Showing 72001 words to 75000 words out of 114314 words
Chapter 25 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
magana Anty ta turata waje tace "ki fita nace Rabii", Maimuna ta buɗe baki za tay mgana Anty ta daka mata tsawa itama ta hankaɗata waje ta rufe ɗakin tace "da so samu ne ma ku fita, ko mala'ikun rahama sun shigo" da haka ta bar wajen ta sauka ƙasa. Maimuna ta mulmulo ashar tace "ni za'a wulaƙanta akan wnn kuturun gidan, wllh gidan da Alhaj ɗina zai sakani yafi wnn sau dubu", Maama ta gasa mata wata shegiyar harara tace "zan ɗuɗɗura miki ashar wllh, Alhaj ɗin banza Alhaj ɗin wofi, yana ina shi Alhaj ɗin", Maimuna ta tsuke ido tace "Maama fa zaginsa kikai?", Maama da take neman gurin huce takaici tace "na zaga ɗin", Maimuna tayi kwafa tace "kin dena cin ƙwandala daga kudinsa wllh, ni na tafi gida bazan zauna ana min gori ba", Maama tace "tsayani mu tafi kar zuciyata ta fashe..", a hankali Maimuna take sauka daga kan stairs din da yasha mable, Maama na biye da ita, fitilun da ke jikin bangon stairs din da kuma na sama suka ja hankalin Maama, ai kam baifi saura stairs shida ba bayan Maimuna ta kai ƙasa ji kake timm Maama ta faɗo, goshinta ya daki tsinin tiles na ƙarshen stairs din, a take jini ya ɓalle, hankalin Jama'ar dake palour suna gabatar da kayan lefe yayo kanta, a gigice ta miƙe ta saka duƙunƙunannen hijab dinta ta dafe goshin, Mama Mardiyya tace "ya salam, taji ciwo ko?", Aysha da ta fito daga guest room da ƙaramar kit ta jewelry na lefe tace "taji ciwo, ga stain din jini a floor", Anty ta taɓe baki ta kawar da kai, kowa na palourn saida yayi mata sannu banda Anty da wasila, Maama ta kyallaro idonta ɗaya wanda yake a buɗe tana kallon akwatunan da suke baje a tsakiyar hamshaƙin palourn, Anty Zulaiha tace "ya kamata a kaita Hospital, naga kamar she's bleeding, Noor yi ma driver magana", Noor da takewa Maama kallon wata psycho tace "ohk" ta tashi ta fita. Mama Mardiyya tace "ga lefen yarinya", Maama ta zaro ido jin an ambaci kalmar lefe, chab wnn ne lefe sai kace na budurwa uku, ya linka wanda aka kawo mata na Nura, Maimuna da ta tsaya gulma ta hura hanci tace "Maama ni kam na tafi sai kiyi ta tsayuwa", Maama bata san lokacin da ta ɓarke da kuka ba, hannunta dafe da goshinta ido ɗaya a rufe ta wuce Maimuna ta fita, Maimuna tabi bayanta da sauri, Mama Mardiyya da daman bata taking shit tace "who is that woman?", Anty tace "kishiyar Babar Hajar ce", Mama Mardiyya tace "Allah ya kyauta, sai kace mai junnu..", Noor ta shigo tace "Ammi (Anty Zulaiha) na gaya masa yace ta fito", Anty Zulaiha tace "ai sun tafi ma..", Noor ta tsaya kusa da Aysha da Khausar tace "mu tafi wajen Amarya..". suka wuce upstairs. bayan su Anty sun gama ganin lefe Mama Mardiyya tace "Alhmdllh, mu dai fatan mu Allah ya basu zaman lafiya", Anty tace "Ameen". da haka suka miƙe domin tafiya don basa son sukay magrib, a lokacin ne kam suka hau sama domin suga fuskar amarya, tinda su Noor suka shigo suka bude mata fuska, Hajar tayi sauri zata rufe fuska ganin su Ummi na shigowa, Anty Zulaiha tayi murmushi tace "ƴar fillo", Mama Mardiyya tace "to ai shknn wataran ma gani" da haka suka fice daga ɗakin. Anty ta keɓe ta sanar da Umma abinda ya faru a waya, ta tambayeta ya za ai da lefen, Umma tace a barsu anan kar a taho dasu. Anty ta shiga wajen Hajar domin mata sallama, Hajar ta riƙe mayafinta ta ringa kuka kamar zata shiɗe, da kyar Anty ta rarrasheta ta samu tayi shiru, Hafsa tayi mata sallama da cewar gobe zata dawo, kowa ya tafi aka bar su Noor da ita, Sakeena ma tabi su Ummi.
★Through out the day Nurain na room ɗinsa, bacci ma yayi abunsa, lokacin sallah ne kawai yake fito dashi, yana dawowa daga sallar magrib ya tarar da su sun dawo kenan, wajen motocin ya dosa yana musu barka da zuwa, suka ringa sa masa albarka tare da fatan Allah ya bada zaman lfy, shi dai baice komai ba saidai ya shafa kai. bayan sun shiga ciki Sakeena tace "So.. ashe kai a angonce ka dawo 9ja, Abba ya kyauta", ya zura hannayensa a pocket yana kallonta da kyau yace "And shknn.. nima na huta da surutun ku, that bla bla bla Nurain kayi aure you're not getting younger..", tace "Sure kuma fa ka huta, am telling you wllh tafi Ruqayyah kyau nesa ba kusa ba, she's beautiful and young bana jin ma ta kai sa'ar Noory", ya ja pointed nose ɗinsa yace "really.. toh yayi kyau", tace "brother harna tausaya maka wllh zaka sha shagwaɓa don shagwaɓaɓɓiya ce, tin fa da aka kawota take kuka har muka taho bata dena ba, ya kamata ka tafi da wuri kaje kayi aikin rarrashi kar ƴar mutane ta haɗiyi zuciya..", yayi ajiyar zuciya yace "wai ke baki san ba auren soyayya bane wnn", tayi hitting ɗinsa lightly tace "that doesn't change the fact that she's your wife, arranged marriage ko kuma auren soyayya ai duk ɗaya ne tinda dai an zama miji da mata, and kar kayi using that bullshit think of you kayi maltreating yarinya..", ya zaro ido yayi pointing kansa yace "Nah?", tace "Yess you", yace "ai kinsan ba halina bane", tace "yeah, i know brother, naji kana wani zance ne daga nace kayi consoling yarinya..", murmushi yayi yace "uhmm ai ba sai kin koya min yadda zan kula da baby wife dina ba", wucewarta tayi ta barsa a wajen tana cewa "shine ka tsaya kana ɓatan lokaci.." ta shiga ciki. ƙarfe takwas da rabi na dare Nurain na tsaye gaban Mirror, buttoning rigar dake jikinsa yake, dakakkiyar shadda ce mai tsadar gaske, sabuwa fil wacca ya ɗinka a lokacin bikinsa da Ruqayyah kuma ya tanade ta ne sbd shiga gidansa na farko wajen matarsa, ashe dai ba Ruqayyah bace, wata ce daban, sai a yanxu ma ya fara tambayar kansa shin ya wacca aka aura masa take, yana gama buttoning ya kafa hula samar cikakkiyar baƙar sumarsa, ya fito a well dressed gentleman, wata ƙaramar trolley da ya haɗa few belongings nasa ya ja ya fito daga room ɗin nasa, ya rufe ya saka key din a pocket, down stairs ya sauka yana zuba ƙamshi, Farooq da ke zaune main palour yana latsa wayarsa ya ɗaga kai ya dubesa, Nurain ya ajiye trolleyn ya wuce part din Mami sukay sallama, tare suka fito da Sakeena, ya shiga part din Abba ita kuma ta ƙarasa wajen Farooq, ta miƙa masa key din motarta tace "plxx brother ka taho min da car na tana can gidan..", yace "what about mine?", tace "ai yanxu a ta Nurain zaku tafi, idan ku ka je sai ka taho da tawa ka bar masa tasa, idan ka dawo saika dauki taka", yace "Ohk, you wet my work fa, banyi niyyar dawowa ba..", tace "sorry, ai daman ma saika dawo tinda zaka ɗakko su Noory..", ya amshi key ɗin ya zura a pocket. Nurain yay sallama da Abbansa snn yace "amm naga alert daga wajenka, what about the money?", Abba yace "ka yi amfani dasu ko wajen siyan foodstuffs ne", Nurain yace "ngd Allah ya saka da alkhairy" da haka ya bar room din, yana fita main palour Farooq ya miƙe yace "let's go..", Nurain ya tsaya yana kallonsa yace "muje zuwa ina?..", Farooq yace "zuwa gidanka mna, amarya na jira", trolleyn kayansa ya ɗauka ya fita compound, parking space ya dosa ya buɗe black ride dinsa, ya bude back seat ya ajiye trolleyn snn ya shiga driver seat, Farooq ya shiga front seat yana cewa "wai rakiyar ce baka so?", direct yace "yap" ya kunna motar yana warming, Farooq yace "i guess right, Mami ce tace nazo ai, you know I can't say no to her", Nurain yace "that's right..", ya fita daga parking lot din da reverse snn ya juya suka bar gidan. A wani babban supermarket yayi parking, yace "zanyi shopping, do you mind going in?", Farooq yace "nope saika fito", Nurain bai kashe motar ba ya barta a kunne sbd AC tinda Farooq na ciki, wajen shopping din ya shiga, after 20min ya gama, shopping yayi sosai da kudin da Abba yay masa transfer kuma a hakan ma ko quarter bai taɓa ba, saida back seat ya cika da ledoji, bayan ya gama ya shiga mota suka bar harabar supermarket din, Nurain yace "i never thought arranged marriage za a min, my wish is to marry someone that I love and she loves me too...", Farooq yace "Allah planned the best for us, wish kuma wani abu ne na rayuwa wasu nasu fulfill wasu kuma unfulfill, in your case ba zamu ce naka unfulfill bane cause you have another three chances", Nurain yace "kuma ba nida niyyar auren mace sama da ɗaya", Farooq yace "Ohk, saika ajiye niyyar kayi fulfilling wish dinka", Nurain yayi ajiyar zuciya baice komai ba, ganin sun wuce wani wajen suya da gashin kaji Farooq yace "kayi mantuwa fa punk", Nurain na murza steering his eye fixed on the road yace "mantuwar me?", Farooq yace "baka siyi roasted chicken ba", yayi slowing down yace "damn it, yanxu kuma naga mun wuce suya..", Farooq yace "sai ka koma ka siyo..", Allah yaso ba suyi nisa sosai ba tinda yau baya gudu, da reverse ya koma wajen Suyar, Kaji guda uku da tsinken tsire shida akay masa wrapping, ya biya bill ya bude back seat ya ajiye, saida suka hau saman titi yace "Allah bashi ka ɗauka dude, wai kana ganin inata wahala bazaka temaka ba ko..", Farooq yayi wani murmushi mai sauti yace "hmmm, toh ai naga kamar u don't need a help, rakiyar ma baka so ba..", Nurain yayi ajiyar zuciya baice komai ba, After 15mins yay parking a gaban gidansa da fitilunsa suka ƙara hasken layin, ya miƙawa Farooq muƙulli yace "buɗe gate", ya amsa ya fita daga motar ya buɗe gidan snn ya shiga ya zuge gate ɗin that's soft in sliding, Nurain ya shigar da motar ciki yay parking. Farooq ya rufe gate en snn ya ƙarasa ciki. Ta jikin window Aysha taga shigowarsu ta dubi su Noor tace "Yaya ya ƙaraso, tare suke da ya Farooq", wani irin nervousness ne ya lulluɓe Hajar, shin da wane irin mutum za tay tozali matsayin mijinta, Khausar tace "gashi can suna knocking", da sauri Aysha ta fita ta sauka ƙasa ta buɗe ƙofa, Farooq yace "ina sauran suke, fetch them now karku ɓata min lokaci", tace "tom", da sauri ta haura sama ta sanar dasu Noor, ai kam da sauri suka haɗa kayansu sbd sun san halin Farooq, yanxu sai ransu ya ɓaci, sukay wa Hajar sallama suka fita, a hankali ta gyara zamanta a gefen gado, ta janyo mayafinta ta ɗora a kai har yana rufe mata goshi, wani irin feeling take ji, zuciyarta na lugude. suna sauka down Farooq da ya shigo da ledoji a hannunsa yace "ku jirani a waje", ba musu sum sum suka fita, Nurain ne ya shiga da ledojin ƙarshe wanda sune na kaji ya ajiye a palour, Farooq ya miƙa masa hannu yace "toh brother, wish you Happy marriage life..", sukay shaking hands Nurain yace "thank you", compound suka fita tare, Farooq ya shiga driver seat na motar Sakeena, Noor a front seat Khausar da Aysha suka shiga back seat. saida suka fita daga gidan snn Nurain ya rufe gate da padlock, ya duba ko ina a compound din yaga dai ba matsala snn ya shiga ciki, ya sakawa ƙofar lock yana sauke ajiyar zuciya, trolleyn kayansa ya ɗauka ya haura sama, ya kalli doors ɗin ɗakunan yana jin wani irin feeling, definitely his wedded wife tana ɗaya daga ciki. part dinsa ya wuce ya ciro key ya buɗe ya shiga, ya lalubi bango ya danna switch, a take haske ya gauraye makaken palourn nasa, kai palourn nan fa ya naɗi pulus, ya wuce master bedroom wanda yafi ko wane ɗaki girma a gidan, tsabar girman dakin daga can nesa zaka hango makeken bed din ɗakin, ya ajiye trolleyn a kusa da closet ya juya ya fita daga part din, a long corridor dake ɗauke da three bedrooms din ya tsaya, ya saki ajiyar zuciya mai karfi kafin ya buɗe room na farko, da sallama ya shiga ya tarar ba anan aka ajiye masa matarsa ba, room na biyu ma haka, yana taɓa door handle na room na uku yaji iced shock, ya murɗa handle din gami ta tura ƙofar ya shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe a hankali yace "Assalamu alaikum...", da cracking voice wacca ta dashe ta amsa ciki ciki, ta sunkuyar da kanta tana kallon slim fingers ɗinta da take wasa dasu, his piercing eyes landed on her slim fingers da suka ji zanen ƙunshi, a hankali ta ajiye numfashi ta lumshe idonta perceiving his pure men scent da rairayin sanyin Ac ya kwaso, takowa ya farayi towards her, yayinda ita kuma taji tamkar an ɗago fuskarta, idonta ya faɗa cikin nasa, ya dakata da tafiyar yana kallon innocent face ɗinta wacca tasa brain ɗinsa ta amsa, sosai idanunsu suka sarƙe, he automatically get froze bayan ya gane wnn fuskar, tamkar robot da aka kunna da remote control haka ta miƙe zumbur, ta zaro lulu eyes ɗinta waje, mayafinta ya zamo daga kanta zuwa shoulders ɗinta kafin ya zame ƙasa gaba ɗaya, ta kurma wani uban ihu kafin ta sulale ƙasa tabi mayafinta.....✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh _feeche
{36..}
At first tsayawa yayi yana kallonta kafin ya ƙara one step, tsananin shock da abinda bata fatan haka ne yasa ta sulale ƙasa, Hajar ta yayibi mayafinta ta miƙe nan ma sai kace robot, ta lulluɓe jikinta gami da kallon mutumin front dinta wanda shima yake analysis me ya kawo wnn yarinyar nan, Hajar da take shivering as a result of shock din da tayi ta nunasa da yatsa tace "me kake yi anan?", da wani irin expression yake kallonta cause he will never accept what his mind is thinking, ta zuba masa lulu eyes ɗinta kawai amsa take jira ya bata, After few seconds of silence ta sake cewa "nace me kake yi anan...", da stern voice yace "that question goes to you young lady, what are you doing in my house...?", shivering da jikinta yake har saida ya ratsa zuwa lips dinta snn yayi birki a muryarta tace "your house..?" kafin ta sake sulalewa ƙasa a karo na biyu, maimakon ƙara da ta fasa wancan karon yanxu kuma saita rushe da kuka, what wnn mutumin da ta ƙi jini, mutumin da bai san darajar ɗan Adam ba, ko 10sec bai ƙara a tsaye ba ya juya ya bar ɗakin, gaba ɗaya brain ɗinsa ta kulle, he can't think otherwise, downstairs ya sauka ya nufi main door, har ya fara murza key sai kuma ya kalli agogon wrist ensa wanda yake nuni da sha ɗaya na dare saura few minutes, fasa buɗe ƙofar yayi ya koma ya zauna akan ɗaya daga cikin exclusive sofa dake palourn, yayi resting jikin kujerar gami da lumshe ido, bayan minti goma ya buɗe idonsa, ya ciro wayarsa daga pocket snn ya tashi ya koma upstairs, part dinsa ya shiga ya zauna a palour, kunna wayar yayi ya fara ƙoƙarin dialing numbern Abbansa, kiran ko shiga beyi ba saiga kiran wacca ta takura masa nan yana shigowa, ya tsaya yana jiran kiran ya katse, yana katsewa wani ya sake shigowa, sau biyar yana attempting kiran Abba amma kiranta ya hana nasa shiga, shi kam bashi da lokacin blocking numberta cause she didn't worth it, idan ma yayi blocking layinta ai ta samu matsayi, daga dawowarsa jiya zuwa yau gaba ɗaya ta hanasa operating wayarsa lfy, daga text messages sai uban kira, fasa kiran Abban yayi ya ajiye wayar gefe guda, yana jin sai vibrating take, yayi ajiyar zuciya ya cire hular kansa ya ajiye kan huge center table dake palourn, shafa cikakkiyar sumarsa yayi yana nazarin demon din dake gabansa. The girl... ya tuna encounter dinsa da ita.. na farko lokacin da ta shafa masa cakwalkwali, cike da tsiwa take magana "malam ba kaga abinda kayi bane??, oh shi bakuga rashin kirkinsa da ya feshe ni da kwatami ba, banga zan iya hakura ba gaskiya". na biyu lokacin da ya kusan bige wani yaro da mota... "malam wai baka san darajar rai bane iyeee?, ya za ai ka kusan bige yaro amma ka wani hakimce a mota bazaka fito ka dubasa ba, ke kinga mutumin nan fa ko a jikinsa, idan da ace ya bige yaron nan fa sai yadda Allah yayi, to Allah ya isan sa kuma a ringa sanin darajar ɗan Adam". encounter na uku... "Fake doctor, i think the name fit you, wanda baisan darajan ɗan Adam ba bazai zama real doctor ba saidai Fake", sai kuma na ƙarshe... "mu bawa juna haƙuri daii". not her gaskiya, da dai ace wata ce daban da zai haqura yayi accepting marriage din nan amma wnn yarinyar mara ta ido, bama ta ido ba bata da manners. tunani kawai yake yana nemawa kansa solution, idan ya saƙa wancan sai ya kwance wancan, after 40mins dai ya samu solution ɗaya, ya tashi ya shiga huge bedroom nasa ya wuce bathroom, alwala yay ya fito yana jan hannun rigarsa da ya tattare, nafila ya shiga jerowa, nap na few hours ya samu kafin sallar asuba, ya sake wata alwala yay sallah, ƙarfe shida da minti hamsin na safe ya fito hannunsa riƙe da car key, ko kallon ƙofar room din da take beyi ba ya gangara downstairs, ya dubi ledojin da ke palourn wanda bai sake bi takansu ba, compound ya fita bayan ya rufe main door din da key, ya wuce wajen motarsa ya bude ya shiga ya kunnata, a kunne ya bar motar tana warming ya fito ya nufi gate ya bude, dawowa yayi ya shiga motar snn ya fito daga gidan, ya sauka ya