Showing 75001 words to 78000 words out of 95238 words

Chapter 26 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt

04 Jan 2025

6676

koshe na ke"


"Sai da ruwan ciki ake jan na rijiya."


"Me?"


Yayi murmushi ya girgiza mata Kai,


"Ba komai... Tashi kici abinci please. Ko kuma bari na kira Bappah Junaid"ya dakko wayar sa yana lalubo contact.


"Zan tashi" Ta mike da sauri tana gyara zaman rigar jikin ta.


Murmushi yayi wanda gefen kumatun sa suka lotsa (dimple) Ya ja kasan leben sa yana tsosa a hankali...


"Tashi to muje...ki yi hakuri Maryaam ba zan gushe ba sai na dinga baki hakuri da yardar Allah...I'm not even bragging"


Tana gaba yana biye da ita a baya... Dayan dakin ta shiga ta dakko hular ta ta saka hadi da janyo mayafin ta ta yafa. Gaba daya kallon da yake bin ta da shi ya ishe ta sai kace zai hadiye ta danya..


Hannun ta ya kama ya kai ta har dinning table ya janyo kujera ya zaunar da ita a kai. Ita abun sai ya fara bata tsoro kuma daga mamaki. Wai wannan Al-mustapha dindai mai jin kan sa yana takama shine keta bin ta kamar wani soko?


Komai da komai ya janyo gaban ta... Yaje ya dakko plate a kitchen bayan ya dauraye ya saka mata kazar akai. Ya bude juice dinma ya ajiye agaban ta.


Ta dauki tsoka daya ta juyar da kai tana ci.... Murmushi yayi cike da farin ciki ganin tana cin kazar tana hadawa da lemo. Tsoka uku taci ta ture plate din tana hamdala,


"Kin koshi?"


"Uhm"


Ya janyo plate din gaban sa ya cinye wanda ta rage... Juice dinma ya dauki ragowar ya shanye bayan ga wasunan da yawa amma natan yake so.. bakin robar juice din ji yake tamkar na Amaal dinne.. Har wani lumshe idanun sa yake da yana shaa..


Wayar sa ce ta fara kara ya dauka da sauri yana duban mai kira Aaayan ne. Ya ki dauka har sau uku. Can wayar Amaal ta fara kara itama.


"Waye?"


"Yaya Aaayan"


"Mts.. ban wayar"


Mika masa tayi batayi musu ba. Ya dauka ya saka a speaker,


"Kuna ina ne haka?"


"An gaya maka kowa tuzuru ne irin ka? Ka kirani ban dauka ba shine zaka kira mun matata me zamuyi maka?"


Aaayan ya saki dogon tsaki yana kwance akan kujerar dakin sa... Sun matukar kona masa rai yace,


"Yan wahala... Na manta waya ta karama ne anan nake son ku kashe ko ku saka a silent sai ka fito mun da ita gobe zan karba inshaa Allah"


"Gaka nan dan wahala.... Baka da matar aure kana wani maganar wayar ka karama ka manta ta anan. Mu bamu san inda take ba malam"


Aaayan ya sake sakin wani tsakin a karo na uku yace,


"Ina Amaal?"


"Tana jin ka"


"Fave cousin"


"Na'am Yaya Aaayan.."


"Kina jina?"


"Eh"


"Dan Allah kakki sassautawa gayen can. Mutumin banza ne, Ki tuno abubuwan daya aikata miki a baya. Dan Allah daren yau ki gurza masa kakki sakko da sauri kuma k"


Al-mustapha ya dauki wayar ya saka ta a kunnen sa cike da bacin rai yace,


"Dan wahala. Kaje ka rungumi pillow kayi bacci.... Mun gama shiryawa da ita. A halin da muke ciki ma yanzu ba zeyiwu mu gaya maka bane kayi yarinta sannan bai kamata ba. Shi yasa ma bamu amsa wayar ka ba da ka kira da farko... Maza maza kaje kayi futsari kayi alwala ka yi nafila ka roki Allah kai ma ya yanke maka kayi aure. Ka kuma kwanta kayi bacci ka kashe babbar wayar da ke hannun ka.. kana ji ko? Samari marasa aure yan uwan ka duk sunyi bacci" Al-mustapha ya fashe da dariya bayan ya fada masa haka..


"Wawa dan wahala.... Allah ya isa" Aayan ya fadawa Al-mustapha ya katse kiran yana jera tsaki.


Amaal tayi murmushi don sun bata dariya kwarai matuka. Mikewa tayi bayan ta dau wayar ta daya ajiye..


"Ko kinsan Arc.. Nurayn..?"


Juyawa tayi da sauri tana fuskantar sa.. Ya kada mata kai yana takawa inda take a tsaye,


"Ni Al-mustapha ni ne na bude account sabo a IG nayi following dinki na fara tura miki dm (direct message)"


"What?" Ta tambaye shi fuskar ta lullube da dimbin mamaki da takaici


"Dan Allah ki yafe mun. Look! Na kasa bayyana miki kaunar da nake miki amatsayina na Al-mustapha. Bayan an yi magaanr auren ki da Hisham abun yayita damuna na kasa sukuni ranar da aka dauke ki ai nine na tsinci wayar ki a kasa na kaiwa su Bappah .Dana duba naga wallpaper kece kuma ba password ki gafarce ni anan na shiga na nemo sunan ki a IG na dauka number wayar ki ta WhatsApp duk da dai na kasa miki magana ta WhatsApp din sai Instagram."


Amaal tayi dariya irin ta kama renamun hankalin nan...


"Na cancancanci kowane hukunci daga gare ki... Ki dake ni ko ki mareni idan har hakan zai sanya ranki yayi fari"


Ta daga hannu zatayi magana ta kasa saboda bacin rai. Wato Nurayn dinma da suke yar soyayyar su a Instagram dinma ba wani bane shine..


Ruwa ya dakko me sanyi ya bude ya mika mata,


"Sha dan Allah, Sha ruwan sanyin nan ko zuciyar ki zata samu saalama... Maryaam ki mun duk hukuncin da kika yanke. I deserved to be punished"


Duban sa tayi sosai tace da shi,


"Ka sallame ni kaban takarda ta na bar maka gidan ka... Wannan shine hukuncin da zuciyata take kauna.."


Bude idanu yayi sosai yana kallon... Ya karasa ya rike ta tanata zillewa... Ya rungumeta sosai jikin sa nata rawa yace,


"Banda wannan hukuncin... Wallahi wallahi bazan taba rabuwa da ke ba in shaa Allah... Ki bar azabtar da zuciyata da kalaman ki Maryaam. Bazan iya rayuwa ba ke ba..." Yana magana yana goga kansa a wuyan ta.. Hadi da saka bakin sa ya sumbaci wuyan nata ya cigaba da cewa,


"Lost in my own world, all I think of is your love Maryaam. Lost in my own breath, all I could smell is your love Maryaam. Your love gives me life and the strength to love you more.... Maryam Ina matukar kaunar ki... Lokaci zai bayyana Hakan.. yess time will surely tell"


Ta shiga zame rikon da yayi mata tana kuka sosai. Har ga Allah ta gaji da abubuwan da yaketa mata sai kache ya samu yar tsana.. ji tayi ya kinkimeta gaba daya.. Ta shiga mintsinin sa tana yakushi ko ajikin sa yace,


"Inde hakan zai sanya miki nutsuwa maryaam ki cigaba... Inde yakushi, mintsini zai saki tausayamun ki yafemun maryam..Dan Allah ki hada da cizo.." Ya ajiyeta akan gadon yayi mata rumfa da jikin sa.


Numfashin su yana dukan fuskokin su... Suka shiga yar kallon kallo... Hannun sa daya na yawo a gefen fuskar ta cikin wani irin salo na bayyana kaunar sa agare ta... Gaba daya yana kuncewa yar muten kandemi lissafin kanta. Ta kasa cewa dashi komai sai hawaye da take..


"Shhhh! Bar kuka Maryaam dena zubar mun da hawayen ki kinji? Bakiji zuciya ta ba... " Magana yake cikin wata iriyar murya yana cigaba da sunbatar gefen fuskar tata, da wuyan ta, da kan kirjin ta... Ya gangaro kan tafun hannun ta yana shafawa ahankali...


"Ina kaunar ki Maryaam... God I'm out of words... maryaam.... Dan Allah kiyi hakuri ki yafe mun....







_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_


*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥




*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*


_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*




FURAR DANKO
Billyn Abdul


-ZAFIN KAI
Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo


Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400


Pay at👇


1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k




_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥
[9/29, 6:58 PM] Hafsaat💞: _PG:_
_4_
_5_






_ADVERT👇_


_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_


_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_


_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_


_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_






_________










***Ya sake goga gashin kansa akan gefen wuyan ta da kan kirjin ta... Wanda ya sata sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara...


Gaba daya abubuwan da yake mata tun dazu sun ishe ta... Gangar jikin ta, tunanin ta kai dama ji da ganin ta sun kasa daukar sabon karatun da yake kokarin sai ta dauki darussan su a dole...


Nema yake yayi loosing control gaba daya... Ga wani kamshi na seductive khumrah data shafa na kamfanin turarukan yerwa incense and more..Da ya sake fuzgar hankalin sa.


Ya sake birkito ta sosai ta dawo kan kijrin sa... Tana kokarin kwacewa yayi azamar saka hannuwan sa duka biyu ya riko ta kugun ta da ruwan cikin ta... Ya yinda kirjin ta da fuskar ta ke kansa.


Ya tsura mata manyan idanun sa... Ta rufe nata idanun ruf hawaye daya na bin daya..


Murmushi ya saki kafin ya saka tongue yana kokarin goge su... Cikin muryar kosawa mai tattare da gajiya tace,


"Sai kace maye? Wayyo Allah na Hayateey" da alamun tabbas maganar zuci ce ta fito mata fili...


Al-mustapha ya saki tattausan murmushi.. anan ta gano baranbaramar da tayi. Hannun sa ya saka yana janye jelar gashin ta dake kokarin shiga mata baki...


A hankali cikin wata iriyar murya irin ta masoyi dake rarrashin masoyiyar sa yace,


"Maryaam... Ni mayen ki ne ai....Na zauce akan ki Maryam... Ji nake kamar a mafarki wallahi... Wai yau kece amatsayin matata... Muna kwance akan gadon mu na sunnah. Kina kan ruwan cikina ina......


Da sauri ta saka hannunta duka biyu ta rufe masa baki saboda taga alamar kunyar sa ragaggiya ce... Tun dazu yake 'barin zance,


"Shikenan ba dirty talk? Ke fa matata ce Maryam... Bari ma kiga yau ni ne malamin ki... Zan fara koyar da ke wasu darussa." Magana yake yana kokarin balle botiran gaban rigar baccin jikin ta,


"Wayyo Allah na... Dan Allah kayi hakuri"


Idan tace 'wayyo Allah na dan Allah kayi hakurin' nan dariya take bashi... Ya sake saka hannuwan sa ya matso ta sosai yayi mata wani riko..


Batai aune ba taji bakin sa akan kunnen ta... Cikin muryar rada rada yake cewa da ita,


"Taya ina da kamar ki a tare da ni zan iya hakura wai? Lafiyayye da ni ke ma lafiyayyar ce kuma... Maryaam bazan taba iya hakuri ba.. Ki bar ni please... I promised to be an excellent lover... " Ya karasa fada yana kamo kasan leben ta..


Duk yadda ta so ta kwache ta kasa... Saboda rikon da yayi mata bana wasa bane kuma ai karfin ba daya bane....


"Yaya Al-mustapha dan Allah..." Ta fada tana kuka sosai.


Murmushi yayi.. ya sanya bakin sa kan karan hancin ta ya sakar mata sumba..


Ya gyara mata kwanciya sosai akan pillow suna fuskantar juna dik da dai ita ta runtse idanun ta.


Ya saka hannun sa daya ya sakalo bayan ta..


"Maryaam..."


"Uhm..."


"Bude idanun ki..... Kinji? Idan ba haka ba na cigaba" ya karasa fada yana kokarin cusa hannun sa cikin rigar ta.


Ta rike hannun nasa da sauri tana girgiza masa kai hawaye na zuba kaman an bude ruwan famfo..


"Kayi hakuri"


"To bude"


Budewa tayi ahankali ta sauke ganin ta akan sa...


"Yauwa wifey... Ko ke fa?"


Ita dai sai raba idanu take... Ta kasa cewa komai.... Ya sanya yatsan sa daya yana zagaye fuskar ta da shi...


"Ka che ka dena idan na bude fuska ta fa" Ta fada cikin muryar ta a shagwaban ce.


Dariya ce ta taho masa ya kanne... Yace,


"To ba kince ba zaki yafe mun ba? Inata rokon ki nace kaunar ki ce sanadi sai wani bani tough time ki ke"


Batace dashi komai ba ta juya daya gefen da sauri. Ya sake saka hannun sa ya juyo da ita ya dora kafar sa daya akanta, Ya Kuma cigaba da tafiyar tsutsar da yake mata afuska da yatsan sa daya... Cikin wani irin salo mai rikirkita tunanin wanda ake wa,


"Maryaam... Komai naki abun kauna ne... Idanun ki mashaa Allah... I'm lost in them.. ga hancin ki ma shaa Allah kamar ke kika zana abun ki... Ji girar ki .. And lips dinki... Yadda kike da kyau haka suke da kyau haka kuma suke da dadin tso....


Bai karasa ba ta saka hannunta ta toshe masa bakin sa..


"Meye faru? Ya zare hannun nata yana sumbatar saman hannun..


"Lefi ne dan miji ya yabi halittun matar sa?"


Bata amsa shi ba nan ma tayi shiru... Idanun ta a kasa. Ya daga hannun nata ya saka yatsunsa ya hade su waje daya ya runtse yana jujjuya su.. dayan hannun kuma ya saka akan gashin ta yana shafawa ahankali..


"Yaya Al-mustapha...."
Ya jiyo ta kira sunan sa muryar ta adaskare,


Ya daga kai ya dube ta sosai, yana ware idanu. Cike da dimbin mamaki yace,


"Na'am lover... My beautiful wife.... My dream come true💕... Ya akai?"


Cikin rau rau da idanu tace,


"Dan Allah..."


"Me? Na cigaba da baki darussan ko?"


Tayi saurin girgiza kai cike da fargaba tace,


"A'a dan Allah... Wallahi bacci nake ji kuma Ina da test gobe."


"Test? Maryaam test yafu darussan da mijin ki ke koya miki?"


Ita dariya ma ya bata da takaici ta sake cewa,


"Dan Allah"


"Ya za'ai daren auren mu ki mun maganar wata test... Ke kinma dena zuwa makarantar daga yau.."


Da iya karfin ta ta kwace rikon sa ta tashi tana kallon sa shima ya zauna yana duban ta,


"Me kace?"


"Nace kin ma dena na zuwa school din.... Kinsan dai ko su Bappah basuda Iko akan ki yanzu sai ni ko? "


Hawayen datake makalewa ne sika shiga zuba daga idanun ta. Gashi bayason bacin ranta daga wasa. Yayi saurin janyota jikin sa ya rungume yana bubbuga bayan ta alamun ban hakuri...


"Wasa fa nake... Ya zaai na hanaki zuwa makaranta? Karfe nawa ne test din?"


"Goma ne..."


"Tohm. Zamu kwanta yanzu amma please ki mun alkwari zaki fuskanci magana ta yanzu da zan miki ki mata duba na tsanaki ki aunata a mizanin hankali da idanun basira Maryam... Ki amince..kinji?"


"Tohm"


Riko hannun ta yayi suka sauka daga kan gadon gaba daya.. ya janyo kujerar gaban mudubi ya dorata akai. Ya zube akasa kaman mai neman gafara ya saka hannuwan sa duka biyun ya riko nata. Gwiwoyon sa a zube akan kasa yace,


"Maryaam... Wallahi tun kina zanin goyo nake kaunar ki.....Maryam ban fahimci meye so ba ma sai akan ki... Maryam akan ki na tabbatar da duk kaunar da Allah ya sanyawa dan Adam a zuciya to fa wallahi bata yankewa..Maryam idan nace ga adadin yadda nake jin ki a zuciyata nayi karya... Ina jin labarin soyayya ne a da, tamkar tatsuniya, amma da lokaci yaja bayan na kasa cire ki a rai na, na gaskata soyayya wata aba ce wadda ke da tasirin sanya farin ciki a cikin zuciya. Ina fatan zaki kasance tare da ni, domin zama maganin damuwata na tsawon rayuwa? Ina kaunar ki Maryaam...


"Nasan abubuwan dana aikata miki a baya idan kinshigo waje na fita... Ko na dinga bata rai. Ko ana magana idan kinsa baki nayi shiru wallahi duk kaunar ki ce ke dawainiya da ni. Ta mun illar da wallahi bana samun nutsuwa...Ke ce kaddarar da na jima ina tsimayin tarar da ita a rayuwata, zan kasance a duk inda kike, zan tsaya a duk inda kika tsayar da ni. Ina son ki, adadin son da kalmomi ba zasu iya siffantawa ba Maryaam...." Ya karasa fada yana dora labban sa akan hannun ta daya rike a nasa tafukan hannayen...


Ya daga kansa da suka ciku taf da hawaye ya dora akanta ya cigaba da cewa,


"Kin zamo cikin thoughts dina na kullum Maryaam.. Tunani na komai naki ne maryam... dake nake kwana a rai na tashi..da ke zuciyata ke zantawa a kullum, wadanda a dukkan lokacin da tunanin ki ya ta so , na kan ji dukkan damuwata na gushewa. Wani irin so nake miki.. kai babu ko shakka matsananciyar kaunar ki ta shiga zuciyata... Ko ranar dana ce ke karbu mukulli ki share daki ki gyara ko'ina ki wanke mun bathroom wallahi kishine ya taso... kinyi kyau cikin red Caribbean rigar nan.. naga mazan family kowa idanun sa akan ki... na kasa nutsuwa Maryaam... shine fa wai dik dan karkiji na fadi haka... Allah beba kuma kikaje din..Ni Kuma naki zuwa saboda I can't take it...kinsan yadda nake son ki kuwa?...."


Ya karasa fada yana rankwafar da fuskar sa saitin inda ta sunkuyar da tata.. Hawayen idanun sa suka shiga diga a tafukan hannuwan ta yace,


"Zakiji hajia na cewa Aaayan nace lalle a kira ku dawo muna aiki da shi.duka fada ta ne kawai so nake ki dawo ga dare yaja...Maryam ki amince wallahi duk abubuwan baya kaunar ki ce sanadin aikata su.. akan kaunar da nake miki na zama gaula, Wawa, kuma kurma...Ina son ki ina kuma fatan zaki amince da ni a matsayin masoyi kuma miji na hakika?..."


Shiru Amaal tayi kawai tana sauraron sa.. dik wata haddar dake cikin kanta ya goge mata su... Aina ya samu wadannan kalaman haka.. wane irin kauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login