Showing 66001 words to 69000 words out of 95238 words

Chapter 23 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt

04 Jan 2025

6665

Amma ita ta amince saboda ganin girman ku da tsananin biyayyar ta tace eh hakane muna soyayya. Wallahi Allah amatsayin Yaya da kanwa muke da ita tamkar na jini. Hasalima ni coaching dinta nake Ina koya mata wasu abubuwan na makaranta ta waya ko messages . Bappah, Baba, Kaka, Hajiya... Dan Allah ku gafarce ni.. ku karbi roko na kada ku aurawa Maryam ni gobe idan Allah ya kaimu wallahi kamar yadda na fadawa Hajiya yarinyar na batada masaniyar abunda nake gaya muku dai dai da rana daya batada daba mun complain na zaluntar ta da nayi ba nace muna soyayya har aka sa mana ranar aure ba, Bata taba nuna mun ba ai karya na shirya nace muna soyayya ba.. Dan Allah karku aurawa Maryam ni. Karku bata mata rayuwa ta auri wanda takewa kallon yayan ta na jini .... Ni Hisham na amince a aura mun wata daga cikin wannan zuriyar na kandemi goben idan Allah ya kai mu.. amman Dan ALLAH jar a aurawa maryam ni. A barta ta auri wani daban.. Dan Allah"


Duk sukayi shiru...Tamkar mafarki ko a kallon wasan kwaikwayo na talabijin. Alhaji Abubakhar ya mike cikin zafin nama ya tattare kasan hannun rigar sa jikake,


'Taasss.. Faaas, Chasss' Ya sharara masa maruka guda uku lafiyayyu a gefe da gefen fuskar sa.


"Mutumin banza... Daman sharri kayi mata ka cuce ta? "


Ya sake daga hannu zai sake marin sa Bappah Nuraddeen ya rike masa hannu. Sarki Junaid ma ya tashi ya janye Hisham daga wajen ya mayar da shi gefen da yake,


"Meye abun marin nasa? Haba Abubakhar? Idan ka bibiyama kila amaal dince ta nuna bata so" Cewar sarki junaid.


"Walahi daidai da minti daga maryaam bata taba nuna mun batason aurena ba. Ba kuma taba cewa ai karya nayi mata ba ba soyayya mike ba. Wallahi Allah " Hisham ya fada cikin tabbatarwa


"Yo ai ni gaba daya ma na rasa abunda zance..."Bappah Nuraddeen ya fada yana tallabe habar sa cike da damuwa


Amaal dake gefen Hajiya jamila sai raba idanuwa take. ita da tai tasan kalau fa suka rabu da shi ya rakata har kofar shiga sashen su.


Haka dai akayita maganar ana neman bakin zaren. Dakyar dai aka hakura kan ba zaa daura auren da Amaal din ba ganin yadda Hisham yake zubar da hawaye sosai kan inde aka daura to wallahi ya shiga hakkin ta kuma Allah ba zai barshi ba.


Ana cikin maganganun ne Hajia maryam tace


"Wai har yanzu dan yaye be kira waya ba an san inda yake? Tukunna ma yana Ina jama'a?"


Duk sukaita tofq albarkacin bakunan su. Yusra dake gefe tace,


"Na kira aminin sa. Habibi Talba yace Hamma Al-mustapha ya tafi Manchester England"


Bappah jalaludden ya bude baki yace,


"Ina?"


"Manchester"


Ya dubi hajia Jidda mahaifiyar su yusra yace,


"Ya gaya miki me?"


"A'ah..."


"To me yaron nan yake nufi?"


"Bappah Al-mustapha ba zai iya zama ana auren amaal ba. Shi yasa ya tafi." Aayaan ya fada cikin tabbatarwa.


"Wai yaron nan dama yana kan bakan sa?"


Hajia maryam tace,


"Ni kallon sa kawai nake... Ya bude baki yayi mata magana yaki sai zurfin ciki. Yadda yake nuna mata kamar yafu kowa tsanar ta a duniya. Bayan tun tana zanin goyo yake kaunar ta."


"Wai Al-mustapha dai namu?" Bappah junaid ya tambaya yana zare idanu,


"Shi dai...Muma rufe mana yake. A nasa haukan ba zamu gane ba. Tun muna Buckingham muka sani. Hotunan ta tun tana karama har na wanda ta girma, ko a'ina ya same su oho, yana nan dasu."


"Ammw yaron nan sakarai ne"


Ita dai Amaal jin su take tamkar a mafarki. Duk abubuwan da suke fada yana shifa ya futa ta dayan kunnen na ta. Al-mustapha kuma? Kai gaskia ba dai ita ba. A duniya ba wanda ya tsane ta sama da shi


"Ni ma na lura yana son ta sosai... Wanda ya zauna anan dinnan ko ranar da muke nan duka?" Hisham yake tambayar Aaayan.


"Shi dai. Ai mugun gara ne dab wahala. Wai shi sharukan baban soyayya ya hakura ya bar ma ka."


Sika saka dariya baki daya... Bappah Abdullahi yace,


"Kuma ba shine ba shida lafiya bane bayasan damuwa sosai?"


"Shine . Can daya Wawa. Ku rabu da shi ya karaci zaman sa acan idan yaga dama ma kar ya waiwayo gidah gaba daya" bappah jalaludden ya fada cikin halin ko in kula


"Ba za'ai haka ba Yaya.. da kai da kaya ai duk mallakar wuya me... Abunda yayi Al-mustapha shi yayi Amaal "sarki junaid ya fada


"Ba fa za'ai abundq kake tunani ba. Ni ba sakarai bane. Ba zaa shiga hakkin yarinya ba "


"Ni na amince tunda 'da na ne" sarki Junaid ya fada


"Ni kuma ban amince ba tunda 'ya ta ce" Cewar Bappah Jalaludden


Yan parlorn suka saka dariya baki daya. Bappah Nuraddeen yace


"Mutane sunzo dai ko'ina gari ya cika idan baa daura aure gobe ba da matsala. Idan Kuma akwai wata hanyar da za abi to tun yanzu a sanar musu a daren nan kan an fasa daurin aure gobe "


"Zaa daura aure inshaa Allahu .. hjsham da ne awaje na. Kuma ya roki alfarma dole zan cika masa .. wa kake so acikin zuriyar kandemi ka fada gobe da yardar Allah sai a daura muku aure kaji?"


Hisham yayi shiru can ya daga kai yana kakaro murmushi yace,


"Duk wadda aka bani Bappa "


"Yusra.... Zaki biyayya ki auri Hisham?"


Yusra da daga Kai da sauri tace,


"Na amince bappah junaid "


Suka saka dariya dika parlorn ciki harda Amaal da ita kanta yusran ta bata dariya.


"Nagode diyar albarka... Hisham yusra ta maka?"


"Bappah .. maganar ma was beyond my expectations. Na karba da hannu dubu bama biyu ba."


Nanma aka sake fashewa da dariya. Aayaan yace


"Dama can kuna crushing juna da alama.. da sauri kowanne na amince Bappah"


Yusra ta jefa mai pillow tana rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta..


"Allah ya muku albarka.... Gobe inshaa Allah sai ayi daurin auren. Aayan kikkira masu hoton yau kache kar su wanke su kar su saka please da tv stations dika dai a cure komai"


". In shaa Allah Bappah "


Haka dai suka yita mayar da zancen aka shiga wata hirar ta daban. Kafin daga bisani kowanne ya nufi sashen sa dan kwanciya bacci saboda dare yaja ainun


====




WASHE-GARI


Bayan sallar jumu'ah dubban mutane ne suka sheda daurin auren jikokin Alhaji Muhammad Wanda aka gabatar a masallacin central mosque da ke cikin masarautar kandemi... Wanda Bappah Nuraddeen ne ya zama waly... Akan sadaki mafi daraja,


Amarya, [Fatima-Yusra Jalaludden Muhammad] da angon ta [Captain. Hisham Abubakhar].


Sai amarya [Maryaam-Amaaal Junaid Muhammad] da angon ta [Arc. Al-mustapha jalaludden Muhammad].


Akayi rantsattsiyar liyafa/grand reception bayan an daura auren na maza. Anci an sha an kuma gyatse..Duk kuwa da babu ango daya wato Al-mustapha...


Yan uwa da abokan arzuka suka bi amare da angwayen da adduoin zaman lafiya da zuriya dayyiba...







AL-MUSTAPHA WEDS MARYAAM AMAAL...
#AWEDDINGTOREMEMBER💞💞




_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥


[9/25, 1:27 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_


_NA:_


_NANA HAFSATU_


_PAGE: 41_


_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._


___


_AMAAL_




*Tana* kwance a dakin Hayateey akan gado... Wani zazzabi taji yana neman rufe ta gaba daya.. jikin ta ya fara daukar zafi yana kakkarwa. Gefe daya kuma kanta ne ke ciwo yana mata barazanar fadowa. Ga gabanta na dukan uku uku...


Sanye take cikin doguwar riga ta lace peach color style din bubu.Dankwalin kanta ya zame, Kwantaccen gashin ta ya bayyana a kanannade yayi bakikkirin da shi irin na larabawa.


Cikin haka mahaifiyar ta ta shiga dakin bakinta dauke da sallama. Amaal ta amsa tana daga kwancen ta dan daga kanta,


"Hayateey..."


"Na'am Habibty"


Zama tayi a kusa da ita akan gadon. Amaal din ta dan mike daga kwancen da take ta zauna ta jingina...


Hajia Jamila sai jujjuya yadda zata fito ta gayawa Amaal zancen an daura mata aure ta ke..


Ganin Amaal din na mutsu mutsu har da rufe idanu tana dan dartse labbanta cikin ciwo...tace da ita,


"Meya same ki?" Ta karasa fada tana dafa kan Amaal din ya dau zafi rau.


"SubhanAllahi baki da lafiya da ma?"


Amaal din ta daga kai dakyar saboda tsananin ciwon da yake mata tace,


"Eh... Gabobi na da kai na kaman ana datsani"


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Tun yaushe kuma baki fada ba fisabilillahi?"


"Ba'a wani dade ba ne Hayateey.. bayan na fito daga wanka"


"Tashi tashi muje asibiti"


"Hayateey zai tsagai ta. Zan tashi na sha Panadol pain and fever"


"Banason musu tashi muje.kin manta abbiey ya hana a shan magani da ka ba tare da prescription din likita ba?"


"Tohm"


Mikewa tayi dakyar. Ta janyo mayafin ta wani madedeci ta yafa shi. Hajia Jamila ta dan dubeta ta ce,


"Canza mayafi saka babba ko hijabi"


Ba tayi musu ba ta janyo hijabin sallar ta ta saka. Don azaton ta Hayateey ta gaya mata hakan ne kila saboda kar ya dinga zame mata tunda batada lafiya.


Wajen motoci suka nufa, Hayateey na rike da hannun Amaal dake jiri ne ke dan daukar ta.


Hamid na ganin su ya taso. Waya ce a hannun sa yana dannawa,


"Hayateey ina zuwa?"


"Wallahi Amaal ce ba lafiya kaganta nan nace muzo muje asibiti"


"SubhanAllahi dearest sissy.. ya jikin?"


"Da sauki Yaya Hamid" ta fada tana runtse idanu saboda yadda kanta ke mata nauyi,


Mota ya shiga ya bude da sauri ya tashe ta ya kawo ta gaban su,


Hajia Jamila ta shigar da Amaal gidan baya ita kuma ta koma gaba ta zauna. Hamid ya jasu suka fita daga cikin sashen zuwa asibitin cikin gidan dake can baya ta dayan gate din


Suna zuwa aka fara mata gwaje gwaje ba baya lokaci. Sakamakon ya fito ta kamu ne da zazzabin ciwon sauro na malaria da kuma zazzabin typhoid.


Nan da nan aka fara mata wasu allurori aka kuma bata magunguna masu kyau. Cikin ikon Allah kuma jikin nata yayi karfi


"Sannu Amaal"


"Yauwa Hayateey"


"Sannu dearest sissy"


"Yauwa Yaya Hamid"


Motar suka koma suka shiga Hamid ya ja sika dauki hanyar gidah... Hayateey ta temaka mata suka shiga cikin sashen su..


Daki ta shige ta kwanta. Ba jimawa kuwa bacci ya dauke ta... Da ke batada nauyin bacci ana budo kofar ta bude idanun ta.


Yusra ce ta shiga bakin ta dauke da sallama... Amaal da ke kwance ta dan daga kanta tana amsa mata,


"Baby sis"


"Yaya yusra.."


Mikewa tayi. Yusran ta karasa tana ce da ita,


"Ashe bakya jin dadi? "


"Eh!!Amma da sauki .. bari nayi brush"
Ta shige bandaki ta wanke bakinta da mouth wash hade da yin brush sannan ta futo,


"Ya jikin na ki to?"


"Da sauki Alhamdulillah Yaya yusra"


Yusran ta nemi gefen gado ta zauna. Sanye take cikin doguwar riga blue color ta zuba adon gwal na sarka da dankunne da zobuna da awarwaraye. Ta yafa mayafin kayan akan ta. Tayi kyau ba kadan ba.


"Sannu kinji?"


"Na wartsake fa yaya yusra"


"Allah ya kara afuwa... Amin"


"An daura ko? Iyye congratulations... Yaya yusra ta zama matar aure"


Yusran tayi murmushi ta dube ta tache,


"Godiya nake baby sis... " So take ta fada mata amman kuma ta rasa yadda zata ce mata ai tare da nasu aka daura auren.


Cikin haka sai ga shigar hajiya Jamila dakin tayi sallama. Suka amsa,


Ta janyo stool ta zauna akai ta dubi yusra tace da ita,


"Bata shirya ba?"


"Ai ban gaya mata ba Aunty"


Hajiya jamila ta kada kanta, ta hada hannuwan ta tana lankwasa su tace,


"Amaal..."


"Na'am Hayateey..."


"Ki tashi ga kaya nan acikin drawer irin na yayarki yusra kalar naki ne dabqn ki saka zaa dauke ku hoto da su Hajiya.... "


Gabanta ne ya tsananta bugawa jin abunda mahaifiyar tata tace,


"Hayateey... Bangane ba?"


"Amaal Allah yayi miki albarka... Ki sani mahaifin ki bai yi miki zaben tumin dare ba. Kamar yadda a fari ma biyayya kikayi kika amince da auren Hisham wannan karon ma biyayyar ce zakiyi ta, ki amshi kaddarar ki da hannu biyu... Dan uwan ki ne... Kuma me kaunar ki ne tun kina zanin goyo kinji da kunnuwan ki. Yau tare da yar uwar ki ysura an daura miki aure da Al-mustapha yayan ki.",


Dummmmmm taji kofofin kunnuwan ta sun toshe.. ganin ta ya fara dishi dishi..take jikin ta ya soma mata kakkarwa. Hawaye masu dumi suka fara zuba daga idanun ta..


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta furta a sanyaye cikin lafazi me ban tausayi. Duk azaton ta dai wallahi ba za'a bata Al-mustapha a matsayin mijin da zata aura ba. Al-mustapha fa? Wanda duk duniya ita ya tsana? Maganganun daya gaggasa mata suka dinga mata yawo akai..


Yusra ta janyo ta jikin ta rungumo ta sosai.. hannunta daya ta saka akan fuskar amaal din tana share mata hawayen da ke zurara,


"Bar kuka dan Allah. I assure you auren ki da hamma alkhairi ne. Nan gaba zaki farin ciki da hakan. Wallahi duk inda masoyi na hakika ya kai to hamma ya zarce gaban haka... Yana kaunar ki sosai. Ni bansan dalilan sa na rashin bayyana miki ba..."


Girgiza kai kawai tayi. Can sai hawaye sharrr. Ta shiga shessheka. Jijiyoyin kanta suka tattashi. Idanunta suka sake kadawa sukai jazir. Saboda Allah ashe sai da aka daura mata aure da Al-mustapha. Duk ga maza nan a dangi


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta fada cikin kuka da muryar ban tausayi..


"Amaal...." Yusra ta kira sunan ta ranta duk baby dadi itama.


"Dakko kayan nata a drawer kina budewa zaki gansu daga sama." Hajiya jamila tace da yusra.


Yusran ta mike ta bude drawer ta dakko mata kayan ta ajiye agaban ta.


"Gashi .. Dan Allah tashi ki saka"


"Amaal karki bari na maimaita zancen saka kayan nan...idan kuma kinfi karfin mu to ki bar su."


Hajiya jamila ta yunkura zata mike kenan Amaal tayi saurin taddo ta ta rungumeta tsam a jikin ta tana kuka sosai.. cikin rawar jiki da murya tace,


"Hayateey kiyi hakuri ki gafarce ni.. "


Hajia Jamila ta saka hannu ta goge mata hawayen da ke zuba a fuskar ta tace,


"Allah ya miki albarka Amaal... Allah ya sanya alkhairi da dimbin albarka a rayuwar auren ku gaba daya. Allah ya kauda duk wata fitna yasa gidajen zaman kune. Yadda kuka yiwa iyayen ku biyayya kukw amince Allah ubangiji ya shi muku albarka ya biya muku dukkanin bukatun ku"


"Aameen Hayateey"


"Aameen Aunty"


Hajia Jamila ta fuce da sauri bayan ta dafa kafadar yusra. Ko da ta fita jingina tayi a bakin kofa hawaye na fita daga idanun ta irama... Hakika tasan ba a yiwa Amaal zabon tumin dare ba. Sannan tasan Al-mustapha zai riketa da alkhairi da yardar Allah. Kawai dai tana tausayin tilon yar tata ne. Batada taba bijirewa na daga abunda su iyayen ta suka zartar akanta ba.. kowane irin hukunci ne haka ta ke karba tun tana karama... Duba da cewa ita kadai ce awajen mahaifiyar ta ta bata sangarta ta ba. Tanada tsananin biyayyar da kauda kai a abu sosai tamkar wata mai manyan shekaru.


"Ki tashi ki wanka ki saka kayan muje ko?"


"Tohm"


Mikewa tayi ta shjge bandaki bayan tayi addu'a. Wanka tayo hadi da dauro alwala. Ta saka kayan nata. Kalar ja ba kadan ba tayi kyau .


"Bari a kira me makeup din ko?"


"Da an barta banaso"


"Banda musu"


"Tohm"


Yusra ta kira me makeup din a waya nan da nan tazo tayi mata makeup din wmma light. Ta daura mata dankwali ba kadan ba Amaal tayi kyau.


Itama ta zuba uban su gold daya gaji da haduwa ya kuma sha kudi masu tarin yawa .


Yusra ta dakko wayarta ta dunga daukar hotunan amaal din saboda tayi kyau sosai,


"Mashaa Allah... A beaute..."


"Nagode Yaya yusra"


"Muje ko?"


"Tohm"


Sauka sukayi suka nufi mota suka shiga direba ya jaa su sashen Hajiya Maryam dake cike da Yan uwa. Nan da nan aka fara daukar su hotuna kala kala .


Kafin daga bisani aka nufi wajen walima akayi wa'azi akaci aka aha aka kuma dauki hotuna hadi da raba gudunmuwa.


Hisham yazo akaita daukar hotuna da shi da amayar sa.


"Ina wuni Yaya Hisham" Amaal ta gayshe shi


"Lafiya lau kanwar mu. Ko ince yayar mu " ya fada yana kallon yusra. Sukayi daria baki daya harda Amaal din..


Yusra ta dauke su hotuna duka su ukun ta kuma dauke su su biyu itada Hisham sannan ta dauki Hisham da Amaal.


Data tashi saka hotunan a status sai wanda Amaal take da Hisham taje ta saka only view by Al-mustapha wato iya shi kadai ze ganshi. So take ya kulu sosai saboda bashida masaniyar daurin auren Amaal da shi kansa, ance kar a gaya masa tukun.


Haka dai aka karasa shagulgulan biki...aka Kai amarya yusra gidan ta.. Amaal kuma tana sashen Hayateey dinta tukunna.


Yan uwa da abokan arzuka duk suka tattafi. Kandem estate ta zama sai wadanda ke cikin ta kawai..




*ENGLAND*
(MANCHESTER)




Yana daga kwance akan gadon sa.... Ya juya ya hararo wayar sa daya kashe ta gaba daya ..


Ya sauke ajiyar zuciya ya kunna yana dan bubbuga kasanta. Tana karasa kunnuwa ya budata da face id ya shiga ciki bayan ya kunna wifi


Sakonni ne sukai ta shigowa wayar sa... Na sauran kafafen social media dana text messages. Messages dinsa ya shiga rututu gasunan na su Habibi Talba, Aayan, Yusra,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login