Showing 39001 words to 42000 words out of 95238 words
Chapter 14 - BAKON MUNAFIKI!! (BA NA MUTUM DAYA BANE) NA NANA HAFSATU MISS ZOZO.txt
daga ciki... Aaayan ya leka yana kiran sa
"Musty fresh meye haka? Zo mu tafu mana"
"Kuje ba zani ba sai dai idan yarinyar nan zaku fasa zuwa da ita... "
Aayaan yaja dogon tsaki yana girgiza kai,
"Wannan kuma baka isa ba kayi kadan... Katon banza katon wofi...."
Ya koma ya zauna yana cewa direban yaja motar su tafi. Su Hindu sai murmushi akeyi Al-mustapha yace yafasa zuwa saboda da amaal zaaje
"Kiyi hakuri kinji sis?"
"Da me fa yaya yusraa?"
" Da abubuwan da hamma Al-mustapha yake miki... "
"Oh.."
"Dan Allah kiyi hakuri kinji? "
"Bakomai..." Amaal ta amsa. Kasan zuciyar ta na mmamakin kiyayyar da yake nuna mata a fili.
Tayi hamdala hadi da sauke katuwar ajiyar zuciya. Don dama idan yaje ma she won't be comfortable...
Direba ya kai su har cikin Nukaa hills and garden.. Suka furfuto da kayayyakin kulolin abincin da suke j da shi da abun sha da sauran abubuwan bukata..
Grass carpet ne kawatacce da aka shimfidee shi awajen ya bada irin picnic site dinnan me maana.. amman duk da haka suka shimfida babbar tabarmar da sukaje da ita suka zazzauna..
Abun shaawa Aayan yasa sika fara addua... Daga bisani Kuma aka fara hira ana zuzzuba abinci da abin Sha.
Bayan sun gama, Yaran ciki sukai swimming wasu sika hau lilo wasu dokuna wasu suka hau pirate ships da motoci da sauran su.
Sai da sukayi sallar laasar suka wuni cur anan sannan sika dauki hanyar gidah nanma Aayan yasa suka tsaya wani joint na ice cream ya sissiyawaa kowa scoop uku da donut daya da shawarma. Sannan suka tafi gidah.
+++++
Har sai da motar su taja sannan ya samu kansa da dai na waiwayan motar ya nufi sashen Hajiya...
Bakin sa dauke da sallama ya shiga. Hajiyan ce kawai a zaune tana jab carbi ta amsa sallamar da yayi. Ya nemi waje ya zauna,
"Ina kakaa?"
"Ya kwanta kansa ke cuwo"
"Allah sarki.... Allah ya bashi lafiya Amin"
"Amin Aameen..."
Hajjya nata jab carbi ta. Ya janyo wayar sa ya shiga WhatsApp. Yana cikin duba statuses. Ya gano na Aayan kaman ba zai dai duba ba sai kuma yayi viewing..
Hotunan su ne kala kala acan wajen. Harda videos.... Gefe daya Kuma hotunan amaal ne ya sassaka su tayi kyau tayi mirror selfie da Wanda tayi video din kanta tana murmushi..
Ya samu kansa da zooming hotunan yana kalla daya bayan daya ..
"Kun fasa zuwanne?" Muryar Hajiya ta doko dodon kunnen sa
"A'ah .... Su sun tafi"
"Kai meyasa bakaje ba?"
Jan kan leben sa yayi yayi yace,
"Banason rashin kunyar yarinyar nan amaal. Jini na be hadu da ita ba shiyasa"
Hajiya Maryam ta kalle shi tana girgiza kai,
"Meyasa kake haka ne Dan yaye? Saboda Allah me yarinyar nan ta maka? Yarinyar da batada kwaramniya ma? Bantaba Jin ko ganin Wanda ke ganin lefinta ba wallahi sai akan ka"
Ya smau kansa da yamutsa fuska... Dai dai lokacin da hannun sa ya danno kan selfie din aaayan da amaal din awajen Wani lilo sin tsattsaya,
Mtscew... Yajaa tsaki da baisan ma ya fito ba
"Tsakin me kake?"
"Bakomai hajiya... Kai na ne ke dam saramun"
"Bari a dakko maka Panadol to."
"A'a zai lafa Hajiya...nagode "
"A zubo abinci ko?"
"A'a Hajiya..
"Ba abunda kake bukata?"
"Babu Hajiya"
"Shikenan..."
Tashi tayi ta shiga daki. Can an dan jima Kuma ta dawo. Gogan naku na zaune akan kujerar lokacin zuwa lokaci kuma ya kan duba agogon dake wutsiyar hannun sa
"Wai tsakin me kake ta faman yi ne?" Hajiya ta tanbaye shi.
Da alama bai masan yanayin tsaki ba. Ya saka hannu ya sosa keyar sa yana kakaro murmushi,
"Bakomai... Network wayata nake son ya dawo"
"Okay tohm"
Can sai suka fara kallo wani tsohon film din hausa da ake a Africa magic hausa. Hajiya ta bada hankalin ta sosai tana kallon. Yayinda Al-mustapha ke Jan kasan leben sa yana taunewa kamar wata alawa..
Ya mike ya daga labule ya koma ya zauna,
"Hajiya"
"Na'am danyaye"
"Ki kira aaayan ki ce su dawo haka?"
"Ah akan me zan kira su su dawo suna can suna kulla zumunci? "
"Hadari ne ke ta haduwa fa.."
"Yo ai ba yara bane dazasu bari ruwa ya dake su dan yaye... zasu samu mafika."
"Akwai....akwai tsare tsaren da muke da Aayan ne akan office dina... Shiysa nake son su dawo da wuri saboda mu samu mu karasa"
"To ka kirawo shi mana..."
"Ba..ban..Banda network a wayar"
"Zasu dawo ai komai dare inshaa Allah.. idan Kuma ka matsu yanzu kakeson kuyi abin to ga waya ta nan ka kira shi.," Ta karasa fada tana mai tura masa wayar gsban sa
Yayi haka zai dauka kenan yajiyo karar budewar gate din sashen... An shigo da zungureriyar motar da sika tafi da ita.
Ya samu kansa da sauke zuciya mai dauke da maduakakiyar farin ciki marar fisaltuwa.
Duk kowanne ya tafi hanyar sa. Aayaan, amaal da yusra Kuma sika tunkari sashen Hajiya
Al-mustapha ya nemi waje ya zauna yana mai sake hade fuskar sa tamau.
Suka shigs parlorn sunata sallama. Hajiys ta amsa musu. Al-mustapha ma ya amsa yana Wani danna wayar sa ya dora kafa daya kan daya
"To ga Aayanun nan ya dawo ai danyaye. Gwara ku karasa aikin da kuke ko?"
Aayaan ya kalli Al-mustapha kallon karin bayani,
"Wane aiki?"
"Babu..."
"Aikin me dalla..?"
Al-mustapha ya mike ya fuce da ga sashen yana eani kobarewa... Yana fita amaal ta sauke numfashi
Da tasan yana sashen Hajiyan kuwa da ba zata ma shigo ba....
Ta rasa wacce iriyar tsana yake mata.. Ta jujjuya kai kawai kasan makoshi ta furta
"Allah ya kyauta..."
A bangaren hajjya sukai magribaa har bayan ishai tukun sannan itaa da yusraa sukayiwa hajiyan sai da safe. Yusra ta nufi bangaren su. Ita Kuma amaal ta nufi sashen Hayateey tanata sake sake a zuciyar ta.....
_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE :(MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_
_INA MA'ABOTA TURARE.. KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE. TSAFTA KUMA TABA CIKIN IMANI ...KU MATSO KUSA.. MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN *YERWA INCENSE AND MORE* DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.. AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO.. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA.._
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU:08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER: yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
*_MATSO KIJI_*👂🏼👂🏼👂🏼👂🏼🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*_KINA DA LABARIN 'YAN BIYAR DINNAN SARAKAN ZAQAQAN LABARAI SUN SAKE DAWO MUKU DA SABON SINQI SINQIN LABARANSU_*
_LABARAI NE MASU TSANANIN ZAQI DANDANO DA TSAYAWA A ZUCIYA_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
_MUTANEN NIJAR KU TUNTUBI +22799643131_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
[9/7, 9:32 PM] Hafsaat💞: _BM_
_NA:_
_NANA HAFSATU_
_PAGE: 27_
_BM vip arewabook: https://arewabooks.com/book?id=64a96774d6e097b6d856cfb9._
___
*Yana* kishingide a parlon sa bayan sallar ishai.. wayar sa ce a hannun sa yana dubawa... Yana kuma duba wata takarda da ya ajiye a gaban sa. Fuskar sa sakale da gilashi na kara gani.
Hamid ne agabansa. Da laptop yana karanto wa sarki Junaid bayani. shima sarki Junaid din yana daga kansa idan Hamid yayi masa bayani..alamun gamsuwa....
"Yauwa gashi nan ranka ya dade... Million takwas dinnan ya za'ai da ita... A saka a bankin ko ....?
Zuruf sai ga shigar hajiya hadiza... Ta wurgawa Hamid harara tana duban sarki Junaid
"Sallamamme... Wai aache ka ajiye naka yaran a gefe. Kaje ka dakko wannan da da abunda ka hada da shi, Ka bashi amanar dukiyar kandemi gaba daya.. wai ajiyan sarki junaid. Sannan yaron da shi da jamila Allah tatsekaa zasu yi.. tatsa zasu yita yi maka kamar saniya.. ka dai canza tsari don mutanen kandemi suna yi da kai kan. ",
Sarki junaidu ya yamutsa fuska. Tinda ta shigo tana magana yana dauke da wayar hannun sa ya yana sosa goshin sa. Cike da kosawa yace,
"Kingama?"
"Da bngama ba ai bzanyi shiru ba ko"
"Hadiza saka lasifika ki kirawo sunan yan gidan mu ... Ki gaya musu abubuwan da ke faruwa..."
"Eh ai saboda ba tsoron su kike ji ba ai shiyasa"
"Sallamamme."
"Fita...walk out", ya fada a tsawace.
Ta futa da sauri har tana zubar da kwalla saboda bacin rai,
A hanyar fita sukai kichibus da su bappah Nuraddeen..
"Hadiza..."
"Ah hadiza ce?"
Kasa musu magana tayi. Ta daga kanta kawai ,, kuka ya kufce mata ta ja baya da sauri tana Jan hanci
"Meya faru?"
"Babu komai.. Barkan ku da warhaka. Na bar ku lafiya" Tana karasa fada tayi gaba tana share hawayen ta
Da sauri suka karasa shiga ciki... Alokacin hamida ya mike da computer a hannun sa yayi masa sallama zai tafi
Ya durkusa ya gayshe su da su sannan ya fuche bayan yayiwa sarki Junaid sai da safe
Gayshe da su yayi cike da girmamawa kamar ba sarki bane agare su,
"Meya faru da hadiza...? Naga ta futa tana kuka?"
"Ba wani abu Kawu.... Hadiza haka take kunsani kuma"
"Tabbas.. amman inason sanin menene ya hadu ku."
"Wai dan taga wannan yaron awaje na muna maganar budget da shi... Banker ne dan gidan kanwar Jamila marigayiya Rukayyah. "
"Kudin take so ba ka bata ba ko Ya ya?"
"Wai akan na bashi ajiyar kandemi.... Thou kawai fa account na sa ya bude na masarauta haka dik abun foundation zaa dinga sakawa a account din ya zama in charge... Meye lefi aciki Kawu? Ko kuwa Yaya?"
"Kasan mata sai ahankali....."
"Hakane kam.. Allah ya rufa asiri"
"Wato Kawu abunda yasa na nemi izinin ganawa da ku akan baba ne.... Ni a nawa tunanin nake gani kaman mu sake fita dashi waje a duba lafiyar sa... Ko kuwa? Tunda ya warware kuma Alhamdulillah yana samun lafiya fiye da baya,.. Amma wannan rashin maganar tasa yana damun Hajiya kwarai matuka.... Ya kuke ga ni?"
"Wannan batu naka yayi sarki., Allah yasa a mizani"
"Gaskia ka kawo shawara me kyau .... Musanman da yanzun naga likitocin basa zuwa Kuma... "
"Nima abunda na lura kenan... Inaga sunyi iya yin su "
"Hakane kam.. Toh Allah ya iya mana da iyawar sa Amin"
"Sai a gayawa su Gwaggon court yadda aka yanke...."
"In shaa Allahu "
"Allah ya dafa mana...... Aameen Yaa Rabbi"
"Toy bari muje.. ka huta lafiya"
"Sai da safe Kawu .... Sai da safe Yaya"
"Allah ya tashemu lafiya Amin"
"Alahumma Aameen."
Suna fita ya sauke ajiyar zuciya. Hadi da daga kansa yana tunani. Hajiya jamila ta shiga bakinta dauke da sallama. Ya amsa mata
"Barka da dare ranka ya dade"
"Barkan mu...."
"Ko zaka watsa ruwa?"
Girgiza mata Kai yayi alamun a'ah
"Ko kana bukatar space ne abbiyen su?"
"No kakki damu kiyi zaman ki."
"To ai ba nason damuwar da ke dabaibaye da Kai... Duk wani tsanani yana tare da sauki, Komai nisan dare gari zai waye Allah zai bayyana mai gaskiya... Dan Allah ka dena saka damuwar nan da yawa .. Dan Allah kaji?" Ta karasa fada muryar ta a raunane... Fuskar ta ta tatrare da damuwar data same shi,
Ya daga kansa ya kalleta yana murmushi. Yayi mata alama da hannu data dawo kusa da shi ta zauna,
"Godiya nake takawaa"
Dan murmushi yayi jin abunda ta fada. Ya saka hannu ya lakuce mata gefen kumatu yace,
"Gimbiya sarauniyar mata..... Allah ya miki albarka"
"Aàmin Aaamin ranks ya dade. Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai amfani ya kara tsare mana Kai da tsarewar sa."
"Aameen Aameen" ya amsa yana mai kamo hannunta cikin nasa yace,
"Wato binciken da akayi na abubuwan da Amaal ta dakko a sashen baba su allurorin Nan?"
"Eh.... "
Wani murmushi yayi me cuwo yaCe,
"Ni mutane na bani mamaki wallahi. Akan neman duniya wai sai ka lalata lahirar ka? Akan wane dalili zaka dinga kokarin kashe mutumin da Allah ya raya kwanansa bai kare ba? "
"Ina sauraron ka abbieyn su..."
"Baki daya tsubbu ne acikin kayan nan Kashi 90.... Kashi goma na ciki kuma ana illata shi ne ta hanyar gurbanta duk wasu sassa na jikin sa ahankali. Wannan tashin da baya iyayi baya komai sai dai a masa... wai ashe wata allura ce da akewa doki kakkarfa turawa keyi ma bama a nan kasar hausa ba. Turawa kewa dokunan su don rage musu karfi. Kuma allurar dokunan ma rabi ake musu bayan kwana biyu ayi musu rabin. Amman babaa kullum daya suke masa. Ki duba kiga karfin doki ana masa rabi ace nutum daya sukutum. Badan yanada sauran kwana ba wallahi da tuni sunci galaba akan sa ya mutu...."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.... Hasbun' Allahu wa ni'imal wakil... Kai duniya Ina zaki damu... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun wallahi gaba daya bakaji yadda jiki na yake rawa ba... "
"Wallahi wasu basajin tsoron Allah ko kadan basa fargabar Allah ya karbi rayukan su ahalin da sike muguntar. Me zasuje su cewa Allah? Ko kinsan Karin ruwan da ake masa shima ruwan tsibbu ne na chusa cuta arasa maganin ta?"
"Kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun....."
"Wasu abubuwan ma na manta.. Amma yarinyar nan amaal sai dai fatan Allah yasa ta gama da duniya lafiya Allah ya saka mata da mafificin alkhairin sa ya biyata da gidan aljanna. Ya bata miji nagari Wanda zai so ta ya kaunace ta har karshen raguwar su Amin"
"Aaamddn Amin."
"Na nemi iznin ganin su Kawu ai basu dade da futa ba..."
"Allah sarki ka sanar da su kenan?"
"Ban fada ba.... Na dai ce ya kamata a mayar da abbiey din asibiti..Amma a kàsar waje don gano dalilin dayasa baya magana.."
"Eh Hakan ya kamata gaskia... Allah yasa aje a sa'a "
"Aameen... Aaameen"
"Ina Aamaal?"
"Tayi bacci...."
Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kansa a sama
"Meya faru... Wani abun ne?"
"Bakomai..... Taci a mata babbar kyauta ne.... Allah ya mata albarka"
"Allahumma Aameen."
"Allah ya kareta da kariyar Sa....."
"Ameen abbieyn su.. a hado tea din?"
"Eh..... Banda sugar amma"
"Tom."
Mikewa tayi ta nufi dinning area komai a killace a Kuma jere yadda ya dache.
Ta hado masa tea din ta kawo masa cike da girmamawa ta durkusa ya karba yana murmushi hadi da shi mata albarka...
======================
Zuciyar sa che ke ta masa saqe saqe yana mamakin samuwar warakar Alhaji Muhamamd bayan dubban kudin da aka kashe na ganin an salwantar da rayuwar sa...
Mikewa yayi ya zura jallabiyar daya cire. Ya futo daga sashen sa ya nufi bangaren Alhaji Muhammad inda yake da bashi da lafiya..
Bude bangaren yayi ya shiga da spare key din hannun sa.. yana shiga ya rufe kofar da key ya haura sama.
Dakin ya shiga ya murda kofar ya rufe.. ya nufi Wani corrdorr ya ciro memoru card ajikin wata yar waya dake makale da CCTV.
Ya zauna akan kujera ya buda laptop din dake gaban sa ya kunnata.. Nan da nan ya sassaka dukkanin abunda zai bukata take faifen bidiyon ya fara haskawa na kowanne kwanaki har ya zuwa ranar da amaal ta hadu da Bappah Nuraddeen awaje lokacin data jiyo ta Kuma gano likitocin suna yiwa Alhaji Muhamamd allura yana kuka me wahalarwa...
Da sanda taje ta curo ruwan jikin sa da allurorin nan gaba daya ta saka aleda ta futar da su.... Yana karasa kalla ya dartsane harshen sa yana ciza cike da takaici.
Ya saka hannu ya dafe kansa saboda tsananin bacin rai. Computer ya janyo ya saka kafar sa akai ya dinga takata kamar ita tayi masa lefin.ya farfasata awajen yayi 'daya daya da ita.
Ya dauki memory card din ya nannade a tissue ya shiga bandaki yajefa a masai yayi flushing ..
Dama jiokin sa ya bashi itace.... yaja tsaki yafu a kirga..wayar sa ya janyo ya rubuta sakon da zai rubuta ya mike yana cewa,
" Uba da 'ya ke hargitsa mun dik wasu lissafi...... Junaid sai kayi dana sanin waiwayowar ka kandemi...Na hane ka kaki hanuwa ko? Ka dawo har ka karbi karagar mulkin kandemi..... To ka sani ka kana gab da shiga cikin matsananciyar musiba mai wahalar fita... Mu zuba!!!!!"
Ficewa yayi daga sashen gaba daya ransa a matukar bache yana sake harzuka tamkar wani kasurgumin zaki.....
*ARDO' K UNIVERSITY NUKAA*
(A U N)
Isa direba ya zura hancin motar cikin jami'ar dataci sunan marigayi mai martaba sarkin Nukaa, Alhaji Ardo kandemi...
Jamii'a ce da ke sahun farko na jerin jam'iyoyi da ake ji da su a garin Nukaa dama najeriya gaba daya.. dalibai daga kasashe ne ke zuwa karkashin ta suyi karatu...
Su ikhram ya fara kai wa departments dinsu daga karshe ya dauki hanyar kai amaal nata department din inda zasuyi lectures
"Hajiya karama aina zan ajiye ki ne?" Isa direba ya tanbayi Hindu dake owners corner tana tauna chingam.
"Department din da zaka kai ta...." Ta bashi amsa tana nuni da amaal da yatsa..
"Toh ranki ya dade..."
Ya kai su har department din. Amaal ta sauka tana gyara zaman jilbab din dake jikin ta Kalar maroon color. Ba kadan ba tayi kyau.
Yayin da Hindu ke sanye cikin riga da skirt sun matse ta .. halittun jikin ta sun bayyana ta yafa yalolon mayafi Kalar kayan .. tayi dauri rabin gashin ta awaje . Fuskar nan tasha foundation kamar amaryar karya. Ta zuba janbaki ja daya kara haskaka ta. Gefe daya Kuma turare ne ke tashi daga jikin ta...
Amaal ta mike ta fara tafiya. Hindu ta kira ta da,
"Ke..."
Ja tayi ta tsaya... Don ta saba ji da haka take kiran ta. Hindun ta taka ta sameta tana cewa,
"Ina ne office dinsa?"
"Wa?"
"Saurayi na da kikace eh malamin ku ne"
"Wallahi bansani ba"
"Karya kike"
"Allah bansani ba... "
"To tsaya dai...." Ta fada tana janyo wayar ta a jaka
Amaal ta dubu agigon dake daure a wutsiyar hannun ta. Batasan tayi latti a lectures. Amma gudun masifa yasa ta ja ta tsaya
Kiran sa Hindu tayi a waya .. sai data kira sau uku kafin ya dauka,
"Na zo fa...."
"Kina department din?"
"Eh...."
"Okay bani minti uku... Na fita bakin gate ne taho da aboki na... Yanzu zamu dawo.. "
"Alright."
"Na tafi ne?"
"No tsaya yazo seki tafi ..."
Amaal saura kadan ta fashe da kuka har ga Allah batasan lecturer din ya rigata shiga don baya bari ashiga idan ya riga shiga.
Sai da aka debi kusan minti Sha bjyar kafin motocin biyu su danno