Showing 21001 words to 24000 words out of 95238 words
Chapter 8 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt
fara fadan wasu maganganu. kuma.shikenan duk wanda yayi ba daidai ba ba zan fada ba sai nayi shiru?"
"Amma dai Yaya"
"Dakata jalaludden inde ka amince gaba na ke da kai ka bar ni na karasa abunda zan fada. Idan kuma kai ka dawo yayan nawa to cigaba Ina sauraron ka."
Alhaji jalaludden yayi shiru bai sake cewa komai ba sai faman dai cika da yake yana batsewa fuskar nan tasa a kumbure ba fara'a. Yanayi yana wullawa amb junaid harara.
Kawu Adamu dai yana rike da kafadun jalaludden yaki cika shi don yana cire rikon da yayi masa to fa zai hau amb Junaid ne da duka. Don baki daya tamkar baya hayyacin sa,
"Yaya dan Allah menene lefi na?" Amb Junaid ya sake tanbayar Yaya Nuraddeen yana girgiza kansa cike da tashin hankali
"Au tambayar lefukan ka ke? Kunji munafuki algungumi ko?" Jalaludden ya fada yana kwafa
"Junaid je ka dan Allah. Tafi sashen ka sai da safen mu."
"Yaya meyasa zan tafi? Wallahi bansan lefin da nayiwa Yaya jalaludden ba."
"Inde na isa da kai kai ma kana kuma ganin girma na to ka bar nan yanzu."
"Shikenan... Sai da safen ku."
Fita yayi gaban sa yanata masa zugi da radadi. Ya rasa wacce iriyar kiyayya dan uwan nasa yake masa. Meya tare mesa? Bayan ko acigaba na rayuwa ya fishi? To haushin sa na me yake ji?
Bangaren hajjyan su yaje ya gayshe da ita. Ta tambayi ya jikin mai gidan na ta ya amsa ta da Alhamdulillah jikin sa yana sauki yana samun lafiya.
Ya dan zauna suna ta yar hira da ita yana matsa mata kafafu . Har bacci ya fara daukar ta tache masa ya tafi ya kwanta shima yayi mata sai da safe ya nufi bangagren sa.
Kansa har wani sara masa yake yi saboda tsananin yadda yake masa nauyi kan. Wata jijiya ta fito radau a gaban goshin sa tanata harbawa.
Yana shiga ya zauna akan kujera yana sauke ajiyar zuciya. Ya sanya hannun sa daya ya dafe goshin sa.
Wayar sache tayi kara ya dauka ya danna ta a handsfree ya ajiye ta a kusa da shi. Matar sa jameelah ce ke kiran sa,
"Assalamu alaikum. Nurul qalb..."
Murmushi sosai yayi jin yau ma kuma da wani sunan data kira shi. Kullum cikin kiran sa da sunaye masu matukar dadi da kwantar masa da zuciya.
Take yaji wani kaso na daga cikin bacin ran nasa ya sauka . Ya dan yi gyaran murya don karta gane damuwar da yake ciki yace,
"Waalaykm Salam... Farhatal qalb..."
Dan murmushi tayi mai sauti ta sake lankwashe harshe tace,
"Da fatan Habibi yana cikin koshi lafiya?"
"Alhamdulillah habibty... "
"Ma shaa Allahu... Ka dawo ne?"
Ta tambaye shi kasancewar kwananta ne.
"Na dawo yanzu ba dadewa kimganni a zaune..."
"Ma shaa Allahu... Toh wanne tea zaa kawo? Chamomile tea? cinnamon and cardamom tea? Ko tumeric/garlic da milk sai a saka masoro kadan? Wanne ko just the usual coffee? Kana jina kuwa Abbiyeyn su?"
Ajiyar zuciya ya sauke, ya sanya hannun sa ya shafo kasan keyar sa. Yayin da idanuwan sa yake lumshe su, dai dai lokacin da Hajiya hadiza ta taho da sand'a tana labewa,
"Ina sauraron ki habibty... Hakika muryar ki na magance mun dimbin damuwa, magnganun ki na tasiri a zuciya ta... Allah ya miki albarka... Ki kawo tumeric tea din inason nayi bacci dama..."
Hajiya jamila tayi murmushi anata bangaren tana kitchen a tsaye. Sai bulala kamshi take. Sanye cikin laffayar data amshi jikin ta sosai.
Kalar ja. Tasha kwalliyar black. Sai ta daure kanta da danjwali baki ta yafa laffayar akai. Ba kadan ba tayi kyau tamkar a dauke ta kaman yar baby.
Wayar a kunnen ta. Yayin da hannunta daya take dakko wani flask transparent ne ana ganin komai na cikin sa. Ta dora shi akan wani tray da cups dinsa suma ta dora su a kananaun tray dinsu..
Nan da nan ta fara hadin shayin tumeric/kurkum din . Tache da shi,
"Yanzu zan kammala na zo habibi da'iman, akwai wani abun da kake so bayan tea din?"
"A'a habibty...."
"Ko dan prawn crackers ka temaka kaci kaji?"
"Abunda kikace shi za'ai s...
Bai karasa ba Hajiya hadiza ta shiga tana tafa hannu tana sallallami tamkar wadda akayiwa mutuwa. Taja kwafa tana kada kai,
"Meye hakan ba sallama?"
"Yo ina zakaji sallama ta kana faman soyayya gotai gotai da kai?"
"Ni ba mahaukaci bane hadiza... Idan kinyi sallama zanji. Wayar da baa kunnena take ba ma."
Hajiya jameah da ke jiye dasu tayi hanzarin kashewa . Saboda batasan tashin hankali sai jikin ta yahau bari tana tsaye hannunta sai rawa yake.
Ya daga wayar zai yi magana yaji tayi ending call din. A fusace ya kallo hadiza yace,
"Kede idan ba tashin hankali kika tasa ba bakya jin dadi hadiza... Ba zaki dena laben nan ba? Wallahil azim a laben nan wataran zaki labewa kan ki Ina rabaki."
Tsaki taja ta kalle shi ta maka masa harara,
"Kai de borin kunya ya isheka, Kanata faman susuta zance. Ni ba wannan ne ya kawo ni ba. Duk da dai na ji zancen da kukeyi.. Allah ya shirya . Da ka aurar da yaran ka da tuni kanada jikoki shine kuke soyewa da matar ka."
"Alhamdulillah kince mata ta. Ba wata daban nake kulawa ba."
"Amman dai kaji kunya... Soyayya da farin gemu."
"Eh naji halal me ai... Matata tace."
"Saboda kana tsoron ta shine ka amince ta dakko dan gidan rukayya? Wato junaidu duk shawarwarin da ake baka ba zaka dauka ba sai da ka amince ta dakko shi? "
Hannun sa ya saka a goshin sa yana dafawa, ciki da kosawa yace,
"Dan Allah hadiza banason tashin hankali wallahi kai na ciwo yake."
"Okay ita da kake kauna ai kace muryar ta na sa maka nutsuwa da kwanciyar hankali ni da ka tsana kuma ciwon kai nake sa ka."
"Ni ba abunda nake nufi ba kenan. Wallahi kai na dama ciwo yake. Kuma kinzo kina kawo wata magana ta daban haba hadiza. "
"Na fuskanci baka son zaman lafiya ba kuma ka kaunata junaidu."
"Kin fara ko hafiza?"
"Ni ce matar ka ko Jamila?"
"Dukan ku mata na ne"
"Ni che ta fari ko ita?"
Ya sauke katuwar zuciya yana junjuya kai,
"Ke che.."
"To banason zaman sa agidan nan ban amince ba don haka da sake ya tattara ya koma inda ya fito....
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[8/18, 2:57 PM] Hafsaat💞: _BM_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_PAGE: 16_
_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._
___
Sauke nannauyar ajiyar zuciya yayi. Surutan ta na dada kara masa ciwon kai. Ya dan karkata ya juya mata baya. Hakan da yayi ba karamin ciwo ya mata ba...
Ta zagaya inda ya juya mata baya din tana ta cika tamkar zata fashe. Cikin takaici hadi da muryar ba da umarni tace,
"Ban amince da zaman sa a gidan nan ba..inata maka magana kayi banza."
'Dagowa yayi ya dubeta cike da kosawa yace,
"Hadiza... Dan Allah fita ki tafi.. Kai na ciwo yake.. ki dinga jan girman ki dan Allah.. Yanzu da kwanan ki ne tazo nan muna hira da tuni kin hau doron zuciya kin tada husuma kuyi ta fada..."
"Junaidu bansan meyasa ka tsane ni ba. Wato ciwon kai nake saka maganar da nake ko? Sannan kabi bayan ta kana gasamun magana gani karya uwar fada ko?"
"Ni bance haka ba... Dan Allah jeki kwanta."
"Nagaya maka ban amince da zaman dan Rukayyah agidan nan ba.."
Daga kai yayi ya dubeta. Fuskar sa ba annuri yace,
"Akan ki yake?"
"Banason zaman sa nide nace."
"Ohkay kin dawo me gidan kenan sai abunda kikace za'ai."
"Junaidu idan kanason zaman lafiya ya wanzu acikin gidan nan to kace ta mayar da shi inda ta rakito shi."
Tsaki yayi mai sauti. Yaja kasan leben sa da hakoran sa yana busar da wata iska mai dumi,
"Na amince da zaman sa agidan nan. Gidah na ne ai ba naki ba ko? Kuma ni ne a sama da ke ko a shekaru. Don haka kar na sake jin kin ambaci maganar barin sa gidan nan. Tashi ki fita."
"Lalle ta wanke ta baka ka sha."
Ya gano sarai me take nufi. Don haka ya yamutsa fuska shima yace,
'har sai ta sha wani wahalar wankewa? Kafa Kai nayi na shanye da kai na. Tashii ki futa mun daga parlor hadiza. tashi" ya daka mata tsawa saboda yadda ta sake dulmiya ransa acikin bakin ciki daman rannan nasa ba dadi kan fadan da sukayi da yayan sa jalaludden
Tsayawa tayi tana narai narai da idanu. Zata fita kenan Hajiya jamila tayi sallama ta shiga ciki
Tun daga bakin kofa take zuba kamshi wani irin Chadian scent ne ke tashi daga jikin ta na kamfanin turarukan yerwa incense and more..
Hajiya hadiza ta dubeta taja tsaki tana dankara mata harara. Har ta bangaje ta shayin ya dan zuba a hannun Hajiya jamila
Ta runtse ido da sauri tana fadin,
"Wayyo Allah na..."
Da sauri ya tashi ya nufeta ya karbi tray din ya ajiye. Ya kamo hannun ta suka zauna akan kujera
Haj hadiza dake labe tana kallon su taja tsaki da har sai da suka waiwaya suka dubeta.
"Matsiyaciya." Ta fada tana hararar haj Jamila
Amb Junaid ya tashi da kansa ya janyo kofar parlorn ya rufe ta da key. Sai da taga ya rufe kofar ne ta tafi tanata mita ita kadai.
Komawa yayi ya zauna yana cewa,
"Allah ya kyauta..."
"Aameen.."
Hannun nasa ya saka ya kamo nata yana dubawa harda haska torchlight din jikin wayar sa.
"Wannan yatsun ne ko?"
"Eh.... Amma ai sun dena"
Ya saka bakin sa yana busa.mata iska a yastun da shayin ya zuba. Gefe daya kuma yana murza su.
"Nagode..." Ta fada tana dan kauda duban ta
"Kiyi hakuri... Kinji?" Ya fada ahankali hadi da saka hannun sa ya juyo da fuskar data juya ta fuskance shi.
"Kinji?"
"Ba abunda ya faru fa abbieyn su"
"No I'm very serious.... Kina da hakuri da kawaici Jamila..Allah ya miki albarka.."
"Aamin tare da ku baki daya...Na dauka ta tafi shiysa na taho"
"Kwanan ki ne Jamila bafa nata ba."
"Na sani. Girman ta na bata ai... Tunda itace ta sama da ni"
Sake sauke gauriwar ajiyat zuciyar yayi yace da ita,
"Jamila hakurin ki yayi yawa... Ni dai Ina mai sake baki hakuri.. ki gafarce mu. Badan kaddara Allah haka ya rubuta ba.. Da tuni kece matata ta fari jameelah... Kananun shekaru sika hana muyi auren... Lokacin dana fito zan sure ki kuma manya suka sa ni gaba kan na daure na fara auren ta.. Saboda tausayin mijin ta daya rasu ya barta da goyon jaririya. Bugu da kari kasancewar ta yar uwa agare ni kuma macece mai rauni, Hakan yasa na amince na fara auren ta da fari. Sai kuma na aure ki daga baya... Kinsan dai Ina kaunar ki Jamila. Bazan so abunda zai cutar da ke ba. Dan Allah ki"
"Abbiye kar ka karasa please. Allah dukan ku ni ba abunda kuka mun... Ya wuce, Allah ya yafe mana gaba daya. "
"Allahumma Aaameen. Allah ya miki albarka. Ya biya miki dukkanin burikan ki...halayen ki nagari da ache mata haka suke da mace machen aure bai yi yawa ba. Ni dai nayi sa'a. Da Allah ya mallalamin ke a matsayin matata tagari."
Dan murmushi kawai tayi ta janyo tray din gaban sa ta dauki flask din ta zuba masa a cikin kofi ta dora akan karamun tray ta mika masa ya karba,
"Wannan kuma meye?"
"🥞 Pancake ne... Da chocolate toppings. "
"Allah ya miki albarka..."
"Aamin..."
Yanaci yana hadawa da tea din suna yar hirar su gwanin shaawa..sosai hirar tasu take yaye masa radadin damuwar da ke cikin zuciyar sa.
Ta dube shi sosai yadda yake shan shayin ahankali kana ganin sa kasan akwai boyayyiyar damuwa a tattare da shi. Wai hausawa suka ce labarin zuciya a tambayi fuska.
"Abbiey.."
"Na''am..."
"Meyake faruwa ne.... ?"
"Me kika gani? Ya tambayeta yana kakaro murmushi..
"Dan Allah baka ji rai na ba ba dadi saboda damuwar da kake ciki? Dan Allah menene?"
Ya sauke gwauron numfashi yace,
"Just the usual...."
"Yaya jalaludden?"
Daga mata kai yayi ya cigaba da shan shayin sa...
"Allah ya shiga lamarin nan na ku ya dedeta tsakanin ku... Amin"
"Allahumma Aaameen... "
Haka dai ta dinga jan sa da hira har ya karasa cinye wa. Ya wanko bakin sa. Yanata shi mata albarka saboda yaji dadin shayin da pancake din.
"Abbiyen su yaya kayi binciken numbers dinnan kuwa?"
"Wanda ake turo mun sakonni?"
"Eh?"
"Banyi ba... "
Shiru tayi batace komai ba sai faman matsa yatsu take..
"An sake turo miki sakonne kema?"
"Kira na akai ma.."
"To fa wai me?"
"Inata kokarin kasa kunne dan gano me muryar na kasa. Saboda haka duk banajin abunda suke fada kawai dai naji daga karshe ance nayi hankali da kishiyoyi na, Musaman hadiza wai tana kokarin salwantar da rayuwata kan kawo Hamid da nayi ya dawo gidan man."
Bai ce komai ba ya daga kansa sama yanata nazari chan yace,
"Koma wanene BAKON MUNAFIKI ne Wanda BA NA MUTUM DAYA BANE...."
"Nima.nayi wannan tunanin abbiyen su..
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[8/23, 7:42 PM] Hafsaat💞: _BM_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_PAGE: 17_
_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._
___
Bai ce komai ba ya sauke gwauron numfashi kawai...
Cikin sigar lallashi mai tattare da tarairaya ta shiga jansa da hira har dai ta samu ta kawar masa da kaso mafi yawa na daga cikin damuwar ta sa.
______
*AMAAL*
A 'darare ta shiga katafaren dakin na su bakin ta dauke da sallama..Ta harde yatsunta waje daya kanta a kasa ta wuce su ta nufi gadon ta ta zauna kasan maqoshi ta furta,
"Ina wunin ku....?"
Basu amsa ta ba. Kowanne daga cikin su ya cigaba da abunda yake yi
"Ke...."
Hindu dake tsaye daga bakin kofa ta sake cewa,
"Ba magana na ke miki ba?" Ta fada a tsawace.
Amaal da ke karanta littafin hannunta ta daga kanta jin kamar ana bin ta da kallo,
Dukkanin idanun su akanta. Su kalle ta su kalli bakin kofa, Hakan yasa ta sha jinin jikin ta, Ta juya bakin kofar da sauri,
"Ya Hindu magana ki ke?"
"A'a haushin kare na ke" sauran yan dakin suka saka dariya
"Kiyi hakuri..."
Dogon tsaki Hindu taja... Tana mai cigaba da taunar cingom irin taunar nan ta rashin mutunci,
"Je ki wanke bandaki zanyi wanka"
Amaal ta bude bakin ta tana bin Hindu da kallo, Bayan ga ma'aikatan da suke yi... Bugu da kari kuma ga dare ache se tayi wankin bandaki.
"Ina magana kin tsaya kina kallo na kamar tsohuwar mayya"
Kiyi hakuri Ya Hindu... Dare yayi ne."
"Zaki tashi kije ko kuwa?"
Mikewa Amaal tayi ta bude bandakin ta shiga. Kawai tsabar mugunta ce da a wannan daren zata sakata wankin bandaki bayan masu aiki sun wanke dazu.
Nan da nan ta taara ruwa ta zuzzuba duk abunda ya kamata na kayan wankewar.. Ta na daga tsaye aciki tana jira abubuwan wankewar su hypo su jiku sosai.
Jiyo su tayi suna ta zancen ta suna tuntsiririn dariya. Wasu zafafan hawaye suka shiga zurara daga idanun ta.
Ta saka bayan hannun ta ta goge ambaliyar hawayen da ke kwarara.
Haka dai ta nannade hannun rigar ta ta shiga wankin bandakin ta gama tas ta rufe kofar,
"Na gama...Ya Hindu."
Hindu na malale akan gado tanata danna wayar ta tana murmushi da alama chatting ta ke.
"Yaaya na gama"
Tashi tayi daga kan gadon tana mai rike da wayar dai a hannun ta,
"Okay gyara mun gadon ma."
"Toh."
Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta karkade gadon ta gyara zanin gadon da bargon.
Taje ta gaya mata ta gyara ta hango ta sakale da waya a kunnen ta tana amsawa,
Don haka ta juya ta koma cikin dakin. Bandaki ta shiga tayo wanka hade da dauro alwala tayi sallar nafila rakaa biyu tayi adduoin bacci ta kwanta.
××WASHE--GARI××
Tun bayan sallar asubah bata koma ba ta shiga shirya wa da sauri saboda so take taje school da wuri akwai text book din da zata karanta a library