Showing 6001 words to 9000 words out of 95238 words
Chapter 3 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt
gashi a zaune na Dr abubakhr ne..
"Duk wani Hisham da kuka gani na gidan mai hotel da sauran su duk na de abubakhar ne yayi masa laqabi da sunan dan sa Hisham, kamar su: Hisham airlines,Hisham travel and tours, Hisham palace, Hisham showroom, Hisham plaza, Hisham oil and gas ltd, Al'Hisham international university., Hisham mart, Hisham luxury. Wadannan kadan kenan daga mallakin tarin kadarorin abubakhr. Babban oil mogul ne na kasar nan. Duk samda zamuzo Nigeria idan kukaga nasa an fita da motoci an musu full tanks to shine yasa lalle na'aika a dibamun mai kyauta... Kadan kenan daga cikin temammakin da yake yi ko ince ya saba yi ya ke kuma kan yi...Na roke ku da duk wanda yayi sallah ko yake addua ya dinga kamo sunan bawan Allah nan yana masa addua. Yana kuma rokon Allah daya kara kareshi ya azurta shi ya biya masa dukkanin bukatunnsa ya kuma yaye masa damuwar sa da lefukan sa. Allah ya saka masa da alkhairi ya jikan mabaifa."
Baki daya parlorn suka shiga amsa addu'oin amb junaid.
Haka dai suka karasa yar hirar dasike yi. Kafin akai su babban masaukin baki da aka tanadar acikin gidan dake dauke da komai na more rayuwar yau da kullum. Komai yaji babuce kawai babu agidan nan.
Amaal waje daya suke da mahaifiyar ta, daki ne yana kallon daki. Bayan tayi wanka a bandakin dake cikin dakinn ta zura babban hijabin dake ajiye akan sallaya ta zura kayan bacci aciki.
"Hayateey bara naje wajen Abbiey."
"Toh."
Fita tayi daga dakin ta nufi dakin da taga an shigar da akwatin mahaifin nata aciki.
Kwankwasa kofar tayi tana daga tsaye a bakin kofar ta waje,
"Shigo..." Ya amsa ta daga cikin dakin
Ta murda kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama.
Yana daga zaune akan wata kujera. Gaban sa kuma laptop ce yana aiki acikin ta. Daga kai yayi ya kalleta yana murmushi
"Hajiyata"
"Naam Abbiey... Barkan ka da dare"
"Barkan mu dai uwata ta kai na
"
Karasa shiga tayi. Ta zube daga dan nesa da shi tana mai aika gaisuwar ta agare shi chike da biyayya,
" Abbiey barka da dare,"
"Me sunan yan gayu... Uwata tafi ta kowa."
Nan ma murmushin tayi. Tana mai hada yatsunta wajen lankwasa su cike da maduakakiyar kunya.
"Menene uwata ?"
Nan ma.shirun tayi tana murmushi.
Ya ajiye wayar sa da ke hannun sa yana nazartar ta sosai,
"Ina jin ki..."
"Abbiey dama... Dama ... "
"Ina jin ki Hajiya ta"
,"Dama zuwa nayi wajen ka na nemi gafara abisa lefin da nayi maka ,"
Ya danyi tattausan murmushi kawai yana girgiza kai,
"Uwata ai bata lefi...... Tashi kije na yafe miki duniya da lahira duk kuwa da ban rike ki da komai ba. Da lefin da kikai da lefukan baya da ki kai dama wadanda zaki agaba. Duka na yafe miki. Allah ya miki albarka..."
Murda kofar dakin akayi aka shigo. Hajiya hadiza ce. Tana tafe da kayanta samfarin riga da skirt da daurin ture kaga tsiya
Ta dubi Amaal shekeke tana yamutsa fuska,
"Hmm an turo ki ki kasa ki tsare kenan , Kai gaskia baki saar gyatuma ba. To kije ki gaya mata idan ta isa tazo nan ba wai ta turo ki ba. ... Tashi ki fita kema chan daya munafuka,"
"Meye haka hadiza?" Cewar amb. J. yana binta da kallon bata kyauta da abunda tayi ba.
"To ai gaskia ne. Naga ba kwanan ta bane. Na wane dalili ne zata turo yar ta kawai don ta zo ta h..."
"Ya isa haka Hadiza. Ba girman ki bane."
"To tashi ta fita. Ko na fadi abunda zai fi karfin sauraron ta wallahi."
Girgiza kai kawai yayi cike da takaicin ta dama kalaman ta marasa kan gado. Ya dubi Amaal dake tsakure duk ta dubibice tanata harde yan yatsunta na hannu yace da ita,
"Je ki ki kwanta uwata... Allah ya tashe mu lafiya. Ya kuma yafe mana baki daya Amin. Ki kwanta ki huta kinji ko?"
"Tohm abbiey."
"Ki saki ranki ki sawa zuciyar ki nutsuwa kinji? "
"Tohm abbiey." Ta bashi amsa tana kokarin murda kofar zata fita
Ya sake cewa da ita,
"Sai da safe. Baki mun komai ba kinji? Allah ya mana afuwa gaba daya Amin. Kar a manta da adduoin bacci kinji ko?"
"Tohm abbiey in shaa Allah. Sai da safe." Tayi saurin fita ta rufe kofar. Sakamakon wasu zafafan harara da hadiza ke aika mata .
Amaal na fita daga cikin dakin ta sauke ajiyar zuciya. Hadi da saka hannu ta dafe kirjin ta dake bugawa tamkar zai fado a kasa saboda tsananin tashin hankalin data shiga...
Samun kanta tayi da fita ta kofar da zata sadaaka da waje.. saboda gumin tsoron da ke zurara daga idanun ta . Wani kayataccen garden mai dauke da fitilu masu matukar kyau da kayatarwa da ke kallon kofar ta shiga
Tamkar tsakar rana saboda yadda hasken fitilu daban daban suka dallare wajen. Ta sanya hannun ta tana shafa fulawawwakin da ke shuke cikin wani gini me basu ruwa.
Ta sake sauke zuciya a karo na ba adadi alokacin da ta tuno mugayen kallon da hadiza ta rika jefa mata. Ta samu kanta da girgiza kai kawai can kasan maqoshi don ita ta dauka a zuci ma tayi tace
"Allah ya kyauta...."
"Amin... Ya kyauta abunda yafu haka ma.."
Da sauri sauran kadan ta saki fitsarin tsoro dubada tasan ita kadai ce awajen gashi dare ne. Uwa uba a zuciya take tunanin tayi maganar kawai taji murya da ta amsata daga bayan ta.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Ta fada da dan karfin ta." Hadi da sake bude baki zata saki zundumemiyar kara yayi saurin zuwa gaban ta, Hadi da saka tattausan hannun sa ya toshe mata baki...
Ya rankwafa har saitin fuskar ta yana bin zara zaren gashin idanun ta da kallo,
"Calm down...Matsoraciya ce ke dama? Meya kwan kiyi addua sai kara da zaki saki? A daren nan kusan kowa yayi bacci meya fito da ke ma?"
Tanata girgiza masa kai. Sam ya manta ya toshe mata baki da tafun hannun sa. Ya nata mata magana shiru
Data gaji ta saka hakora ta gartsana masa cizo ya saki hannun dakyar yana yarfe shi hade da runtse idanun sa.
"Akan wane dalili zaki cijeni?"
"Bakinta ka rufe mana..."
Ya juya ya dankara mata harara yana mulmula wajen da ta cije shi.
"Lefuka biyu kika mun...." Ya fada yana hura iska awajen data gartsana masa cizo
"Ba abunda na maka.." tafada tana tafiya hanyar fita zata gudu ya sha gaban ta da sauri
"A Madina kika zuba mun milkshake a jiki na... Yanzu kuma kin cije ni. "
"Duka ba da gangan nayi ba. Allah ya baka hakuri" magana take tana turo baki gaba saboda tsabar shagwaba ta autanci
"Zo ki dressing mun cizon nan da kika mun. Da hakoran ki kaman na vampire "
"Ka samu babba yamaka...ni ba muharramar ka bace." Ta fada tana tuna kashedin da Hayateey ke mata shekarun baya na karta bari namii ya taba ko da hannun ta ne zata haihu.
Dariya abun ya bashi gege daya kuma ya yaba da hankalin ta,
"Shekarun ki nawa?"
"I'm clocking sixteen...."
"Sha shida?" Ya sake tanbayar ta cike da madaukakin mamaki.
"Eh"
"Ashe ke girman finkaso ce da su buredi?"
'tubarkAllah..."
Ta tabe baki Hadi da ketarewa ta bayan sa ta fuce da sauri har tana tuntube tayi cikin masaukin su..
Ta shedawa Hayateey dinta dukkanin abinda ya faru da take wajen Abbiey dinsu dama lekawarta garden inda Hisham ya sameta
Mahaifiyar tata ta sake jan kunnenta sosai game da ilimin rayuwa. Sun dan jima suna yan hirarrakun su, Kafin daga bisani kuma subi lafiyar gadajen dakunan nasu bayan sunyi tsarki...
×××
Kwanakin su biyu a burnin Abuja dakyar amb ya amince suka kwan biyun ma saboda yadda aminin na sa ya dinga rokon sa dan Allah su sake kwana
Ai kwa suna cike kwanaki biyun suka biyi jirgin safe daga babban birnin Nigeria wato Abuja zuwa ga garin NUKAA.. wato NUKAA STATE dake nahiyar kasar Nigeria...
Motoci da masu tsaro ne suka je suka dakko su daga filin jirgi zuwa babbar unguwar datafi kowace unguwa tsadar rayuwa da manyan masu kudi .
A cikin unguwar katafaren babban gidan. Ko ince girman gidan kusan yankin wani kauyen.. Anan hamshakin gidan yake.
Gidah ne na yan uwa masu zumunci dai dai misali.. Wanda suka ta-da kai suka koma koshi da kudi... Ana damawa da su a nahiyoyi da ketare.
Babban gidah ne na yan uwan da suka hada manyan maaikatan gwamnati, manyan yan siyasa, alkalai na kotu, frofesoshi na jami'u, manyan malami na sunna da dai sauran su.
Estate daya ce me kama da gari guda ko karamin kauye saboda tsananin girman ta. Kudi yayi kuka agidan nan domun ya hada komai idan aka cire babu da dangin ta.
×× A tare motocin da sukayi convoy suka shiga cikin babban jijjigaggen gate din dake dauke da gidaje masu matukar kyau da tsada. Ciki harda islamiya, computer school , gym, garden, swimming pool da dai sauran abubuwan more rayuwa na yau da kullum...kaf birnin NUKAA ko na cikin kauyuka sunsan attajirar zuriyar KANDEM...
*KANDEM ESTATE......*
Babban gidah ne na zuri'ar yan uwa da suka kunshi rassa......
--------
_ANAN NA KAWO SHAFUKAN KYAUTA NA WANNAN LITTAFI MAI SUNA A SAMA.._
_KU ZO A DAMA DAKU CIKIN TAFIYAR ZAFAFA BIYAR AKAN KUDI MAI RAHUSA.. AKWAI DARUSSA SOSAI NA QARUWA ACIKI..._
_LITTAFIN BAKON MUNAFIKI YAZO DA WANI SALO NA DABAN..._
_YA ZATA KAYA NE A KANDEM ESTATE? SHIN WACECE KO WANENE BAKON MUNAFIKIN ACIKI?_
_YA RAYUWAR AMAAL ZATA KASANCE???WACCE CAKWAKIYA CHE ZATA CHUDE TA?_
_AMB JUNAID MAGIDANCI NE MAI MATA UKU DA TARIN YARA CIKI HARDA AGOLA DA YAKE RIKO..._
_TUKUNNA MA ME KANDEM ESTATE DIN TA KE CIKI NE? GA TARIN ZURI'AH DA SUKA HADU WAJE DAYA? ZUMUNCHIN ZAI TARWATSE NE KO KUWA MATSALOLIN CIKIN SA NE ZASU WARWARE ZUMUNTAR TA SAKE QULLUWA?_
_KADA KU MANTA AMAAL A SHAFUKAN KYAUTA TANA YARINYA YAR SHEKARU SHA SHIDA..YA ZATA KAYA IDAN TA SAKE GIRMA? MENENE ZAI KUNNO KAI KUMA....?_
_GEFE DAYA KUMA GA HISHAAM KYAKKYAWAN MATASHIN MATUKIN JIRGI MAI JINI A JIKA, WANDA YA TASO CIKIN DUKIYA YA BAWA KADARORI BAYA..._
_AAYAN, AL-MUSDHAFA, HAMID/HABIBI TALBA ..RIGIJI GABJIN FA KENAN TO SU KUMA WADANNAN DIN SU WAYE🙊???_
_DANKARI MAKARI...AKWAI KASURGUMAR CHAKWAKIYA MAI LULLUBE DA TARKO NA ZUMUNTA....._
_DUKA DUKA AMSOSHIN TAMBAYOYIN DAMA WADANDA BAN LISSAFO BA ZASU ZO MUKU NE CIKIN LITTAFIN NA:_
_BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_
..
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[8/7, 7:06 PM] Hafsaat💞: _*BAKON MUNAFIKI!!!*_
_(BA NA MUTUM DAYA BANE)_
_👺🏡👩👩👦👦_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_©️ZAFAFA BIYAR WRITERS_
_®️NANA HAFSATU (MSS XOXO)_
__AREWABOOKS:MSSXOXO_
_WATTPAD:MISSXOXO00_
_PAID PAGE:06_
*KANDEM ESTATE*
Babban gidah ne da ke dauke da jimillar yan uwa wanda suka hadu waje daya suka zama tsintsiya madaurin ki daya.
Dukkanin wanda ke a birnin Nukaa ya san da ahalin zuri'ar kandem. Fulani ne na usul. Tarihi ya bayyana cewa tsatson ahalin zuri'ar kandem sune suka kafa garin Nukaa..
Domin a shekaru masu tarin shudewa ance ahalin nasu ne suka taho suka yanki jeji suka baza dabbobin su. Suke kuma sassake bishiyu suna yin itache dasu suna hada wuta suna zama abakin ta. Shanuwa suke tatsa suna sha shine abincin su....
Ance kakan kakan kakan su wato Ardo kandemi..... Bayan zuwan hausawa da basu iya fayyace sunan ba saboda harshen fulatanci ne a hausan ce sai suke cewa da shi 'Ado Kandem...' a haka kuma sunan ya zamo ya tumbatsa har ya zama cibiyar kasuwanci. Allah ya sanyawa yankin albarka ake ce da gurbin kasuwar kandem...
Bayan sun hayayyafa sun tara iyalai masu tarin yawa. Sai ya zamto sun mamaye ilahirin yankin da gaurayen sa. Sai ake kiran wajen yankin kandem...
Daga nan bayan samuwar yanci da zaman lafiya ya yawaita sai aka basu masarautar garin baki daya tunda su suka samar da yankin ake cewa da wajen garin kandem..
Daga nan bayan mulkin damokaradiyya sai ya zamto an yarje musu. Kasa ma ta san da birnin sosai. Ya zamto shine cibiyar kasuwanci ta kasar baki daya.
Ardo kandemi wato kakan kakan kakannin usulin dangin ya zamto yana da matan sa na aure biyu. Akwai yafendo asalin sunan ta 'Nusaibatu.' Sai Yagwalgwal ita kuma usul din sunan ta 'Kausar'...
Alokacin da kasar ta samu yancin kanta ... A baya lokacin mulkin sojoji kenan, Sai wanda yake a matsayin shine shugaban sojojin da ke mulkar kasar sai ya zamto ya sanyawa yankin kandem suna. Da farkon sunayen matan Ardo, wato Nusaibatu da Kausar... Ya yi masa laqabi da birnin 'NUKAA'
Masarautar kuma sai ake cewa da ita masautar kandem... Wanda zuriyar Ardo kandemi ke karagar mulki suna mulkar garin...
To a hakane cikin ikon Allah da buwayar sa da hikimar sa zuri'ar marigayi Ardo kandemi ta tumbatsa tayi reshe tayi ya'ya da jikoki da tattaba kunne da uhumhum masu tarin yawa da albarka ..
Har ya zuwa lokacin da Nigeria ta karbi yancin kai ta nada Lagos a matsayin babbar birnin ta ya zuwa sanda akalar komai ta koma birnin Abuja...
Zuri'ar Ardo kandem ta wuce duk inda ake tunani. Sun zama reshe da ko'ina yayi ya'ya. Duk wani bangaren alkalanci na kotu, likitanci, injiniiyoyi, frofesosi, masu aikin gidan jarida da na tv, gidajen rediyo, Yan siyasa, hakimai da sarakai da dakatai, Yan kasuwa , jakadun Nigeria dake sauran kasashe... Kai da duk ma wani babban mukami na gidah dana waje idan aka duba kashi chassa'in cikin dari zuri'ar Ardo kandem ne. Allah ya sanya musu tarin albarka da dimbin nasibi mai tarin alkhairai...
Wasun su na zama ne a kasashen waje, wasun su na wasu garuruwan, wasu na wadansu anguwoyin acikin garin Nukaa din wadanda aure ya sauya musu wajajen zama. Ma'ana mafi yawan matan dangin dake auro wasu mazan da ga wasu dangin... Duk kuwa da kashi tamanin na cikin dari auren zumunci suke yi. An taba samun sabani ne sau biyu akan wasu auren da aka hada na zumunta. Har abun ya fara kawo tangarda da son rabuwar zumuntar. Dakyar aka iya sasantawa aka kuma kawo karshen hadin auren zumuntar. Ya zama dik me son auren babu takura yaje waje ya auro...
×××××
Hancin motocin su Amb. Junaid ne da iyalan sa suka shiga dandatsetsen katafaren babban gidan na kandem estate.
Babban gidah ne daya ci sunan a kira shi da 'aljannar duniya' komai yaji. Domin tsayawa ma a baku labarin yadda gidan ya kawaatu da komai na rayuwa tabbas bata lokaci ne. Sannan zuciya zata iya tantama akan hakan.
Masu gadin suka tashi da sauri suka yo kan motocin da number jikin plates din motar ke rubuce da manyan bakin kandem 01 zuwa kandem 05...
Tsayawa motocin sukayi. Amb junaid ya bude kofar mazaunin da yake. Masu gadin da maaikatan gidan maza sukayi dafifi akan sa. Sanin shi mutum ne mai karamci da adalci, dattako ya kamata, da Kuma kyautatawa da jikin sa, gumin sa da kuma aljihun sa.
Haka ya rika basu hannu suna musaba. Bakin sa abude yanata musu murmushi suma suna rissina masa cike da girmamawa.
Sai da ya tabbatar ya gaysa da kowa acikin su sannan ya daga musu hannu . Suka rufe masa murfin motar direbobin suka ja motar zuwa ciki.
Kai tsaye motocin sukayi bangaren mahaifiyar sa... Wanda shima nasa gidajen a sashen suke. Gate ne kawai ya raba su. Nata yayi dama nasa ya kalli hagu. Amma da yar tazara a tsakani.
Motocin suka danna kai cikin gate din. Suna karasa parking suka furfuto daga cikin motar . Shine agaba suna biye da shi a baya...
Ya doka sallama ya shiga cikin babban parlorn. Dattijuwar hajiyar na zaune akan wata kujera samfurin Italy. Babban Qurani ne a hannun ta. Fuskar ta saqale da gilashin kara ganin ta.
"Hajjaju na.... Hajiya ta" ya fada da sauri cike da madaukakiyar murna marar misaltuwa
Ta dago ta kalle su tana amsa sallamae. Murmushi tayi faffada. Ta mayar da kanta kan quranin da take karantawa. Ka'dane sai ta kai aya take ajiyewa. Allah ya temaka tana karshen shafin tana karashewa kuwa ta daga hannun ta tana addua kamar ko da yaushe . Suma suka daddaga hannuwan.
Amb Junaid nata kada kai yana cewa,
"Aamin, Allah ya amsa... Allah ya amsa Hajiya... Amin Amin."
Karbar Qur'anin yayi ya ajiye a inda take ajiyewa.
Tayi murmushi tana kallon su daya bayan daya,
"Allah yasa Qur'ani ya cecemu. Amin"
"Amin Hajiya"
"Aamin Amin"
"Allahumma Aamin hajia."
Suka shiga amsa adduar da tayi. Domin Hajiya Maryam akwai Ibada da yawon karanta alqurani. Tunda kananuna shekarun ta har girman ta. Shi yasa Allah ya amince duk tsufan ta ganinta bai tafi ba. Tana iya karanta komai idan rubutu yayi karanchi ne take karawa da temakwan gilashin karatu na kara girman ganin rubutu.
"Hajjaju barka da Rana... Mun same ku lafiya? Ya jiki hikin na ki? Fatan komai da komai kalau Hajiya? Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa yasa kifi ha ka, Amin...."
"Amin junaidu, Allah ya maka albarka, Allah ya maka albarka, Allah ya maka albarka junaidu."
"Amin Hajiya Amin."
Ya matsa daf da ita. Hawayen dadi daya nabin daya a fuskar sa. Duk girman sa idan yana gaban hajiyar su ganin sa yake dan karami.
"Allah ya albarkaci zuriyar ka junaidu. Allah ya albarkaci dukiyar ka junaidu, Allah ya albarkaci komai na ka junaidu. Allah Amin."
"Aamin Hajiya... Aamin."
Nan da nan daya bayan daya suka rika tasowa suna gaishe da Hajiya tanata amsa musu. Amb Junaid yaki matsawa daga gaban ta sai ma sake gyara zama da yayi sosai yana jin sa cikin wani irin nishadi marar misaltuwa
Amaal ce karshen tasowa ta nufi wajen hajiyan tana murmushi. Hajiya Maryam ta bude baki tana murmushi.
"Ahh