Showing 33001 words to 36000 words out of 114314 words
Chapter 12 - HAJAR Book Complete document by Feenerh_feeche .txt
a hankali suka fara daɗewa bayan sunyi masa sallama da fatan Allah ya bada abinda za a tafi nema, Dr Marwan ne ƙarshen fita, har ya miƙe zai fita Nurain yace "Dr wait", Marwan ya dawo ya zauna kujerar dake facing ta Nurain, Nurain ya ɗauki papern gabansa ya miƙa masa yace "plxx, ka duba wnn patient ɗin", Marwan ya karɓa ya buɗe ya karanta, yana gama karantawa ya rufe yace "it is a cardiac arrest?", Nurain ya gyaɗa kai yace "yeah", Marwan yace "toh yana ina?", Nurain yace "yana cikin hospital ɗin nan, plxx kasa a nemo maka shi", Marwan yace "sure" ya miƙe ya fita da papern a hannunsa. ƙarfe uku da ƴan mintina Nurain ya koma gida, direct room ɗinsa ya wuce, after taking his bath ya shirya cikin ƙananan kaya ya fito sallar la'asar, bayan ya dawo salla ya wuce wajen Mami, saida ya dangana da bedroom snn ya tarar da ita tana sallah, palour ya dawo ya zauna yana latsa wayarsa, sai after 20minutes Mami ta fito sanye da hijab ɗin da tayi sallah ta zauna kan kujera three seater, Mami tace "ka dawo?", Nurain ya ajiye wayar da yake latsawa yace "Eh, tin ɗazu ma na shigo", Mami tace "Ohk, kaci abinci?", Nurain yace "A'a yanzu nake jiran Noor ta shigo saita kawo min", Mami tace "Noor bata dawo schl ba, saidai Laure ta kawo maka", Nurain ya shafa kansa yace "No, bari Noor ɗin dai ta dawo", Mami ta taɓe baki tace "toh ai shknn", ta gama rafko jirginsa, ya raina tsaftar Laure. Nurain yace "Mami daga yau bazan sake zuwa Hospital ba har saina dawo daga tafiya, na gama komai da zanyi a can, insha Allah ina sa ran ranar Friday zan tafi", Mood ɗin Mami ya canza, ta ƙurawa TV ido ba tace komai ba, Nurain ya ringa kallonta........✍️
💛 HAJAR 💛
by Feenerh_feeche
{18..}
After the silence of about 5mins Mami tace "kuma kai hakan shi yafi yi maka?", Nurain ya kalleta yaga har lokacin idonta na kan TV, ya shafa kansa ya kwantar da voice yace "yeah Mami hakan shi yafi min", tace "Ohk shknn, Allah ya bada sa'a", yace "Ameen". Mami ta tashi ta fita ɗakin, bata daɗe ba ta dawo da tray a hannunta, akan carpet ta ajiye ta koma position ɗinta ta zauna, ta kalli Nurain tace "saika sauka kaci abincin", ya kalli trayn snn ya ajiye wayarsa akan hannun kujera ya sauka kan carpet, wamers ɗin ya fara buɗewa snn ya ɗauki plate ya zuba abincin, yana fara cin abinci akay knocking door, Mami tace "shigo" cause tasan waye, Laure ce ta shigo hannunta riƙe da tray mai ɗauke da bottle water sai lemon kwali da cup, Mami ta nuna mata Centre table tace "ajiye anan", a hankali ta ajiye kana ta juya ta fita, a hankali Nurain yake cin abincinsa har ya gama, ya ɗauki bottle water ya tsiyaya a cup ya sha, Mami tace "karka yi tafiyar nan ba tare da kaje kunyi sallama da Hajiya ba", yace "insha Allah Mami, zanje muyi sallama". tace "yawwa", ya tashi ya ɗauki wayarsa yace "zan ɗan fita", tace "wajen Hajiyar zaka?", yace "No", tace "Okay, ka taho min da counter", yace "tom" snn ya wuce ƙofa ya murɗa handle ya fita, room ɗinsa ya wuce ya ɗakko muƙullin Mota, daga nan ya fita compound ya shiga motarsa, slowly yake driving listing to the qira'a of Sheikh Husary, A wani annakakken wajen siyar da wayoyi yayi parking, same wajen da ya siyi sabuwar wayar hannunsa, bayan ya shiga building din da akay molding dinsa da pattern ɗin cell phone, tsayawa yayi yana tunanin wace wayar zai siyawa Noor, taɓe baki yayi ya nufi ɓangaren iPhone cause yasan sune ake yayi, ko wace ƴan mata tafi son iPhone, Shi kam waya indai ba Samsung bace ba toh a barta, iPhone mai kyau da tsada ya siya full series, credit card ɗinsa ya miƙawa cashier ta cire kuɗin snn ta miƙa masa with due respect, yana gamawa ya fito ya shiga motarsa, A junction yaga mai counter ya siyi guda uku mai haɗe da agogo, lokacin da ya koma gida har Magrib tayi, saida yayi sallah snn ya shiga ciki, Noor ta amsa sallamarsa, tayi wani dafa'an tana kallon stuff dinta na Kdrama, tace "yaya ina yini", yace "lfy lou", zama yayi akan kujera duk da ba hakan yaso ba, with stern Voice yace "zo nan", ta matsa gabansa ta zauna daga ƙasan carpet, ledar da ya shigo da ita ya ajiye mata akan cinya yace "your birthday presence", Noor tayi murmushi snn ta buɗe ledar, ai tana ganin abinda yake ciki ta daka tsalle ta rungumesa tace "thank you so much, nagode Allah ya saka da alkhairy yayana", yace "you know the rules right?, kuma kinsan warning ɗin da nayi miki ko?", ta gyaɗa kai da sauri all her white tooth out, ya shiga part din Mami ya kai mata counter, ya fito ya haura room ɗinsa cause yana so ya gama duk wani shirye-shirye kafin nanda Wednesday.
★Hajar na zaune a palour tare da Hafsa da Humaira suna kallon wani film a MBC 2 mai suna IT, Humaira duk ta ruɗe sbd film ɗin akwai abin tsoro, Hajar kam kwata kwata mind ɗinta was somewhere else, ita bata ma san me akeyi a film ɗinba, time to time kuma saita ja long hiss, Hafsa ta kalleta tace "wai me ya faru ne tin ɗazu kike mana tsaki?", Hajar ta sake yin wani tsakin tace "uhmm bazaki gane yadda nake jin haushi ba ne", Hafsa ta taɓe baki tace "toh ki gayamin mana, me ya baki haushin?", Hajar tace "wllh wani ɗan rainin hankali ne ya haɗamin zafi ɗazu a asibiti", Hafsa ta tare hammar da ta yanko mata tace "ni kam bangane wane rainin hankalin kike magana akai ba?", Hajar tace "ai shiyasa nace bazaki gane ba", Hafsa tace "taya za kice bazan gane ba bayan baki yimin yadda zan gane ɗin ba", Hajar tace "forget it kawai, Allah ya kaimu gobe, ai zan koma asibitin, wllh sai ya bani takardar test ɗin Babana", Hafsa ta koma tayi resting a jikin kujera tace "uhmm, ke kika sani dai", Anty ce ta fito daga ƙofar part ɗin mijinta, ta ƙare musu kallo snn tace "la'ila ƙarfe nawa har yanzu baki kwanta ba Humaira?", Humaira ta turo baki tace "ai su yaya ne sunƙi zuwa mu kwanta, kuma ni tsoro nake ji", Anty ta zauna ta kalli Hafsa da take ta faman hamma tace "toh kuje ku kwanta mana, sai zabga hamma kike, gobe da schl kinsan da hakan aii", Hafsa tace "Hajar nake jira", Anty tace "Ina ruwanki da ita, ita ba schl take zuwa ba don haka anytime zata iya kwanciya abinta", Hafsa tace "toh saina gama kallon film ɗin nan", Humaira tace "Anty ni tsoro nake ji, kuma bacci zanyi", Hafsa ta nasa mata harara tace "keee, wuce ki kwanta, tin ɗazu nayi miki shimfiɗa", Humaira ta noƙe kafaɗa ta koma cinyar Anty ta kwanta, Anty ta kalli Hajar tace "An sallami Baba", Hajar tace "yaushe?", Anty tace "ɗazu", Hajar ta gyaɗa kai tace "toh yaga likitan?", Anty tace "Eh, Adda tace har daƙi likita yazo ya dubasa, kuma likitan ne yazo da takardar test ɗin", Hajar was speechless sbd mamaki, how comes?, a ina doctorn ya samu test ɗin?, ko dai result ɗin biyu ne?, ganin bata da amsar waɗan nan questions ɗin saita ɓige da jinjina kai, sai kuma tace "gobe da safe zasu tafi gida knn?", Anty tace "Eh". Washe gari da wuri Hajar ta gama gyara gida, ta shiga toilet tayi wanka, ta fito ta ɗauki mai ta shafa, wardrobe ta buɗe ta ɗakko kaya ta saka, Hafsa dai saida ta jere mata kayan nan a press snn ranta yayi sanyi, wani material ta saka mai kyau, Anty ce ma ta bata shi ita da Sabra waccan sallar da ta wuce. gaban mirror ta tsaya tana kallon gashin kanta mai cika, yaushe rabon da ta taɓa sa, gashi nan kam duk ya cukurkuɗe alamar ba a untangling ɗinsa frequently amma kuma babu datti, cause tana wankesa akai akai amma fa tajewa ne yake mata wahala sbd cikarsa, most of the time ma Umma ce take taje mata, roban hair oil ta buɗe ta zauna akan stool, she spent almost 30mins making her black silky hair tide, a ƙeya tayi parking ta ɗaure da ribbon, ta tufke jelar wacca ta saukar mata har midback. ta mayar da comb ɗin cikin drawer snn ta rufe roban hair oil ɗin, ta ɗaura dan kwali ta fita palour, kitchen ta shiga ta tsiyayi ruwan Lipton a cup, ta haɗa tea snn ta ɗauki 4slice of bread ta koma ɗakinsu Hafsa. tana cikin ci wayarta ta fara ringing, sosai tayi mamakin wane yake kiranta at this time, cup ɗin tean ta ajiye ta miƙe ta ɗakko wayar, kallon screen ɗin wayar ta tsaya yi ganin bata son numbern dake kiranta ba, har kiran ya yanke wani ya sake shigowa, slim finger ɗinta ta kai tayi picking snn ta kara wayar a right ear ɗinta haɗe da yin sallama with her cool voice, ɓoyayyen ajiyar zuciya taji an sauke snn aka amsa mata sallamar, ta yamutsa fuska jin muryar namiji, ta ciro wayar daga kunnen dama ta mayar da ita na hagu tace "Ahmm bangane mai magana ba?", yace "Eh, am Ahmad, na samu numbern ki a wajen friend ɗinki", ta taɓe baki sbd ta fahimci shine wanda Zainab tace zata basa digit dinta, tace "okay, but how can I help you?", yace "i want to talk to you", tace "Sorry, ba sai kayi magana ba ma, ina fatan dai Zainab tayi maka bayani", yace "wane bayanin?", tace "akwai baiko a kaina", daga haka ta katse kiran ta cigaba da shan shayinta, tana ajiye wayar saiga wani kiran nan yana shigowa, saida tayi ringing twice kafin ta ɗauka, yace "why did you hanged up?", ta juya lulu eyes ɗinta tace "ina aiki ne", yace "Okay, a gama lfy, zan kira later plxx pick up", tace "tom" ta katse.
★Ƙarfe goma da rabi na safe Naseer da Mu'azzam da kuma Huzaifa wanda ya baro lectures ɗinsa ya dawo gida suka shigo gida tare da mahaifinsu, Baba duk ya faɗa ya rame sosai, Umma ta fito ɗakinta tana musu barka da dawowa, ta wuce ƙofar ɗakin Baba ta buɗe padlock, Huzaifa ya tallafi Baba ya shiga ɗakinsa, ɗakin a gyara yake fes fes sai ƙamshin turaren tsinke yake, Umma ce ta gyara sa da sassafe tinda a gida take kwana. Mu'azzam ya shigo da ledar drugs ɗin Baba ya ajiye gefe, Umma ta fita tana kallon ɗakin Maama ta shiga nata, flask ɗin da ta dama kunun gyaɗa ta ɗauka da cup ta fita, ta kalli Mu'azzam da yake ƙoƙarin fitowa daga ɗakin tace "zaka sha kunu na zuba maka?", ya gyaɗa kai yace "Eh zan sha", ta ƙarasa shiga ɗakin Baba, ta ajiye flask din gefe, Huzaifa ya jingina pillow a bayan Baba snn yace "sannu Baba, Allah ya baka lfy", Baba yace "Ameen, Allah yayi muku albarka", Huzaifa da Umma suka ce Ameen, Umma tace "Huzaifa ina Naseer?", yace "ya shiga ɗaki", tace "ga kunu idan zaku sha na zuba muku?", Huzaifa yace "tom". cup guda uku Umma ta cika da groundnut pap, Huzaifa ya ɗauki nasa dana Naseer ya shigar musu dashi ɗakinsu, Umma ta rufewa Mu'azzam nasa da ya shiga toilet, Baba ya kalli Umma yace "ina Hajara?", tace "tana nan", yace "kirowamin Rabi", Umma ta waro ido amma ba tace komai ba ta tashi ta fito tsakar gida, A ƙofar ɗakinsu Naseer ta tsaya ta kira Huzaifa, ya fito hannunsa riƙe da kofin kununsa da har ya kusa shanyewa yace "na'am", tace "ka kira Maamanku tazo inji Malam", yace "tom" ya shiga ɗaki ya ajiye kofin kunun snn ya fito ya wuce ɗakin Maama, Umma tana ganin ya shiga wajen Maama ta koma ɗakin Baba tace masa gata nan zuwa. Huzaifa ya ringa kallon Maama wacca take zaune dafa'an akan ƙullin kayan wanki, ya durƙusa yace "Maama barka da safiya", tana karkaɗa ƙafa tace "ba yawwa ba, tinda kwanten gaisuwa zaka jefeni da ita, wai har waccar mayyar matar ta fini daraja a idanunku kai da Nasiru, ƙiri ƙiri bakwa kallona a matsayin mahaifiyarku, ace miƙiyyata itace wacca zaku fifita, koda yake ba laifin ku bane tinda an zuba a kunu an baku kun tanɗe..", Huzaifa dai ya shafa kai yace "Baba yana kiranki", ta taɓe baki tace "toh me zan masa da yake kirani, ince dai ga mayyar matarsa nan a tare dashi koh", shiru Huzaifa yayi baice komai ba. Maimuna da take kan gado rashe rashe itada Nabilah ce ta miƙe zaune tana hamma, wani irin wage baki tayi babu addu'ar neman tsari ga shaiɗan bare ta kai ga rufe wawakeken bakinta, buɗe idonta tayi tana soshe soshe snn ta zabga tsaki tace "Allah ya isa wllh, Sauro da kuɗin cizo sun suburbuɗe ni yasin, shiyasa Sa'adatu ta tsani gidan nan wllh, nima dai daf nake da barin kangon nan alkur'an...", dakatawa tayi da tijarar tana micincina idanu ganin Huzaifa, ta sakko daga gadon tace "Laa yaya ina kwana", tsaki yayi ya miƙe ya fita a ɗakin. Maimuna ta taɓe baki tace "ni kam Maama sai naga kamar yaya Huzaifa yana juyewa kamar yaya Naseer", Maama tayi kwafa tace "uhmm shima ai an shanyesa, har kunu fa ake damawa a basa, kinga kam bayan shanyewa har damesa akai". Maimuna ta cigaba da soshe soshe kafin tace "ni kam Maama wai ina ragowar piya-piyan nan yake yau na fesa a katifa?, kuɗin cizon nan yayi yawa", Maama ta ɗauke kanta tace "ya ƙare, daman Sa'adatu ce mai siya kuma kinga tin shekaran jiya rabonta da gidan nan, itace mai zuciyar siyar piya piya ayi feshi, ke kam tsimilmila da maƙo bazasu barki kiyi abin arziƙi ba, koni nan uwarki ba morarki nake ba, ko kuɗin kika samo saidai ki cinye ke kaɗai sbd rowar masifa, nasan yanzu haka kinada uban kuɗi a ƙugunki amma bazaki iya fitar da ɗari biyar a siyi piya piyan ba kin gwammace kuɗin cizon suyi ta cizonki....", Maimuna tace "kaiiii Maama", Maama ta harareta tace "gafara can za wani kicemin kaiiii, aa ba kaii ba hannu ko ƙafa, sakarya kawai, ki kira Sa'adatu yanzun nan kice mata ta dawo gida an sallamo malam, jiya naga kunyi waya da ita kuma nasan ƴan albarkar ƙawayenta har sun mayar mata da tsaleliyar wayar da ta rasa", Maimuna ta ringa ƙunƙuni snn ta ɗauki wayarta a ƙarƙashin pillow ta shiga dokawa Sa'adatu kira, sau uku ta kira wayar na ta ringing amma ba a ɗauka ba, ta zabga tsaki tace "Maama kinga dai bata ɗauka ba ko?, ni dai ba ruwana idan yaya Naseer ya sake lakaɗa mata na jaki", Maama ta harareta tace "sake kira", Maimuna tace "bafa ɗauka za tayi ba don nasan bacci ma take yanxu" ta shiga kiran Sa'adatu for the fourth time. daf kiran zai tsinke aka ɗaga, Maimuna tace "ke Sa'adatu toh ki taho gida inji Maama an sallamo Baba daga asibiti kuma yaya Naseer yana nan..". ƙit aka kashe wayar bayan wani dogon tsaki, Maimuna ta kalli screen ɗin wayar ta mulmulo ashar tace "Alfarmar Annabi da Alkur'ani sai Yaya Naseer ya lakaɗa miki duka"......✍️
💛 HAJAR💛
by Feenerh_feeche
{19..}
Maama ta hangame baki tana kallon Maimuna tace "A'a kaji mun muguwar yarinya, ya zaki ringa mata mugun fata kina wani cewa Naseer ya lakaɗa mata duka iyee?, akan me kike mata wnn fatan sbd ƙeta?", Maimuna ta hade gira tace "toh daga temako shine zata wulaƙantani?, kawai saita yimin tsaki ta kashemin waya daga temako", Maama tace "sake kiramin ita ki bani wayar nida kaina nayi mata magana", Maimuna tace "ba dai da katin wayata ba wllh" ta miƙe ta saka wayar a wardrobe. Maama tayi ƙwafa ta miƙe ta fita a ɗakin ta shiga na Baba, sallama tayi ta ƙarasa shiga ciki, Baba da yake jingine da pillow ya amsa mata, ta kalli Umma da take zuba kunu a cup ta taɓe baki snn ta koma gefe ta zauna tace "ya kufan jikin mal?", Baba na kallonta da kyau yace "da sauƙi alhmdllh, ina Sa'adatu da Maimuna sune ban gani ba a asibiti", Maama ta dubi Umma tace "Baiwar Allah saiki tashi ki fita ko, zanyi magana da uban ƴaƴana", Umma ta cigaba da abinda take ko dubanta ba tay ba, Maama tace "Keee magana nake miki fa, ko kurma ce?", Umma ta rufe flask din kunun ta ɗauki wanda ta zuba a cup ta kai gaban Baba tace "gashi, bari naje na ɗora faten accar", Maama ta buɗe ƙananan idanunta tamkar an kwantali ɗata tace "kai jama'a ki fita nace kike reto sai kace mai maula", Umma ta ɗauki flask ɗin snn ta fita ɗakin, da wata muguwar harara Maama ta bita sai kuma ta kalli Baba tace "ka gani ko?, ina mata magana tayi banza dani sbd wulaƙanci", Baba ya ɗauki kofin kunun ya kurɓa snn yace "wllh duk ranar da keda ƴaƴanki kuka kasheni kin shiga uku Rabii", tace "na shiga uku a ina?, sai kace wata mara madogara", wani tari ne ya sarƙe sa ya nunata da yatsa yace "fita Rabii", ya cigaba ta tarin a hankali, ta taɓe baki tace "Sannu, mura ce ta kamaka kenan?". da kyar Baba ya samu tarin ya lafa masa, ya lumshe idonsa ƙirjinsa na suya, Maama ta miƙe tana gyara haɓar zaninta tace "to bari na baka guri ka huta mal, tinda daga magana sai tarii kar ace ni na tayar maka da ciwo" da haka ta fice a ɗakin. Naseer da ya fito a ɗakinsu ta kalla tace "biyoni" ta shiga ɗakinta, Naseer ya shafa kai snn yabi bayanta, ya zauna kan ruɓaɓɓiyar ledar ɗakin, Maama dake gafen gado zaune kusa da Nabilah da take baccin asara ta dubesa tace "wai me yake damun mal ne?", yace "hawan jininsa ne ya tashi snn kuma ya kamu da ciwon zuciya", Maama ta gwalo micimicin idanunta waje ta dafe ƙirji tace "ciwon