Showing 63001 words to 66000 words out of 114314 words
Chapter 22 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
ya samu lambar. Daga ta cikin gida kam gidan biki ya ɗau harami, Umma sai warkajaminta take cikin riga da zani na atamfa mai shegen kyau, ta kashe ɗaurinta ture kaga tsiya, Hajar kam tana ɗakin Baba tare da ƙawayenta, kai kana kallonta kasan itace Amarya, tayi kyau harta gaji, abinda yafi birgeni da kwalliyarta shine yadda tayi maintaining natural beautyn ta, ba wata make-up da akay mata, Hafsa ce ta gyara mata fuska, powder mai tsane gumi kawai ta shafa mata sai zizaren kwalli da kuma colourless lip gloss wanda yasa pink lips ɗinta shining matuƙa, sassanyar kyau tayi kam ba ƙarya, ko nanda shekara ashirin ba a kalli hoton bikinta ayi dariya ba, dan wnn make-up ɗin ta zamani canja kamanni take ainun. Zainab ta kalli agogon wayarta tace "uhmm yaci ace an ɗaura fa, Hajar ta kusa zama matar ya sayyadi Nura", murmushi Hajar tayi tana jin wani daɗi har cikin ranta, hannunta da yaji zanen ƙunshi ta saka ta janyo wayarta, mesaage din da ya turo mata yau da safe ta binciko, ta karanta fuskarta ƙunshe da murmushi sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana juya lulu eyes ɗinta da yayi wani fari sol tamkar madara sbd kwallin da aka zizara masa, Hafsa tace "ko na zubo mana abinci ne?", Zainab tace "Eh kam gwara muci yanxu don nasan bayan ɗaurin aure sha'anin yini zamu shiga", Hafsa ta fita tsakar gida ta fara neman Anty tinda itace incharge of abinci, a ɗakin Umma ta sameta tana zuba tuwo sinasir wainar shinkafa da gurasa a mabanbantan warmers, Hafsa tace "Anty zan zuba mana abinci", Anty tace "tom ga plates can, idan kin gama zuba muku ki fita ki kiramin Mu'azzam ko Abdallah su fitar da na ƴan daurin aure gashi nan na fitar musu da nasu", Hafsa tace "tom", ta dauki plate ta zuba musu waina da sinasir, wani plate ɗin ta ɗauka ta zuba miyar taushe da isasshen tantakwashi, saida ta kai abincin ɗakin da suke snn ta fito ta doshi soro, leƙawa tayi waiko zata hango Mu'azzam amma bata ganshi ba, juyawa tayi kawai zata koma gida sai kuma ta tsaya tana sauraron wasu maganganu, cikin gida ta koma ta tarar da Anty ta fito tsakar gida, wajenta ta isa ta rage murya tace "Anty, kinji wai har yanxu dangin Angon basu zo ba", Anty tace "kamarya basu zo ba ai na ɗauka ma an gama ɗaura aure shiyasa nace ki fita kira Mu'azzam", Hafsa tace "A'a wllh ba a ɗaura ba", Anty tace "ikon Allah ko mene ya makarar dasu". Hafsa tace "bari naje muci abinci" da haka ta shige wajensu Hajar. wata shegiyar dariya Maama ta ɓarke da ita ta miƙawa Balaraba hannu suka kashe, Maama tace "ga dukkan alamu aiki yayi kyau, kinga har yanzu mirsisi banji maroƙi ya ambaci cewa an ɗaura aure ba", Balaraba tace "hmm ke dai bari, yanxu kawai tashi mu fita tsakar gida yadda zamu sha kallo muga ƴan bori", Maama ta tuntsure da dariya zuciyarta wasai tace "wllh kam ƴan bori, dan wllh tllh idan aka fasa auren nan tsaf faɗima za tayi bori", su Nabilah dai kawai binsu suke da kallo don basu rafko jirgin ba, miƙewa Maama tayi ta fita tsakar gida Balaraba biye da ita, kawai kallon Umma take tana yamutsa fuska cike da tsantsar tsana. A hankali yake shigowa cikin lungun yana ratsa mutane da suke basa hanya da kansu sbd shigarsa ta kamala, hehehe akace kuɗi ƙumbar susa, yana zuwa ƙofar gidan nan ma aka bashi hanya, ido huɗu sukay da Baba da ya kafe ƙofa da ido yana fatan dangin ango su shigo, Baba ya goge fuskarsa da handkerchief ya miƙe tsaye yace "Muktar, barka da isowa", Alhj Muktar yace "Amma Adam jiya fa muka haɗu da kai amma baka sanar min da abin arziƙin nan ba", Baba dai baice komai ba sbd hankalinsa baya jikinsa, Alhj Muktar ya gaggaisa da mutanen soron snn ya samu waje ya zauna.
★Wata zufa ce mai shegen yawa take tsattsafowa Nura, tamkar ƙaramin yaro haka yayi dafa'an gaban Hajiyarsa, fuskarta a murtuke tamkar baƙin hadari, Nura da zuciyarsa ke wani irin tafarfasa gami da dagargajewa yace "dan girman Allah Hajiyarmu kar ki min haka, kiyi haƙuri dan Allah", Hajiya dake zaune bisa kujera ta wani harɗe ƙafa tace "Nuraddeen", yace "na'am Hajiyarmu", with seriousness in her tone tace "matuƙar ni na kawoka duniya, matuƙar ni na ɗauki cikinka na wata tara, matuƙar ni na shayar da kai, matuƙar ni na raineka, matuƙar ina da daraja da kima a idonka to nace bana son auren nan, nace a fasa yin sa bazaka auri yarinyar ba", wata gudumar tashin hankali ce ta doka a kwanyarsa, kansa ya ɗau zafin da ya saka jinin jikinsa tafarfasa wanda ya linka tsiyayar gumi a sassan jikinsa, tamkar wanda aka sharawa ruwa haka gumi ya jiƙasa, farar Sabuwa shaddar jikinsa mai kyalli ta jiƙe sharkaf, idonsa da ya rine yayi jajur ya ɗago yace "Hajiyata, karki min haka dan Allah, me yasa.....", tsawa ta daka masa tace "tambayata kake Nuraddeen, akan wata zaka zo ka titsiyeni kana min tambaya sai kace sa'arka, wllh tllh indai baka tashi daga gabana ba yanzun nan saina tsine maka, kaji mu da mara kunyar yaro, daman an haifi wata yarinya a duniyar nan da zaka zauna a gabana ina fada kana fada akanta, to wllh kar a kuskura a ɗaura auren nan na gaya maka", shi dai kawai kallonta yake sbd canzawar da tayi, kamar ba Hajiyarsa ba, wacca bata masa tsawa, wacca kullum cikin saka masa albarka take, sai kace wacca aljanu suka shafa, sai ranar ɗaurin aure za tace a fasa, to me yake faruwa ne, kamar ba ita bace ta daɗe tana jiran wnn rana, guiwa a sace ya miƙe ya fita daga palourn nata, Babban palourn gidan ya shiga inda Uncles da kuma Aunties ɗinsa ke jiransa, tin ɗazu da Hajiya ta tubure aka kasa shawo kanta shine yace zaije da kansa ya bata haƙuri, shimfiɗar fuskarsa ma kaɗai amsa ce, kallonsa suka ringa yi kafin Uncle ɗinsa Saminu yace "ta haƙura Nuraddeen", Nura ya haɗiyi wani yawu wanda ya gagara wuce maƙogoronsa yace "A'a, tace tsine min za tayi", baki buɗe Saminu yace "A haba dai, ina zuwa", ya miƙe ya shiga palourn Hajiyar, haj Yahanasu ƙanwar Hajiya ta miƙe itama ta shiga palourn Hajiyar, Nura da kansa ke juya masa ya koma da baya ya tsaya a bakin palourn, duk abinda suke cewa yana ji a inda yake tsaye daga bakin ƙofa, Hajiya har ƙwarewa tayi tana kumfar bala'i ita Nura ba zaiyi aure ba, haj Yahanasu ta sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya tace "Haba dan Allah yaya ki yiwa yaron nan adalci mana, mene dalilinki da zaki ce ba zai yi aure ba?, ki dubi Allah kuma kiji tsoronsa karki ɗauki haƙƙin yaron nan dan kina matsayin mahaifiyarsa", Hajiya tace "dakata Yahanasu karki min wata maganar banza a nan, cewa nayi kar yayi aure, ni ban hana Nuraddeen aure ba, abinda nace shine ba zai auri yarinyar can ba", haj Yahanasu tace "Yaya karki datse soyayyar dake tsakanin yaran nan dan girman Allah...", a matukar hasale Hajiya tace "Yahanasu karki kaini bango, dan wllh tllh zan iya zazzabga miki marii, kuma zan tsinewa Nuraddeen Albarka", sai a yanxu Saminu ya tanka yace "Hajiya ayi haƙuri, Nura fa ba yaro bane, tinda har yace aure zaiyi to ayi masa...", hannu Hajiya ta ɗaga masa tana karkaɗa ƙafa tace "wai ku me yasa baku da hankali ne, nifa ban hana Nuraddeen aure ba, amma tinda har kun ɗauki haramar fassarani baibai, bari na kashe bakin tsanya, ka aura masa ƴar wajenka Maryam yanzun nan, ai yarinyar na sonsa shine ya ƙi yace wai ƴar gidan gini yake so, ai aure dai aure ne ko wane iri ne, na yarda a aura masa Maryam a maimakon ƴar gidan gini", Nura ya jinginar da kansa a bango ya lumshe idanunsa da suke masa zugi, a zuciyarsa ya furta "innalillah wa'inna ilayhirraji'un", wai shine zai rasa Hajar ɗinsa, wnn wace irin mummunar ƙaddara ce, shekara sama da goma ya rayu da soyayyar Hajar ɗinsa, tin tana ƴar yarinya yake sonta har lokacin da ta mallaki hankalinta ta gane kuma Allah ya haɗa zuciyoyinsu, ya sake furta kalmar "innalillah wa'inna ilayhirraji'un" a fili. Saminu ya shafa tsigaggen gemunsa yace "anyi haka kuwa Hajiya, karfa ayi abinda zai ɓata zumunci", Hajiya tace "wnn abu ai saidai ya gyara zumunci Saminu, idan ka amince ka bayar da Maryam magana ta ƙare, na gaya maka Maryam tana sonsa, tin tini nasan da hakan har maganarta nayi masa kwanaki", Saminu ya sauke ajiyar zuciya don sosai ya aminta da hakan, barin ma da yaga Nura ya fara tara abin duniya. cikin mintinan da basu wuce ashirin ba aka ɗaura auren Nura da Maryam a babban palourn gidan, Nura da already ya fara ganin baƙi baƙi ya tashi yana haɗa hanya ya shige ɗakinsa. daga nan kuma wani ƙanin Hajiya ya bada shawarar cewa aje gidansu Hajar a sanar musu cewa an fasa auren, su uku ne suka shirya suka nufi gidan. wajen da aka bubbuɗa musu a soron suka zauna, wani sanyi Baba yaji a zuciyarsa, Bappa kam kallonsu yake ganin hannunsu siƙam babu goron ɗaurin aure, ƙanin Hajiya wanda shine Babba a cikinsu ya fara koro bayani, rufa rufa yayi ya musu bayani mai cike da nutsuwa ta hanyar da bai bayyana ainahin abinda ya faru ba, sarawa kan Baba yayi ya miƙe yace "ku dai ba mutanen kwarai bane wllh, baku san darajar alƙawari ba, kunsan baku shirya aurar da dan naku ba kuka nemi da a basa auren yarinya....", sarƙewa maganar tayi ya fara tari, da sauri Naseer ya miƙe ya riƙosa yana ƙoƙarin zaunar dashi, Bappa ya gyaɗa kai cike da takaici yace "Allah ubangijj ya musanya mata da wanda yafi ɗan ku Alkhairy a gareta, muma mun fasa aura muku ƴar mu", Saminu yace "Ayi haƙuri, dan Allah idan an nutsu kuje ku kwashe kayanku da ku ka zuba a gidan yaron mu, muma wanda muka kawo muku ku dawo mana da abin mu, ai da sulhu muka zo", Bappa yace "karku damu za a dawo muku da komai tsinke ba za a bari ba". Saminu yace "Allah ya haɗa kowa da rabonsa", da haka suka bar soron, ƴan ɗaurin aure suka fara tashi da nufin tafiya, wasu na jajantawa yayinda wasu suka samu abin gulma, tamkar saukar wahayi daga sama haka soron ya amsa ƙuwwa da kalmomi shida da suka fita daga bakinsa "ina nemawa ɗana auren wnn yarinya", Bappa ya dubi Alhj Muktar da yayi wnn furuci, Baba ma da yake cikin tashin hankali ya dubesa, mutanen da suka fara tashi da sauri suka koma suka zauna, Alhj Muktar ya miƙe ya isa gaban Baba yace "Adam ina nemawa ɗana auren ƴar wajenka da aka fasa aura yanxu", wani ɗaci ne ya kauraye bakin Baba wanda yake jin tamkar an musanya masa miyau da ruwan maɗaci, expression ɗin fuskarsa bazai misaltu ba, kasa cewa komai yayi, Bappa ya girgiza kai yace "A'a, ba zan iya aura mata wanda bansan koshi waye ba, ban san komai a kansa da ya kamata na sani kafin aure ba...", Alhj Muktar yace "nine mahaifinsa, amma nasan bana daga cikin jerin mutanen da za a tambaya shaida a kansa, koda ba za a tambayeni ba amma zan faɗa cewa ɗana nagartacce ne, halayensa masu kyau ne saidai kuma ko wane ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, a matsayina na uba kuma mahaifi wanda bazan so abinda zai cutar da ƴaƴana ba toh haka zalika bazan cutar da ƴaƴan wasu ba, ba nida wata manufa na nemawa ɗana auren wnn yarinya face manufar alkhairy". Bappa ya sake girgiza kai, Naseer ma dai girgiza kan yayi kuma har cikin ransa bai aminta ba, Baba ya dubi fuskar aminin nasa Alhj Muktar snn ya dubi ta ƙaninsa Bappa, ajiyar zuciya yayi yace "Muktar na amince maka, Bappa a ɗaurawa Hajara aure da ɗan gidan Muktar".........✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{32..}
Bappa ya ringa kallon Baba kafin yace "kace na daurawa Hajara aure da yaron da ba musan waye shiba?", Alhj Muktar yayi murmushin manya yace "naji daɗin wnn furuci naka, tabbas kanada gsky sosai, nima hkan zanyi idan na samu kaina a matsayinka na yanzu, kuma nima na taɓa shiga irin wnn yanayin da Adam ya shiga yanzu, na sake faɗa cewa ɗana nagartacce ne, amma idan zuciyarka ba ta aminta ba shknn ba damuwa", Baba ya dubi Bappa yace "A ɗaura mata aure da ɗan gidan Muktar, ba nida shakku ko kaɗan a kalamansa, na yarda dashi...", Bappa yayi ajiyar zuciya yace "tom, Allah ubangiji ya tabbatar da Alkairi" sai kuma ya dubi Alhj Muktar yace "fatan dai akwai sadaki a kusa", Alhj Muktar da walwala ta bayyana ƙarara a fuskarsa yace "akwai, bani minti uku", wayarsa ya ciro daga aljihu ya kira drivernsa, da sauri driver ya ɗauka, Alhj Muktar ya umarcesa da ya ɗakko masa kuɗi a mota, bayan minti bakwai driver ya bayyana a soron, ya durƙusa gaban Boss dinsa ya ciro wasu maƙudan kuɗi daga pocket ya ajiye, Alhj Muktar yace "zauna ka zama shaida", ba musu ya zauna ya tankwashe ƙafa, Alhj Muktar ya ɗauki uwar kuɗin ya ajiye gaban Bappa, Bappa ya dubi kuɗin ya girgiza kai yace "wnn kuɗin sunyi yawa", Alhj Muktar yace "ba suyi yawa ba, sadaki ai baya yawa saidai yayi kaɗan", ( Ehennnn a zamanin nan sai kaji mutane suna cewa wai ba a tsawwala sadaki ai ba siyar da yarinya za ai ba, to ga point of correction ba wani siyar da yarinya, shi fa sadakin aure baya yawa a musulunce, matuƙar kanada ikon bawa matarka zunzurutun dukiya mai yawa matsayin sadaki toh ba matsala, tauye sa shine matsala, wllh idan ma kanada arziƙin raba kano gida biyu ka bata rabi matsayin sadaki hakan daidai ne). An ɗaura auren Hajar da ɗan gidan Alhj Muktar bisa sadaki mai tsoka, ɗaurin auren ya samu shaidu masu yawa, Baba ya lumshe idonsa ya furta "alhmdllh", maroƙi ya ɗaga murya yana sanar da jama'a cewa ɗaurin aure ya kammala, muryarsa har cikin gida ta ratsa, wani mugun bugu zuciyar Maama tayi jin muryar maroƙi ta daki dodon kunnenta, ta juya ta kalli Balaraba da ta hangame baki har ƙuda na ƙoƙarin afkawa ciki, Wasila ta ɗaga zureren hancinta sama ta rangaɗa guɗa, murmushi mai kyau Umma tayi. Maama da idonta ya kisfe tsabar takaici tace "wllh sai malamin nan ya biya ni kuɗi na, kadan ba sai ya biya ba", Balaraba tace "abin fa da mamaki, tinda nake dashi bai taɓamin aiki baici ba, wllh a tarihin aikinsa ma baya faɗuwa, gaskiya akai abinda ya faru Rabii", Maama tace "Eh ai kam ga aiki nan na gani", Balaraba ta dafe kai tace "Rabii akwai lauje cikin naɗi, mu tsaya dai muyi kallo". Mu'azzam ne da Huzaifa suka ringa firfita da abinci, walima aka baje a soro ana kwasar dabge. Alhj Muktar da Baba suka fita daga soron zuwa can inda babu taron jama'a, godiya Alhj Muktar ya ringa yiwa Baba, shima Baban godiya yake masa domin kwa ya fitar dashi kunya, Alhj Muktar yace "insha Allah da yamma zasu zo", Baba yace "bana ganin ɗaukar yarinyar nan zai yiwu a yau, a bari zuwa gobe, kaga dai yadda lamarin ya jirkita, shima yaro ai sai an sanar dashi...", Alhj Muktar yace "toh ba damuwa da yau da gobe ai duk ɗaya ne, karka damu yaro a shirye yake", Baba yace "nagode fa, kaxo domin mu gana sai kuma wnn batu ya gifta bamu samu lokacin ganawarba", Alhj Muktar yace "daman nazo ne domin naga inda kake Adam", Baba yace "Allah sarki", Alhj Muktar ya miƙa masa hannu sukay sallama snn ya tafi. saida rurumar ƴar ɗaurin aure ta tsagaita snn Baba ya samu shiga gidan nasa, nan fa akay masa caa da gaisuwa da kuma fatan alkhairy, da sakakkiyar fuska ya ringa amsawa yana neman Umma da idanu, daga ɗakinta ta fito fuskarta ƙunshe da walwala, Baba ya dubeta yace "ɗakinsu Nasiru a buɗe yake?", tace "bari na duba", ta wuce ƙofar ɗakin ta tura taga a buɗe take, tace "Eh a buɗe take", ya ƙarasa ƙofar ɗakin yace "ina son ganinki" ya shiga ciki. afujajan Maama ta fito daga ɗakinta jin muryar Baba, wuwwurga idanu ta fara yi duk ta jiƙe da gumi, hangosa tayi lokacin da ya shiga ɗakinsu Huzaifa, da sauri ta wuce har tana ƙoƙarin bangaje Umma ta shiga ɗakin, kallonta Baba da yake shirin zama yayi, Umma dai ta shigo ta samu waje ta zauna, daga tsaye Maama tace "tin safe ka hana mu kudin abinci a gidan nan mal", yace "kuɗin abinci kuma Rabii?, ga abinci nan ku zuba kuci", tace "a ina yake abincin?, ni bangani ba", ya ciro 1k daga aljihun gaban rigarsa ya miƙa mata yace "gashi", amshewa tayi tace "yo da an barni da yunwa nida ƴaƴana", ta juya zata fita sai kuma ta dubi Umma tana yamutsa fuska, dawowa tayi ta zauna ta wani sha kunu, Baba yace "ba na baki kuɗin abincin ba", gefe ta kalla tace "Eh anan zan zauna", Baba yayi ajiyar zuciya baice komai ba, shiru ɗakin ya ɗauka babu wanda ya sake magana, bayan wani lokaci Umma tace "mal ko na tafi ne akwai baƙi da suke jirana", Baba ya girgiza kai yana kallonta yace "Faɗima", tace "na'am". kaf ya wassafa mata abinda ya faru akan auren ƴarta. wata katafariyar shewa Maama ta daka, ta miƙe da sauri ta fice tana gyara haɓar zaninta, saida ta shiga tsakiyar ƴan biki tace "ahayye riiiiiii, an yanka ta tashi, kowa ya baje an gama biki", ta afka ɗakinta domin ta sheƙawa Balaraba nasarar da suka samu, murna suka shiga ɓarkawa a ɗaki tamkar waɗanda akay wa bushara da gidan aljanna, sosai suka saki baki suna zance sbd su Nabilah sun fice daga gidan. Umma ta tuge ture kaga tsiyar kanta ta share zufar da ta tsattsafo mata tace "innalillah wa'inna ilayhirraji'un, mal dama baka