Showing 51001 words to 54000 words out of 95238 words
Chapter 18 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt
mai hankali da nutsuwa... Ran sarki ya dade ko akwai wani da kuke takun saaka? Ko kuma daga wajen gari ne kidnappers dinnan sai ahankali.. sun kira waya kuwa? Ina nufin wadanda suka sache ta..."
Sarki junaidu yayi shiru kansa akasa... Can ya dago ya dubi aminin nasa Alhaji abubukahr yace da shi,
"A iya sani na sa ma da kowa wanda ke nan zai iya bayarda sheda.. yarinyar nan batada abokin fadaa.. ita ba me kwaramniya bache bama ballantana ache sunyi hsyaniya da wani ko wata an dau fansa akai... Sai dai Ina tabbatarwa da koma su wanene sika yanke wannan danyen hukuncin... Tabbas don ni akayi.."
"Subhanallahi.. junaidu kasan me kake cewa kuwa? To Kai din ai halin ka tayi.. dika Kai da mahaifiyar ta ba kuda abokin faada ba ajin kan ku da kowa... Ya zaka ce haka?" Kawu Adamu ya tsawatar masa..
"Kawu ku amince.... Wanda ko ince wadanda suka dauke Amaal ba yan waje bane... Daga zuriyar Ardo kandemi ne... A tsakanin mu ne... " Cewar sarki Junaid.. ransa ba dadi.. kana kallon sa kasan yana cikin damuwa marar misaltuwa
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Me kake nufi junaidu?" Gwaggon court ta tambaye shi fuskar ta dauke da damuwa.
"Ina nufin dan zuriyar nanne ya dauke ko ince suka sache ta.."
"Ranka ya dade yan zuriyar nan fa kache... Meyasa kake tunanin haka?"
"Ba tunani nake ba... Daman ansha tsoratar da ni da mugayen kalamai ta kafafen sadarwa ko ta text messages ta nambobi kala kala... Tun sakonnin basa gabana har lamarin ya fara bani shakku akai... Nagano tabbas akwai me bibiyata yana son yaga bayana... Kuma wadannan sakonni da ake turomun na tsoratarwa ba iyani kadai ba har wasu daga cikin iyalina ma anayi wa tun muna kasar waje kafin ma mu waiwayo gidah. Bayan mun dawo dinma baa dena turowar ba. Ko yau bayan an sache ta dinma sai da aka turomin sako... Ina faada kikavin kilama kafin a sace ta dinne..."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. " kawu Adamu yayita mainatawa cikin damuwa sosai.
“Abunda yasa aka dauke Amaal saboda ta ceto rayuwar Baba gashi a zaune dan dai ba zai iya magana bane bakinsa a rufe….”
“Me kake nufi kache junaidu” cewar prof Abdullah… shi dama dan boko ne babu ruwan shi da shiga sabgar su sosai. Kullum cikin karatu yake
“Ina zuwa… Bari kuji.” Wayar sa ya dakko ya sanya recordings din duka na binciken da akayi nasa akan allurori da karin ruwan da akewa mahaifin nasu don akashe shi.
“Innalillahi wa inna ilahi raji’un … Ke duniya Ina zaki damu? To akan duniya sai mutum ya nemi ya kashe rai? “Kawu Adamu ya fada yana jinjina lamarin.
“Amaal Itace wadda ta ceto rayuwar Baba………” ya fadi dukkanin abubuwan da Amaal ta fada musu tun ranar farkon data fara zuwa bangaren da alhaji Muhammad yake jinya. Ya k’ark’are da,
“Shine cikin dabara da hikima ta dakko allurorin da ruwan su da kuma karin ruwan da akeyi masa… kun dai ji da kunnuwan ku muggan tsibbun da akayi amfani da su ana masa karin ruwa. Haka kuma allurorin lalata masa gabbban jikin sa dama komai nasa ne baki d’aya allurar da akewa dokuna don rage musu kuzari a kasar waje... Texas precisely.. rabi fa kunji akeyi wa dokunan amman shi baba fin d’aya ake yi masa…..”
“Innalillah wa inna ilaihirrajiun duk a Yaushe akai haka?” Gwaggo aisha ta tambaye shi tana girgiza kai.
“Yaya nuraddeen, Yaya jalaludden, Almustapha da aaayan lokacin da kuka hadu da Amaal a bakin gate zaku shjga wajen baba kuna shiga kuka tarar da shi ya farfado ko?”
“Tabbas bima naje na same shi har yana ninke rigar sa,Bayan sun kira ni…” Kawu Adamu ya fada yana tsiyayar da hawaye..
“Me kake nufi junaidu? Me kake son cewa? Nufin ka acikin mu BAKON MUNAFIKIn yake?” Alhaji jalaludden ya tambaye shi idanu cikin idanu.
“Yanzu na gama maganar nan dai anan wajen…. Kamar yadda na fada zan sake maimaitawa… Ranar da Amaal ta jiyo kukan baba da numfarfashi da yake yi yana sauke ajiyar zuciyar wahala…. Wanda ya shiga sashen bayan likitocin sun kammala allurorin su kai ka shiga yaya..”
“Kana nufin kache ni ne zan kashe mahaifin mu kenan?”
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Wannan Duk bata ta so ba… Kuyi hak’uri rashin fahimta ne.” Kawu ya shjga raba tsakanin su ganin sun hayayyakowa juna zasuyi fada
“Gashi kunaji yache ni na shiga.”
“Eh yaya kai ne ka shiga… kai ne wanda ka kira waya kace ‘Mungode sosai sun aiwatar da komai yadda akeso cikin kwarewa.’ Ka kuma bawa likitocin da suke masa allurorin kudin mota suka tafi…..”
“Innalilahi wa inna ilaihirrajiun….. kunajin abunda yake cewa?”
“Wanene mai turamun sakkonni a waya na barazanar Kar na waiwayo Nukaa? Kar mana dawo kasar gaba d’aya? Wanene wanda ya ke kullallaliya aka kafe ni awaje naki dawo wa gidah’ wanene baya son ganin Farin ciki na dana y’aya na? Ko gayshe ka sukayi baka amsawa musanman Amaal…. Me ta tsare maka? Ku kalli tarun sak’onnin baranazar da yake aiko mun kuma dama duk kuna wajen sanda aka ce ni Za’a bawa sarautar kandemi wane Furuci yayi? Karya nayi?”
“Dan Allah abar maganar nan…”
“Ba za abari ba Aisha… Rabu da shi ya cigaba…”
“Kache ka tsanani, ka tsani wanda yake kaunata ma ka tsani ka wayi idanu ka ganni a kandemi… Duk akan sarauta? Kasani dai dai da minti d’aya bantaba kaunar rawanin nan ba. Kuma a yau a dai dai yanzu ni junaidu na sauka daga karagar mulkin kandemi.. A dawomin da ‘ya ta… Zan tafi na bar maka kasar gaba d’aya, Ga rawanin ku nan...."
Alhaji jalaludden ya mike… Cikin fushi ya daga hannu ya shararawa junaidu mari, Sai da kowa ya girgiza yace
"Kache ni ne me?"
Sarki junaid ya mike tsaye ya saka hannu ya nuna shi da yatsa yace,
“Nache anyi walkiya mun gan ka.. Ko nan jiya da ake maganar harda batun auren Amaal kowa sheda ne bakace komai ba. Karewaar ta ma bakin ma da kyar ka bari kuka gaysa saboda tsananin kiyayyar da kake nuna mun da iyali na. Nache kai ne BAKON MUNAFIKI… kai din BA NA MUTUM DAYA BA NE… duk cikin mu nan kai ne me raba kawunan mu kana shiga tsakanin zumunci kake kuma son salwantar da rayuwar mahaifin mu don ka gaji sarautar kandemi
Dai dai lokacin da Almustapha ya shiga sashen da wayoyi biyu rike a hannun sa bakinsa dauke da sallama…
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[9/14, 9:22 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_PAGE: 33_
_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._
___
*Al-Mustapha* Ya karasa shiga tsakiyar parlorn. Yana ta duban fuskokin su dake dauke da damuwa marar misaltuwa kowannen su .
Ya zauna a tsakiyar parlorn akan carpet ya hada gaisuwar gaba d’aya yayi musu… Suka amsa. Gwaggon court da yake a gefen ta yake ta dube shi tache,
“Baka da lafiya ne Musty?”
“Alhamdulillah Gwaggo… Da fever ne kwana ne.. Amman da sauki. So bayan nayi asubah sai na koma na kwanta shine ban dade da tashi ba.”
“Sannu ya jikin toh?”
“Da sauki Alhamdulillah…”
“Allah yakara afuwa.”
“Aameen Gwaggon court…”
Suka shiga yi masa ya jiki cikin kulawa, Ya amsa su duka cike da girmamawa .
Ganin yanayin d’aya samu fuskokin su da irin zaman da sukeyi kallo d’aya yayi musu ya gano akwai matsala don haka yace,
“Meyake faruwa ne Gwaggo? Naga yanayin ku gaba d’aya wani iri?”
“Kanwar ku aka sache musty…”
Gabansa ya buga da karfi… Ya dube ta yache,
“Amaal?”
“Ko da yake zakaji ma.. Tunda abu ya zagaya ko'ina…”
Ya girgiza kai da sauri yace,
“Tashi na kenan nayi wanka na fito… awajen garden hanyar islamiya naga wannan wayar tana kara ana kira. Kaman bazan sunkuya na dauka ba dak saboda a kasa take sai kuma na tsugunna ganin wallpaper din jiki Amaal dince yasa tabbatar wayar tache… Shine nache bari na kawowa hajiya sai ta bata… subhan' Allah sachewa fa? Mutum sukutum? Kuma acikin kandemi.? Ina securities din gidan gaba d’aya?”
"Wallahi Musty... Lamarin ne gaba daya akwai rikitarwa.. Allah ya bayyana ta yasa ta fada hannu na gari Allahumma Aameen.",
Daya wayar da ke hannun sa ce tayi kara kafin ya mikawa mahaifin nasa ta katse aka sake kira,
"Bappah dayar wayar kace daka barta ake kira a gidah..."
"Aina kaga wannan wayar kuma? Ansa ka mikomun..." Garin dannawa ya danno harda speaker.
"Hello Jalaludden..... Mun aiwatar da kudurin ka... Muradin da ka dade kana bege ya kusa tabbatuwa . Nan bada jimawa ba mulkin kandemi zai dawo tafun hannun ka.. A yanzu haka Amaal mun dauketa tana tare da mu"
Jikake tassss.. Wayar ta fadi a kasa . Jalaludden ya bude idanuwan sa. Dika yan parlorn suka bude bakunan su suna binsa da kallon mamaki..
"Innalillahi wa innalillahi rajiun!" Kawu Adamu ya ambata da karfi yana girgiza kai. Ya sake cewa,
"Jalaludden! Ashe duk zantukan da junaidu ke fada akan ka dagaske ne?"
Kasa magana jalaludden yayi... Jikinsa ya fara rawa yace,
"Bani bane.. hear me out . Bani bane"
Sarki junaidu yayi murmushin takaicin kawai ya mike ya dakko wayar Amaal dake gaban Al-mustapha ya rike a hannun sa. Wayar tata ba password don haka ya shjga cikin call logs dinta numbers ne na kawayenta ne da alama suka kikkira, sai kiran Hisham dana Aayan dana mahaifiyar ta fal dana Hamid. Missed calls dai rututu..
"Call recording ya shiga yana duba time ko zaiyi suspecting wani kiran da maybe shine tanan aka sache ta. Hannun sa ya danno na kan mahaifiyar ta wanda shine last call din ta data answering kuma yayi dai dai da jiya da batazo faada ba sai sashen Hajiya ta same su gaba daya..
Ya daga kai ya dubu Hindu dake tsakure a kusa da hajiya hadiza yace,
"Meya hana amaal zuwa faada jiya? Kowa ya hallara babu ita? Gayamun gaskia. Ikhram, Ikhlas, Na'eelah, Najwa... Idan har gaskiyar lamari ta futo Kuna da hannu aciki na rantse da kadaitar ubangiji dukkanin ku sai kunyi kuka da kan ku. Ai ba jiya kuka fara hade mata kawunan ku ba .. Ina sane da komai .. duk abunda kuke mata yana dawowa kunne na . Kuma ba ita ke fada ba.. akwai masu kawomun maganar.."
Ikhram da Ikhlas Yan biyun Hajiya Ruwaida suka hada idanun su tsoro ya kama su . Ikhram tayi sauri don tasan fushinn abbiyen su Kuma idan yayi magana daya ya zartar da hukunci shikenan don haka da sauri tace
"Ita da Yaya Hindu ne...... "
"Hindu meya hada ku da Amaal?"
"Babu komai Abbiey... Kawai dai na mareta tabbas.. saboda ta yi amfaki da asiri ta rabani da saurayi na da zamuyi aure."
"Kenan har wani sauryi kike da da maganar aure tayi karfi bamu sani ba?"
"Ba haka take nufi ba.. yarinta ce" Hajiya hadiza ta faada tana tabo Hindu alamaun tayi shiru
"Yarinya? Ai ko su ikhram ba zaa cewa yara ba bare Hindu data girme mu su nesa ba kusa ba...Akan saurayj kika mari kanwar ki.. Ko ba Kya kara ki kanwar da ita? Waye saurayin inason ganin sa.. yanzu ba sai anjima ba.. su doctor nogan, Faysal, de gwanzam duka suma dss zasu kawo su yanzu. Duk wani wanda sunan sa ya fito dole ne mu bincike sa... Gwara a warware zaren kawai yau kowa zai gane tabbacin BAKON MUNAFIKI.... Wanda BANA MUTUM DAYA BANE me shiga cikin zumunci yana raba kawuna... Kafin sannan wane dalilin ne babba yasa zaki mareta?"
"Abbiey asiri tayi masa saboda lecturer dinsu ne.. ranar da muka hadu dashi a faculty dinsu ya ganmu tare.. zance yayi nisa fa bayan mun dawo gidah ya dena daukan kira na da waya dana takura masa da magaanar yace shi bani yake so ba Amaal yake so da aure... Abbiey jikin ta take ba...
Bata karasa ba Al-mustapha ya daka mata tsawa,
"Hindu..."
Baki dayan parlorn suka juya suna kallon sa.. sai a sannan ya farga ashe da karfi ya kira sunan ta yace,
"Habibi Talba aboki na ne Bappah...." Ya fadi karfin alakar su tare da tattare maganar da Habibi Talba yayi akan hindun ya faada ya Kuma dora da shima ya sanar masa yana son amaal saboda kyawawan halayen ta. Ya sanya musu voice notes din habibi talban ma yanata rokon sa ta WhatsApp kan ya fada agidah dan Allah abazhi Amaal... Hindu kuma bai taba cewa yana son ta ba . Ita take masa magana . Ta nace sai ta hadu da shi.. Ba kuma ta da kamun kai tana exposing jikin ta a waje... Gaba daya dai tarbiya ta mata karanchi a 'ya mace baliga me hankali...
"Sai me yafaru Ikhlas...?"
"Abbiey Suma fa sun gaggasa mata magnganu.", Hindu ta fada tana hararo su.
"Fadan yan uwa ne fa na yau da kullum yanzu maganar batan ta ake Junaid."
"Ya isa.... Ba dake nake ba . Zan zo kanki ai nasan kina ciki dole.."
"Me kake nufi innalillahi wa inna ilaihi rajiun." Hadiza ta faada tana dafe kirji
Hajiya jamila dai tunda aka aika aka kira ta tana gefe ta kife kanta a cinyar ta tana rera kuka marar sauti irin me tsuma zuciyar duk wanda ya saurara dinnan..
Hannu ya saka ya danno kan recording na farko . Muryar Hajiya hadiza ce tana kwakwazo bayan ta shararawa amaal din mari ana jiyo kara ta wayar ta kuma ce,
"Wallahi sai na salwantar da rayuwar ki Amaal .. Sai kinyi dana sanin shiga hurumin da ba naki ba...."
Kit recording din ya yi shuu da ga karshe sai muryar hajiya Jamila na cewa
"Amaal kina jina? Karar meye wannan? Kizo abbieyn ku na tanbayr ki anyi baki su Hisham sun iso fa... Hello kina kina kusa?"
Yana karasa kaiwa karshe yajuya ya dubi Hajiya hafiza yace,
"Ina Amaal??? Tabbas kin salwantar da rayuwar ta .. Tana Ina?" Ya daka masa tsawa daga karshe
Cikin inda inda ta saka hannu tana mai nuni da jalaludden.... Alokacin kuma dss suka taso keyar su Doctor Nogan cikin parlorn...
"Yaya jalaludden ne.... Ni dai go ahead kawai na bayar da ya turomun sakon nace na amince .."
Alhaji jalaludden yana zaune sai ya mike ya nunata ya nusa kansa har yana in-ina yace,
"Hadiza kinsan me kike fada kuwa? Ni kuma?"
Baki daya sai parlorn ya kichime... Alhaji Alkali Muhamamd dake kan kujera babba doguwa Hajiya Maryam na gefensa tunda suka fara zacen bunsu kawai yake da ido yayi gyaran murya yana daga hannu mamaki ya cika su sosai ..
Ya saka hannun ya yi nuni da Bappah Jalaludden da yatsa yace,
"Jalaludden zauna... ku dakata haka nan, Ku bar musu... BAKON MUNAFIKIn dai tabbas yana tare damu a yanzu haka ma....Kuma BANA MUTUM DAYA BANE Kam... Zagaye yake da kowa na cikin ku... Yana bin diddigin kowa da komai .... Shi ke hada komai ya kuma yanke hukunci yadda yake so... "
Duk sai baki daya suka sake gigicewa, ga farin cikin samuwar budewar bakin mahaifin na su ga kuma abunda mahaifin na su ya fada daga karshe... Kawu Adamu ya tashi ya koma kusa da dan uwan nasa yana dafa shi.
Sai kuma ya sunkuya yayi sujjaada yana daga hannu sama alamun godiya ga Allah...
"Alhamdulillah! Nayi matukar farin ciki" ya fada yana murmushi
Alhaji Muhammad shima murmushin yayi ya saka hannun sa ya daafa kafadar dan uwan na sa yace ..
"Ina ka kai AMAAL? ADAMU!!!.........
KAWU ADAMU!!!!????????
fuskokin dukkanin su suka dauka da madaukakin mamakin Kawu Adamu ne BAKON MUNAFIKIn ba Bappah Jalaludden ba kuma? Lalle ana zaton wuta a maqera....
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[9/15, 9:44 PM] Hafsaat💞: _BAKON MUNAFIKI_
_(BA NA MUTUM DAYA BA NE)_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_PAGE: 34_
_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._
___
*Kawu Adamu* ya bude manyan idanun sa da