Showing 90001 words to 93000 words out of 95238 words
Chapter 31 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt
bar aka bude kusa da office... My poor baby.. Allah yabada sa'ar karatu kinji? I love and miss you soo much...Tausayi da tausasawa su ake kira “so” kowa yana da wacce yake so, Ni ke nake so.... Na ke kuma kauna fiye da kalmomi... Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba...Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina kaunar ki sosai...Zan zo na dauke ki da kai na mun karasa meeting din Ina compiling details dinne kawai.."
Tana daga wayar ta taga reply din sa.. Nan da nan ta karanta tana murmushi...Ta manna wayar a kirjin ta tana lumshe idanu hadi da sauke zuciya... Farin ciki ya bayyana a fuskar ta ji take inama yana kusa da ita kawai...
Lecturer din yana gama lectures dinsa ya fita... Daliban kowa ya dinga hamdala saboda baki daya babu dadi lakcar ranar...
Suna zaune da su Zaarah su ma kafin direbobin su suzo daukar su. Chan sai ga tunkarowar motar Al-mustapha department din na su..
A hankali ya karasa parking motar ya bude ya fita... Tana ganin sa ta mike ya nufeta da sauri yana murmushi, daliban nata kallon su suna admiring din su.
"Ina wuni?" Su Zaarah suka hada baki wajen gayshe shi
"Alhamdulillah... Sannun ku...muje ko love?"
"Yeah... Bye!! Ladies" Amaal ta daga musu hannu tana musu gwalo suna dariya.
Bude mata gaban motar yayi ta shiga, daliban kowa nata,
"Awwwwwnnnn"
Sannan ya koma mazaunin sa ya zauna ya tashi motar bakin sa dauke da addua,
"Sannu Baby love..."
"Sannun mu Boothang"
"Me kike so ki ci yanzu?"
"A koshe na ke"
"Banason musu... Abincin school me ze miki? Bari mu karasa la comida corner sai muyi takeaway"
"Tohm..Allah ya saka maka da alkhairi ya kara maka budi me albarka"
"Aameen zumaa taa"
Yar dariyar data rike ta saki sosai tana kallon sa,
"Bana ce ka dena fadar sunan nan ba? Haba baby"
"Akan me zan dai na fada? Ai banyi karya ba, Ke kin ma fi zumar... Allah dai ya karawa daadi daadi"
Amaal ta rufe fuskar ta da tafukan hannuwan ta.. duk sanda ya fadi haka kunya ce take mata dabaibayi..
Haka dai suka cigaba da tafiya a motar suna hirarrakin su na soyayya kamar wasu saurayi da budurwa.. Daga nan suka biya wajen sayar da abincin sukayi ordering favorites din su suka kaama hanyar gidah..
Amaal ta dube shi tana rau rau da idanu, duk sanda dama take son wani abun da haka take farawa,
Ya dubeta yana gimtse dariyar data taho mai, Yasan abunda zata fada... Yace,
"Ya akai? Uhm? Waya taba mun rabin rai na?"
"Kai ne mana..."
"Ni kuma? Da nayi me lover?" Ya tambayeta cike da kulawa.
Ya gangara bakin titi yayi parking motar, Ya juya baaki daya yana fuskantar ta ya sake cewa,
"I'm all ears.... Banason fushin ki Boo, Meya faru? Uhm? Menayi? Uhmmm?"
Tana lankwasa hannuwanta cike da turo bakin ta gaba cikin shagwaba tace,
"Ka 'ki ka kai ni gidan Yaya Yusra, Ta zazzo ita har tace tayi fushi mun ki zuwa... Kace zaka kai ni, ko yaushe idan na maka magana, sai kace abari sai gobe, sai jibi ranakun nata wucewa"
Ya saka hannun sa ya lakuce mata kumatu yana murmushi yace,
"Tuba nake gimbiyar mata... Kiyi mun afuwa dan Allah... Inshaa Allah gobe da yardar Allah zamu je kinji? Bar fushi kinji? Kin hakura? Kin yafe mun?"
Ta kada kai da sauri, tana goge dan guntun hawayen da ke zurara daga idanun ta,
"That's my baby girl.... Kin hakura?"
"Uhm"
"Toh Alhamdulillah..."
Ya tashi motar suka cigaba da tafiya suna hira suna dariya, haka suka karasa gidah gwanin ban sha'awa..
Tare suka ci abincin, suka yi wanka tare hadi da tsarki... Al-mustapha ya fita masallaci yayi sallah. Daya dawo kuma ya tayata assignment din da aka basu kamar ko da yaushe.. kasancewar fannin karatun su daya, na architecture. duk abunda ya sha mata, kai shi take tuntuba....
--------------------
*Haka* rayuwar ta cigaba da garawa... Safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare.... Lalle Allah mabuwayi ne gagara misali..
Kowanne bangare na cikin labarin nan an samu karuwa ta fannin farin ciki da kuma akasin hakan, domin daman gaba daya haka rayuwar ta gaada. Yau da daadi gobe babu...
Su Ikram dasu Najla duk an kawo kudaden auren su an kuma yi tambayar aure tuni... Lefe ake jira akawo. Don an sassaka musu rana gaba daya.. Sarki Junaid da kansa ya taara su baki dayan iyalan nasa yace kowacce ta futo da mijin aure tunda suna da masoyan a kasa ga karamar kanwar su nan Amaal tayi biyayya an aurar da ita tana zaune agidan mijin ta. Don haka suma kowacce ta futo da wanda take so a aurar da ita. Haka suma mazan yace duk su fadi inda suke neman auren aje a tattambayo a hada a aurar da su baki daya. Ya babba su jari mai tsoka kowannen su ciki harda Amaal dake gidan auren ta..
Hindu ce kawai ke gallafiri ba mijin auren, Ba tada wani wanda yake sonta a kasa. Kullum sai ta zubar da hawayen bakin ciki....
Ta shirya zata futa zuwa computer school din da take zuwa ta nufi inda motocin gidan suke don anan direbobin suke gaba daya a zazzaune..
Ta sha mamaki kwarai matuka data ga ba mota ko daya kowanne ya futa kenan..? Taja ta tsaya tana taune kasan murfin biron data saka a baki...
Chan sai ga motar Aayan ta tunkari wajen... Tana hango shi ta dashare baki tana tsayar da shi.. alokacin Hamid ya nufi motar sa shima zai shiga,
"Yaya Aaayan"
"Na'am sis Hindu... "
"Ina kwana?"
"Lafiya lau... Wani abun kike jira ne?"
"Eh! Banga drivers ko daya bane zanje school ne"
Aayaan ya duba agogon hannun sa yana kallonta yafe,
"Ayya gsshi sauri nake dana kai ki"
"Bakomai .... Nasan yanzu wani zai dawo"
"To shikenan sai kin dawo"
"Yauwa"
Motar sa yaja yayi gaba, tabi bayan sa da kallo tana tabe baki
Hamid dake dubanta yayi murmushi. Ya shiga motar sa ya tashe ta ya karasa har gaban Hindun yana zuge gilashi yace,
"Zo na sauke ki"
"Banaso"" Tayi gaba tana hade rai
Ya sake binta da motar yana cewa,
"Haba hindatullah.... Dan Allah kizo na sauke ki.... Kinji?"
"Wai dan Allah meye darangami na da kai? Haba kacika shiga lamarin da banaka ba"
Hamid yayi murmushi yace,
"Lefi ne kenan daga temako?"
"Banason temakon na ka nace"
"Ki temaka kizo na kai ki"
Hindu tayi kwafa ta dube shi a shake tace,
"Idan na shiga ba zaka sake shiga lammurana ba ka amince?"
"Shigo... Naji"
Ya zare lock din daya saka. Ta shiga tana eani yauki... Ya bita da kallo yana mrunushi yace,
"Baki gayshe ni ba"
"Toh sannu"
"Toh sannu ai ba gaisuwa ba ce.. well akace durkusawa waada ba gajiyawa bane.. barka da safiya hindatullah... Fatan kin tashi lafiya?"
"Da ban tashi lafiya ba zaka ganni haka ne?"
"Tuba nake.... Ina ne inda zaa sauke ki?"
Ya ja motar da sauri suka futa daga cikin kandem estate din..
"Second corner by your left... Sai ka shiga you turn na farko by your right adjacent to kinkin mart, nan zan suaka"
"Okay computer school dinnan?"
"Uhm.."
Hamid yayi murmushi, shi dariya Hindu take sa shi sam bakaken maganganun da da hargagiyar ta basa sha masa kai... Ya sauketa har kofar makarantar ta hude zata futa taji lock
"Bude mun na fita mana meye haka?"
"Calm down! Dan ALLAH kinsan dai bazan sace ki ba ko?"
"Yo waya sani wannan abu a dubu?"
"Toh Allah ya kiyaye .... Dan ALLAH wani temako nakeso kiyi mun kinji?"
Ta kalle shi shakeke tace,
"Temako?"
Ya daga kansa cikin tabbatarwa... Domin gaba daya tun ranar da ya ganta a jami'ar su Amaal dinnan tun daga rannan zuciyar sa ke azalzalar sa da son kasancewar Hindu a matsayin wadda zaiyi rayuwa da ita. Yana tausayin ta sosai, Kuma yaji yana son ta lokaci daya..
"Kiban number ki"
Hindu ta fashe da dariya tana nuna kanta,
"Ni Hindu ni zan baka number ta? Akan me?"
"To haramun ne? Number ki nake so mana... Kuma yau dinnan a yanzu nake so ki bani, don ba zaki fita daga motar nan bama sai kin karanto mun"
"Lalle baka da lafiya"
"Uhm na yadda ko me zaki fada"
"Bude mun na fita"
"Anki din"
"Ka bude nache"
"Lalle zamu kwanta a haka... " Yayi baya da kujerar sa yana saukar da kansa zai kwanta tace,
"Wane kalar rashin mutunci ne wannan eh?"
"Ssssssh Hindu ki dinga tausasa harshen ki kefa macece.... Kinji?"
"Ba zan tausasa ba"
"Rokon ki nake ni dai... Ina kallon ki ne tamkar Amaal kanwata.."
"Ba abunda ya hadani da kai da ita"
Hamid yayi murmushi yace,
"Ni bana wani jan magana... straight to the point na ke...Number ki nake so saboda I like you...." Ya fada yana daga nata kafada
Hindu tayi shiru... Gaba daya ko da wasa bata taba kawo haka ba. Duk sai ta dubibice,
"Budemun na fita.."
"Naki din"
"Dan Allah ka bude mun"
"Zan bude idan kika karanto mun number ta ki"
Ta dan saci kallon sa. Kyakkyawar ne na ajin karshe don har yafi Habibi Talba kyau. Sai dai kwafsin dan uwan Hajiya jamila ne kishiyar mahaifiyar ta. Ta yamutsa fuska tace
"Taya zaka so ni kasan dai matsalar da take tsakanin mu ko?"
"Ta ke tsananin su dai.... Hindu alakar mu bata shafi nan ba... Mu rufe kunnuwan mu muyi abinda ya dace ai Allah be hana ba. Zan samu Hayateey na gaya mata abunda nake ji akan ki. Ni wallahi tsakani da Allah nake kaunar ki tun ranar da na ganku dinnan a AUN... Zaki bani ko ba zaki bani ba?"
Hindu tayi shiru ... Idan ta hanashin tana da wanda yake sonta ne? Ko kare baya zuwa wajenta . Bata da kowa ba me zuwa zance,
"Ina wayar?"
ya dakko da sauri ya mika mata ta karba ta saka masa number
Sai daya kira ya tabbatar number tace tayi ringing, kuma tayi saving alokacin tukun sannan yace,
"Karfe nawa zaki tashi nazo na dauke ki?"
"Uku"
"Toh shikenan Allah yabada sa'ar karatu.. kinji?"
Hindu tayi masa murmushi ta daga masa hannu ta shige ciki shi kuma yaja motar ya tafi...
Kamar wasa abu sai ya zama gaske.. zazzafar kauna ta shiga tsakanin Hindu da Hamid. Ya samu Hajiya jamila da sarki Junaid da maganar dukan su suka amince sun kuma bashi goyon baya. Ya sake samun Amaal da maganar itama tayi na'am taji dadi sosai...
Ko da Hindu ta samu Hajiya hadiza da zancen da farko kin yarda tayi, sai da Hindun ta sake wayar mata da kai tukun sannan ta amince sukayi ta murna..Har sukaje suka samu Hajiya Jamila aka yayyafi juna gaba daya...
Aka saka ranar auren su suma a tare da sauran gaba daya harda na Aaayan shima
Aka shirya meeting na dangin gaba daya gwanin ban sha'awa. Akayita tunatarwa akan zumunci ana kuma Allah wadai da Kawu Adamu daya kasance BAKON MUNAFIKin da BANA MUTUM DAYA BANE... Don tuni ma kotun shari'ar musulunci ta yanke musu hukunci da shi da mukarraban sa dai dai dai da laifukan da sukayi...
Hajia maryam ta sake gyara zaman gilashin idanun ta tace
"MENENE TUSHEN MUNAFURCI? : 1. Da farko dai Munafurci wata irin cuta ce acikin zuciya, wacce idan ta kama zuciyar, tana cinye imani ne har sai ya zama babu saura. Daga nan sai Mutum ya zama cikakken MUNAFIKI wato WANDA YAKE BAYYANA IMANI AKQN HARSHENSA, AMMA ZUCIYARSA TANA CIKE DA KAFURCI. Munafukan Farko wadanda suka zauna zamani guda tare da Manzon Allah (saww) sun kasance SUNA SALLAH, SUNA AZUMI, KUMA SUNA RAKA MANZON ALLAH (SAWW) WAJEN YAQI AWASU LOKUTAN. Amma duk da haka Allah (swt) yace “SU FASIQAI NE” Awani wajen ma Allah yayi wahayi ga Annabinsa (saww) cewa : “HAR ABADA KAR KA QARA YIN SALLAH ABISA ‘DAYANSU IDAN YA MUTU. KUMA KAR KA QARA TSAYAWA KAN QABARINSA. SABODA YADDA LAMARIN YAKE, SU SUN KAFIRCE MA ALLAH DA MANZONSA KUMA SUN MUTU SUNA FASIQANCI”. (Suratul Taubah ayah ta 84). SUBHANALLAH!!! Awani wajen kuma Allah ya gaya ma Annabinsa cewa: “DAIDAI NE AGARESU. KO KA NEMA MUSU GAFARA KO KUMA KAR KA NEMA MUSU GAFARA, ALLAH BA ZAI TA’BA YAFE MUSU BA. HAKIKA ALLAH BA YA SHIRYAR DA MUTANE FASIQAI. (YANA YIN AZABA GARESU). (Suratul Munafiqun ayah ta 6). Lallai munafurci ba Qaramar chuta bace.. Idan ta kama zuciyar dan Adam, tana da wahalar ganewa, kuma tana da wahalar warkewa. kuma tana jawowa mai yinta azaba ta har abada. Amma sai dai Munafurci a mahangar hausawa yana da ‘dan bambanci da Munafurci a mahangar Musulunci.. Ya Allah ka tsare mana zukatanmu daga halayen Munafurci. Aamin.... Idan muka waiwayo fannin zumunta... Shin menene ma,
"Ma’anar sada zumunci:
Sada zumunci shi ne kyautatawa da jinkai da bibiyar ’yan uwa (ma’abota zumunci), ta hanyar sadar da dukan alheri gare su, da kawar da dukan sharri daga gare su gwargwadon iko. Ziyartarsu da amsa kira da gayyatarsu da taimaka musu da dukiya da tausasa magana gare su da kawar da kai daga kura-kuransu da yi musu addu’ar alheri, duk bangare ne na sada zumunci.
"Haka Hadisai sun bayyana muhimmancin zumunci, kamar yadda Imam Bukhari da Muslim sun rawaito daga Sayyidina Jubairu dan Mud’im (R.A), ya ce: “Annabi (SAW) ya ce: “Mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba...MUSULUNCI
‘Yan uwantaka da kaunar juna a musulunci babbar ni’ima ce mai tarin muhimmanci kuma wata babbar hanya ce wacce take kiyaye al’umma daga dukkan nau’oi na cutarwa da rarrabuwa, domin za mu ga cewa ta hanyar ne a kan samu hadin kai mai karfi, kuma a kan kasance tare har a yi aiki domin bunkasa addini da warware matsaloli da bukatun al’umma, wanda hakan zai kara taimakawa al’umma su samu yalwatar arziki, dankon-zumunci da kyakkyawar alaka da tarbiyya, kuma su nisanta daga dukkan kaidin makiya na ciki da na waje. Kamar dai yadda za mu iya ganin haka a cikin nassosi na Qur’ani da hadisan Ma’asumai (as).... Alhamdulillahi! Alhamdulillahi! Alhamdulillahi! Allah ya karfafa mana zumuntar mu, ya kara hade kawunan ahalin marigayi Bappah Ardo kandemi gaba daya cikin lumana da kaunar juna da kuma kwanciyar hankula da wadatar zuciya Amin..."
Bayan ta karasa, sauran bappanin kowannen su ya shiga karin haske akan abubuwan da Hajiya ta fadaa. Akaci aka sha har hotuna akayi kamar wani biki. Baki daya kawunan su sun hade babu wata sauran baraaka.
Aka saka shagalin bukukuwan nan da sati biyu masu zuwa.. Akayi bukukuwan na gani na fada a dangi da kasa baki daya... Angwaye da Amare kowanne ya tare a muhallinsa...
Bayan bikin da sati bjyu Al-mustapha da Amaal ma suka tare a sabon gidan su kasancewar an gama ginin gidan yayi kyau sosai, ginin zamani na 3d sama da kasa komai yaji dukiya tayi ta'adi agidan.. suka cigaba da zaman su cikin lumana da kaunar junan su gwanin ban sha'awa....
Tana zaune a sashen Hajiya... Tun da driver ya dakkota a school ta wuce kandem estate wajen Hajiya Maryam anan ta sake yin wanka, taci abinci, ta kwanta a dakin Hajiya abunta har da yin bacci ..
Wayar tace ta fara kara ta dauka da sauri ta kara a kunnenta,
"Ki shirya nazo na dauke ki ..."
"Babes yau daya dai ka bar ni na kwana mana anan please, har na kwanta fa a dakin Hajiya"
"Kinsan dai sarai bazan iya bacci ba idan banji dumin jikin ki ha ko? Gani nan zan karaso mu tafi"
"Ni! Ni! Ni...gaskia anan zan kwana.."
Al-mustapha ya gigice ya kashe wayar ya kara gudun da yake a mota ya nufi kandem estate. Tun a mota ya kira Hajiya Maryam bayan sun gaysa yace da ita,
"Bana samun Amaal a waya, Hajiya kice ta karasa shiryawa gani nan na zo daukar ta"
"To dan yaye, Amma har ta kwanta ma fa, Amma bari a taso ta"
Ko kadan baiji kunya ba, ya murje idanun sa da kasa yace
"To Hajiya a gaya matan nagode"..
Murmushi hajiyan tayi data ajiye wayar tasa safiya mai aiki taje ta taso Amaal din. Amaal ta zura hijabin ta tanata kunkuni ta fita parlorn,
"Hajiya dan Allah kice masa yabar ni nayi bacci"
"Banason rigimar dan yaye takwara, Yace yazo daukar taki ma fa, daure ku tafi kinji Allah ya miki albarka"
Don ma kar ya shiga hajiyan tace ya kyale Amaal din. Sai yayi zaman sa amota bayan ya kira Amaal yace ta futo su tafi. Amaal tayiwa Hajiya sallama ta fita
Ya bude mata motar ta shiga ta zauna tanata muzurai. Ruwan daya taho dashi me sanyi ya mika mata yana kanne dariyar dake shirin fita
"Sha ki sanyaya zuciyar ki Maryam"
"Bana sha"
"Haba kyakkyawa ta.... Kiyi mun afuwa kinji...Duk wani abu da zan furta yau a gare ki ba zai wuce, ina son ki ba, ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, sannan kuma kina d’aya daga cikin mutanen da ba zan ta’ba mantawa da su ba har abada a rayuwata.... Sha ruwan nan zuciyar ki ta samu saalama kinji tawaje na.?"
"Na koshi... "
Ya danyi kasa da kansa yana dariya daman yasan zasu kwashe haka. Don haka ya juya kan motar sa suka dauki hanyar gidan su dake wata unguwa ta daban ba dai nisa can sosai da kandem estate.
Suna zuwa ta wuce sama fuuu. Ta shige dakin ta . Bandaki ta shiga ta sake yin wanka ta zura kayan bacci tabi lafiyar gado ta kwanta taja bargo ta lullube kanta
Al-mustapha ma dakinsa ya shige yayi wanka ya sake kayan bacci ya nufi dakin nata dauke da wata 🌹 flower a hannun sa.. ya shiga bakinsa dauke da sallama Amaal dake cikin bargo ta amsa masa.
Ya sadaada ya shige cikin bargon jikin sa har yana rawa,
"Maaaryam"
"Ya akai?"
"Dan Allah dan girman Allah dan ALLAH tashi muyi magana"
Sunan Allah da yaketa hadata dashi yasa ta tashi zaune tana kallon gefe,
"Ni me lefi ne awajen ki, Dan Allah kiyafe mun. Allah bazan iya kwana bake a kusa dani ba shiyasa... Kinji?"
"Naji"
"Ki yafemun, Dan Allah... Ga flower din ban hakuri ta soyayya kinji? Rose flower ce "
"Madalla.. ka gama?"
"Kin yafemun?"
"Uhm"
"To kiyi dariya"
"Banajin yi"
"Ba kyajin yin dariyar?"
"Uhm"
"Tohm kwanta habibty"
Kwanciya tayi ta dakko pillow ta jera a tsakanin su. Al-mustapha yayi dariya yana kallon ta. Ta kwanta tana juya masa baya hade da kashe futilun side lamp.
Sai da yabari ta kwanta zata fara bacci ya sadaada jikin ta ya rungumeta, duk yadda tayi ta kwace ya hanata ya kashe mata jiki gaba daya, da zafafan sumbar da yake bawa duk wani sashe na jikin ta. A dole ta hakura ta saki jikinta suka gwangwaje daren ranar da