Showing 54001 words to 57000 words out of 95238 words

Chapter 19 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt

04 Jan 2025

6680

suke nuni da madaukakin mamakin da ya shiga... Fuskar sa ta bayyana wani yanayi mai wuyar fassarawa..


Ji yake garin yayi tsit... Wani duumm cikin kunnen sa tamkar an dauke masa jin sa... Gashi dukkanin su sunyi shiru suna bin sa da kallon karin bayani..


Labbansa sunyi masa nauyi... Ya kasa cewa komai.. Alhaji Muhammadu ya duba fuskar agogon dake daure a hannun sa ya sake cewa da shi,


"Adamu lokaci yana kurewa fa..... Ka sanya dik inda aka kai yarinyar nan aje a dakkota a dawo da ita gaban iyayen ta cikin lafiya tamkar yadda aka dauke ta....."


Kawu Adamu ya daga kansa dakyar ya sauke a gefen Alhaji Muhammad... Ya kasa yadda su hada idanu.. Cikin dakewar murya yace,


"Yaya.. Bansan me kake nufi ba... Bani da masaniyar inda Amaal take.. Ko dai rashin lafiyar ta kace ta dawo? Ni ne fa Adamun ka. Ni ne fa"


Alhaji Muhammad ya girgiza kai cike da takaicin kalaman Kawu Adamu ya ce da shi,


"Banason waiwayo da hannun agogo baya.... Banason bayyana abubuwan da suka riga suka shude. Kai da mahaliccin ka...Badan batan yarinyar nan bama bazan taba bude baki nace gashi gashi ba har sai su da kansu sun gano BAKON MUNAFIKIn da ke dabaibaye da su. Yanzu maganar Maryaam akeyi.... Idan ba zaka sa Wanda suka dauke ta ba su dawo da ita ba to mu anan sai a sanya wasu suje inda aka kaitan su dakkota."


Kawu Adamu ya sake fuzgewa yache,


"Jalaludden 'dan wajen ka shine BAKON MUNAFIKIn.... Ba ni kani agare ka ba kake tozarta ni agaban 'yaya da jikoki... Ku tuhume shi ya fito muku da ita ni bani acikin lefin da ake qalaamun... A zuriyar ka ne... Ku dai sake bincikawa."


Ya mike ya tashi... Alhaji Muhammad shima ya tashi ya taaka har inda Kawu Adamu yake ya dafa kafadar sa..


Alhaji jalaludden shima ya mike daga inda yake zaunen yace,


"Babaa wallahi Allah ni ba ni ne MUNAFIKIn nan da aketa ikirari ba... Dukkanin komai ni ma gayamun akeyi, duk abunda na aikata ko na faada cikin fushi da rashin sani ba yin kai na bane, Wayar da Al-mustapha ya kawo ma last week aka aiko da ita anonymously..Duk set-up ne ga abunda ya biyo baya..." Ya karasa fada yana dafe goshin sa .


Alhaji Muhammd ya daga masa hannu alamar ya dakata yayi shiru .... Ya juya yana fuskantar Kawu Adamu daya tsaya bai juyo ba,


"Adamu magana nake maka fa...."


Kawu Adamu ya doke hannun Alhaji Muhammd cikin fushi yace,


"Nayi... Ni Adamu ni ne nan tare da masu tayani aiki na muke aiwatar da komai... Yes ni nan na yi maka asiri a zuciyar ka da akayi maka kaho shekarun baya... Ni ne nan na biya Dr. Nogan makudan kudi lokacin da muka dawo da kai daga kasar waje... Nayiyyi yadda zanyi kar ka dawo ka dawo domin na samu muradi na sai da ka dawo... Asiri ya sake hawa kanka akayi asibitin Dr. Nogan muka shirya komai da shi tun a waya... Aka dawo da kai gidah... Ni Adamu ni ne nan na saka aka aiko da allurorin da akeyi maka na dakushewar ka gaba daya ...haka zalika ruwan da ake dura maka kuma yake lalata dik wasu rassa na jikin ka lungu da sako...


"Kawu.... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun " sarki Junaid ya ambata yana zubar da hawaye..


"Baa nan kadai na tsaya ba .... Ni ne nan dagaske nake bin diddigin kafatanun zuriyar ka don ganin na lalata ku gaba daya na dedeta ku... Duka 'yayan ka da iyalan su ni ne nan BAKON MUNAFIKIn da ke bibiyar su, Ina cin dundunoyar su ina tura musu sakonni Ina jan raayin su... Nayi amfani da jalaludden ne saboda shi din yanada karanchin hankali a cikin su .. yanada hawa doron zuciya Kuma da wuri yake daukar zugar da akeyi... Tabbas alkali bakai karya ba ... Kiyayyar da nake maka tun muna kanana tana nan ba inda taje.... Dukkanin komai ni Adamu ni ne nan nake juyashi a tafun hannu na... Haka zalika ni na saka aka dauke Amaal saboda junaidu na kaunarta gashi akanta ya ajiye sarautar sa..... Kasan meyasa Alkali?"


Alhaji Muhammd ya girgiza kansa yana zubar da hawaye,


"Saboda har yanzu na tsane ka... Kiyayyar ka hauhawa take a birnin zuciya ta kullum... Ka fini komai a rayuwa, arziki, martaba, ilimi, soyayyar iyaye... Komai ka kere ni...Na meye ba zaka kyale ka barni na karbi ragamar mulkin Nukaa ba?.... Har ache tunda kai din bakada lafiya abani mana, Amman aka tsame ni aka dakko daya daga cikin zuriyar ka aka nad'ashi... Kowa da komai a bangaren ka yake.. ni kenan kullum a tsiyace ina binka na zama jela.......??






Ayi hakuri da wannan shafin...๐Ÿ™




_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ‘‚๐Ÿผ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ๐Ÿ”ฅ




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR โ€˜KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at๐Ÿ‘‡


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐Ÿ‘‡


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐Ÿ‘‡
09033181070


VIP๐Ÿ”ฅ๐Ÿ’ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*๐Ÿฅฐ


Zafafa๐Ÿซถ๐Ÿ”ฅ
[9/16, 7:33 PM] Hafsaat๐Ÿ’ž: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 35_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___







**Alhaji Muhammd ya girgiza kansa cike da rashin jin dadin zantukan da dan uwan nasa yake ta yi yache,


"Meye alfanun hakan da kakeyi Adamu? Wacce riba ka samu?"


Kawu Adamu ya juya ya fuskance shi sosai... Ya daga hannu yana nuni da iyalan Alhaji Muhammad daya bayan daya,


"Dole ka tambaye ni me cece ribar da na samu... Wato kai saboda Allah ya buda maka kofofin arzika yaran ka da jikokin ka duk sun zama wani abu a rayuwa ko.... Daga wanda ya rike mukamin minister, Sai na Ambassador (jakada) sai likita, da farfesa, gefe daya ga alkali ta court ga babban dan kasuwa.... Jikokin ka suma duk sun taada kai kudi ya zauna... Ka kwanta akan dukiya kana ci... Duka bayan wadannan tarun kadarorin da kake da su kuma ache sarautar ma kai aka zaba za'a bawa.. don masifa da bala'i ma ba zaka iya rike wa bama aka dauki daya daga cikin yaran naka aka bashi. Wato dole a komai dai ni ne koma baya.. "


"Allah ubangiji ya shirye ka Adamu Allah ya sanya maka nutsuwa da kwanciyar hankali a zuciyar ka. Ya biya maka dukkanin buka


"Rufemun baki.. Algungumi!! Wallahi wallahi na so naga bayan zuriyar ka gaba daya... Na so 'dai'daita ku na hanaku sukunin zaman duniya... Na so na zama ajalin ka ta hangar wulakantacciyar mutuwar da zan sa kayi. Namun jeji su dinga yagarka sala sala..


"Kawu dan Allah ya isa haka" Cewar Alhaji Nuraddeen


Kawu Adamu ya juya ya kalle shi yana yamutsa fuska,


"Matsiyata... Ko bayan rai na sai duniya ta juya muku baya... Dukkan ku nan dukan ku nayi ALLAH wadaida ku.",


"Assalamu alaikum wa rahmatu Allah..." Bappah Hasan, Bappah Husain, Bappah Maher suka shiga cikin parlorn bakunan su dauke da sallama


"Tun daga waje can ake jiyo kakarun muryar ka.. mun dakata mun saurari abubuwan da kake fada baki daya Adamu... Ashe mai hali baya fasa halin sa? Ashe shirun da kayi na shekaru daman akwai kulalliyar da kake kullawa?..." Cewar bappah Maher, cikin fushi ..


"Gaskia Adamu ka bamu mamaki wallahi... Yau da ache samu na a kayi aka sanar mun ba lalle na aminche ba. Amma da kunne na na jiyo abubuwan da ka kake fada..Adamu wacce iriyar musiba ka tsoma kan kan aciki? " Bappah Husain ya faada cikin muryar Allah wadai..


"Fiye da hakama Adamu zeyi... Na sha sheda muku ku sake shiga tsakanin sa da danwuwan sa. Wallahi har yanzu ba kaunar sa yake ba kuke cewa baya ta wuce wannan harda kananun shekaru da sauran su... Mutum mugu ice ne.. wani me halayyar baya sauyawa.. Adamu idan da akwai fuska dari ma itache dashi.. BAKON MUNAFIKI ne wanda BANA MUTUM DAYA BANE... Zagaye yayi tayi cikin iyalan Muhammad sai da ya tabbatar ya cinma galaba akan su, Ya chusa kansa sun aminta da shi dari bisa dari tukun sannan.." Bappah Usayn ya karasa fada yana girgiza kai..


Kawu Adamu sai hura hanci yake yana muzurai irin ba wani shege dinnan.. bappah Maher ya sake duban sa yaja dogon tsaki yace,


"Wani abun takaicin ma.. ache bai zauna da zuciya daya da yaran Muhammad ba.. yajasu ajiki ya nuna nusu yana kaunar su yana yi da su . Ya rungume su ajiki sosai ya maye musu gurbin rashin mahafin su dake kwance ba lafiya tun shekarun baya .. nayi tir da halaye irin naka adamu.tir da halayen ka. Ko azamanin jahiliya banajin akwai wanda yayi kwatankwacin abubuwan da ka yiyyi kake kan yi ma.... Kaga kalle ni nan yanzu zan dauke ka da mari maras mutincj maras imani.. wallahi munyi ALLAH wadai da samun irin ka a zuriyar ardo kandemi . Walahi kaf zuriyar mu babu mai irin halayen Ka."


Kawu Adamu ya sake yamutsa fuska yana kobare kafada cikin gadara yace,


"Daman ai ku na dade da ganowa bakwa kaunata.. Kune masu kushe ni a duk sanda yan kwamitin sarki zasu ce wa za bawa rikon kwarya..kunfi haba habaa da Muhammd saboda shi yanada kudi... Yanada tarin dukiya da yake sammuku. Domin kudin kaji ne sai da tsaba. S....


Bappah Maher bai bari Kawu Adamu ya karasa magana ba yadaga hannu ya zabga masa mari.. ya sake daga hannu ya sharara masa a a daya kuncin sa.. hannun sa da jikin sa suka hau rawa yana nuna Kawu Adamu yace,


"Kunji dan iskan yaron nan ko? Ku ku ka haife mu ko mu muka haife ku da zaka tsaya kana gaya mun wadannan maganganun? Idan baka sani ba ka sani yau... Mu ke kokarin fado halayen ka masu kyau muna fadawa kwamitin sarki... Kaf kandemi kowa hakuri yake da halayen ka.. an gaya maka labari bai zo mana ba kana sayar da hatsin masarauta? Ko kuwa dokuna takwas rannan da aka wayi gari babu su ba kai bane? Komai yana dawo mana kunnuwan mu... Ga securities can awaje an gama interrogating dinsu zamu sbjgo muna jiyowa suna cewa kai ne ka biya su kudi da safe kache su bar sashen gaba daya baki na alfarma zasu wuce da dakarun su na presidency don haka an basu awa uku suje su huta... Saboda zaka saka a sace Amaal? Saboda haka ka shiga taitayin ka.. sanyi nayi wallahi. Ka tanbayi wanene maheeru kandemi zaa gaya maka sanda nayi tashen samartaka ta ma ca ake mun mutum me karfin mutane hudu da rabin mutum.. doki bakayi nauyin banza ba.. 'bab'balla mutane nake idan akayi mun shirme... Don haka Ina Amaal?


"Assalamu alimumm sir my apologies.. ga cctv footage din wajen garden din anciro...", Wani maaikaci ya shiga parlorn ya bada wani harddisk ya fita...


"Ina Amaal nache?" Bappah maheer ya sake dakawa Kawu Adamu tsawa


"Tana tsaunin zagayen makarantar mata dake karshen lungun wadawa na unguwar balbelu...."๐Ÿ˜ญ


"Kaji bakin mugun ko? Kunji unguwar da take ma? Kai Adamu bakada Imani. Wallahi wallahi baka da Imani. Makarangar matan da ke unguwar balbelu din tun yaushe gwamnati ma tache a dena amfani da makarantar saboda miyagun da ake tunanin suna bibiyar ta da yn shaye-shaye.... " Bappah maheer ya fada yana girgiza kai cike da takaicin Adamun


"Gaskia na kara tabbatarwa ba Allah a ranka... Allah ubangiji ya kyauta.. ka guji bakin duniya. Adduar Wanda aka zalunta wallahi batada hijabi da Allah . Yarinyar nan hakin ta na cutar da ita da kayi wallahi Allah ba zai taba barin kaba.." bappah usayni ya fada yana girgiza kai.


"Nima Kuna nuna mun kiyayya ai... Daman tinda nazo doron duniya nasan bakwa kaunata.. Don haka maganganun ku basa damuna... " Ya kasa kai zai fuce. Dss din sake tsaron kofar sika sake bude kafafun su.


Bappah maheer ya kira sunan sa da karfi,


"Ba magana ake maka ba ne... Wallahi Ina mai tabbatar maka idan aka dakko yarinyar nan akaga an mata wani abun na illa na rantse da kadaitar ubangiji Adamu sai kayi dana sanin samuwar kanka a zuriyar kandemi .."


Kawu Adamu yayi murmushi... Ya nemi gefen stand na tv ya zauna, Cikin muryar ko ajikina dinnan yache,


"Ko kanada masaniyar tsananin kiyayyar da kuke nuna mun che yasa dukkanin ku kuma nabi na toshe wasu ababen farin cikin ... ku kuka fara kamar yadda kuke da hannu a hanewar sarautar da nake da gadon ta .. Bappah maheer ko ka tuno wata kwangila ta mambila da zaka samu miliyoyi kanata murna daga baya aka hanaka aka bawa aminin ka? Ni ne silar hanaka.. Bappah usayni Ina gidajen da akace gwanmati ta bawa ku tsofaffin maaikata Kai da abokan aikin ka gidajen Ikeja da ke Lagos? Ai kaga daga baya aka cure sunan ka aka kore kama ma daga masu karban pension... Bakowa bane sila ni ne nan.. Bappah Hassan aikin da zakaje embassy na Ecuador bakowa bane ya hana asa maka hannu a takardar tafiyar fache ni... Wadannan kadan ne daga cikin abubuwan danayi na ramako akan muguntar da kuma kuka mun kuke kan yi mun..."


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Adamu! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Daman ance makashin ka na g* ka . Allah ubangiji ya kyauta.. "


"Kwarai kuwa... Rama cuta ce ga macuci... Kunmin na muku... Da da ran iyayen mu duk haka ba zata faru ba... ai kamar jalaludden ne... Dana dinga amfani da na'ura mai kimiyya Ina sanya nasa kiyayyar dan uwan sa a ransa.. Baya kaunar sarauta amman na dage na dinga tura masa sakonni masu jan raayi har ya amince.. da niyyar sanya zazzafar kiyayyar idan tayi tasiri ku kwamktin saka sarki zakuu tsaidani a sarautar kujerar Nukaa amman kuka ki.. Da hanyoyi na bi na saka aka saka hannu akayi stamp amatsayin junaidu ne yasa aka zartar aka hana jalaludden babban mukamin da yakeso na matemakin shugaban kasa... Tun daga nan na fara saka kiyayya a tsakanin su.. Na kuma koma kan junaidu shima, Na sanya aka kara masa wa'adi aka ki dawo da shi Nigeria, Ina kuma tura masa sakonni masu tsoratarwar amman shi ban gama nuna masa jalaludden bane sai dana bari ya dawo Nukaa gaba daya. alokacin dana saka aka dauke yaran sa acan kasar na awanni nayi hakane da...


"Dakata hakanan Adamu na tabbatar kai din BAKON MUNAFIKI ne Kai din Kuma BANA MUTUM DAYA BANE... Kana bin kowa na cikin mu kana cin dudduniyar sa kana kuma saka kiyayyar juna a tsakanin yan uwa.. Dan uwan ka ma baka barshi ba da kuka fito ciki daya ballantana mu da kuma yayan yan uwan ka.. "


"Kwarai.. ko matan gasunan ni ke raba kansu dik dan su bujire junaidu kar ya waiwayo kasar ma amman ya dawo. Ban kuma dena dinba na cigaba fiye da abaya ma.. " yakara sa fada yana nuni da su Hajiya Hadiza


"Musanman ke da ke bada gundunmuwa sosai... Duk da dai tun kafin na fara turo sakonni dama can bakya kaunar jamila..kuma kin amince a salwantar da rayuwar Amaal din.. junaidu ko ka tuno sanda kake gaya mana ka bawa Hamid gashinan ragamar asusun bankin kandemi? ... A ranar na kara tabbatarwa da sai na illata zuriyar ka da mafi soyuwar abunda ke ranka tunda naga alama ka bada himma sosai kana kuma kaunar abunda nake muradin son samu.."


"Ya isa dakata.... Illa ce kayiwa kowannen mu kai da Allah mahallicin ka. Yanzu dai muje a dakko yarinyar nan daga nan Kuma sai a yanke maka hukunci dai dai da Kai" bappah maheer ya fada hadi da saka hannu ya janyo Kawu Adamu da karfi ya tura shi awajen kofar fita, ya dubi yan parlorn yace,


"Ina masu motoci a kusa? Muje ko"


Al-mustapha ya tashi da sauri .... Hakama Aayan daya mike shima ya bi bayan Bappah maheer. Sai sauran bappanin na su suka dunguma sukai waje. Hamid da Hajiya jamila ma wajen sukai. Ta shiga gaban motar hamid da sauri..


Motoci suka shisshiga aka chusa keyar Kawu Adamu agaban mota. Suka tafu a jere kusan motoci bakwai suka dauki titi, A convoy zuwa inda amaal take a boye....


Parlor ya zama sai Hajiya Maryam da Alhaji Alkali Muhamamd da su Bappah Abdullahi, Haj Aisha matar Alhaji Abubakhar mahaifin Hisham, da Hisham din kansa, da su Hajiya hadiza daketa raba idanu musanman datasan ta bada gudunmuwa na kason lefi a dauke Amaal... Sai jimami suke... Tu'ajjabin maganganun da Kawu Adamu ya fayyace ya bayyana a fuskokin su cike da dimbin tarin mamaki marar misaltuwa..



============


Har bakin kofar makarantar suka faffaka motocin... Kallo daya zakai wa makarantar ka tabbatar ta zama fankoo (unwanted building) Ga juji nan a gefe an mayar da wajen reshen zuba shara...






_ADVERT๐Ÿ‘‡_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login