Showing 45001 words to 48000 words out of 114314 words
Chapter 16 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
kayanta tass, komai da komai ta haɗa, a ƙasan zuciyarta kam wani irin daɗi take ji zata koma gidansu wajen Ummanta. Da yamma kam suka shirya duk kansu harda Hafsa da Humaira, Hafsa dai bata ji daɗin wnn lamari ba, tinda mai Napep ya saukesu a daidai lungun ƙunshi Hajar take murmushi, Hafsa ce ta fara shiga gidan snn Humaira da Anty sai Hajar tare da almajirin da ya ɗakko jakar kayanta, da sauri Umma ta fito daga ɗaki tana musu brka da zuwa, Anty ta tsaya a tsakar gida suka gaisa da Baba dake zaune bisa darduma a ƙofar ɗakinsa, su Hafsa ma suka gaisa snn suka shiga wajen Umma. Hajar ta sunkuya gaban mahaifin nata tace "Baba barka da yamma", yace "ywwa Hajara", tace "ya kufan jiki?" yace "alhmdllh", tace "Allah ya ƙara afuwa" tayi zamanta nan kusa dashi. Sa'adatu ta leƙo ta ruɓaɓɓiyar windown ɗakin Maama tana yamutsa fuska tace "gayyar tsiya knn". Su Anty basu wani jima ba suka wuce gida, har bakin Titi Hajar da Sabra suka rakasu, Hajar ta kamo hannun Humaira ta damƙa mata rabin kuɗin da Antyn ta bata ɗazu tace karta gayawa kowa, bayan su Anty sun hau Napep sun wuce Hajar da Sabra suka koma gida.
★Washe gari Friday, a hankali Nurain yake sakkowa daga stairs, hannunsa riƙe da ƴar ƙaramar trolley da ya zuba kayansa, yayi matuƙar kyau cikin shigar ƙananan kayan da yayi all back, hakan sai ya sake haska caramel skin ɗinsa sosai, wata shegiyar Pcap black ya ɗora akan cikakkiyar sumarsa and that makes him to look younger than his age, Mami Noor sai Khausar da ta zo jiya ne zaune a main palourn, daman Noor da Khausar ƴan rakiyar airport ne, duk kansu Abaya suka saka ta Noor black ta khausar kuma maroon, Mami ta dubi ɗan nata tace "har ka fito Uthman?", a hankali ya ƙaraso kusa da ita yace "yeah Mami", Mami tace "toh ka yiwa Abba sallama naga time ya ja tinda jirgin 9am ne, yanxu gashi eight har ta gota". Majestically Nurain ya wuce palourn Abba, Abba ya fito daga bedroom ɗinsa yace "za ka wuce knn?", Nurain ya durƙusa yace "Eh Abba", Abba yace "wane zai kaika airport?", Nurain yace "Driver", Abba yace "toh Allah ya kiyaye, you call me right away after landing..", Nurain yace "insha Allah Abba" ya miƙe ya fita dan already takwas da minti goma ta gota, yana fitowa daga palourn Mami ta miƙe ta nufi part ɗinta, Nurain yace "Mami" sai kuma ya cire Pcap ɗin kansa ya ƙarasa gabanta, murmushi tayi ta shafa kansa tace "Allah ya tsare Son", baice komai ba ya rungumeta yana lumshe ido. har compound Mami ta raka sa, Noor da Khausar suka shiga back seats, Nurain ya kalli drivern da zai tuƙasu yace "bani key", ba musu drivern ya miƙa masa, ya san drivern baya gudu tinda dokar Abba yake bi, shi kuma yanxu sauri yake kar yayi missing flight, driver seat Nurain ya shiga drivern kuma ya shiga kujerar mai zaman banza, Garba da sauran ma'aikatan gidan na ɗaga masa hannu ya fita daga gidan, suna hawa saman titi Nurain ya take accelerator, ai kam few minutes of a ride suka isa airport, 9:05 dot jirginsu Nurain yayi take off, driver ne ya mayar da su Noor gida. Bayan minti goma da take off ɗin jirgin da zai tafi India jirgin da yazo daga Egypt yayi landing. a hankali passengers ɗin suke sakkowa daga matattakalar jirgin. wani murmushi Ruqayyah tayi bayan ta shaƙi iskar 9ja, a hankali ta ƙarasa fitowa daga airport ɗin bayan ta gama bin duk wasu procedures, wayarta ta ciro daga handbag ta kira bolt dake within her location. after 15minutes bolt ɗin ta ƙaraso, a boot drivern bolt din ya saka mata jakarta snn ya buɗe mata back seat ta shiga. location ɗin da ta gaya masa nan ya ringa bi, wani irin bugawa zuciyar Ruqayyah tayi da taga sun shiga street ɗin gidansu. a ƙofar gidansu tace ma mai bolt ɗin yayi parking, a hankali ta sakko daga motar, tayi masa transfer ɗin kuɗinsa, ya ciro mata jakarta daga boot snn ya shiga motarsa ya juya ya fita daga street ɗin. Ruqayyah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon gate ɗin gidansu, har lokacin wani irin bugu zuciyarta take tamkar zata bulluƙo, da kyar ta kai hannu tayi knocking a hankali.........✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{ 23..}
Har wajen minti biyar tana knocking amma ba wani respond, da ɗan karfi ta buga tana karanto duk addu'ar da tazo mata baki, mai gadi ne ya buɗe, idonsa duk a kumbure alamar bacci, bake bake yayi a hanya yace "wai waye ne?", Ruqayyah da bugun zuciyarta ya ƙaru tace "sallau bani hanya na wuce", zaro kumburarrun idanunsa yayi ya saki baki yana kallonta, lokacin guda kuma ya saki kabbara yace "alhmdllh, Allah mun gode maka da ka bayyana Hajiya ƙarama....", Ruqayyah ta yamutsa fuska tace "ba ɓata nayi ba sallau ƙasar waje naje", yace "barka da dawowa hajiya", da sauri ya matsa mata hanya, sai kace wacca take taka rurutaccen garwashin wuta haka take tafiya a ɗan madaidaicin compound ɗin gidan nasu, mai gadi biye da ita da jakar kayanta, ajiyar zuciya ta shiga jerawa da idonta ya kyallaro motar Daddy dake parking space, knn bai fita work ba, a bakin ƙofar shiga main building ɗin ta tsaya, mai gadi ya ajiye mata jakarta ya ƙara gaba. a hankali ta kai hannu ta murɗa handle ɗin ƙofar snn ta shiga ciki sai kace wata ɓarauniya, palourn ta tsaya ƙarewa kallo sai kace wani baƙonta, babu kowa sai motsin da take jiyowa daga kitchen. murya na rawa tace "Assalamu alaikum..." tana raba idanu. Momy ce ta fito daga kitchen hannunta riƙe da Mug, wani irin kamewa tayi tana kallon ƴarta ta da wani weird expression, Ruqayyah tace "Mommyy.." sai kuma ta nufi Mahaifiyar ta ta da sauri da nufin rungumeta, Momy tana ganin haka ta juya ta koma kitchen fuskarta ba yabo ba fallasa, a take Ruqayyah ta fara shan jinin jikinta, kitchen ɗin ta bita ta tarar da ita tana kaɗa kwai, hawaye har ya ciko idonta ta ƙarasa gaban Momy tace "Momy... Please let me explain", banza Momy tayi da ita ta kunna gas ta ɗora kasko ta fara frying omelette, kusa da ita Ruqayyah ta matsa tana ƙoƙarin riƙo hannunta, da wani irin zafin nama Momy ta hankaɗa ta, Ruqayyah ta afka can jikin cabinet ragowar tafarfasasshen ruwan zafi a kettle ya kwararo mata a hannu, ƙara ta fasa sbd zafin ruwan ta shiga sosa wajen a gigice. Momy ko a jikinta ta cigaba da juya kwan da take soyawa a kasko. sink Ruqayyah ta nufa da sauri ta buɗe famfo ta shiga zuba ruwan sanyi a wajen da ta ƙone, ai kam ta ƙone sosai domin kwa wajen yayi jajur har fatar ma ta tattare. Ruqayyah ba ta sake gigin zuwa kusa da Momy ba, sai yanxu take ganin girman laifin da tayi, ita ta sha abun ba zai kai haka ba, wai Momyn ta ce ta ƙonata da ruwan zafi amma ko a jikinta, lallai akwai lukutar masifa, Momy ta gama haɗa komai na breakfast ta jera a tray snn ta fita kitchen ɗin. Bayanta Ruqayyah tabi ta zube a gabanta lokacin da ta ƙarasa palour, duk ka ƙafafuwan Momy Ruqayyah ta riƙe ta fara kuka tace "dan girman Allah Momy ki saurareni, wllh ban aikata hakan wai don bana son auren ba, ina son auren wllh, ki tsaya nayi miki bayani dan Allah...", Momy ta ajiye trayn hannunta akan kujerar da ke kusa da ita. Ruqayyah na ɗago kai ta ɗauketa da wani gigitaccen marii a kuncin dama, bata gama dawowa hayyacinta ba ta sauke mata wani a kuncin hagu har saida ta kifa, Ruqayyah da ke ganin wasu white stars na haskawa a idonta ta rushe da matsanancin kuka tace "na shiga uku Momyyy kin tsiyayar min da ruwan ido", Momy na huci tace "shut up Ruqayyah, dabba ma ya fiki tunani, are you mad da zaki zo kina cemin na tsaya kimin bayani?, bayanin uban me zaki min nonsense, wllh kika sake magana saina sumar dake Coward..." da haka Momy ta ɗauki trayn ta wuce part ɗin Daddy, Ruqayyah kuka take kamar ranta zai fita, ba ta taɓa tunanin abin zai dagule haka ba, ta ɗauka faɗa kawai za ai mata amma shine harda mugayen maruka, toh Momy ma knn inaga Daddy, da sallama Momy ta shiga palourn Daddy, Daddy da ke kallon news ya amsa sallamar yana nazarin expression ɗin fuskarta, Momy daurewa kawai take har ta gama serving ɗinsa abinci, Daddy yayi sipping tea yana kallon fuskarta yace "what happened?", remote control ta ɗauka ta ƙara volume tace "A'a, ba komai", yace "alright indai akan Ruqayyah ne ai jiya naje police station na shigar da report, yau ma zan koma naji ya ake ciki", Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "Ohk idan ka koma sai kasa ayi closing case ɗin cause Ruqayyah tana gidan nan yanzu haka..", bread ɗin hannunsa ya ajiye yace "Ruqayyah na gidan nan?", Momy tayi resting a jikin kujera tace "Eh, ba ta daɗe da shigowa ba, she's perfectly fine..", gyaɗa kai Daddy yayi ya cigaba da cin abincinsa yace "daman na gaya miki don't stress yourself about Ruqayyah's missing, gashi nan ta dawo aii..", Momy ta sauke numfashi a hankali har lokacin zuciyarta zafii take. saida Ruqayyah taci kukanta ta ƙoshi snn ta ja jiki ta shiga room ɗinta, toilet ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta tsaya a gaban mirror tana kallon fuskar, a hankali ta kai hannu ta shafa kuncinta inda ya kumbura da shatin yatsun Momy biyar ciff. fita tayi daga ɗakin ta kama hanyar part ɗin Daddy, da sallama ta murɗa handle ta shiga kanta a ƙasa, kallo ɗaya Daddy yayi mata ya kawar da kai, Ruqayyah ta zube nan kan carpet kusa da ƙafarsa tace "Daddy ina kwana..", without looking at her yace "lfy Ruqayyah, kinga dama kin dawo knn", shiru tai ba tace komai ba, Momy dake karkaɗa legs tace "fita malama, ban san ganinki...", Daddy ya ɗaga mata hannu yace "No leave her, Ruqayyah kin dawo ko?, toh shknn sannu da zuwa", hawaye ne ya zubo idon Ruqayyah ta ɗago kai tace "Daddy I'm very sorry...", yace "No Ruqayyah sorry for yourself, ke kikai loosing.." da haka ya miƙe ya shiga bedroom ɗinsa, Momy tabi bayansa da kallo snn ta miƙe ta fita palourn, da kyar Ruqayyah ta miƙe itama ta fita daga palourn, duk wani hope da karsashinta ya tsiyaye, sosai reaction ɗin Daddy ya dagargaza mata zuciya, toh da wnn action ɗin ai gara shima ya falla mata mari kamar Momy, jakar kayanta ta ɗauka ta shiga room ɗinta sai kace wacca kwai ya fashewa a ciki.
★Hajar ce tsaye gaban wardrobe tana jera kayanta, tana gama jera kayan ta linke Ghana most gon ta ɗaga katifar gado ta saka, tsintsiyar laushi ta ɗauka a bayan ƙofa ta fara share ledar ɗakin, tass ta share ta gyara ko ina, ta kunna turaren tsinke, zanin wanka ta ɗaura a ƙirji snn ta cire kayan jikinta, ta saka dogon hijab ta ɗauki kwandon soso da sabulu ta fita. Umma na yanka albasa cikin ƙullun alale, Hajar tace "Umma nazo na shafa miki manja a gwanayen?, tin ɗazu na wanke yanxu nasan sun bushe", Umma ta kalleta tace "ba wanka za kiyi ba?", Hajar tace "Eh wanka zanyi", Umma tace "toh jeki kiyi wankanki na karasa", Hajar tace "tom" ta wuce gaban tukwanen ruwa, bokiti ta ɗauka ta fara kanfatar ruwan tana zubawa. tana gama cika bokitin ta ɗauka ta wuce hanyar toilet, da gudu Nabilah da ta fito daga ɗaki tazo ta bangajeta ta shige banɗakin, Hajar tayi ƴar ƙara sbd bokitin ruwan da ya saukar mata a ƙafa, a fusace Hajar ta buɗe baki za tay magana sai kuma tayi shiru ta tsaya tana kallon ƙofar banɗakin, juyawa tayi ta dawo tsakar gida ta ɗauki kwandon da ta kife gwangwanaye ta ajiye kusa da Umma, ta koma ta ɗakko tasar manja da audiga suma ta kai gaban Umma ta ajiye, durƙusawa tayi ta fara shafa Manjan jikin tin, Umma tace "yawwa Hajara haka nake so, ko sun takaleki dan Allah karki kulasu", Hajar tayi murmushi tace "insha Allah Umma..", Umma tace "yawwa Allah ya yi miki albarka". sai bayan minti ashirin snn Nabilah ta fito daga toilet tana yatsine, ta kalli Umma da Hajar ta buga uban tsaki tace "annoba" ta shige ɗaki. Hajar ta miƙe ta sake ɗiban wani ruwan ta shiga wanka. Nabilah da ta shiga ɗaki ta dubi Sa'adatu tace "banza, wai ke Sa'adatu wane irin gigin bacci kike ne?, sai ki ringa tattaɓa jikin mutum sai kace wata ƴar yaye, wllh jiya da kyar nayi bacci duk kin ƙadabaibaiye ni sai kace wata ƙadandoniya, mtswww", wani shu'umin kallo Sa'adatu tayi mata tace "ina Maama?", Nabilah tace "ta tafi gidan Balaraba ita da Maimuna", Sa'adatu tayi wani murmushi mai ma'ana daban daban tace "Nabilah kina so ki samu mazajen kuɗi?", Nabilah ta zaro ido tace "so kai", Sa'adatu ta dafa kafaɗarta tace "wllh kizo na haɗaki da zeenatu da Mabaruka, zaki samu kuɗin a wajensu wllh tallahi..", Nabilah tace "Allah, aikatau zan musu?", Sa'adatu tace "lah lah lah ko ɗaya babu aikin da za ki musu, rayuwa irin ta wayayyun mata kawai zaku ringa yi, kiji daɗi ina gaya miki malam, kici mai kyau ki sha mai, ki kwanta a lafiyayyen gado fatarki ta sha raɓa, ga kuma uban kuɗi a aljihunki", Nabilah tace "toh wai mene rayuwar wayayyun matan?", Sa'adatu tace "rayuwar ƴanci knn ba ruwan mu da maza mu kaɗai mun ishi kan mu", Nabilah ta taɓe baki tace "mtswww, dalla malama ni ban fahimta ba", Sa'adatu ta hura hanci tace "idan kin yarda gobe zani gidansu saiki rakani kiga irin rayuwar da nake nufii", Nabilah ta gyaɗa kai tace "zanyi tunani". Bayan an sakko daga masallaci sallar juma'a Baba ya shigo gida tare da Mu'azzam, nan tsakar gida Baba ya zauna daga jikin inuwa. Mu'azzam ya durƙusa gabansa yace "Baba zan wuce aiki", Baba yace "har yanzu baku gama sakawa gidan tiles ba?", Mu'azzam yace "mun gama tarazo mukewa farfajiyar gidan", Baba yace "toh Allah ya temaka, ka kai Maimuna makarantar da nace ka mayar da ita?", Mu'azzam ya shafa kai yace "A'a Baba, ai ranar Litinin ɗin muna asibiti", Baba ya gyaɗa kai yace "toh jibi saika kaita", Mu'azzam yace "tom" ya miƙe ya leƙa ɗakin Umma yayi mata sallama snn ya fita. Baba ya ringa kwalawa Maimuna kira amma shiru, Nabilah ce ta fito tace "Bata nan sun fita da Maama", yace "ina Sa'adatu?", tace "tana ɗaki", yace "kira min ita", tace "tom" ta koma ɗaki, Sa'adatu sai gyatsine take tinda taji komai, Nabilah tace "Eh ai kinji dai ko?, saiki je". Sa'adatu ta fice fuu ta sha kunu, can gefen Baba ta koma ta rakuɓe tana zumɓuro baki, Baba yace "toh kema ki shirya jibi Mu'azzam zai mayar dake makaranta ke da Maimuna..", zaro ido tayi tace "Baba makaranta fa kace", yace "Eh, idan kuma ba kya son karatun saiki fito da miji na aurar da ke, itama Nabilah na bata lokacii..", Sa'adatu ta girgiza kai tace "wllh ni bana son aure, gwara na koma makaranta", Baba ya ringa kallonta kafin yace "tashi ki ban waje, saiki shirya ranar litinin...", bazar bazar ta koma ɗaki tana taɓe baki wai ita shagwaɓaɓɓiya.
★Raqayyah ta sake dialing numbern da tayi saving da dearest a wajen karo na ashirin tin dawowarta gida, abu ɗaya dai ake ta nanata mata wato the number you dial is switched off, wurgi tayi da wayar akan gado tana jin wani zafi a zuciyarta, she madly missed his stern voice, sound of his deep breathe out, komai nashi tayi missing sosai. lumshe ido tayi tana jin tsantsar kewarsa a duka sassan jikinta, maganarsa ta ƙarshe da tayi hitting eardrums ɗinta wacca she'll never forget ( sleep tight for today tomorrow in my arms), a fili tace "Soon dearest". towel ta ɗora a jikinta ta shiga wanka, ɗaure da towel ta fito tana tsane fresh fair skin ɗinta da hand towel, ta buɗe press ɗinta, ganin babu kaya aciki ta mayar ta rufe, ta tina ashe fa kayanta na ɗakin Momy acikin ɗaya daga cikin boxes ɗin lefenta, Abayar da ta cire ta mayar snn ta fita zuwa ɗakin Momy, a hankali tayi knocking ta shiga, ta tarar Momy ba ta nan don haka ta fara surveying ɗakin da idonta tana neman boxes ɗin lefenta. har press ta buɗe amma ba taga alamar akwatunan lefe ba, tana rufe press Momy ta shigo, Momy ta kalleta sama da ƙasa tace "kee me kike yimin a ɗaki?", Ruqayyah tayi gathering courage tace "amm Boxes ɗin lefe nake nema zan ɗauki kaya", wata muguwar harara Momy ta galla mata ta nuna mata wata box dake kusa da shoe shelf tace "ga kayan ki can, ba ki ma da hankali da kike neman wasu akwatunan lefe, toh kwananki biyu da guduwa muka mayarwa da Nurain kayansa..", da ƙarfi zuciyar Ruqayyah ta buga, ji tayi kamar ta fita daga ƙirjinta ta koma ciki sbd anan take jin bugunta, a lokacin idan akace mata ta haɗiyi zuciyarta ne to fa ba za tayi musu ba. lips ɗinta na zikiri tace "Momyy... wllh banji me kika ce ba, me aka mayar?".......✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{24..}
Momy ta ringa kallonta kafin tace "Au maimaita miki zanyi knn, kada Allah yasa kiji, take your belongings and leave my room idiot", Ruqayyah da har lokacin bata gama recover ba tace "Momy call me anything amma dan Allah ba a mayar da lefena ba ko?", tsaki Momy tayi ta janyo box ɗin kayan ta dire mata tace "hmmm, ƙarya zan miki, ko na taɓa miki ƙarya ne?", wani kuka ne ya kwace mata tace "A'a Momy, wllh baki taɓa min ƙarya ba", Momy ta haɗe girar sama da ƙasa tace "toh sai kuma me?, ba dai auren ne bakya so ba har da su guduwa?, toh everything was cancelled, ba wata maganar