Showing 30001 words to 33000 words out of 95238 words
Chapter 11 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt
ganin sa da magana da shi har yan level 4 amman yau yar level one karamar yarinya yanata jan ta da hira amman tana sha masa kamshi
Ya samu kansa da jin haushin kansa. Duk da haka dai bai hakura ba ya sake ce mata,
"Care for a free ride?"
Tayi hanzarin girgiza masa kanta.. cikin sanyin murya tace,
"Nagode..... Za'a zo a dauke ni"
"Ya sunan ki?"
"Amaal...."
"Amaal..." Ya maimaita sunan yana jan sa.
Kada masa kai kawai tayi. Ta dan ketare ta gefen sa saboda yadda wayar ta tafara ringing ,
"An zo dauka na." Ta fada tayi gaba abunta
Juyawa yayi yana bin bayan ta da kallo. Wai yau abunda yake wa wadan su shi ake yiwa,
Don haka ya girgiza kai kawai yana murmushi yayi wajen shima. Yanata sauri zai je airport ya dakko babban aminin sa.
Mota ta bude ta shiga da sauri tana ajiyar zuciya. Gaba daya a tsorace take tunda malamin nasu ya tsaya yana mata magana har kawowar tafiyar sa.
Ta dan juya ta kalle shi ta mudubin baya alokacin dayayi reverse ya haye kan tigi.
"Ranki ya dade wanj abun kike so? " Direban ya tambayeta alokacin daya ga ta bawa mudubin baya nutsuwar ta baki daya tana kallo,
"Bakomai..."
"Muje?"
"Eh.... Muje"
Kai tsaye direban ya dauki hanya daga department dinsu na architecture zuwa kandemi..
Yana kai wa gidah ta nufi sashen su ta ajiye kayan ta. Ta shiga bandaki tayi wanka jadi da dauro alwala.
Kayan ta ta sauya zuwa doguwar riga ta atamfa.. Bata daura dankwali ba sai ta yafe kanta da mayafin karami irin na abaya.
"Ke Dr. Habibi Talba ya fara muku lectures kuwa?" Hindu ta tanbayi Amaal datayai hanyar kofa zata fita,
"Habibi Talba?" Ta maimaita sunan tanason tunowa,
Kanta a sama dai tanata son ta tunano inda taji sunan ta kasa ,
"Eh... Wani gaye me tsawo"
"Gaskia ban gane shi ba"
"Ke banason wasa.
"ko wani ne daya mun magana yau..."
Hindu ta tuntsire da dariya daga karshe taja dogon tsaki
"Habibi ne ze miki magana? Whole habjbj Talba ..gurl stop lying. Ba shi bane gaskia. Shi mata ma basa gaban sa. Baya ma tsayawa yayi magana da mace ko malama ce balle ke level one student. Da yake daukar ku ku wajen dari... Har zai tsame ki ya miki magana ke kadai .."
"Inaga wani ne malaman da yawa.."
Da hannu Hindu ta alamae dataje. Ta koma ta mayar da kanta ta kan pillow tana waka.
Amaal ta fita daga bangaren nasu tayi na mahaifiyar ta.
Suna zaune ita da Hamid dake aiki a computer dake gaban sa...
Ta gayshe da su duka. Suka amsa suna sakar mata murmushi.
"Hirar me ake Hayateey?"
"Hirar farin ciki"
"Akan meye"
"Abbiey dinku ne yace yana son ya dora yayan ki akan wani aiki"
"Ma shaa Allah aikin me?"
"Bai fadw ba tukun "
"Allah sa muji alkhairi"
"Aamin"
"Bari naje na gayshe da Hajiya"
"To sai kin dawo"
Mikewa tayi yar wayat ta a hannun ta ta fita. Har tayi bangaren hajjya sai kuma ta fasa..
Sashen da aka kwantar da kakan nasu ta ta shiga
Shiru ba kowa sai karar sautin al- Quran ni ke tashi ahankali.
Tanata sallama.ba amsa ba. Duk azaton ta ma ko suna can cikin dakin marar lafiyar.
Wata irin karar wahalaliya taji ana saukewa ahankali ga marayan kuka da akeyin ahankali ba sauti sosai. Shima sai ka kasa kai
Da sauri ta kutsa cikin. Ba kowa a babban parlorn sai karar tv da keyi tana nuna faifon bidiyon Aljazeera
Sautin muryoyi take ji suna tashi a dakin da marar lafiyar yake. Har zata murda ta shiga. Sai kuma taji sautin takalman kamar zasu fito daga dakin tayi sauei ta zagaya ta baya dayan window ta tsaya jikinta sai rawa yake..
Ana hango cikin dakin da muryar tasu ta 'yar net data yage ta jikin windon
Hannuwan ta dika biyu ta saka ta toshe bakinta alokacin data hango kakan nasu ya daga hannun sa dakyar yana rokon mutanen biyu da bata ganin fuskar su zai bayan su.
"Dama ashe yana magana.... Ko meyake faruwa? " Ta samu kanta da tanbayar zuciyar ta dake cikin waswasi..
"Dan Allah.... Ku kyale ni haka.. ku kashe ni kawai..."
Hawaye ne suka shiga reto a kyakkywar fuskar ta. Alokacin data hango daya daga cikin mutanen biyu ya dakko wata zundumemiyar allura taf da sirinji ya zurmuka masa
Ya saki kuka me tsuma zuciyar duk wanda ya saurara yace,
"Allah ba zai barku ba.... "
Allurar na gama shiga jikin sa. Ya shiga kakkafe jikin sa yana wani irin tari da sauke numfashi.
Can kuma luuu. Tamkar jikin sa ya shanye. Sai kache kayan wanki haka suka matsae da shi suka kwantar dashi akan gadon. Kaman kayan wanki
Ido kawai yake binsuu da shi. Duk wasu sassa na jikin sa suka sake dena aiki. Sai hawaye dake tsiyaya
Ya koma tamkar mutum mutumi kamar ko da yaushe baya magana sai jdanuwan sa da suke abude kawai. Baya iya motsa komai na jikin sa sai dai ataimaka masa ayi masa dukkanin abubuwa..
Amaal ta sake kafa idanun ta alokacin dataga daya daga cikin mutanen dake sanye da facemask baa ganin sa ya taka stool ya mayar da allurar da sirinjin cikin locker dake can saman gadon wajen ac baa ganin ta...
Neman waje sukayi suka zazzauna akan kujerun dake dakin..
Ba jimawa sai ga bappah jalaludden ya shiga dakin bakinnsa dauke da sallama.
Suna ganin sa suka mimmike sika bashi hannu suka gaysa,
"Kun gama komai?"
"Komai yallabai..."
Suka bashi amsa dukkanin su....
Wayar sa ya dakko... Ya shiga contact list ya danno wata number ya kira.
"Mungode sosai fa.... Sun aiwatar da komai cikin kwarewar su .. Yauwa."
Ya katse kiran ya mayar da wayar sa aljihun yayin da ya shiga taka musu zuwa bakin kofa,
"Ga wannan ku kara da kudin mota"
"Mungode yallabai."
"Muje da godia doctor. Sai wani checkup din kenan ko?"
"Eh."Cewar Dr Faisal..
Raka su yayi har bakin kofar fita suka shiga mota suka tafi. Ya yinda shi Kuma ya dawo ciki ya shiga dakin mahaifin na su ya zauna
Amaal da ke sandare a tsaye ta fita daga cikin sashen baki daya da sauri har tana tuntube jikin ta sai rawa yake.
Sauran kadan ta buge kan Bappah Nuraddeen dake tafiya zai shiga ciki
"Ke meye haka?"
"Ba... Bann... B"
Ta kasa magana gaba daya. Ya lura da ita sosai bata hayyacin ta.
"Me kikeson cewa?"
'ba komai Bappah"
"Kin tabbata?" Ya sake tanbayar ta cike da kulawa
"Eh Bappa"
"To shikenan... Je ki"
Ta wuce da sauri shi kuma ya shige ciki yana mamakin abunda ya sauya mata yanayi baki daya...
Zata shjga sashen Hajiya Maryam kakar su wayar ta tafara kara. Hisham ne ke kiranta. Kamar ba zata dauka ba sai kuma ta dauka ta gayshe shi.
Domin shakuwa sosai ta shiga tsakanin su.... Kullum ne sai ya kira sau nawa... Tun bata saki jikin ta da shi ba har sabo ya wanzu a zukatan su.
Tana karasa amsa kiran nasa ta shiga parlorn hajia bakinta dauke da sallama... Babbar tabarma ce irinta cin abinci dinnan akai aka shimfida a parlorn. Yayin da ma'aikatan ke ta jera abinci. Kana ganin hakan kasan tanadin wasu manyan bakin ake...
Hajiyan ta futo daga cikin daki tana dogaraawa da yar sandar ta. Dai dai lokacin da Aayaan ya shigo ciki shima.
Amaal ta gayshe su duka. Ta zauna a gefen Hajiya daga kasa tana matsa mata kafafun ta,
"Hajiya baki za'ai ne?"
"Eh takwara.... Yayan ku ne zai dawo daga kasar waje. zai dawo gidah gaba daya da zama."
"Yayan mu?" Amaal ta tambaya tana kallon Aayaan. Don bata san wane yayan bane..
"cousin dinki ne zai dawo mana.... Mighty, Al-mustapha jalaludden... Musty fresh
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[8/31, 6:56 PM] Hafsaat💞: _BM_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_PAGE: 22_
_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._
___
"Dan gidan Bappan ku... Kin manta Al-mustaphan? Ko da yake gaskia ba lalle ki iya tunawa ba.." Hajiya kakar su ta fada..
"Favorite baza ki iya tuna Musty Fresh ba?"
Ita dai Amaal shiru tayi baki daya... Don gaskia bata gane shi ba. Ta san dai akwai cousin dinta Al-mustaphan bappah jalaludden amma ta manta kamannin sa.
"Na san sunan sa Hajiya.."
"Amman baki sheda shi a fuska ba ko?"
"Eh"
"Gaskia ba lalle ta iya tuna shi ba... Kece karama a wajen Bappah ko?"
"Eh.."
"Tabbas. Ba zata gane shi ba Hajiya. "
Haka dai sukai ta yar hirar su su uku .. Duk kuwa da Amaal dauriya kawai take tana magana jefi jefi. Gaba daya abubuwan data ji ta kuma gano kawai take tunanowa...
Wayar Aayaan ce ta fara kara ya dauka ya kara a kunnen sa,
"Amma kai banza ne wallahi .. Gani nan to"
Hajiya ta dashare baki... Fuskar ta ta mamaye da farin ciki,
"Shi ne?"
"Eh..... Favorite ga wanda ya doke faadar ki nan awajen Hajiya."
Amaal tayi dariya kawai. Hajiya Maryam ta ce,
"Kowa a bayan takwara yake."
"Ai Hajiya kaf kandemi ciki da wajen ta kowa yasan Al-mustapha ne na gaban goshin ki."
Hajiya tayi murmushi kawai batace komai ba.. Aayaan ya futa ba jimawa sai gashi sun shigo tare
Aayaan ne agaba.. Al-mustapha na biye da shi a baya..
Kamshin turaren jikin sa ne ya fara nuna alamun isowar sa gun... Wani irin kamshi mai sanya nutsuwa da kwanciyar hankali ga duk wanda ya shaaka.
Yana sallama Hajiya na amsawa ta fara tafi,
"Dan yaye dan yaye..." Ta shiha fadar sunan da ta kan kira shi da shi. Dake ita ta yaye shi don haka akwai shakuwa sosai a tsakanin su..
Wajen ta ya nufa da sauri . Suka rungume juna.. sanye yake cikin kananun kaya yan kanti.
Rigar ja me ratsin baki sai wando naki.. kananannden gashin kansa ya kwanta luf.
"Hajiya barka da yammaci.... Na same ku lafiya? Ya jiki jikin naki? Allah yakara miki lafiya da nisan kwana mai amfani"
"Da imanin Allah dan yaye "
"In shaa Allahu Hajiya ",
"Ina wuni?" Amaal ta gayshe shi kanta akan wayar ta da take dannawa.
Bai amsa ba ya cigaba da cewa da Hajiya,
"Saura kadan hazl ya hanamu sauka a jirgi yau"
"Subhanallahi Allah ya tsare gaba.. Tana gayshe ka"
"Na amsa.."
"Baka amsa ba Malam.. zaka fada abun naka ko?" Aaayan ya fada yana girgiza kai.
"Baka amsa ba dan yaye."
Ya dan daga Kai ya dube ta..... Don baki daya bai san aina take azaune ba ma.. Ya dai jiyo muryar ta tana gaishe shi.
Gefen fuskar ta kawai yake hangowa saboda ta juya masa baya.. Kuma ta karkace zaman nata sosai..
"Lafiya lau"
Tabe baki tayi ta mike daga zaunen da take,
"Hajiya zan tafi ... Sai da safe."
"Ina zaki je? Zauna ki ci abinci kar ma kice kin koshi maza zauna."
Ba yadda zata yi don ba zatai musu da Hajiya ba. Sai kawai ta koma ta zauna
"Sannu da dawowa dan yaye..."
"Yauwa Hajiya ta.... "
"Takwara zuzzuba muku abincin."
Amaal ji take tamkar ta tashi ta zura a guje.. Data sani bata zo sashen Hajiya ba yau.
"Tohm Hajiya"
Sauka tayi daga kan kujera ta zauna akan tabarmar ta dakko plates tana bubbude food flasks da abincin yake aciki,
"Ka gane ta kuwa?"
"Wa?"
"Gata nan kanwar ku.."
Bai ko kalli inda amaal take ba ya girgiza kai alamun a'ah
"Yar wajen Bappan ku ce. Yar autar sa. Diyar wajen Hajiya Jamila."
"Oh..."
Amaal dake tsugunne tana zuba musu abinci ta tabe baki.
"Yaya Aayaan ya ishe ka haka?"
"Ya isa favorite cousin... Nagode"
Jan nata plate din tayi takai gabanta. Dan kadan ta zuba tana ci.
"Ka sakko kaci naka Malam." Aayaan yace da Al-mustapha.
Almustapha ya dan juyo da kansa ya dubi abincin da Aayaan yake nuna masa.
Amaal ta mike da plate a hannun ta ta kai kitchen,
"Hajiya sai da safe..."
"Toh sai da safe... Allah ya tashe mu lafiya"
Aayaan yayi saurin ajiye plate din hannun sa ya mike,
"Favorite...tafiya?"
"Eh Yaa Aayaan.."
"Ya nagan ki soo down ne... Me ke damun ki?"
"Bakomai fa.."
"To shikenan muje na rakaki"
Fita tayi ya bi bayan ta... Hajiya da Al-mustapha na ta hirarrakin su
"Sanyi garin "
"Gaskia ba lefi"
"Ko hadari ne ya wuce"
"Ma shaa Allah garin yayi dadi"
Dan kallon ta aaayan yayi. Gaba daya yana yinta ya canza don haka ya sake ce mata,
"Ko Al-mustapha ne ya bata miki rai ko?"
"Waye haka?"
Dariya ta bashi. Don haka ya dara sosai kafin yace,
"Wancen gayen na parlorn hajiya mana"
"Oh"
"Shi ya bata miki rai ko?"
"No bakomai fa"
"Look... Karki saka abunnan ya bata miki ranki.. please"
Dariya ma zancen sa ya bataa. Don haka yayi murmushi kawai.
"To me yayi ruining mood din favorite dina?
"Bakomi yaya kawai dai ba.."
"Uhm ina jinki"
"Bakomai.... Sai da safe"
Cikin gidah tayi da sauri har tana hadawa da gudu.
Murmushi kawai yayi hade da girgiza kai ya juya ya koma bangaren Hajiya
Ko da ta shiga Hajiya jamila da Hamid suna zaune still suna hira..
Bakinta dauke da sallama ta shiga
"Na dawo"
"Sannu da dawowa"
"Sannu sissy"
"Ya Hamid"
"Na'am sister sister"
"Aiki kake har yanzu? Sannu da kokari"
"Yauwa sannun mu... Na kusa ksrssawa sawa saura kadan"
"Je ki zuba abinci ki ci"
"A koshe nake Hayateey.."
"A koshe kuma?"
"Eh naci awajen Hajiya.. Ni da Yaya Aayaan ne ma da Yaya wa ma"
"Bako akayi?"
"Wai dan gidan Bappah Jalaludden ne ya dawo Nigeria da zama gaba daya.. "
"Al-mustapha kenan"
"Yauwa eh shi.."
"Allah sarki da tare wai zasu dawo gaba daya da su Hajiya Jidda (mahaifiyar shi) sai shi ko visa dinsa ta samu matsala ne sai da aka gyara"
"Allah sarki . Hayateey kinsan me?"
"A'ah sai kin fada"
"Kafin naje wajen. Hajjya na fara zuwa sashen kakaa"
"Kin duba jikin nasa?"
Amaal ta daga kai tare da taune kasan leban ta.
Hajiya jamila ta dubi yadda amaal din ke malkwasa yatsun hannuwan ta tasan tabbas wata damuwar na damunta,
"Ina sauraron ki.."
Amaal ta dan juya baya sai kache wadda aka biyo a girgige take tache,
"Hayateey.... So suke su kashe shi..."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Amaal kinsan me kike cewa kuwa?"
Amaal ta daga kai can sai hawaye sharr.. gaba daya a rikice take..
Hajiya jamila ta janyota jikin ta. Hakama Hamid duk ya rude ya rufe laptop din da yake aiki ya ajiye,
"Sissy menene? Eh? Ko na baku wuri?"
Saurin girgiza kai tayi. Yayinda ya samu lafiyayyar harara daga Hajiya jamila tace,
"Ka fara ko? Kai da ita ba daya bane? Haba Hamid."
"Tuba nake Hayateey"
"Ina sauraron ki... Kinji?"
"Hayateey dana futa daga nan zanje wajen Hajiya. Sai na fasa kawai na tafi sashen sa... Ba kowa inata sallama baa amsawa. Karatun alqurani yana ta tashi.."
"Uhum... Sai akai Yaya?"
"Zan shjga dakin sai najiyo motsin takalma. Da wata iriyar wahalalliyar kara ana kuka marar sauti sosai... Sai na yi sauri na buya abayan window ta baya wajen corrior dinnan."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Ina jin ki?"
"Shikenan sai na leka ta windown akwai wani waje a ragar ya yage ta kasa. Ina hango kaka a kwance. Sai wasu mutane bjyu baa ganin fuskar su."
"Ina jin ki"
"Ashe yana magana? "
"Ke Amaal? Baya magana.... Banason kago labari"
"Wallahi ba wasa nake ba Hayateey.. "
"To Ina sauraron ki"
"Sai naji cikin muryar roko da tsantsar ciwo yana ce da su, Dan Allah ku kyale ni .. Ku kashe ni kawai. Basu barshi haka ba Hayateey.. sika dakko wata alura ta cika fal suka masa ità... Yace Allah ba zai barku ba. Shikenan jikin sa ya fara wata iriyar rawa idanun sa na kakkafewa.. sika dauke shi kaman kayan wanki Hayateey suka kwantar da shi akan gadon shikenan ya koma yadda yake a baya kaman ko da yaushe. Suna ciki sai ga Bappah ya shigo ciki suka gaysa ya amsa waya yace wa na cikin wayar sungode sosai sun aiwatar da komai yadda akeso cikin kwarewa. Ya basu kudin mota suka tafi.. " tana karasa fada ta fashe da kuka
Hajiya jamila ta sake ringumeta tsam a jkkin ta tana bubbuga bayan ta cikin rarrashi,
"Wane Bappan?"
"Bappan Hajiya... Bappah jalaludden"
"Mutanen wasu iri ne?"
"Likitocine kaman"
"Ahto kinga ai kila allurar da suka masa ce tasa shi wannan surutan bakin nasa ya sake rufewa bayan ta shiga ciki"
"Hayateey kafin a masa ne fa na jiyo kukan sa da wata iriyar kara... Kila wasu abubuwan muguntar de suke masa Hayateey hear me out"
"Amaal bakyau zato.. zunubi ne ko da ya zamanto gaskiya..Kinga daida mugunta suke bappan Hajiya daya shiga zai gano ko? So possibly kokarin bashi temako suke... Kinji ki kwantar da hankalin ki"
Mikewa tayi tana goge hawayen ta. Yadda taga suna màasa ta tabbatar cutarwa suke ba temako ba. Amman tasan ba wanda zai yadda da ita,
"Bappan Hajiyan kin gaya masa?"
"A'ah... Banma shiga dakin ya ganni ba na fito da sauri"
"Ki kwantar da hankalin ki bakomai kinji ko?"
"To Allah yasa"
"In shaa Allahu... Sai alkhairi "
"Bari na tafi daki"
"To Allah ya tashemu lafiya"
"Sai da safe Yaya Hamid"
"Sai da safe sissy ."
Tafiya tayi sashen su tanata sake sake a zuciyar ta. Ita dai sam hankalin ta bai kwanta ba gaskia ...
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN