'a tace "toh wai ke Maama me mukay miki ne?", wata muguwar ashariya Maama ta lafta mata tace "uban ki kikai min, ji nake cemin kukai faƙiri ne ke neman auren Hajara, toh ba kuga uban kuɗin da aka kawo ba na aure", Sa'adatu tace "wai uban kuɗi naji fa Baba yace ƙwandala goma", Maama da zuciyarta ke tafarfasa tace "toh wasu dunƙulallun kuɗi ne ƴan dubu dubu, kaurinsu da aukinsu inajin sun doshi miliyan...", baki suka haɗa sukace "Aaaaaa Maama haba dai", cike da takaici ta shiga kutuntuma musu ashar tace "ƙarya nake knn?", Nabilah ta fashe da dariya tace "A haba dai Maama ya zai kiyi ƙarya ai saidai ki faɗa ba daidai ba ko Maimu", Maimuna tace "kwarai kuwa, Maama na rasa me yasa kika ɗaga hankalinki a kan wanda waccar matsiyaciyar zata aura", Maama ta gasa mata harara tace "yo ba dole hankalina ya tashi ba, ha kurum sai taci gaba kuna zaune jaɓar kuna kallonta..", Sa'adatu tace "Maama nifa kinsan ba aure zanyi ba, indai cigaba na aure kike magana toh na yarda Hajara ta fini a wnn fannin", Maama ta saki baki tana kallonta tace "Au haka zaki zauna a gidan ba xaki gidan mijinki ba...", Nabilah ta taɓe baki tace "Ayyah Maama ai ki saka Sa'adatu a addu'ar ki ta koda yaushe, dan na gaya miki irin alfashar da nake tunanin suna aikatawa da tumakan ƙawayenta amma kin ƙi yarda", Sa'adatu tace "dalla malama ban kasafta dake ba bare ki dauka..", Nabilah tace "kinyi kaɗan bari kiji in gaya miki, toh baki kai nan....", Maama tace "ya ishesku, zaku fara raba halin naku knn", Maimuna tace "dama kin rabu dasu yauma nasha kallo, ai sun iya bawa hammata iska" ta fashe dariya. Da misalin tara da rabi na dare wayar Hajar tay ringing, yamutsa fuska tayi snn ta sakata a silent, yau dai baza tay picking ba, gado ta hau tayi kwanciyarta zuciyarta wasai, an kawo kuɗin aurenta da ya sayyadi, washe gari ta tashi ta gama komai na gyaran gida da ta saba, har waken kulele saida ta wanke, bayan ta gama komai ta shiga wanka, tana shafa mai Umma ta shigo ɗakin, gaban wardrobe ta tsaya ta ciro kuɗi snn ta koma gefen gado ta zauna tace "idan kin shirya zan aikeki gidan Jamila", Hajar tace "tom" ta cigaba da rubbing cream a fatarta, doguwar rigar atamfa ta saka, ta sanya hijab da ya tsaya mata a guiwa tace "Umma na gama", Umma ta miƙa mata kuɗin hannunta tace "ki kai mata wnn, za muyi waya da ita", Hajar ta amshi kuɗin ta saka a jakarta tace "na tafi", Umma tace "karki kai yamma", tace "tom" ta ɗauki flat shoe a ƙarƙashin gado ta fita, a soro ta tarar da Naseer da yazo jiya, ta sunkuya tace "yaya ina yini", yana kallonta yace "lfy lou, ina zaki haka?", tace "Umma ce ta aiken gidan Anty Jamilah", gyaɗa kai yayi yace "Okay" ya wuce ciki ita kuma ta fita, cike da nutsuwa take tafiya har ta isa bakin titi, cikin sa'a kam ta samu Napep da wuri, tana zuwa gidan ta tsaya bakin gate tayi knocking, Hafsa ce ta buɗe tana ganinta ta zaro ido tace "the bride to be wnn bazata hka", Hajar ta shiga gidan tace "ina Tahfeez din, yau naga asabar..", Hafsa tace "ba nida lafiya". da haka suka shiga ciki, Hajar ta durƙusa ta gaida Anty, Anty tace "lfy lou, ya mutan gidan", Hajar tace "suna lfy", Anty tace "madallah", Hajar ta zuge jakarta ta ciro aiken ta mikawa Anty tace "gashi inji Umma".......✍️




💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche


{27..}
Da mamaki a fuskar Anty ta amshi kuɗin tace "toh, na mene?", Hajar ta girgiza kai tace "bansani ba amma tace za kuyi waya", Anty ta gyaɗa kai tace "Okay". Hafsa ta tashi ta nufi ɗakinsu, wayarta da ke kan mirror ta ɗauka, call log ta shiga ta nemo wata number ta shiga dialing, tana fara ringing akay rejecting few seconds kira ya shiga daga same numbern, ta kara a kunne tace "Assalamu alaikum", from the other side Ahmad yace "Wa'alaykissam salam, young lady", tace "yawwa, nace ba, yau idan babu damuwa zaka iya zuwa na cika alkawarin da nayi maka", keenly yace "Okay, na ɗauka ma kin manta ashe ba haka bane", tace "yap, sai kazo immediately after Asr prayer", yace "insha Allah", kashe wayar tayi tace "kar alƙawari ya zarbaɗo ƙafata ranar lahira ya hanani gudun famfalaƙi..", palour ta fito ta zauna, Anty ta kwashe kuɗin da ta ajiye hannun kujera ta shiga room ɗinta, wayarta ta dauka, missed call ta gani daga ƴar uwarta, zama tayi gefen gado ta shiga kiranta, Umma na dauka suka gaisa, Anty tace "Hajar taxo da saƙo, Adda kuɗin na mene?", Umma tace "kinsan jiya aka kawo kuɗin auren Hajara, Jamila ba a fafe gora ranar tafiya, wnn kuɗin wnda nake ɗan tarawa ne tin tini, shine nace bari na turo miki su sai a fara mata ƴan tsince tsince sha'anin aure da yawa..", Anty tace "gaskiya haka ne ba a fafe gora ranar tafiya, toh mai za a tsinto da wadan nan kuɗin?", Umma tace "abinda kika ga ya dace Jamila, koma mene asiya a ajiye", Anty tace "wata shida suka sa ko?", Umma tace "Eh, kinga kwa ba lokaci, yanxu sai kiga abin yaxo kusa, idan na sake tara wasu saina turo miki kafin lokacin muga abinda za muyi", Anty tace "gsky kam, toh wnn kuɗin dai saidai na siya mata decorants, kayan kitchen nawa ne ni zan mata", Umma tace "Kaii Jamila abun fa da yawa", Anty tace "she's my daughter fa, insha Allah zan mata duk wani abu da ya danganci kitchen, cikin rufin asiri zamu kaita insha Allah babu me rainata a dangin miji ko kuma a goranta mata". Umma ta ajiye numfashi tace "toh Ameen, Allah ya tabbatar mana da alkhairy", Anty tace "Ameen". Hafsa ta kalli Hajar tace "gsky fa zanyi amarancin a bikinki, daman nice ƙirjin biki kuma babbar aminiyar amarya", Hajar tayi murmushi tace "yayi kyau..", Hafsa tace "anko kala uku zan fitar mana na ƙawayen amarya snn kuma zan shiga na ƴan gida, ga wanda zanyi iri ɗaya da amarya ranar yini, kai abinfa ba a cewa komai gsky zan zuba amaranci", Hajar dai ta ringa binta da ido tana murmushi, wai itace wacca ake maganar bikinta, bikin ma da rabin zuciyarta Nura. Hafsa tace "amma dai ba yau zaki tafi ba ko?", harararta Hajar tayi tace "chab ana yin sallar la'asar zan samfe..", Hafsa tace "kaiii dan Allah ki kwana", Hajar tace "yau naga jalala daga zuwa kuma sai kwana, A'a wllh tafiya zanyi", Hafsa ta haɗe gira ta tashi tace "sai ki ta tafiya" ta wuce kitchen, Hajar tace "ai daman tafiyar zanyi", Abinci ta zubo musu ta kawo ta ajiye, ta koma kitchen ta ɗakko gaseous drink da pure water ta kawo ta ajiye, tana hararar Hajar ƙasa ƙasa tace "saiki matso muci", salon ta sake bata haushi tace "na ƙoshi", Hafsa ta ajiye spoon ɗin hannunta tace "ke kin isa, kadan ba sai kinci ba", Hajar ta tashi ta cire hijab ɗinta snn ta zauna ta ɗauki spoon, Hafsa ta kai spoon baki tace "toh ki bari ƙarfe biyar da rabi ko shida saiki tafi", Hajar ta noƙe kafaɗa ta cigaba da cin abincinta, suna gama ci Hafsa ta tattare plate da empty bottle na drink ɗin ta wuce kitchen dasu, ganin ta daɗe bata fito ba Hajar ta bi bayanta, tarar da ita tayi tana wanke wanke bakin sink, Hajar tace "Au wanke wanke kika tsaya", Hafsa tace "harda left over na safe da banyi ba". Hajar ta tattare hannun rigarta ta matsa gaban sink ɗin ta fara temaka mata da ɗauraya, Hafsa tace "kina fa da kirki amma kaɗan" Hajar tace "point of correction bani dashi". wata small pot Hafsa ta ringa gurzawa soson ƙarfe tace "Abdallah ne ya babbaka indomie da safe", Hajar ta leƙa cikin tukunyar ganin yadda tayi baƙi ta fashe da dariya tace "amma dai Indomien ba tada maraba da gawayi", Hafsa tace "uhmm gobara ya kusan tayarwa fa, ba kiga faɗan da yasha ba kuwa wajen Abba, har suka fita kasuwa Abba na faɗa", Hajar tace "wai Allah ya kiyaye". Ana yin sallar la'asar Hajar ta fara shirin tafiya, ta tsaya gaban mirror tana gyara ɗaurin dankwali, hijab ɗinta ta janyo zata saka Hafsa tayi wuf ta amshe tace "ki bari ba yanzu ba", Hajar ta riƙe ƙugu tace "ka jimu da mata, toh wai me zan miki?", Hafsa tayi serious face ta nuna mata kusa da ita tace "dan Allah zauna kiji", Hajar ta zauna tana kallonta tace "what..?", Hafsa ta marairaice fuska tace "tin kina nan gidan nayi masa alƙawari", Hajar da ta ƙosa taji mene tace "wa knn?", Hafsa tace "wnn mutumin da muka haɗu a supermarket", Hajar ta ƙanƙance ido tana nazari, lokaci guda ta gwalo ido waje tace "alƙawarin me kikai masa", kaf Hafsa ta gaya mata abinda ya faru, Hajar tace "toh yanxu ya kike so ayi?", Hafsa tace "so nake idan yazo ki fita, ni ko biki masa magana ba hakan ya wadatar", Hajar tace "da baikon a kaina zan tsaya da wni namijin", Hafsa tace "ai manufar abin zaki duba, bawai zaki tsaya dashi bane a matsayin saurayi, dan Allah don't turn me down just say Hi shknn", Hajar ta dafe kanta tace "wllh kin tafka wauta, idan ya wuce huɗu da arba'in tafiya zanyi wllh", Hafsa tace "bazai ma kai haka ba..." ko gama rufe baki ba tayi ba saiga kira nan yana shigowa wayarta, numbern kawai ta gani tayi ajiyar zuciya ta ɗauka, kara wayar tayi a kunne, yace "nazo", tace "Alright, wait a minute". ta kashe wayar ta kalli Hajar dake kallonta tace "yazo", gyaɗa kai Hajar tayi tace "toh sai muje ko", Hafsa ta gwalo ido waje tace "wai tare zamu, kefa kaɗai zaki", Hajar ta gyara zama tace "kince kar naje knn", Hafsa tace "toh sai ki yiwa Anty sallama daga nan ki wuce kinga na samu hanya sai nace rakaki zanyi", Hafsa ta saka hijab dinta, dakin Anty Hajar ta shiga tayi mata sallama, Anty ta bata 1k kuɗin mota, Hafsa tace "Anty na fita rakata", tare suka fita gate, Hajar ta matsa gefe tace "fara fita", buɗe ƙofar gate ɗin Hafsa tayi snn ta fita, yau ma dai a wata jugunanniyar motar yazo saɓanin ta ranan, yana hangota ta tint glass ɗin ya buɗe motar ya fito, mayar da door yayi ya rufe snn ya ƙaraso wajenta yayi sallama, tace "wslm, ina yini", yace "lfy lou, ykk?", tace "alhmdllh am great", juyawa tayi da nufi mgana da Hajar ai kam taga wayam, tace "lemme get her" ta shiga gida, a tsaye ta ganta da wani expression bisa fuskarta, Hafsa tace "toh muje", Hajar tace "wllh ban san me zance masa ba", Hafsa ta ja hannunta tace "anything" saida ta kaita har gabansa snn ta cikata, Hajar ta ja baya making some distance between them, Hafsa tace "As promised", waje ta basu ta shiga maƙotansu, gefe Hajar ta kalla tace "ina yini", bai amsa ba ya jefa mata tambaya "you blocked my number right?", kanta a ƙasa tace "yess", kallon fuskarta kawai yake yace "why?", tace "sorry you ask for a chance da bazan iya baka ba, kayi haƙuri dan Allah, wllh a lokacin inada manemi wnda yaje wajen iyayena, bana so na ɓata maka lokaci shiyasa", wani iri ya ji har cikin zuciyarsa yace "Alright, ynxu fa?", tace "ynxu kam an riga an min baiko, kayi haƙuri..", wani deep breathe ya sauke yace "ba damuwa Hajar, loosing you is one of my destiny, may Allah choose the best for us", a karo na farko da ta ɗago ta dubesa, ta mayar da kanta da sauri tace "Ameen, nagode", gidan da Hafsa ta shiga ta nufa ta fara knocking, Hafsa ce ta buɗe ganinta ta fito tace "har ya tafi..." shiru tayi ganinsa a tsaye yana kallonsu, ta ƙarasa inda yake tace "then ynxu dai na fita daga jerin masu yanke fate, na cika alkawari", yace "thank you", tace "don't mention, sai anjima", yayi waving ɗinta slightly snn ya juya ya shiga motarsa zuciyarsa a dagargaje, wani irin cin taya yayi ya juya kan motar, da gudu yabar unguwar tamkar zai tashi sama, Hajar tabi ƙurar da ya tayar da kallo snn ta matsa kusa da Hafsa suka sauka kan titi, Hajar tace "ya bani tausayi wllh", Hafsa tace "Allah ya basa wata". da haka Hajar ta tsari Napep ta wuce gida.


★A kwana a tashi lokaci bashi da wuya wajen shuɗewa a wajen Ubangijin talikai, mu shagalallun bayi mu muke ganin jimawarsa harda ɗokin cika burikan rayuwa ( yau HAJAR ya ɗakko wani daga cikin scene na littafina SOHANA), A wannan rana ta laraba saura wata ɗaya bikin Hajar, kuma a wnn rana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login