Showing 33001 words to 36000 words out of 95238 words
Chapter 12 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt
SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR โKASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at๐
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐
09033181070
VIP๐ฅ๐ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*๐ฅฐ
Zafafa๐ซถ๐ฅ
[9/1, 10:31 PM] Hafsaat๐: _BM_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_PAGE: 23_
_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._
___
*A* kishingide yake akan doguwar kujerar da ke hadadden parlorn sa na alfama..
Ya yinda hannun sa ke rike da wayar sa yana dannawa..
Kawu Adamu ne da Bappah Nuraddeen suka shiga parlorn na sa. Yana ganin su ya tashi daga kishingiden da yake.
"Ah ranka ya dade koma ka jingina dan Allah."
Bappah Nuraddeen ya fada masa yana dariya,
"Wane mutum Yaya? Barkan ku da yammaci."
"Barkan ka ranka ya dade"
"Barka kadai"
Dariya suka bashi... Ya danyi murmushi kawai, Cike da girmamawa yace da su,
"Fatan kuna cikin koshin lafiya Amin.."
"Aameen"
"Aameen ranka ya dade."
Kawu Adamu ya dan nisa kafin ya juya ya kalli bappah Nuraddeen.
"Ka kira shi kuma?"
"Wallahi na gaya masa"
"Kawu wani abun ne ya faru?"
"Meeting ne kawai zamuyi... Abdullahi baya kusa shi yasa nace to ayi iua kudin?"
"Lafiya?"
"Alhamdulillah kakka samu."
Suna dai zaune bayan dibar wani lokaci sai gashi ya shiga cikin inda suke. Ya nemi waje daga can gefe ya zauna yana muzurai,
"Yaya da Kawu barkan ku."
"Barka kadai"
"Barkan mu Bappan Hajiya"
"Yaya barka... Fatan kana lafiya?" Sarki Junaid ya gayshe da yayan nasa,
Bai amsa ba ya shiga danna wayar da ke hannun sa,
"Jalaludden yana maka magana"
"Da ba kalau nake ba zaka ganni ne? Makiri.."
"Haba jalaludden."
"Ba girman ka bane."
"Kayi mun gafara Yaya" sarki Junaid ya fada kansa a kasa."
"Wai maganar me za'a tattauna ne da har za'a janyo ni nan? Idan wani abune daya danganci sarkin ku to fa na gaya muku ku cireni aciki. Wallahi wallahi bazan yi ba"
"Na isa da kai?" Kawu Adamu ya tambaye shi yana mai nuni da kansa
"Ka isa mana."
"To ka saurara da wadannan magnganun ka bamu hankalin ka nan."
Komawa yayi ya zauna yanata cicije lebe hadi da hahhade ransa,
Kawu Adamu ya sauke katuwar bahaguwar zuciya yace,
"Jikin alkali ya matsa sosai..... Har bansan me zan iya cewa ba. Astagfirullah" Kawu Adamu ya fada cikin numfasawa,
"Na ma yiwa doctor nogan magana yace mu sake hakuri.... A kuma cigaba da addua kawai" Bappah Nuraddeen ya bashi amsa.
"To dama duk cutar da akeyi da sihiri kuma aketa cigaba da hura mata wuta ai tana da wahala"
"Jalaludden meya kawo wannan maganar?"
"Maganar gaskiya ce Yaya..Ni fa bana rufe rufe.. Wanda yayi yasan kansa Kuma kuuma kun sani"
Sarki Junaid na daga kan kujerar sa a zaune da yake kai bai ce komai ba. Yayi murmushin takaicin maganar jalaludden yayan nasa.
"Banason wannan maganar karka sake... Ni abunda ya sa na nemi muyi wannan zaman saboda mu kamo bakin zaren mu gano hanyar da zamubi..."
"To Kawu magana ce ta gaskiya... Kaf kandemi kowa yasan wanene me makarkashiyar dukkanin abubuwan da ke faruwa. Ciwon baban nan tun kan ya kai haka kowa ya sa
"Ya isa dakata. Haba jalaludden kana ji Kawu yana kayi shiru amman ka cigaba da magana?"
Kawu Adamu ya girgiza kai kawai ya dubi sarki junaid dake binsu da kallo kawai tunda sika fadar maganar ba ya tanka su,
"Ranka ya dade me kake gani akan wannan batu?"
"Cuta lokaci daya take shiga... Haka zalika fitar ta ta kan dau lokaci. Sannan sai yadda Allah ya tsara a kudurin sa... Fatana Allah ya bashi lafiya mai dorewa yasa kaffarane... "
"Kaji ko? Ai dama ba abunda zai faru da zai wuce wannan. Yo idan ba shine wanda ya sakawa ubansa ciwo ba zai fadi haka ne? Kun kalle shi yana magana cikin gadara da izza yaushe ya zama me rikon kwaryar ne da har yake ganin kansa wani ne? To ku gaya masa ni..
"Dan Allah jalaludden ya isa haka Nan...Kawu kayi hakuri dan Allah idan aka sake shirya zaman ayi gaba daya da kowa."
"Hakan yayi Nuruddeen Allah ya maka albarka."
Fuuu jalaludden ya mike bayan ya kade rigar sa akan su ya mike cikin fushi yana mai jera tsaki wani bayan wanji.
Basu wani kara daukar lokaci ba suma suka yiwa sarki Junaidu sallama suka tafi.
Yana daga zaune akan kujerar sa yana mamakin dukkanin komai. Ya kasa gane wutar kiyayyar da ke ruruwa a zuciyar jalaludden da har iyalan sa ma ya na neman hana su zumunci da shi.
Ya sauke katuwar zuciya ya amsa sallamar da ya jiyo muryar amaal tanayi,
Har gaban sa taje ta rissina ta gayshe shi cike da girmamawa ya amsa yana saka mata albarka.
Maganar wasu kudi ta masa na handouts da take so da wasu littafai da akace su nema..
Tana dai zaune bayan sun gama magana ya mata transfer kudin fiye da yadda ta bukata yace da ita,
"Me yake damun ki ne uwata?"
Amaal ta fashe da kuka tana jujjuya kai duk yadda taso ta rike kukan sai da ya zubo tace,
"Abbiey kayi hakuri.... Zuciyata ta kasa amincewa na kasa yadda"
"Ina sauraron ki uwata..share hawayen ki ki dena kuka kinji uwata? Maza maza fadamun damuwar ki kinji? "
Ta kada kai tana jan majina da ke taho mata ta hancin ta saka mata mura saboda kukan da take.
"Gayamun mana"
Ahankali cikin kasa da kai hadi da lankwasa hannuwanta ta labarta masa komai ta karkare da,
"Abbiey har mafarkai na ke akan hakan... Tabbas kakaa ana masa sihiri."
Shiru yayi na dan wani lokavi kagij yace,
"Mahaifiyar ki ta gayamun yadda kika fada... Kuma kamar yadda ta gaya mikin nima haka zance ki dena zato ko da ya zamanto gaskia... Sannan ni da sauran bappanin ku yanzu suka bar nan ma zamu yi duba akai sosai... Kinji ko?"
"Tohm Bappah"
"Ba wai bance zancen ki ba haka bane... Fiye da haka ma zata faru... Sai dai zaton ne banaso ki saka a ranki.. na kuma ji dadi da nuna kulawar ki kwarai matuka... Allah ya miki albarka."
"Allahumma Aameen Bappah.. Sai da safe"
"Allah ya tashe mu lafiya... Allah ya miki albarka kinji? Ki cire komai a ranki kinji ko? In shaa Allah Khairan "
"Tohm abbiey.. sai da safe"
Ta wuce sashen su ta yo wanka ta kwanta bayan tayi alwala tayi azkhar. Bata jima ba bayan ta seta alarm bacci ya dauke ta.
*WASHE-GARI*
Da wuri ta tashi ta tafi makaranta, Ta siyo handouts da sauran abubuwan da zata bukata sannan ta dawo gidah
Kai tsaye ta wuce sashen Hajiya dauke da littafan ta a hannu wasu a jaka. Sanye cikin doguwar rigar A shape ta yafa wadataccen mayafi daya shiga da kayan.
Tana shiga taja tayi turus ganin sa ale ale a doguwar kujerar Hajiya yana danna waya. Yayinda Hajiya ke daga gefen dayar kujerar da rediyo sakale a kunnen ta,
Sallama tayi suka amsa. Hajiyan ta yi murmushi,
"Takwara.."
"Na'am Hajiya.. barkan ku da safiya, An tashi lafiya?"
"Barka kadai takwarata.. daga makaranta ake ne ko tafiya zaki?"
"Dawowa ta kenan"
"Ajiye wayar sarkin yan danna waya.. ga kanwar ka baku gaysa ba."
Zuruf sai ga shigowar Aaayan ,
"Gaskia da alama bai santaba."
Tsaki yaja cike da takaicin maganar aayan yace,
"Maryaam Amaal me sunan Hajiyan din ce bansani ba?
Tsananin mamaki ne ya cikata ta dago da sauri dai dai lokacin da shima idanun sa akanta suke. Idanun su suka hadu... kallon su ya sarqe dana juna...
..
_ADVERT๐_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR โKASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at๐
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan๐
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan๐
09033181070
VIP๐ฅ๐ฏ
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*๐ฅฐ
Zafafa๐ซถ๐ฅ
[9/4, 5:36 PM] Hafsaat๐: _BM_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_PAGE: 24_
_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._
___
*Da* sauri Amaal ta janye nata idanun.. Ta saka hannun ta akan carpet tana jan gashin carpet din.
"Menene kike kallo naa?" Ta jiyo muryar sa...
Abun ya bata mamaki... Wai take kallon sa bayan shine ya fara kallon ta tsautsayi yasa ta daga kai suka hada idanuwan su.. yanzun kuma ta janye kanta yana kan carpet amman ya ce wai meye take kallon sa.
"Kaji wani zancen... Kai da wane idanun kasan tana kallon ka?" Aayaan ya tambaye shi yana hararar sa
"Kai ai banza ne..."
"To kallo kuma ame yake dan yaye? Ko ka manta kai din yayan ta ne?"
"A'a Hajiya... Kawai de naga tanata bi na da kallo..Banason kallo ne shi yasa"
Amaal tayi murmushi.. Gaba daya lamarin dariya ma ya bata. Tayi murmushin da yafu kuka ciwo kawai. Gefe daya kuma, Maganganun sa sun bata mamaki kwarai matuka.
"Ni ban kalle ka ba.." Ta fada ranta na ta susa..
"Rabu da shi takwara ta."
"Bari na tafi hajiya"
"Ah na hira zaki tafi? Ki bari mana zuwa anjima"
"Tohm" neman waje tayi ta sake zama badan taso bam sai dan batasan musu da Hajiya.
Laptop din dake gefen sa ya dauka ya daga robar ruwa ya sha. Yana mai danna laptop din bakin sa na motsawa a hankali da alama magana yake, amman maganar da ta shafu abunda yake a kan na'urar.
Aayaan ya zura kai yana kallon computer da Al-mustapha yake dannawa,
"Wow... Woah... Omoo"
"Yayi kyau?"
"Sosai ma... Ai angama finishing dinma"
"An gama sai yan abubuwan da ba zaa rasa ba.."
"Gaskia na taya ka murna"
"Nagode... Hajiya kin ga"
Ya tashi ya koma kusa da hajiyan ya dora mata laptop din akan cinyar ta yana nuna mata hotunan da faifen bidiyon,
"Har an kammala kenan?"
"Eh...."
"Ma shaa Allahu. Allah ya sanya alkhairi da albarka yasa a bude a sa'a Amin"
"Allahumma Aameen hajiyata"
"Takwara kinga ofishin Dan yaye da ya gina"
Dan daga kai amaal tayi ta dubi laptop din ta kauda kanta gefe,
"Nagani"
Tsaki Al-mustapha yaja... Ya samu kansa da tashi daga kusa da hajiyan yana hade rai yace
"Yarinyar nan na lura batada kunya."
"Gaskia musty fresh ka dena abunda kake. Ni banga abunda amaal ta maka ba wallahi. Kai kadai kake ta hawa doron zuciya."
"Allah ya baka.hakuri... ... Hajiya... Yaa Aayan sai da safe"
"Favorite! wait."
"Inaa fucewa tayi da sauri bata tsaya jin kiran da Aayaan yake mata ba. Ya cimmata da sauri,
"Kiyi hakuri favorite... Kinji?"
Wani kuka ne ya kufce mata hawaye suka shiga zuba daga idanun ta cikin muryaa mai tattare da bacin rai tace,
"Bansan menawa Yaya Al-mustapha ba... Haka kawai ya tsane ni."
"Rabu da dan wahala... Halayyar sa ce sai a hankali.. wani jrin nutum ne. Kiyi hakuri kinji?"
"Bakomai... Ya wuce."
Da sauri ta shige sashen su tana goge idanun nata sosai. Ta tsaya awajen kitchen ta goge idanun tas tukun sannan ta shiga dakin su bakin ta dauke da sallama
Ikhram data gano su ta window itada Aayan lokacin suna tsaye tace,
"Kede yarinyar nan kin shiga uku da bin maza... Hisham, Aaayan, Hamid yake kowa... ? Yanzu Kuma kin fara rawar kafa da Yaya Aayaan kinaso ya hada ki da Yaya Al-mustapha. To shi dai Yaya Al-mustapha ba tsaran ki bane. Ya na da class bayaa kula classless.. idan kikaga maza seki kasa zaune ki kasa tsaye"
'Yan dakin suka saka dariya gaba daya... Amaal na daga kwance tana Jin komai. Sai kyalkyala dariya suke marar dadi suna tafa hannuwan su...
"Ai yarinyar nan son maza ne fal acikin ta..."
Ta kasa danne maganganun da suke ta yaada mata don haka ta mike daga kwance da take, Abunda bata taba yi ba.
"Dan allah ya isa haka.....Ban taba tanka muku ba sai yau. Ku dai na aibata ni akan abunda bakuda masaniya akai. Yaya aayan first cousin din mu ne haka Kuma Yaya Hisham dan babban aminin abbiey ne dika cikin su ba Wanda muke wata alaka fyace ta Yan uwantaka..Kuma su sika fara nema na ba ni nake musu magana ba. Yaya Al-mustapha da kuke ta kamo sunan sa kuma ko sanin sa ban ba. Ina dai jin sunan sa.. sai wannan zuwan na su ku tambaye su ku ji..Sai wadanne mazan kuma? Dan Allah respect yourselves... Dan Allah na roke ku"
"Ahh iyye..Yaya Hindu kinaji? Ah alle yarinya ta zama ishasshiya"
"Baki ga ma na kasa mayar mata ba? Ai mamaki ne ya cika ni... Kinsanmace idan ta fara sanin maza."
Amaal data juya zata kwanta sai ta fasa. Saboda maganr Hindu ta bata mata rai,
"Haba Yaya Hindu... Gaskia karki sake gayamun wannan maganar."
"Ke ni kike cewa gaskia kar na sake abu?" Tayo kanta zata mare ta.
Amaal ta mike da sauri ta goche,
"Ba magana na gaya miki ba Yaya... Amma ki duba kiga abunda kika ce mun fa"
"To karya nauo?"
"Yo gaskia ni ba haka nake ba.. Allah shahidi"
"Kai Kai Kai wallahi yarinyar nan idanun ta sun bude. Ke kinsan me kike fada kuwa?" Ikram ta fada tana tafa hannuwa.
Hindu ta sake kai hannu zata daketa amaal ta goche...
"Yar iskar kawai..."
"Yaya Hindu... Ina girmama ku duka... Zan iya tabbatarwa kuma kun sani bantaba musayar yawu da ku ba. Amma cin fuskar da kuke akai na yayi yawa. Wadannan maganganun da kuke ta fada dik wanda aka gayawa acikin ku sai inda karfin sa ya karl e. Musanman idan kagaggen zance ne akan ka ba gaskiya bane.."
"Wa ke miki karyar?"
Amaal bata sake cewa komai ba. Ta haye kan gado ta kwanta taja bargo hadi da kashe bed side lamp dake gefen drawer din jikin gadon ta.
"Zan koya miki hankali.... Duk karatun da kika zubar zaki kwashe ki mayar kan ki marar kunya futsararriya."
Amaal na jinsu ta bargo ta sake ja ta lullube kanta.. Ta na jiyo su sunata mayar da zancen suna zagin ta bata sake bi takan su ba . Bacci ya dauke tah..
_______-----------_______------------_______
Da ke mid semester break suke yi... Hakan yasa tana tashi daga bacci ta nufi sashen mahaifiyar ta.
A parlor ta tarar da ita tana shafa kulaccam kamshi ya gauraye ciki da wajen sa.
"Hayateey barka da safiya"
"Barkan mu dai habity... Kin tashi lafiya?"
"Alhamdulillah...... Hayateey kinji kamshi kuwa.. Allah na dauka turaren wuta aka saka."
"Kadan ma fa wai nake lakuta na shafa.. Kulaccam din kayan turaren yerwa incense and more (08095215215) ne .. kinsan kayanta na da kyau ba algus."
"Gaskia kayanta nada kyau Allah kaman kamfanin haramein oud da kin shigo sai kamshin oud"
"Eh ai oudi scent ce wannan... Gashi a rubuce "oud oudi kulaccam by yerwa incense and more..."
"Ma shaa Allah... Ta fruity scent dinma kadan na shafa kaman ka lashe jikin ka wallahi me kamshin vanilla dinnan da strawberry "
"Kya lasowa kanki asibiti kuwa"
Suka tuntsire da dariya gaba daya..
"Ina Yaya Hamid?"
"Ya tafi office ... Tun sassafe"
"Allah sarki Yaya.. Allah ya temaka Amin"
"Aamin Aamin"
"Kinje kin gayda Hajiya?"
"A'ah..."
"Hajiyan taki kuma yau?"
"Wannan Yaya Al-mustapha dinne ya tsaneni Hayateey.kuma kullum yana can."
"Ki dena cewa an tsane ki ba kyau. Bai tsane ki ba. Shi mutum ne kawai marar kwaramniya.. Batun kullum kina ganin sa acan kuma ita ta yaye shi. Yafu shakuwa da ita akan iyayen sa. Dan ko komawar su waje dakyar yabi su sai da akayi da gaske.."
"Hayateey kinsan me ya yace akai na jiya?",
"A'ah...."
"Ana hira da su Hajiya da Yaa Aayan sai can wai Ina kallon sa shi bayason kallo..."
"To ke meye na kallon sa uhm?"
"Allah Hayateey bakisan da yanayin daya bafada ba..Kuma shi ya fara kallo na ina daga kai muka hada ido.. sai kuma yace banda kunya... Wai akan menene ma yauwa akan yana nunawa Hajiya saban office dinsa a laptop. Hajiya tace nagani? nace nagani."
"Bakyau yiwa babba rashin kunya. Nasan dai ba halin ki bane. An kuma sheda bakya yi. Aman dai bana nan akayi wannan don haka bazan tabbatar da kinyi masa ba ko ba kiyii ba"
"Allah ki tanbayi Yaya aayan shine ma yai ta ban hakuri da zan shigo wajen ki sai kawai na wucs bangaren mu. Inata kuka fa. Naje can ma kuma suka taru akai na suna gasamun magnganu marasa dadi ... Yau dai na kasa hakuri nache banaso su dena mun"
Hajiya jamila ta dan daga Kai ta kalleta sai kuma ta saukar da shi kan robar kulaccam fdn hannunta tana dubawa tace,
"Allah ya kyauta.... Nide na gaya miki ba sa'oinki bane... Ki dena bi ta kan duk abubuwan da zasu biki da shi"
"Har fa mari na ya Hindu zatai ... Sunata fadar magana maza maza.. Ina kulaa maza waye waye. Walahi Hayateey ko a school bana bi ta kan course mates dinmu mazan. Anan gidah Yaya ayaan ne shima kuma shike kira na awaya ko chat . Sai Yaya Hisham wallahi shima shi ya karbi number na ai na gaya miki tun Ina ssce yana coaching dina wasu abubuwan..Yaya Al-mustapha dinnan kuwa wlh bansan shi ba. Na san dai sunan sa"
"Allah ya rufa asiri... Ni dai na gaya miki a ko'ina kike ki tsare nutincin kan ki ... Baki da muharraami sai wanda kuka fito tsatso daya...Allah ya cigaba da kare ki ya tsare miki mutuncin ki har gaban abadan"
"Allahumma Aameen Hayateey.."
"Bari na duba Hajiya"
"To sai kin dawo. Ki