Showing 27001 words to 30000 words out of 95238 words

Chapter 10 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt

04 Jan 2025

6673

ta ke.. Wallahi ko da me zaa hadani ba zan iya sarauta ba.. Duk nan zamu jya cewa zamuyi tunda gadon mu ce. Amman aka duba cancanta aka zabi junaidu. Ba gamon kan mu mu kai ba.. Manyan mu da Yan majalisa ne Hadi da wasu daga cikin alumma ne sika hada Kai suka Zabe shi. Don haka amincewar ka ko akasinta duk ba a damuwar mu bace .... Junaidu shine sarkin birnin Nukaa da yardar Allah s...


Bai karasa ba amb Junaid ya fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciyar dik wanda ya saurara...


"Junaidu kukan me kake?" Bappah imrana ya tambaye shi.


Amb Junaid ya daga kansa, idanuwan sa sun kada sunyi jajir... Wata jijiya ta tashi daga goshin sa tayi radau.


"Lafiyar ka junaidu?" Bappah Usayn ya tambaye shi cike da kulawa


"Bappah....Kuyi hakuri amman ba zan iya karbar ragamar sarautar Nukaa ba. Bajda sani banida ilimi na Sarauta, kamar yadda Yaya jalaludden ya fada ban cancanta na zama sarki ba wallahi... A bawa wani daga cikin su Bappah. Su din manya na ne Kuma sunfini ilimin sarauta zasu Fi iya rikon kandemi...Musanman Yaya jalaludden zai fi dacewa"


Bappah Imran yaja dogon tsaki, Cike da hasalewa yace,


"Asabar satin sama kenan da safe za'a yi taron nadin a babbar fadar yamma. Katin gayyatar zasu fito gobe da safe inshaa Allah zaa fara rabawa. Zakuma a aikowa kowannen ku kasonsa ya rabawa abokanan arziki. Kaje ka fara shiri. Sannan Yan majalisar sarki ma zasuyi zama da Kai. Allah ya taya ka riko... Allah ya baka sa'a ya yi riko da hannuwan ka yasa kayi Mulki me adalci... Allah ya hade kawunan ku da Yan uwan ka ya kauda dik wata baraaka... Ku tashi muje Usayn"


Yana gama magana ya mike .. su Bappah Usayn suka bi bayan sa.....


Jalaludden ya buga tsaki ya fita daga dakin taron ransa a matukar Bache..


Sosai junaidu ya ke kuka tamkar wani karamun yaro. Alhaji Adamu da su Gwaggon court suka dinga bashi hakuri suna kwantar masa da hankali.


Sun dan dauki lokaci a haka tukun sannan sika yi masa rakiya wajen Hajiyan su. Sake fashewa yayi da kuka ya kasa cewa komai. Sai sune suka yiwa hajiyan bayani.


Ta tausashe shi sosai ta kuma yi farin ciki kwarai matuka da kasancewar hakan.


Sai da dare yaja bayan duk sun watse daga shi sai hajiyan take sake bashi hakuri da tabbatar masa da cewar daman mahaifin na su yana yawan cewa dama junaidu ne akan karagar mulkin birnin Nukaa.. Tun kafin kwanciyar sa ciwo daman ya fadawa Yan majalisar sarkin kan ko da Wani abun zai tashi Dan Allah a sanya Junaid ya zama sarki domin shi yafi cancanta da zama sarkin kandemi.


Sai da Hajiya ta tabbatar da damuwar sa ta Ragu tukun sannan tace masa yaje ya kwanta. Yayi mata sallama ya tafi


Samun kansa yayi da kiran iyalan nasa baki daya suka hallara Nan yake sheda musu halin da ake ciki.


Sunyi na'am da zancen... Sun Kuma yi murna kwarai matuka... Yache sai su tayashi da addua Allah ya zabi abunda yafu alkhairi


Shima a daren ranar yayi addu'oin sa sosai ya Kuma yi istikhara domin neman zabin Allah..



===========




Tuni aka fara aikawa mutane katin gayyatar bikin nadin sarautar Amb juanidu Muhamamd a matsayin sarkin birnin Nukaa... Gari gari kasa kasa..


Nigeria ta dauka... Kowane who is who masu farcinan Susa a Nigeria zai halarci babban taron nadin sarautar


Babban aminin sa wato Alhaji Abdulhamid oil mogul ya bada jirgi sukutum don jigilar dakkowa da mayar da bakin da zasu halarci taron zuwa garuruwan su... Wato Hisham airlines..


Tun bayan saura kwanaki uku ayi nadin sarautar Alhaji Abdulhamid da iyalan sa suka iso garin birnin Nukaa. Ciki harda Hisham tilon 'da agare shi.....


..
_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[8/28, 10:03 PM] Hafsaat💞: _BM_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 20_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___



*Hakika* anyi taron da kaf Nigeria ciki da wajen ta ba'a taba irin sa ba..Taro ne da ya zama lamba daya a tarihin tarukan najeriya..


Dubban mutane ne suka sheda nadin sarautar Alhaji Junaidu Muhammad a matsayin sarkin birnin Nukaa da ke karkashin jagorancin zuriyar Ardo kandemi..


Anci an sha... An raba kyautttuka da sandar girma ga masu sarauta. Haka zalika akwai wasu tarun kyauttukan ga bakin da suka halarci taron gaba daya. Baya ga zundumemiyar jaka ta rabo mai dauke da kayan makulashe aciki.


Cikin gidah ma anyi walima da saukar karatun alqurani mai girma. Bayan an nadashin ne kuma aka yi masa rakiya wajen Hajiyan su yaje ya gayshe ta tayi ta saka masa albarka.


Shi da sauran yan uwan sa da suke tare idan aka tsame Alhaji jalaludden da ya bar estate din tun ana sauran kwanaki ayi nadin sarautar...


Hadaddiyar liyafa ce mai dauke da samfurin abinci na gidah da ketare. Bayaga haka ga masu hoto kala kala da masu bada tsaro na farin kaya suma sun zagaye ciki da wajen gidan.


Atamfa ce wata maroon mai kwalliyar ratsin silver color.. itace wadda Gwaggon court ta kawo bandir bandir tasa aka rarraba yara da manya yan uwa mata kowa ya saka ta zama ankon bikin nadin sarauta.a matsayin tata gudunmuwar...


Amaal na zaune akan dressing mirror din dakin su ita kadai... Ta yi kyau tamkar babyn roba. Sanye cikin atamfa ta wajen Gwaggon court data fitar.


Ba wata kwalliya tayi ba amman kwarai matuka tayi kyau.. Atamfar ta amshi yanayin tsarin jikin ta... Samfurin A shape da ya sha stones.


Ta daura dankwali design din channel O ta yane kanta da mayafin daya amshi atamfar.


Hoda kadai ta shafa fara sai kwalli da man leben marar kala. Amman da ke labban nata pink ne sai man leben ya sa kalar su ta dada turuwa sai sheki suke.


Gefe daya mild turaren data shafa sai tashi yake dukkuwa da kasancewar sa marar karfi.


Lokaci zusa lokaci takan daga wayar dake hannun ta ta kalli screen har yanzu basu kira ta ba.


Wayar tace tayi kara da sauri ta dauka ganin mahaifiyar tache,


"Kina Ina ne Amaal?"


"Ina daki Hayateey.."


"Anata hotuna da abbieyn ku yana tanbayar Ina kike? Yan uwan ki sunce basu sani ba. Da kina nan kika tashi kika tafi tun dazu."


"Haka suka ce? Yaa Hindu ce tache mu zo sashen mu mu huta, Muna zuwa kuma mun zazzauna daya bayan daya sai suka tafi suka barni da ita tanata danna waya can ta mike wai tana zuwa zasu kirawo ni. Kar na kuskura wai na dawo wajen ku basanan ayi musu fada. Su fa nake ta jiran kiran su dama mugunta kenan suka shirya mun?"


Hajiya jamila ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kawai....Dan tashi tayi dama ta koma gefe take kiran wayar tata a waya...


Sanye take cikin atamfar da gwaggon court ta bayar a matsayin tata gudunmuwar. Amman sai ta dora dankarereriyar laffaya silver color akai ba kadan ba tayi kyau.


"Kina dakin naku yanzu?"


"Eh su nake ta jira fa ko calls dinsu kamar yadda Yaa Hindu tache."


Hajiya jamila ta yi murmushin dayafi kuka ciwo. Ganin dukkanin yaran gasunan sunata daukar hotuna kala kala da abbiey din na su mugunta suka hada mata ashe..


"Na zo ko Hayateey.?"


"Kizo.."


Tana katse kiran ta mike ta sauka... Ta nufi sashen da ake hidimar. Gashi da yar tazara a tsakanin su.


Sai sauri takeyi tanata dube dube ko zata hango wani ya taho a mota. Cikin ikon Allah kuwa sai ga Yayan ta Hamid cikin motar Hayateey .


Tana hanun sa ta tsaya tana murmushi. Yana tsayawa da motar ta bude ta shiga,


"Ina wuni Yaya?"


"Lafiya kalau sissy.... Yana ganki anan?"


"Hmm mugunta su Ya Hindu suka shirya mun. Sukace na zauna zasu kira ni ..Ashe karya suke trap ne. Sai yanzu Hayateey ta kirani tace Ina inane ? Nace mata Ina daki su ya Hindu nake jira su kira mu taho tare. Tache waye su hindun gasu can suna ta hoto da Abbiey. Yama tambayi Ina nake since basu sani ba. Sun dai ga na na tashi na fita tun dazu... Ya dace su mun wannan abun Yaya? Mena musu? " Magana take muryar ta na rawa saboda baki daya sun dagula mata lissafi.


"Kiyi hakuri.... Kinji lovely sis"


"Tohm Yayaa." Ta amsa shi hawayen data makale suka shiga zuba daga idanun ta


"Ki dena kuka please.... Precious hawayen sissy gida? Noo ki dena zubar mana dasu pls... Ungo tissue maza maza goge."


Karbar tissue din tayi ta shiga goge hawayen nata. Maganr sa ta bata dariya tayi murmushi mai sauri.


Daman haka yake son ya ga tayi daria. Don haka ya dan sake fadar wasu abubuwan da zasu sakata dariyar. Tayi dariya kamar yadda ya bukata,


"Yauwa ko kefa..."


"Nagode Yaya...."


Ya karasa da ita har cikin wajen taron.


"Kazo muje mana..."


"Munyi hotuna tun dazu a faada... Amma bara na miki rakiya."


"Yauwa."


Fitowa sukayi daga cikin motar zaka rantse Yaya da kanwa ne uwa daya uba daya saboda yadda suke tsananin kama..


Gashi yaci ado cikin wani arnen yadi silver color.. (Kalar toka) sai suka sake sajewa da atamfar jikin ta.


A haka suka jera suka shiga wajen bakunan su dauke da sallama. Haj jameelah na gano su ta saki murmushi.


Ta nufe su da sauri tana cewa,


"Yauwa... Ku zo a dauki hotunan ko?"


"Ai mun dauka a faada da shi"


"Banason musu Hamid... Na faaada daban wannan daban."


"Tuba nake ranki ya dade"


Dariya sukai baki daya su ukun. Kan maganar Hamid. Sika karasa inda sarki Junaid yake a tsaye masu hotuna nata faman aikin su....


Su Hindu tamkar su hadiye zuciya saboda bakin cikin ganin ta …


Sarki Junaidu na hango su ya fada’da murmushin sa… Ya saka hannu yana musu alamun su karaso fuskar sa kumshe da murmushi.


Amaal ta karasa kusa da shi , Ya janyo hamid gefen sa yayin da hajiya jamila ke gefen Amaal din. Sai suka bada wani style na daban.


Masu hoto suka fara baza musu hotuna ta ko'ina. Amaal ma ta daga wayar ta tayi musu harda vedio. Hamid ma ya karbi wayar Amaal din ya musu su uku. Sarki junaid da Amaal da hajiya jamila.


“Ranka ya dade ka tsaya haka. Yauwa hajiya ke dan dora kanki a kafadarsa. Yauwa kema kanwata koma tacan ki dora kan ki akan kafadar tasa. “ mai hoto ya basu style


Ai kuwa hakan sukayi ba karamin kyau hotunan sukai ba. Hajiya hadiza sai tsaki take jerawa


Data kasa rike hassadar ta sai ta mike ta mangaje me hotan ta wuce. Ya juya yana kallon ta. Saboda ga hanyoyi da zatabi Amman taki sedata mangaje shi tukun.


Haka dai aka cigaba da liyafa aka kare. Mutane suka fara watsewa … jirgi ya shiga jigilar mayar da nesa garuruwan su.


Wanda suke a gidah birnin nukaa kuma suka tattafi gidajen su. Yayinda wadanda suke a wasu kasashen suka tattafi airport.


KANDEM estate ta zama sai yan uwa da abokan arziki tsirari kawai.


Tunda suka fara hotuna har suka gama idanuwan sa akanta suke. Haka ta sake girma? Ya tanbayi zuciyar sa.


Kasa hak’uri yayi saboda BAKON yanayin da ya samu kansa aciki na so yayi mata magana.


Ai kuwa tana futa yabi bayanta da sauri yana kiran sunan ta,


“Amaal…”


Da sauri ta juya don ganin me kiran sunan nata. Hasken wutar kantarki ya haskaka ko'ina da gauraye…


Duk suka tsaya suna fuskantar juna. Gashi ya kafeta da idanu . Dakyar ta iya cewa,


.”Ina wuni? Yaya hisham.?”


“Lafiya kalau….. Kwana da yawa.”


Dan murmushi tayi kawai. Tana lankwasa hannuwan ta.


“Sai anjima” ta fada batare da ta sake cewa komai ba ta juya zata tafi,


Ya bu bayanta da sauri,


“Korata kike?”


“zanje na kwanta ne,. Akwai sch gobe.”


"Kina da waya?”


“Uhm… what about it?”


“Number ki zaki ban”


Tayi saurin girgiza kanta


,”Meyasa?”


"Saboda wayar karatu ce kawai bata amsa waya ba…An hana mu magana da maza"


“Ni ba yayan bane ba… ko kin manta?”


Ta kada kanta. Yayi murmushi ganin ya mata wayo ya sosa keyar sa yace,


“Ban number din to… zan zama online coach dinki, Duk abunda baki sani ba akan studies dinki don’t hesitate to ask me…”


“In shaa Allah”


“Fadi Ina jin ki…. Ga wayan dai”


Ya mika mata wayar tasa. Wallpaper din hotan sa ne agaban rigar tasa an saka hisham07


Ta shiga ta rubuta masa number ta mika masa. Yana karba tayi gaba da sauri har tana hadawa da gudu.


Shi dariya ma abun ya bashi… Ya kuma sake yabawa da nutsuwar ta sosai.


Ya girgiza kai kawai ya juya ya nufi sashen da aka sauke su…


::::::::::::::::::::::




Haka dai rayuwa ta cigaba da garawa.. Abubuwa na dad'i da akasin haka sun faffaru...


BAKON MUNAFIKI na cigaba da bibiyar zuriyar kandemi.


Gefe daya kuma su Amaal sun kammala makarantar secondary har sunyi jamb ma. Sun samu gurbin karatu a jami'ar.


ARDO K UNIVERSITY NUKAA (AUN)..




_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[8/30, 2:21 PM] Hafsaat💞: _BM_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 21_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___




*ARDO K UNIVERSITY NUKAA*
(A U N)


Tana zaune a kofar twin theater lecture hall dinsu da ke department din da take na architecture. Direba take jira yazo ya dauke ta don ta gama lectures dinta na ranar...


Shiru shiru lokaci yanata ja dai taga ya kamata ache yazo ya dauke ta. Don haka ta mike daga zaunen da take ta karkade rigar jikin ta samfarin doguwar riga kirar Egypt. Navy blue color data sha kawaatuwa da wasu duwatsu masu kyalkyali.


Ta yane kanta da mayafin rigar ba kadan ba tayi kyau .. gefen kafadar ta kuma jaka ce blue colo,r zip din ma a zuge yake sakamakon littafai da suka cika jakar da laptop. Ga handsout ta rike a hannun ta.


Ba kadan ba ta kara wani irin musulmin kyawu me tafiya da duk wanda ya daga idanun sa ya dora akan ta..


Ta sake zama cikakkiyar budurwa, kyawun ta ya dada karuwa. Jikin ta ya kara murmurewa da cika sosai.


Hakika dik wanda ya dora idanun sa akan ta ya janye sai ya kara dauka ya dora akanta a a karo na ba adadi saboda zatin halittar da Allah ya azurta ta da shi...


Takawa ta farayi zata fita daga cikin department din zuwa waje.... Malamin su ya futo daga cikin ofishin sa yanata sauri da alama fita zai yi shima


Ta dan ja baya ta bashi dama ya shige. Har ya wuce sai kuma ya juya ya kalleta...


"Ina wuno?" Ta gayshe shi kanta a gefe.


Tsayawa yayi.. Ya dan saci kallon ta... Yadda take lankwasa yatsun hannun ta da suka sha jan lalle da zanen baki ya masa kyau kwarai matuka.


Shima matashin saurayin malami ne da yake ji da kyau da kuma kambun ilimi.. sanye yake cikin riga da wando yan kanti da suka sake bayyana kyawun sa na fulanin usul.


"Lafiya kalau..... A department din ecology kike?" Ya tanbayeta kai kache dagaske yake..sarai yasan a department dinsu take student dinsa ce amma ya samu kansa da zolayar ta,


"A'a..." Ta amsa shi kanta a kasa dai bata dago ba.


"Wane department?"


"Anan department din"


"Architecture ko linguistic da yake baya?"


"Architecture.."


"Oh really...level nawa?"


"Level one na ke.."


"Ahh fresher.... Jambito... Jolly just come jjc"


Ita dai Amaal murmushi kawai tayi. Wanda ya sake sanya shi sake ce mata,


"Amma ai kun gama lectures ko?"


"Eh."


"Karatu kike baki tafi gidah ba?"


"Ina jiran azo dauka na ne..."


"Okay Allah sarki.... Kingane ni ?"


Ta gane shi sarai. Amman ta grigiza kai alamun a'ah.. Yayi mamaki sosai yace,


"Ni din?"


"Eh.."


"Lalle bakya shiga lectures.."


"Ina shiga"


"Amma baki sanni ba a Malaman ku? Ni me daukar 1301.... "


"Oh okay"


Ya sake satar kallon ta. Wannan karon ta daga kanta tana kallon daya bangaren. Wai shi da students mata ke tururuwar son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login