Showing 63001 words to 66000 words out of 95238 words

Chapter 22 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt

04 Jan 2025

6677

jikin da akeyi mata.. Suna doso su kamshin ke dada mamaye ko'ina..wani irin sanyayyen musulmin kamshi mai dadi.


Gyaran jikin da ake mata ya karbe ta. Domin fatar nan tata ta sake haske tayi santsi da laushi.. Tamkar an sake kara mata kyau. Harta gashin girar ta sun sake cika da baki. Leben nan nata ta shafa man baki sai kyalli yake da laushi..


Sanye take cikin doguwar rigar hijab bubu..Ta yane kanta da mayafin daya shiiga da kalar sa ja da ratsin baki..


"Ina wunin ku?" Yusra ta gayshe su. Suka amsa...


Amaal ma ta dan sunkuya cike da ladabi tace,


"Barkan ku da yammaci..."


"Amaal... Amarya" Habibi Talba ya fada yana murmushi


"Malam" ta fada cike da kunya


"Allah ya sanya alkhairi. Yasa gidan zamanki ne"


"Aameen" Yusra ta amsa shi. Saboda amaal din jtada dai kanta a kasa tana lankwasa hannuwan ta cike da kunya...


Tunda suka zo wajen Al-mustapha ya kasa dauke kansa daga kallon amaal da yaketa yi tamkar zai mayar da ita cikin sa..


Tana dago Kai suka hada idanu ya bata rai ya bar wajen da sauri. Habibi Talba yabu bayan sa yana cewa da shi,


"Jirani mana garanbawul.. Kai fa dan wahala ne."


Sashen Hajiya Maryam ya nufa Habibi Talba na biye da shi a baya.. suka shiga ciki bakunan su dauke da sallama.. sika gaysa da hajiyan.


"Wannan aboki ka ne?"


"Eh hajia kin manta shi ko?"


"Kaman dai nasan fuskar nan tabbas"


"Habibi Talba ne.. Tun Muna kanana muke tare. Mahaifin shi abokin su Bappah ne.. yanada sarautar Talban gabas na garin Yalwanje... "


"Haka .... Ma shaa Allahu. Ya mahaifan na ka kalau?"


"Alhamdulillah Hajiya".


"Safiya kawo musu abinci" Hajiya ta dan daga murya tana kiran me aikin ta


Nan da nan me aikin ta shiga kawo musu abincin da trays tana ajiyewa da ruwa da lemuka.


"Ku zuba kuci dan Allah"


"Tohm Hajiya. Allah ya saka da alkhairi "


"Aameen Aameen Habibi"


Cikin haka Aayaan ya shiga ya same su .. suka gaysa ya zauna ya debi abincin ya fara ci,


"Hajia wannan shine malamin su Amaal fa da hindu ke magana" aaayan ya fada yana sake zura lomar abinci a bakin sa..


"Au shine.... Allah sarki"


Habibi Talba yayi murmushi yace,


"Ni ne hajiya"


"An ka samu ni da kai" Aayaan ya fada yana dariya.


Shi dai Habibi Talba murmushi kawai yayi masa. Al-mustapha kuwa kanzil bai ce ba ya cigaba da cin abinci yana korawa da ruwa.


Sun dan jima bayan sun kammala cin abincin suna ta hira daga bisani Al-mustapha da Habibi Talba suka yiwa Hajiya sallama suka fita...


"Muje ka ajiye ni a site can nabar motar"


"Nagaji maza.."


"Haba mana"


"Muje"


Motar sika koma suka shiga.. Al-mustapha ya kai Habibi Talba har site..


"Dan Allah Ina zakaje? Yaushe zaka tafi? Kuma yaushe zaka dawo"


"Meye haka? Kaman wani wanda yaci bashin gidan rediyo?"


"Dagaske nake please"


"Manchester..... "


"England dai?"


"Yes..."


"Yaushe zaka tafi? "


"Soon inshaa Allah"


"Exact date nake son sani"


"Will let you know .."


"To yaushe zaka dawo?"


"Sai na huta"


"Sai kayi healing dai... "


"Whatever... "


"Later.. will holla you"


"Alright. ka gayda su mummy"


"In shaa Allah.",


Yaja motar sa ya koma gidah ransa duk babu dadi kwata kwata.. Kai tsaye ya shige daki bayan ya shiga bangaren su.


Ko da aka tambaye shi akace akawo masa abinci ma yace a'a yaci awajen hajia. Kwana yayi bayyi bacci ba yanata sake sake sai salllar nafila da yayi ya roki Allah yasanya hakan ya zamo shine alkhairi agare shi.


A daren ya hada kayan sa a akwati da hotunan Amaal gaba daya da niyyaar idan yabar kandemi sai ya samu waje ya kona su duka..


:::::::




Shirye shiryen biki aka fara yi. Kwanakin bikin suka karaso.. Da ke Amaal din batason taro hakan yasa ba wani events za'ai ba. Akwai gagarumun Grand kamu/ royal mother's eve dai daza ayi. Sai daurin aure da walima shikenan..


Ranar Thursday yammatan gidan cousins suka hada bridal tea party. Iya su kadai ne kawai da amarya Amaal da kawayen ta. ...


Tayi shiga cikin barbie gown pink color kaman wata princess. Ta nade kanta da mayafi shima pink. Sai takalman ta silver color. Ba kadan ba tayi kyau.


Sun ci sun sha sun gyagije. Sunata games, Ita dai tana zaune a kujera tana kallon su. Wayar ta a hannun ta notification ya shjgar mata ta Instagram, ta bude. Arc. Nurayn ne ya turo mata message da,


"Assalamu alaikum wa rahamatu Allah wa barakatuh! Hey! Maryaam, I know you are seeing this… I want to thank you for being in my life. Also, I want to wish you the best! You deserve the whole world! Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nake bazan taba mantawa dake ba, Na kan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata... Daga karshe kuma Allah yayi ni da ke ba masu zama a karkashin inuwa daya ta maaurata bane. Na shigo rayuwar ki a BAKON masoyi wanda yazo a qure. Ban bayyana miki kaunar da nake miki ba har Allah ya yi hukuncin sa dai ke din ba tawa bace. Ki sani kaunar ki ta dade acikin rai na, Ina miki fatan alkhairi a sabuwar rayuwar da zaki shiga. Allah ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa Amin... Na bar ki lafiya..
Arc... Nurayn!! Thou dai ki gafarce ni nurayn suna ne kawai na saka a social media. Amma usulin sunana na yanka ba haka bane.. Na bar ki lafiya. Allah ya yafe mana kurakuren mu Amin.."


Ta karasa karantawa hawaye 'daya ya zurara daga idanunta tayi sauri ta goge hawayen.. ta rubuta masa,


"Wa'alykm Salam... Nagode kwarai. Allah ya saka da alkhairi. Goodbye" Tana karasa tura masa tayi sauri ta shiga tayi blocking dinsa already shima har yayi unfollowing dinta.


Haka dai suka karasa event din ranar dakyar ta samu ta daidai ta kanta... Akayi hotuna sosai... Bridal tea party din yayi dadi sosai..


Washegari da safe Al-mustapha ya sulale kaman ya tafi office ya bar kasar.... A kuma ranar ne zaa fara hidimar babbar liyafar bikin da duk Nigeria ta dauka har kafafen yada labarai anata haskawa.


Yan uwa da abokan arzuka, Matan sarakuna, gwamnoni dana ministici, daktoci, furofesoshi,jakadu kai da duk wani who is who ya bayyana a babban dakin liyafar da za'a gudanar da biki irin na sarauta na, gimbiya Amaal.. Wato Grand kamu/ Royal mother's eve..


Duke decorations din wajen royal blue color ne da brown.. waje ne daya hadu wanda alkalami yayi kadan wajen zayyano muku haduwa da tsaruwar wajen... Sai dai mu kira shi da monumental event....


Hajia Jamila tayi shiga cikin wata rantsattsiyar lafaya golden color me kyalkyalin blue. Gwal kam ta zuba shi a hannu da yatsu da wuya da kunne... Lamarin sai wanda ya hasaso kawai..


Hakama dukkanin sauran yan'uwa kowanne yaci ado ya koshi cikin asoebi na Royal blue color..


Sai bayan da aka hallara ango da amarya suka shiga...kanta a nannade yake da mayafin daya dache da golden rigar da ke jikin ta tana jan kasa ... Rigar ta hadu hakama takalmin ta da yar clutch bag din dake hannun ta....itama ta zuba ruwan gold ba karya.. sai dai a lullube take cikin alkyabba blue color take kanta a kasa..


Ango Hisham na gefe cikin wani haddaden yadi daya sha aiki me tsada. Takalmin sa da agogon sa da hular sa dik kalar yadin jikin sa ne.. sai azurfar da ke kyalkyali a yatsan sa..


Algaita ce ke tashi.... Da kirarin dogarai da jakadai da ke gefe da gefe... Kawai kuyi picturing komai..


Magana ake ta TheRoyalWedding.... #H&MIslamicDuo💞🥳


_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[9/22, 5:08 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 40_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___



*Bayan* shigar amarya da ango.... A kayi addu'oi.. Daga bisani MC yana kallon ipad din dake hannun sa yace yana umartar ango Hisham ya fita za'ayi kamun amarya ba 'bata lokaci..


Hakan kuwa akayi... Hisham ya mike wani abokin sa yayi masa rakiya suka fita waje suka koma mota suka zauna..


Daga nan kaman yadda al'adar su take aka fara mata kamu da nono a kwarya.. Yan uwa duk suka taru akanta. Bayan an kammala aka cire mata alkyabbar aka dakko sabon lace aka bude aka rufa mata akanta.. Yan uwan ango suka taso aka tsadance da kawayen amarya suka biya kudi mai tarin yawa aka kama Amaal amarya.. Aka yiyyi hotuna... Ango ya shiga shima akayi da shi ..


Daga nan kuma kawayen amarya suka dauki amarya suka fita da ita bayan an danyi photo-sessions da ita...


Mc ya sake bada umarni kan ayi shiru a kuma mike don karrama shigowar amarya da dangin ta tare da kawayen ta..


Ba da jimawa ba kuwa sai ga kawayen amarya a gaba sun fara shiga ciki. Daga baya kuma Amaal ce da yan uwanta baki daya sunyi anko mazan ma sun saka hula blue akan manyan kayan dake jikin su.


Gwanin ban sha'awa haka suka rakata har high table ta zauna. Ta sauya wasu kayan zuwa wasu yan gaske da sukayi matukar mata kyau sika kuma karbi jikin ta..


Hamid shine ya bada tarihin amarya.. don tausayi sai da mutane da yawa suka zubar da hawaye. Kasancewar ya bada takaitaccen tarihin yadda Amaal din ta shaku da mahaifiyar ta sosai. Da wasu daga cikin kyawawan halayen ta na biyayaya da yadda da kaddara. Ya bada tarihin makarantun da tayi tun tana karama har ya zuwa matakin karatun da take na jami'a.


Bayan ya gama kuma ya mikawa abokin ango mic inda shima ya bada tarihin ango Hisham da kyawawan halayen sa.


Atakaice dai dukkan su sunada kyawawan halaye kuma sun dace da juna.


Anci, an sha, an gyagije an raba kyautttuka an dau hotuna.. kawayen amarya da angwaye sunyi games suma sun ci gifts sosai


Daga karshe aka tashi daga hadaddiyar liyafar. Duk wanda ya halarta ya futa daga dakin taron cikin dimbin farin ciki marar misaltuwa.


Mota suka shiga shi da ita da a baya, Sai Yusra agaba. Abokin sa kuma na gaba yana tukawa suka koma kandemi.Yusra da abokin suka fita daga motar suka basu waje..


Amaal nata lankwasa hannuwan ta. Mamaki dankare a kirjinta ji take kaman mafarki wai yau itace ake bikin ta?


"Babe...."


Da sauri ta juya ta kalle shi... Kallon ta yake shima.. ya sakar mata murmushi yace,


"Tunanin me kikeyi?"


"Bakomai.."


"Dagaske..?"


"Uhm..."


"Shikenan... Kinga kyan da kikayi yau kuwa?"


Hannuwanta tasaka da suka sha kunshi ta rufe fuskar ta da su.. Cike da jin kunyar kalaman sa


Ya dan rankwafa yana kallon fuskar data rufe ya girgiza kai yana murmushi yace,


"Dole na biya kudin kwalliyar nan.. da farko dai waye yayi gyaran jiki? Uhm? Ta cancanci kyauta matuka..."


"Kamfanin turaren yerwa incense and more ."


"Ma shaa Allahu... Tana wane gari?"


"Kano."


"Ki aiko da account number dinta zan saka mata wani abun. Allah ya saka mata da alkhairi. "


"Inshaa' Allahu.. Aameen."


"Kwalliyar fa?"


"Beelanah beaute.... Itama a kano take."


"Photographer?"


"Zaarah. Ng itama a kano take"


"Wanda tayi abinci fa? Bana kasar wajen ba"


"La comida corner ce, Da rano scrumptious meals.."


"Ma shaa Allahu... Dika ki aiko mun da bank details dinsu. "


"In shaa Allahu.."


"Maryaam "


"Na'am..."


"Gobe zaa daura mana aure..."


Kanta a kasa tace,


"Eh.."


"Maryaam inaso ki yafe mun dukkanin wani abu danayi miki akan sani ko rashin sa. Dan Allah ki gafarce ni kinji?"


Amaal ta daga kai ta dube shi... Da sauri tace,


"Meya kawo wannan zancen Yaya Hisham? Ba abunda ka mun"


"Maryam! Dana saka zaa aura mun kema ai na cuce ki .. Ba fa so na kike ba Amaal biyayya kikaiwa iyayen ki kawai",


"Ban tsane ka ba Yaya Hisham"


"Amma bakya so na ai maryaam"


"Inayj mana "


"Son yaya da kanwa ba... Ba son zamantakewar aure ba ."


Batace masa komai ba.. kanta dai yana kasa tana lankwasa hannuwan ta,


"Ki yafemun kinji..?"


"Ba abunda ka mun fa... To nima ka yafe mun"


"Yauwa ko ke fa . Toh Allah ya miki albarka Amin"


"Amin..."


Bude kofa yayi ya fito itama ta bude ta fita. Yusra tayi murmushi tace dasu,


"Kun shanya mu kamar wasu kayan wanki.. gobe de za'a daura ku tattara ku tafi"


Hisham yayi murmushi yace,


"Ku gafarce mu ..... Bamu wani gaisa bane duk yau shine muka gaysa "


Abokin sa ya bashi hannu suka tafa yana dariya..


Har kofar sashen Hajiya jamila Hisham ya raka Amaal. Mutane nata tsokanar su,


"Sai da safe .... Allah ya tashemu lafiya ma'abociyar kyau da kyawun hali"


"Mu kwana lafiya Yaya hisham..."


"Yaya Hisham this Yaya Hisham that .. Ana cutata ana cemun wani Yaya bana so."


Murmushi tayi tache,


"To shikenan na daina."


Sai da suka shige cikin gidah sannan ya juya ya koma wajen abokin sa, abokin har yayi wajen mota yace da shi,


"Zo ka raka ni ciki "


"Okay tohm"


Sashen Hajiya Maryam suka nifa... Ba mutane sosai. Suka gaggaysa da su. Duk aka fita aka basu waje su da hajiyan. Ya sake durkusawa ya gayshe ta cike da girmamawa,


"Ango ango"


"Na'am hajjaju...." Ya faada a kunyace,


"Allah ya sa albarka da alkhairi kaji ko"


"Ameen hajia... Dama wajen ki na zo" ya fada yana lankwasa yatsu cike da kunyar data dabaibaye shi


"Toh Allah yasa muji alkhairi...."


"Aameen Hajiya.."


Abokin nasa ya mike ya basu waje ya fita.. hajiyan tace,


"Ina sauraron ka? Ko mu koma daaka yafu sirri?"


"Nanma ya isa hajia"


"Toh Allah yayi albarka"


"Aamin Hajiya... " Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya,


"Ina sauraron ka...."


"Hajiya dama zuwa nayi na roke ki abisa abunda nake tafe dashi. Kuma ina fatan zaki duba zance na da tsanaki ki goyi bayana"


"Toh... Allah yasa muji alkhairi. Ina sauraron ka"


Hisham ya sake muskutawa yace,


"Dan Allah Hajiya ku dbi girman biyayyar da Maryam tayi muku"


"Wani lefin tayi?"


"Wallahi ba abunda tayi Hajiya. Zan iya ce miki tunda nake da ita Allah bata tabamun wani lefi wai dazesa naji haushin ta ba. Tana bani girma sosai. Kuma tanada nutsuwa da hankali ga biyayya. Don biyayyar cema ta amince zata aureni"


"Ina sauraron ka"


"Wato Hajiya nayi duba na tsanaki, Kuma na sassaurari wa'azi duk da ba wai nace abu ne mekyau ba kasancewar budurwa ma ca akai a mata zabin miji bazawara kuma a barta ta zaba da kanta"..


"Wannan zance naka haka yake"


"To Hajiya.... Magana ta gaskiya idan na amince aka daura aure na da Maryam wallahi wallahi wallahi na kwareta... Kuma Allah zai mata sakayya"


"SubhanAllahi meyasa kache haka hashimu? Bayan kowa yasan kai da ita kuna kaunar juna?"


"Wallahi hadin zance na ne na samu su baba nace da su soyaya mike ai muna waya da magana ta kafar sadarwa. Tabbas muna waya da magana ta kafar sadarwar amman karatu nake koya mata kuma wallahi amatsayin Yaya da kanwa muke maganar. Ni ne na sawa raina wani kuduri naji Ina son kasancewa da ita a inuwar aure. Na samu iyaye na da maganar sukace sai sun tabbatar idan tana sona.. da akayi maganar anan parlorn naki nema bata nuna ba haka bane tache eh munayi ta kuma amince. Wallahi hajiya na ha'inceta idan har aka daura auren nan gobe. Wallahi wallahi biyayya kawai takeyi amman ...


Bai karasa ba Hajiya ta girgiza kai kawai tace,


"Idan na fuskance ka so kake a fasa daura auren nan gobe idan Allah ya Kai mu?"


"Eh...."


"Me zaku gayawa mahaifan ku ?"


'wallahi Allah maryaam batada masaniyar dukkanin abunda na gaya miki. Ni na yanke shawara ta. Saboda zuciyata ta kasa nutsuwa. Banason Allah ya kamani akan abunda ba haka bane. Na mata kazafi na nuna da yardarta itw kuma tayi biyayya ta amince. Hajiya dan Allah ki saka baki kada a daura auren nan gobe idan Allah ya kai mu"


"Tirkashi..." Hajiya tafada tana mai sauke nannauyar ajiyar zuciya. Baki daya itama kanta ya kulle. Ta cigaba da cewa


"Ai idan kukayi auren zaku daidaita kanku hashimu .. zata so ka sannu ahankali " Ta fada cikin tabbatarwa, Ko kadan bata damu da ba daidai take fadan sunan nasa ba. Hisham ne take kiran sa da hashimu


Ya girgiza kai yana hada hannuwan sa yace,


"Wallahi bazan iya auren maryam ba hajia. Na amince a hadani da koma wacece acikin zuriyar kandemi amman banda Maryam ba zan shiga hakkin ta ba."


"Ni bansan me zan fada ba hashimu. Bari a kira su gaba daya.. Duk hukuncin da suka yanke shine daidai.. Ungo dannomun lambar Nuraddeen." Ta Mika masa yar wayarta


Karba yayi ya kira mata Bappah Nuraddeen. Ta saka a kunne bugu bjyu ya dauka ta sheda masa ya tatttaro kan kowa suzo bangaren ta harda Amaal.


Ta kuma tashi ta shiga dakin mai gidan ta Alhaji Muhammad shima ta kirawo shi. Suka gaysa da Hisham ya zauna akan kujera. Hisham din na gaban su a zaune kansa akasa


Ba jimawa kuwa sai ga tuttulowar su gaaba daya. Ciki harda sarki Junaid da iyayen Hisham din. Gaba daya dai suka hallara


"Maimaita abunda kache hashimu"


"Hisham ne Hajia" Yusra ta fada tana dariya


Duk suka danyi Daria. Hisham din ya dan saci kallon mahafin sa. Muryar sa na dan rawa ya zayyane komai tun daga farko ya sake fada ya karkade da,


"Wallahi wallahi wallahi bazan iya auren maryaam ba. Idan na bari aka aura mata ni hakika na cuceta, Na ha'inceta, na zalunceta na kuma shiga hakkin ta kuma Allah ba zai bar ni ba. Tunda karya na hada na fada muku cikin tabbatarwa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login