Showing 78001 words to 81000 words out of 95238 words
Chapter 27 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt
yake mata da har yake neman illata kansa haka? Ta sake jiyo shi yana cewa,
"Zai iya kasancewa, niba ajin ki bane, ba irin namijin da kike so bane, amma inaso ki saka a zuciyar ki cewa nayi alkawarin zama irin namijin da kike mafarkin samu a rayuwar ki, nidai dama na ke bukata awajen ki... Domin awaje na kece muradin rayuwata ..Maryaam, You are my answered prayer, my fulfilled wish and my realised dream… You are not someone I want to be with. You are someone I cannot be without... Maryaam ki yafe mun please... Ki karbe ni amatsayin miji na tabbata bazaki dana sanin amincewar hadakar auren da aka hadamu ba kuma zamu yiwa iyayen mu godiyar aurar da mu da sukayi nan gaba...Kinji?"
Ita fa gaba daya bai sani ba ya gama kunce mata notinan kanta gaba daya...Ya sake langabar da kansa ya kwantar da kansa sosai akan cinyar ta.. ya zame hannuwan ya riko ta ta baya.... Tana jiyo tururun dukan numfashin sa akan tafukan hannuwan ta da dumin hawayen sa... Cikin rawar murya mai tattare da ban roko yace,
"Maryam Allah daya haliccemu ma muna yi masa lefi wani kan wani kuma yace mu roke shi ya yafe mana. mu fa yan Adam ne masu tarin lefuka maryam... Nasan ni me lefi ne awajen ki Ina rokon alfarma da kokon barar yafiya daga gare ki...Dan Allah kinji..?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta danyi dan murmushi... Ya daga kansa da sauri ya kalleta,
"Kin yafe mun?"
"Allah ya yafe mana gaba daya.... Bacci nake ji Yaya Al-mustapha"
Gabas ya juya yayi sujjaada ya daga hannu yana yiwa Allah godiya. Batai aune ba taji yayi sama da ita a hannu yana zagaye dakin da ita.. yanata hamdala kamar wanda aka biya masa wani gagarumin abu..
Ya ajiyeta dakyar yana tallabo fuskar ta. Ya saka labban sa akan goshin ta ya yi mata kiss yace,
"Nagode..Nagode Allah ya miki albarka maryaam..."
Juyawa tayi ta shige bandaki da sauri ita dai..wanka tayo hadi da sabon tsarki.. tayi kan gado da sauri taja bargo ta lullube,
Shima bandakin ya shiga ya tsaftace jikin sa.. ya haye kan gadon bayan yayi addua. Ya janyota jikin sa tana ta tirjewa,
"Dan dai hugs and kisses dinnan Maryaam ki kyaleni mana... Babban darasin mu barshi zuwa gobe bayan kinyi test inshaa Allahu ba daga kafa."
Batace da shi komai ba.. tana jinsa yanata neman magana ajikin ta tayi masa shiru..Hakan datayi ba karamin dadi yaji ba yayita budurin sa yadda yaso daga baya ya rungumeta tsam yana cewa,
"Ina so kiyi mun wata alfarma guda daya, inaso fuskar ki ayayin da kike murmushi ta zama fuskar da zan gani karshe kafin na dinga kwanciya kamar yau, haka zalika fuskar da zan gani bayan na tashi daga bacci duk safiya. Zaki iya bani wannan damar?"
Shiru tayi masa dariya ma ya bata ta sake cusa kanta kawai a pillow. Tana jiyo shi ya zame pillow din ya mayar da kanta kan kirjin sa... A haka bacci ya dauke su..
***
Tun asubah masu aikin Hajiya maryam suka kawo musu abun karin kumallo don haka da safe wajen bakwai Maryam tayi warming dinsu taci tabarwa Al-mustapha nasa tanata sauri... Ta leka har yanzu bai tashi ba tun bayan daya dawo daga sallar asubah. Don haka ta harhada handouts dinta direba ya kaita makaranta karta makara saboda test.
Al-mustapha daya tashi yasha mamakin ganin bata nan ya kalli agogo.. ashe shine ya makara.?.. Ta tafi test kenan? Yayi murmushi yace,
"Allah yabada nasara da sakamako mekyau Maryamu tahh..."
Bandaki ya shiga yayo wanka yaci abinci ya sauya kaya ya tafi office kai tsaye..
Ko da ya dawo wajen 12 kai tsaye ya nufi sashen su bata nan... Yanata tunanin inda take . Kawai ya tafi bangaren Hajiya Maryam dake bayaan su. Inde bata nan to fa kunya ba zata barshi ya duba bagaren hajia Jamila ba ko na su....
Bakin sa dauke da sallama ya shiga parlorn Hajiya... Tare da hannuwan sa dake zube cikin aljihun wandon jeans din dake jikin sa... Ya dora riga ja me ratsin baki da dogon hannu ta kamfanin dkny... Bakadan ba yayi kyau sai wani annashuwa yake ji a tattare da shi..wai shi Al-mustapha angon Maryam Amaal.
Yana shiga idanun sa na kan Maryaam Aamaal dake zaune tana jotting rubutu daga wayar ta. Sanye take cikin doguwar rigar atamfa datayi matukar amsar jikin ta..mayafin kayan ta ta rufa shi daga gefen ta .
"Ahh wa'alykm salam... Dan yaye ka dawo?" Hajia maryam ta amsa shi tana murmushi
Gogon naku sam bai ji maganar da hajiyan ke yi masa ba. Ya nufi inda Amaal din take ya ja mayafin ya lullube mata jiki gaba daya.. ya durkusa agaban ta yana cewa,
"My baby♥️yaushe kika dawo???"
Maryam da duk kunya ta dubibiyeta tace,
"Haj... Hajiya na maka magana..." Ta fada harda wata yar in'inar data taho mata alokacin...
Ya mike da sauri yana sosa keyar sa..
"Hajjaju mutan makka...Barka da rana...
ZAFAFA BIYAR WRITERS♥️
[10/2, 5:13 PM] Hafsaat💞: _4_
_6_
____
***Hajiya Maryaam tayi murmushi. tace da shi,
"Alhamdulillah dan yaye.... Ya aikin?"
"Lafiya kalau Hajia.."
"Toh Ma'shaa Allahu... Allah ya kara temakawa"
"Aameen Aaameen Hajiya"
"Ka ci abinci...? Ko da yake an kai muku na rana ma sashen ku"
"Mungode Allah ya saka da alkhairi Allah yakara arziki"
"Aameen,.. Nasan baka ci ba. Wato har yanzu ba zaka dena wasa da cikin ka ba ko?"
"Tuba nake hajjaju makkatun... Zanje naci yanzu inshaa Allah"
"Yauwa ko kai fa..."
Aaayan ya shiga parlorn Hajiya bakin sa dauke da sallama.... Ya nemi waje ya zauna bayan sun gaysa da su Hajiyan
"Dan wahala... Kana nan ashe?" Aayan ya dubi Al-mustapha yana tsokanar sa
"Ni da kai ansan ko waye dan wahalar ai... Wawa"
"Oho dai... "
Mikewa Al-mustapha yayi yana sosa keyar sa... Ya dan saci kallon Amaal dake cigaba da rubutun ta.
Aayan ya dube shi ya dubu Amaal din yace
"Menene? Ka zuba mata idanu kuma ka kasa cewa komai?"
"Ina ruwan ka? Maryam kinci abinci?"
Amaal dake rubutu ta daga kai ta dube shi kafin ta mayar kan wayar ta tace,
"Sai anjima.."
"Toh " ya amsa a sanyaye yayi hanyar fita
Hajiya maryam ta dube ta ta ce,
"Je ki zuba masa abincin.. Kamar karamin yaro sai an saka shi a gaba ai kullum.."
"Tohm" Amaal ta fada tana zura wayar da littafin hannunta a jaka..
Aayan ya dube su ya sheke da dariya yace,
"Wallahi Hajiya ki dena shagwaba katon mutumin nan... Kina wani ce masa dan yaye kullum kansa yana girma"
"Ina ruwan ka? " Al-mustapha ya harare shi.
Hajia ita dai dariya tayi.... Amaal ta musu sallama ta fita. Al-mustapha yabu bayanta har yana tuntube garin sauri.
Ya saka mukullin hannun sa ya bude kofar suka shiga bakunan su dauke da sallama...
Daki ta wuce ta ajiye jakarta... Ta zare kayan ta ta saka rigar wanka ta shige bandaki bakinta dauke da addua. Wanka tayo hadi da alwala.. ta sauya wasu kayan marasa nauyi.. irin rigar nan yar kanti mai gajeran hannu sai ta yafa wadataccen mayafi bayan ta shafa turaruka..
Yana zaune a parlorn ta wuce wajen socket ta jona burner ta saka turaren wuta nan da nan gidan ya gauraye gaba daya da kamshin turaren sandal munawwara na kamfanin turaren yerwa incense and more...
Al-mustapha ya lumshe idanun sa ya bude saboda tsananin kamshin turaren daya mamaye shi gaba daya kamar a kamfanin haramein oud.
Wajen dinning ta nufa ta dauki plate ta zuba abincin, waina ce ta shinkafa sai miyar ganye data ji naman kasuwa. Ta zuba soup din kazar shima a cikin wani karamin plate taja kujera ta zauna bayan ta dauki kofi ta tsiyayi kunan ayan dake cike da madara da kankara har wani kamshin flavor ne ke tashi acikin sa.
Ya jawo kujerar kusa da ita ya zauna... Ya tallabe habar sa da hannun sa yana kallon ta cike da kaunar da yake mata mirar misaltuwa..
Ta dan kalle shi ta kauda kanta kasa kasa tace,
"A zuba maka?"
"Na koshi...." Ya fada yana kwantar da kansa akan hannun sa ya mayar da kallon sa gaba daya kanta. Har wani lumshe idanu yake
"Amma Hajiya tace ka ci fa"
"To zan ci wannan nakin"
"Tohm gashi" ta matsar masa da su gefen sa zata bude kulolin ta zuba nata ya saka hannun sa ya riko nata da sauri
Wani electric shock ya ziyar ci dukkanin su.. Amaal ta janye hannun ta da sauri tana matsawa gefe,
"Muci nakin mana tare please.... Kinji maryaam?"
Ba yadda zatayi ta koma ta zauna... Al-mustapha yayi murmushi yasake matsar da kujerar sa daf da ita har suna shakar numfashin juna..
"Feed me.... "
Ya wani bude baki yana lumshe ido.. dariya ma abun ya bata ta dangwala da miyar ta saka a bakinta tana taunawa ahankali...
"Baki bani ba fa?" Ya marairace yana narkar mata da idanun sa..
"Yunwa nake ji. Kaci da kanka mama"
"Uhm uhm...ni ke nakeso ki bani" yana langanar da kansa a kafadar sa cikin muryar shagwaba
Ita dai ta share shi ta cigabaa da cin wainar ta... Daya tabbatar dai ba bashin zatai ba sai ya saka hannu shima yana gutsira ahankali yanaci.
"Ya test din?"
"Alhamdulillah"
"Komai kin rubuta yadda ya kamata?"
"Eh...."
"Ma shaa Allah... Allah ya sa mu ga sakamako mekyau"
"Aamin.… Ka ci abinci mana"
Dadi ya kama shi yau Amaal ce da kanta tache yaci abincin mana... Ya dashare hakora ya shiga zura loma yana korawa da ruwa..
Mikewa tayi ta wanko hannun ta. Bayan ya gama ta tattare komai ta kai kitchen. Ta hada ruwan kumfa ta fara wankewa sai ga shigar sa yana nannade hannun rigar sa,
"Kawo na dauraye"
"Ka barshi"
Yatsan sa ya saka akan lebenta alamar tayi shiru... Ya rankwafa saitin kunnenta ya rada mata,
"Banda musu Maryaamu.... Ki wanke sai na dauraye.. kinji?" Ya karasa fada yana hura mata iskar bakin sa acikin kunnenta. Ya Kuma sumbaci gefen kunnen yana dan jan kasan sa a hankali
Batai aune ba ta jiyo hannuwan sa ya zagaye da su ta ruwan cikin ta yayi mata rumfa,, kansa akan kafadar ta yana dauraye plates dinsu biyu da kofina ta haka..
BAKON yanayin daya jefata yasa da hanzari ta karasa wankewa ta matsa daga jikin sa.. shima saurin yayi ya dauraye ya kife inda yaga ta saka..
Ta goggoge ko'ina ta zuba yar sharar da suka bata a dustbin. Sannan ta fita daga cikin kitchen din ya bita a baya..
Oudi carpets/chairs/curtains scented spray (turaren fesawa na labulaye da kujeru da carpet) din kamfanin turaren yerwa incense and more ta dakko ta faffesa a parlon bayan ta kintsa ko'ina..
Shi dai sai bin ta yake da kallo yana admiring din dukkanin abubuwan da takeyi. Ba kadan ba take da tsafta hakan ya sake sanyata a wani sashe na daban dake cikin zuciyar sa..
Suka zauna dika akan kujeru suna kallon shirin wasan da ake nunawa a talabijin din na 'shes the man'
Lokaci zuwa lokaci yakan daga kansa ya dora akan ta. ta mayar da hankalin ta sosai tana kallo.. shi kuma baki daya ita ya mayar TV dakyar yake kifta idanun sa...
Aka kira sallar magriba ya tashi ya tafi masallacin dake cikin gidan. Ita kuma ta nufi dakin tayi tata.
Bai dawo ba har akai salllar ishai.... Amaal ta mike tayi wanka dama kullum ne ka'idarta sai tayi wankan dare duk sanyin da akeyi kuwa baya hanata.
Tayo wanka ta dakko kayan baccin da zata saka. Wai aciki ma shine na mutunci akan sauran.. riga ne da wando. Rigar iya cibiya ta tsaya wandon kuma be kai gwiwa ba.
"Kai Yaya Yusra a gayshe ki kema..." Ta fada tana zabga tagumi. Domin duk yusran ce ta hada mata nighties..
Kamar ta rusa kuka haka taji. Taya zata iya saka wadannan kayan fisabilillahi? Sanyin ac sai kadaata yake. Hakan yasa ta zura su kawai bayan ta shafa night kulaccam ajikin ta.
Ta janyo zumbulelen hijabi har kasa ta saka shi. Hayewa tayi kan gado ta kwanta bayan tayi adduoin ta. Ta kashe fitilar ta bar side lamp kawai..
Al-mustapha yanata sauri ya karasa sashen nasu. Chocolates da cakes da ice cream ya siyo a shopping mart din dake tsallaken kandem estate..
Bakinsa dauke da sallama ya shiga... Shiru ba kowa a parlorn sai kamshin turare da na air freshener ne ke tashi. Gege daya kuma karatun alqurani ne ke yi da qira'ar Maheer.
Ya lumshe idanun ya bude... Jinsa yake tamkar a wata duniyar ta daban.. wai a gidan su yake shi da muradin ran sa Amaal...
Freezer ya bude ya sassaka su aciki. Har ya nufi dakin ta zai shiga sai kuma ya fasa..
Ya bude nasa dakin ya shiga ya yo wanka hadi da dauro alwala... Ya nufi kofar dakin nata ya kwankwasa .
"Maryaam.."
Ta jiyo muryar sa yana kiran ta.. kamar ba zata amsa ba sai kuma tace,
"naam"
"Zo"
"Ga ni nan" Ta fada da sauri... Rigar ta ta janyo wadda ta cure ta dora akan kayan baccin jikin ta saboda gaskia ba zata iya fita daga su sai hijabi ba duk kuwa da har kasa yake kuma ba sharashara bane yana da kauri..
Ta bude kofar dakin ta fita.. Ta hango shi akan kujera a zaune ya shimfida sallaya.
"Ga ni..."
"Zo mana" Ya amsata yana mika hannun sa.
Karasawa tayi ta tsaya daga gefe. Ya mike tsaye yana kamo hannuwan ta ya rike su cikin nasa yana murzawa ahankali,
"Zamuyi sallar nafila ne mu godewa Allah abisa ni'imar da yayi mana ta kasancewa acikin ahalin musulunci. Da kuma kasancewar mu a inuwa daya ta aure.."
Gyada masa kai tayi alamun to... Ya nufi kan sallar don jansu sallar. Ya jasu rakaa biyu.. suka sallame ya daga hannu yanata kwararo addu'oi ya shafa itama ta shafa
Ya juya ya fuskance ta sosai yana murmushi yace,
"Ga chocolates can da ice_creams cakes da sauran stuffs dai na saka maki a freezer"
"Nagode" Ta amsa shi tana lankwasa yatsun hannun ta..
Ya saka hannun sa ya dafa kanta ya karanto addu'oi... Bayan ya kammala ya shiga yi mata tambayoyi abisa addini ta amsa shi daidai gwargwadon Iko. Yaji dadi da kasancewar ta mai tarin ilimi da basira haka,
"Allah ya miki albarka Maryaam... Allah yasanya mana alkhairi da dimbin albarka me yalwa a rayuwar auren mu"
"Aameen... "
"Allah kuma ya kauda dik wani sharrin masu sharri da duk wasu abubuwan 'ki...Allah kuma ya hade kawunan mu yasa iyayen mu suyi alfaharin hada auren mu. Allah ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankula da yalwar arziki da wadatar zuciya. Hakuri da kuma dangana da yarda da kaddara. Allah kuma ya azurta mu da 'ya'ya nagari masu tarin albarka kuma hafizan alqurani... Ko Maryam?"
Ya dan sunkuyar da kansa yana kallon ta. Idanunta a kasa da alama ta tafi tunani. Ya saka hannun sa ya lakuto kumatun ta ta daga kanta da sauri. Domin ita tatafi tunano labarin da Hanayya amaryar ajin su ta basu na first night... Zancen gaskiya bata shiryawa daren nan ba. Domin taga alamar shi dinne don duk abunda hanayyan ta fada musu irin su Al-mustapha keyi. Don haka hawaye suka fara zuba daga idanun nata tace,
"Dan Allah kayi hakuri" kuka ta shjga yi sosai wanda yasa Al-mustapha dariya. Ya janyota tsam jikin sa yana shafa tun daga kan gadon bayanta,
"Zo nan habibty ana.... Uhm... Menene? Waya taba mun ke?"
Ji take inama ta kwace kanta ta gudu. Ta jiyo hannun sa yana shafa gefen fuskar ta tace,
"Kai na ke ciwo..."
"Kan ki? Wayyo .." Ya saka hannun nasa ya taba goshin ta,
"Muje na baki magani " Batai aune ba ta ga ya dagaata chak ya nufi daki da ita kamar wata jaririya.
Al-mustapha ya bude kofar dakin da hannun sa. Ya kuma rufe kofar da kafar sa bayan sun shiga bakin sa dauke da sallama..
Kokarin zare mata hijabin yake ta damke shi da sauri tana cewa,
"Ka... Bari..."
Dariya ta taso masa.. Don ya gano ko maganar ciwon kan ma zancen ta ta hada, ya danne yace,
"I have the right.... Beside kanki ke ciwo fa Maryam. Banda musu" Ya zatre hijabin ya cilla shi gefe...
Rigar jikin nata irin me maballin man ce ya fara zare botiran ahankali.. duk cure botir daya sai yace,
"Sannu maryam... Kinji?"
Ita dai dai daga masa kai take tana jiran ikon Allah. Jikin ta har ya fara rawa... Gajeren wandon baccin jikin ta ya bayyana bayan ya zare botiran wajen. Ya cigaba da zare su tayi saurin rike hannun sa.. ya bude idanu yana duban ta hadi da jan kasan leben sa yace,
"Menene Maryaam... What's wrong?"
"Ka bar shi haka?"
"No... Kalla fa yadda kika hada gumi. Da alama ciwon kan ya sauka ma ko? Banda musu kinji?"
Tayi saurin juyar da kanta... Ya karasa zare rigar itama ya yi wulli da ita gefe... Riga da wandon jikin ta suka bayyana..
Ya shjga kare mata kallo tun daga saman ta zuwa kasa.. Wandon be kai gwiwa ba haka zalika rigar ma bata kai cibiya ba. Wani abu ya hadiye yayi saurin janyo robar ruwan daya hango akan bedside ya sha yana sauke zuciya. Launin idanun sa suka canza.. ya saka hannu ya mayar da bedside lamp hasken dim...
Ya rarumo Amaal jikin sa... Yana yi mata tafiyar tsutsa tun daga kan gwiwar ta...
....
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari