Showing 84001 words to 87000 words out of 95238 words

Chapter 29 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt

04 Jan 2025

6661

kasa dai still. Al-mustapha yace,


"Bari to mu sake karawa.."


"Zan kalla ... Allah zan kalle ka yi hakuri"


"To dago ki kalle ni... Dazu fa na kamaki kina kalle mun fuska da jiki na gaba daya. Waya san ma da me dame kika taba a jikin nawa uhm..Maryaam"


"Wayyo wallahi bantaba komai ba"


"Fadi gaskiya dai...Ko na kara ne? Ba zaki kalle ni ba wai?"


Ta shiga daga kanta a hankali ta sauke idanun ta a kansa. Da sauri ta janye tana yarfe hannu,


Al-mustapha ya kamo hannuwanta cikin nasa yana murzawa ahankali yace,


"Maryaam ni fa mijin kine na sunnah.. Ba dadewa muka gama sharholiyar mu akan gadon nan ni da ke dik munsan yanayin halittun da ke jikin mu... Har fa kusan wanka na miki da na kai ki bandaki naga komai da komai. Har tawadar Allah kike da ita agefen bakin nan dinki daga baya" ya karasa fada yana dora hannun sa a saitin dayan kirjinta.


Tayi surin buge hannun nasa... Ji take kamar ta kurma ihu kunya duk ta dabaibaye ta..


"Zo muje muci abinci ko? Naji ana knocking kofa"


Mikewa tayi zata fitan yayi saurin daukar ta chak ya yage mayafin ya cullar a gefe ya nufu parlor da ita a hannu tanata yakicewa yaki sakin ta..


Ya ajiye ta akan kujera ya nufi kofa ya bude. Mai aiki ce ta kawo musu kulolin abinci tana cewa,


"Dazu nazo inata bugawa baa bude ba. Idan da abunda kuke so wai ku fada sai a kawo."


"Sannu da kokari. No komai yayi. Maryaam ko kina son wani abun?"


"A'ah"


"Shikenan kice mungode"


Yar aikin ta juya ta tafi... Shi kuma ya kai kulolin kan dinning ya ajiye.... Ya tafi kitchen ya dakko plates da su kofuna bayan ya dauraye.


Doya ce da dankali da sauce din kodar kaza. Sai soup din kazar da kuma kunun gyada dake tashin kayan kamshi


Ya zuzzuba komai a babban tray ya kai har gaban Maryaam... Ita dai tana zaune akan kujerar daya dorata tana kallon ikon Allah..


Ya koma kusa da ita ya zauna bayan ya dora tray din akan cinyar sa.


"Matso kici...."


"Zan iya ci da kai na fa"


"Banason musu.... Haaa bude bakin"


Dariya ma ya bata tayi murmushi kawai..


"Bude mana"


Dan budewa tayi .. Ya zura mata a bakin ta.. Tana taunawa tana hadiyewa har sai da taji ta koshi tace,


"Na koshi"


"Anya?"


"Allah na koshi..."


"Toh turn dinki ne... Ba ni nima" Ya dora mata tray din akan cinyar ta ya bude bakin yana nuna mata cikin bakin nasa da yatsansa,


"Zura mun"


Tana zura masa loma daya yayi saurin runtse idanun sa.


"Ruwa."


"Bari na dak...


Ta mike zata dakko yayi saurin janyo ta ta fada kansa. Bakin ta ya kama kawai ya shiga kissing har sai daya tabbatar yajin ya tafi ya zare a hankali yana cewa,


"Wani abu na tauna mai yaji"


Ita dai bata ce komai ba. Ta mike zata dakko ruwan ya riko ta,


"Ina zaki?"


"Ruwan zan dakko maka"


"Ai kin bani ruwa na sha.. Kin manta?" Yana kanne mata ido daya.


'sam bashi da ta ido.' Ta fada cikin zuciyar ta.


"Zan saka turare ne..."


"Sa mana kamshin na jiya ya sunan su please?"


"Khajingru da bakhkur oud mukarrama"


"Nice.... Na yerwa incense and more dinne dai?"


"Eh"


"Suna da kamshi sosai .. ki saka mana order din wasu nawa ne? Sai na tura mata"


"Sai na tambayeta tukun" Ta fada tana jona burner nan da nan ta saka turaruwan ko'ina ya dauka da kamshi...


"Zo Maryaam."


Ta koma ta zauna dan nesa da shi. Ya tashi ya koma inda take ya matsota jikin sa sosai,


"Dan Allah kayi hakuri"


"Meyasa kike tsoro na da yawa haka?"


"Bakomai"


"Saboda mun raya sunna Maryaam? Dik ma'aurata sunyi fa ba akan mu aka fara ba... Ko dan kin tsaneni kawai?"


Tayi shiru kanta a kasa batace komai ba. Ya sake dago da fuskar ta yana sanya idanun sa cikin nata yace,


"Ki mun magana please ..Maryaam ...kinsan yadda nake kaunar ki kuwa?"


"Ban tsane ka ba fa"


"Ni wa?"


"Kai mana"


"Eh dama baki tsane ni ba mana a yan uwantaka, Amma a matsayin miji agare ki Maryaam kin tsane ni mana.. ki ce wani abu"


"A'ah..."


"Ina da wata idea ko ince plan... Let's start all over again.... Let's get to know ourselves ko?"


"Toh...."


Yayi murmushi yana mika mata hannun sa,


"Sunana Al-mustapha jalaludden Muhammad... Shekaru na talatin da biyar... Nayi makaranta ta ta primary da sakandire anan Nigeria inda muka koma england anan na karasa high school na shiga jami'a. Na karanci harkar zane na gidaje da sauran su wato architecture. Ni ne babba awajen iyaye na. Mu biyu Allah ya azurta iyayen mu, Ni da kanwata Fatima muna kiran ta da Yusra. Ina aiki a karkashin kamfanin mahaifi na sannan jnada ofishina na kai na dake nan birnin Nukaa muna gine gine da zane muna kwangila da sauran su. Inason kasancewa atare da ke har karshen rayuwata... Ina fatan har a aljanna mu kasance a matsayin mata da miji... Sai turn dinki..."


Ta danyi murmushi ta hude baki zatai magana sai kuma ta kasa kanta a kasa.


"Zanyi kissing dinki deep idan baki magana ba" ya fada yana zagaye lips din nata da hannun sa..


"Zanyi zanyi"


"To yi"


"Sunana Maryaam ana kirana da Amaal....sunan mahaifina Junaid Muhammad. Shekaru na sha tara, Nayi karatu na nursery and primary anan Nigeria . Inda na cigaba da karatu na a Cappadocia turkey . Daga nan muka koma madeenah anan na karasa highschool. So bayan mun dawo Nigeria sai muka koma baya na nayi aji biyu ko ince daya da rabin term. Anan na karasa secondary school. Yanzu Ina university Ina karantar architecture. Ni daya Allah ya azurta iyaye na da su. "


"Mashaa Allahu.... Maryaam zan iya samun number wayar ki? Ya ke yammata na... Duk da dai ni Ina da number ki kece baki da tawa kawo na saka miki"


Batayi musu ba ta dakko ta bashi ya karba ya saka number wayar sa yayi saving da 'Honey Bunny ♥️' Ya zaro wayar sa shima ya gyara sunan daga A zuwa 'Light of my life♥️'


"Kinga yadda nayi saving sunan ki? Ga yadda nayi nawa ma a wayar ki .."


Karbar wayar tayi ta kalla ta ajiye ta agefe. Al-mustapha ya bude baki zaiyi magana wayar sa ta fara ringing yaki dauka har sai da aka kira sau uku sannan ya dauka yana tsaki ya sakata a kunnen sa,


"Okay gani nan inshaa Allah..." ya katse wayar ya ajiyeta acikin aljihu..


Ya mayar da duban sa ga Maryaam da kanta ke kan kujera ita dai tayi shiru,


"Zan fita.... A office ne ake kirana wani mutumi da mikewa zane baya kasar ya dawo yanzu ne yana jirana a office"


"Tohm.. Allah yaba da sa'a"


Bude baki yayi cike da mamaki abunda ta fada yayu murmushi dadi ya mamayeshi gaba daya yace,


"Ba mafarki nake ba ko?"


Ita dai murmushi tayi. Ya sake fadaada faraar sa yace,


"Allah ya miki albarka.... Kankana uwar r....


Bai karasa ba ta saka hannu ta rufe bakin sa tana cewa,


"Jiran ka fa suke?"


"Sai na gama gayawa iyali na kalamai tukun..."


"Zanje sashen Hajiya"


Ya rankwafa saitin fuskar ta har tana jiyo bugun zuciyar sa. Daidai kofar kunnenta na dama yace,


"Kin manta? Hajiyan data aiko mana da me aiki ta kawo abinci bamu tashi ba. Tace tanata buga kofa ba'a bude ba...lokacin fa muna gado muna sharholiya. Anyways jeki idan bakyajin kunyar agano abunda mukayi. Da tafiyar ki kaman ta yara masu koyan tafiya... Sai na dawo, take care... I love you way too much"ya karasa fada yana sakar mata sumba rantsattsiya.


Kunya duk ta dabaibaye ta na kalamannsa da yayi.... Ta kasa cewa komai.


"Na tafi"


"Toh..."


Dariya ta taho masa ya kanne yace,


"Me kikeso na taho miki da shi? "


"Bakomai...."


"To na fasa fitar"


"Uhm wannan "


"Me?"


"Ko meye ma"


"To shikenan... Allah ya miki albarka matar kirki. Sai na dawo"


Ya fice yana daga mata hannu. Yana fita ta sauke katuwar ajiyar zuciya. Kitchen ta nufa ta bude freezer ta daddauki su chocolates da cakes da ice cream ta koma parlor ta zauna tana ci tana kallon tv dake nuna shirin wasan kwaiwayo a Africa magic hausa na 'Carbin kwai...'










ZAFAFA BIYAR WRITERS 💕
[10/5, 7:50 PM] Hafsaat💞: _4_
_9_




____




**Al-mustapha bai baro office ba sai bayan sallar isha'i. Anan suka yi jam'i tare da abokan aikin nasa da wadanda suka kawo aikin na su..


Suna idarwa bayan sun kammala komai ya shiga mota ya dauki hanyar gidah... Akan hanyar tasa ne yanata saaqe-saaqen abunda zai sayawa Amaal kawai ya tsaya a wani shopping mart dake bakin titi..


Akwai tukubar mai gashin kazar hausa awajen da kayan ciki. Ya shiga cikin babban ginin shagon ya dakko mata cookies da choco biscuits. Ya tsaya awajen me kazar nan ma ya sayo gasassu ya dauki hanyar gidah..


Yana zuwa masu gadi suka bude masa ya shigar da motar sa har sashen na su. A mota ya tsaya bai futo ba ya kira Amaal.


Alokacin kuma ta futo kenan daga wanka ta saka vest da underwear tana kokarin zura riga akai ta jiyo wayar ta tana kara.


Dauka tayi ganin Al-mustapha ne ke kiranta ta kara a kunnen ta,


"Hello......." Ta jiyo muryar sa..


"Assalamu Alaikum.." Ta fada tana kallon kanta ta mudubi. Ya amsa sallamar yana cewa da ita,


"Na zo...."


"Kazo ina?"


"Ba Maryaam ba ce?"


"Itace" Ta amsa cike da mamaki,


"Okay Al-mustapha ne... Nazo Ina kofar gidan ku ina bakin gate.."


"Okay meya faru?"


"Ki futo mana yammata na...ke nake jira nazo zance"


"Ohh... Okay" Ta amsa shi.


Kit.. Taji ya kashe wayar, Tabi fuskar wayar da kallo bayan ta zare ta daga kunnenta..


"Wata sabuwa... Zance kuma?"Ta sauke gwauron numfashi ta zura hijabin ta har kasa me hannu ta faffesa turare ta fita da wayar ta a hannu.


Hango shi tayi ya futo daga mota yana jingine a bakin motar ya zura hannuwan sa acikin aljihu.. Yana ganin ta taho yayi murmushi. Hasken fitilun wajen ya haskaka ko'ina kamar rana..


Tana karasawa ya bude mata gaba .. Ta tsaya tana kallon sa


"Shiga mana gimbiyar mata...." Ya nuna mata kan kujera,


Shiga tayi ta zauna tana kallon ikon Allah... Shima ya koma mazanun direba ya zauna ... Bai kashe motar ba ya kunna musu ac..


"Yammata..."


"Na'am" Ta amsa tana satar kallon sa


"Na same ki lafiya?"


"Alhamdulillah....."


"Mashaa Allah... Nayi matukar farin ciki... Zamu dora ne daga inda muka tsaya dazu. Maryaam nazo wajen ki ne a yau, a kuma yanzu a matsayin wanda yazo da kokon barar sa yake neman ki temaka masa... Ina fatan kina saurara?"


"Eh...."


"Maryaam... Inason ki cire duk wasu abubuwa da suka faru a baya kiyi fatali da su ki dau rayuwar da muka samu kammu aciki a yanzu ki dasata a zuciyar ki , ranki dama gangar jikin ki gaba daya.. kinaji?"


"Eh"


"Ki dau auren mu a matsayin kaddarar da Allah ya rubuta akan mu gaba daya sai ta same mu. Maryaam inshaa Allahu ba zaki dana sanin aurena ba I assure you inshaa Allah.. kada ki manta da kaunar ki na tashi acikin rai na tun kina zanin goyo...Maryam na mallaki hankalin kai na gaba daya na gane rai na ya kamu da zazzafar son kasancewa da ke a matsayin wadda nake so muyi rayuwa ta har abada atare... Ina nufin rayuwar aure... Mukazo daga karshe Allah ya amince mana muka zama a inuwar ma'aurata... Maryaam me zanyi ki kaunace ni? Maryaam mai zance miki ki amince da kaunata? Maryaam fadi duk abunda kikeso idan har befi karfi na ba ni zanyi miki kawai don na samu ki sassauta kiyayyar da kike mun... Wallahi tallahi billahi babu macen da nake kauna a duniya bayan mahaifiyata da kanwata sai ke... Dik duniya idan kika ajiye su agefe babu macen da nake son kasancewa da ita har karshen rayuwata irin ki Maryaam.. wallahi idanu na ko kallon wasu matan su burge su basayi. Ba ma na jin kaunar wata mace a duniya sama da ke.... Maryaam ko kinsan kaunar da nake miki ce tayi sanadin samuwar depression dina a baya.? Yes ciwon damuwa kusan duka bappanin mu sun sani ma....."


Amaal tayi shiru tana sauraron sa... Tabbas ranar nan taji Bappah Abdullahi lokacin da suka zauna a parlorn hajiya baki daya sanda ana maganar auren su. Taji yana cewa Al-mustapha ba shine marar lafiyar nan ba?


"Maryaam..." Ta jiyo muryar sa ya sake kiran ta...


"Na'am..."


"Ina miki kauna tacacciya marar gauraye. Ina miki son so, Ina miki kaunar kauna... Ina kaunar ki da rai na, zuciyata da jikina gaba daya.. Maryam son ki ya mamayemun gangar jiki da ruhi gaba daya I'm not even joking. Maryaam..."


"Na'am


"I love you way too much... Maryam wata iriyar kauna nake miki..." Ya kamo hannunta ya saka akan saitin zuciyar sa ya cigaba da cewa,..


"Saurari yadda zuciyata take bugu Maryaam... Bugun adadin kaunar da nake miki ne matyaam. Zuciyata a duk inda nake inde aka kamo sunan ki saita sauya salon bugawar ta... Maryaam hear me out.. Dan Allah Dan Allah dan girman Allah ki karbi kokon barata ki kaunace ni .. ki nunamun kauna... Kaunar da nake miki ta Kai bazan iya bijerewa abunda kike kaunata ba ko menene shi. Maryaam idan ranki yafu kaunar ki rabu dani wallahi na amince zan sawwake miki din.... Maryaam me kike so.. zaki karbi soyayyata ki kin amince na rabu da ke?" Ya yago paper da sauri ya rike biro.


Take idanuwan sa suka fara zubar da ambaliyar hawaye... Kuka ya shiga yi sosai harda shessheka.. ya bude motar ya futa ya koma bangaren datake ya tsugunna da gwiwiyon sa akasa.


Ya rike paper da biro yana dubanta muryar sa da jikin sa suna rawa sosai yace,


"Wallahi kaunar da nake miki bazan iya tauye miki hakki ba.. maryaam bazan iya miki tilashe ba. Maryaam raina da zuciyata sun raja'ane da zazzafar kaunar ki. Ki dauki option daya. Ni Al-mustapha nayi alkawarin cika miki burin ki ko menene shi..." Ya karasa fada yana zubar da hawaye. Hannun sa sai rawa yake ya rike biro.


Maryaam idajuwanta suka ciko da ruwa fal. Gaba daya mamakine yasa ta kasa magana. Gege daya da tsoro mai tattare da fargaba. Ita kanta ta kasa gane irin kaunar da Al-mustapha ke mata.... Lamarin har tsoro yake bata yadda yake nuna mata kauna kamar zararre


"Maryaam kiyi magana please..... Kaunar ki ce sanadi.. and I promised you ... Na tabbatar miki bazan taba fadawa su Hajiya ai kece me son rabuwa da ni ba. Zan dorawa kai na lefi inshaa Allahu dede da kwayar zarra ba wanda zaiga lefin ki Maryaam... Kinji?"


Kuka tafashe da shi. Kalaaman sa sun mata nauyin data kasa jurewa. Cikin lallashi ya rungumeta shima yana hawayen,


"Ko mun rabu bazan taba ganin lefin ki ba Maryaam... Zan rubuta miki takarda yanzu inshaa Allah" Yana neman zare jikin sa tayi saurin rarumo shi ta kara manne shi da jikin ta tace,


"Karka sake ni....",


Ya daga da sauri yana dubanta. Murmushi ya fadada akan fuskar sa yace,


"Kin amince? Zaki dena tsanata maryaam?"


Ta share hawayen ta tana jan hancin ta tace,


"Ban tsane ka ba dama yaya Al-mustapha... Na amince "


Dadi kashe Al-mustapha ya bude gaban motar sosai ya nannade hannuwa ya dauketa charan cas ya shige cike da ita cikin gida ya ajiyeta har daki akan gado.


Ya koma mota jikinsa nata rawa ya kwaso komai ya Kai kitchen ya ajiye kowanne inda ya kamata. Ya rufe kofar sashen na su ya shiga dakin da sauri bakinsa har kunne....


"Bari nayi sauri nayi wanka don kara tabbatarwa shin da gaske kunnuwana da idanuwana sika jiye da ganemun abunda Maryamu ta ke fada? An bani dama nayi wankan? Ranki ya dade?"


Amaal ta gyada masa kai tana murmushi... Ya wuce dakinsa da sauri ya shige bandaki ya fyallo wanka ya jima agaban mudubi yana shafe shafen turaruka masu dadin kamshi. Ya taje kansa ya fesa turaren baki me kamshin vanilla ya fita yana mai yaba kyawun da shi kansa yayisa kansa.


Kofar dakin ta ya nufa ya kwankwasa . Amaal ta jiyo ana kwankwasawa tace,


"Waye?"


"Ni ne.... Gimbiya! An bani izini na shigo?"


Tayi murmushi tana daga Inda take a kwance tace,


"Ka shigo"


"Godiya nake Maryamu tahh..."


Shiga yayi bakinsa dauke da sallama,


"Assalamu Alaikum wa rahamatu Allah..."


Ta amsa shi tana dan kauda kanta gefe cike da kunya.... Ya karasa ya haye kan gadon shima ya sadaada ya kwanta a kusa da ita ya zura hannun sa ya kamo kafadar ta yayi mata pillow da kirjin sa..


"Ki cire hijabin mana... Yi hakuri"


Tunowa tayi da vest ce kawai da underwear a jikin ta ta grigiza Kai da sauri ..


"Yi hakuri bar abun ki maryamtu Tah ... Yadda kikace ai haka za'ayi.. kinci abinci?"


"Eh..."


"Ga cookies can da su kaza na sayo miki suna kitchen"


"Nagode Allah ya saka da alkhairi. Allah ya kara budi mai albarka Amin"


Da sauri ya juyo da fuskar ta yana dubanta,


"Amin... A'ina kika koyo wannan adduar haka? I'm impressed"


"Awajen Hayateey..."


"Mashaa Allah! Shi yasa akeso ka auri yar gidan mutinci da sanin yakamata. Gidan tarbiyya da dattako. Maryaam komai kin hada nayi dace sosai. Allah nagode maka. Alhamdulillah" ya daga hannu yana addua.


Ita abun ma dariya ya bata.. gefe daya bacci datake ji. Ya sake gyara mata kwanciya yana shafa bayan ta yace,


"Bacci kike ji ne?"


"Eh...."


"Meye ake boye munne ta cikin hijabin?" Ya karasa fada yana zura hannunsa ta kasan hijabin ta


Ta damke hijabin tamau tana raba idanu. Murmushi yayi alokacin daya gano dalilin kin curewar hijabin nata..


Jira take ya cire hannun nasa amman yaki daga cewa zai ga meyasa sai ya zarce da taba nan taba can. Tamkar zata shide saboda yadda yake mata tafiyar tsutsa da hannun nasa cike da kwarewa da son nuna kauna ga abunda ake nunawa kaunar...


"Bac... Bacci nake ji" ta fada masa tana janye hannun sa daga cikin rigar ta


"Tohm Maryaam.... Na dena yi baccin ki kawai rage zafi zanyi dai.. amman bayaga haka ba abunda zan sake yi. Karkisa tsoro aran ki",


Ta gyara kwanciyar ta saboda baccin da take ji yacu karfin ta. Nan da nan kuwa bacci ya dauke ta. Al-mustapha kuwa tamkar ya samu baby doll yayi nan da ita yayi can da ita Yanata neman magana daga karshe shima yayi baccin bayan ya tashi yaje parlor ya hada tea ya sha... Bai ci abinci ba don bayada cin abinci shi sai hajiyan tayita takura masa wani lokacin sai idan yunwa ce ta tasoshi sosai agaba tukun sannan yake nema da kansa...



***********




Haka zaman na su ya kasance... Al-mustapha na cigaba da nunawa Amaal zallar kaunar da yake mata. Sannu ahankali kuma tana sakin jiki da shi sosai ba kamar da ba.


Sai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login