Showing 36001 words to 39000 words out of 91674 words
Chapter 13 - SALON SO SABON SALO COMPLETE Book by Momyn Fareesa.txt
garinsu"dole abinciki Abba sosai.....yaya sadeeq kayi shiru?"menene kake tunani to?"tafad'a tana kallonsa"yadubeta suka had'a ido"sunkuyadda kanta k'asa tayi"dan yanzun batasan meyasa batason had'a ido dashi ba"cikin cool voice yace"nooryn yaya sadeeq kece nake tunani ko?"gabanta taji yafad'i amma batayi mgn ba"shikuma yayima iro falshing"da sauri yabud'e k'ofar driver sit yashiga yaja motar"Ahankali sadeeq yadubeta duk ta masa y'ar rama"bakyason cin abinci ko noor?"da sauri ta dubesa sai kuma ta dukar da kanta"tana fad'in kaima ai haka"toba kece kika jaba"duk kin tayarmun da hankali noor"pls karmu koma fushi da juna irin haka kinjiko?"dato ta amsa"yakalli gashin gaban goshinta"murya can ciki yace"anjima zamuje nakaiki amiki saloon naga bakyason kitso ko?"da sauri ta koma jawo mayafin yarufe kanta sosai tana fad'in kaima ai bakayi aski ba ko?"kinaso amun ne?"kanta kawai ta gyad'a masa"kinga Allah mgn zakimun ba wani body language ba"murmushi tasaki tana fad'in wai yaushe ka koyi surutu haka yaya sadeeq?"nidai nasan kana iya sama da awa 2 bakayi mgn ba"hmm! bake bace da nura kuka koyamun surutu ba"turo baki tayi tace"yau bakayi kyau ba"dama ni wani kyau ne dani?"ai zallar kyau sai noory nah ko?"kadai fad'a ne yaya sadeeq"amma kai ai kullum kanada kyau"ko yauma kayi kyau tsokanarka nakeyi"kuma idan aka maka gyaran fuska zakafi haka kyau"da gske ?"Eh mana"to shikenan anjima sai muje ki rakani ko?"nima kuma zan rama tsokanata da kikayi"duk suna mgn ne Ahankali"iro driver bayajin me suke fad'a"amma yasan surutu sukeyi"kuma ransa yabashi ogansa yakamu da son wannan y'ar yarinyar"parking iro yayi yafito yabud'e ma sadeeq k'ofar"atare suka fito shida noor yana fad'in kibar pic d'in aciki anjima kin d'auka"dato ta amsa ta rufe k'ofar"suka jero suka nufi ciki"gaba d'aya yau noor saita tsintsi kanta dajin nauyin mamy"shi kansa sadeeq na lura da yanayinta kamar kunya takeji"har zasu tura k'ofar saiya tsaya yana k'ok'arin ganin sun had'a ido da ita"ita kuma tak'i yarda"yana tsaye dab da ita hartana jin hucin numfashinsa"cikin murya mai kama da rad'a yace"menene duk kink'i sakin jikinki?"tana d'an murmushi ta matsa nesa dashi tana fad'in meka gani yaya sadeeq?"my noor kenan! nifa yanzun ko yaya kika canza nasan mekike nufi"k'ilan kunyar mamy kikeji zataga naje nayi bikonki ko?"dariya noor tayi dan yabata dariya"shi kuma yayi murmushi yatura k'ofar suka shigo atare"mamy na zaune kan kujera"gabanta center table ne an aza ruwa da cup asama"da alama tana jira su rage sanyi tasha ne"amsa sallamar su tayi tana murmushi tace"ga yarana ga yarana"sadeeq fuska asake yazo ya zauna agefenta"noor ta duk'a har k'asa tana gaisheta"ta amsa cike da kulawa tana tambayarta yatake"kafin noor ta amsa ta tashi ta zauna kan kujera"sadeeq ko ajikinsa yace"mamy kinga naje na rarrasheta harta hak'ura ko?"hakane ta kyauta ai"ya shirye shiryen azumi kuma noor?"Alhmdllh mamy saura kwana 5 yau afara ko?"Eh insha Allah"dg haka mamy ta tashi ta nufi kitchen"sadeeq yad'auki ruwan da cup yadawo gefen noor ya zauna yana fad'in" keda bakya sallah kike zancen ankusa fara azumi ko jinin ya d'auke ne??"tsabar tsaninin kunyar da kalamansa suka bama noor jitayi kamar k'asa ta tsage ta shige"tayi k'asa da kanta tak'i mgn"tab'e baki yayi danshi bega wani abun jin kunya a nan ba"ruwan yazuba acikin cup yana fad'in ga ruwa kisha babbar bak'uwa ta"yafad'a yana nufar bakinta da cup d'in"yamatso sosai dab da ita"saida ta d'an matsa sannan ta karb'a idanuwanta alumshe ta shanye"dama kishirwa takeji"sun isheki?"yafad'a yana kallon ta"uhmm! kinji?"sun isa"to shi yaya sadeeq bazaki zuba kibashi yashaba?"zakasha ne?"idan ranki yabaki zansha to zansha"idan kuma ranki yabaki bazan shaba to bazan shaba"yafad'a yana ajiye cup d'in"d'an murmushi tayi tace"nidai zakasha raina yabani"ta fad'a tana zuba ruwan acup ta mik'a masa"amamakinta saiyaki amsa ya matso da fuskarsa yakafa bakinsa jikin cup d'in"bbu yadda ta iya itama haka tabashi yasha kamar yadda yabata" tana masa dariyar wai yana shan yanga....gaba d'aya sun shagyala acikin shaukin kasancewa da juna basuma son mamy ta wuce ta gefensu ba ta nufi dining area"saida noor ta ajiye cup d'in sannan ta lura da mamy data koma wucesu"tana murmushi tana mamakin namiji bashida kunya"wai sadeeq ne duk yabi yasusuce akan mace"sbd duk kan Idonta taga suna bama juna ruwa"amma zata barsa taga zai sanar mata yana son noor ko kuwa?"
gaba d'aya noor kunyace ta kamata"ta fahimci sadeeq marar kunya ne lamba d'aya"tashi muje nayi break fast"dama tun d'azun bakayiba ka zauna da yunwa?"ta fad'a batare data kallesaba"bata abincin nakeyiba noor"fatana kawai kidena fushi dani shine kawai"da sauri ta tashi tana fad'in muje to"bece komaiba yabi bayanta"bayan sun iso yaja kujera ya zauna"ita kuma tana dg tsaye ta had'a wannan ta zuba wannan duk ta loda masa"shi kuma yanata aikin kallonta ta k'asan ido harta gama"ta tura masa komai agabansa tana tsuke fuska ta wani turo baki tace"nidai Allah bana son karage komai anan yaya sadeeq"yadda tayi mgn cikin kwantar da murya dayin k'asa da ita sai yaji bazaima iya yimata musu ba"cup d'in kunun gyad'a data zuba masa ta yad'auka yana fad'in kema kizuba mana"ni nak'oshi ne dan Allah karka tursasa ni"shikenan ai"yafad'a yana yin bissimilah yafara kurb'a.....cikin few minutes yashanye ya ajiye cup d'in"sannan yaja plate d'in doya da k'wai da farfesun kaji data zuba yanata k'amshi"noor na masa fira sama sama yana murmushi sbd wani firan duk shirmene"sai gashi sadeeq yalodi abincin dayafi k'arfinsa batare daya saniba"dan da k'yar yake nishi"noor na murmushi tace"wayofa na maka yaya sadeeq gashi kaci abinci ka k'oshi ko?"kadena zama da yunwa dan Allah...ai kin kyauta noor dakika saka yaci da yawa"wlh acikin satin nan beson cin abinci.....sukaji muryar mamy abayansu"sosai noor taji kunya"tana mamakin wai meyasa Idonta ke rufewa bata lura da mamy na wajen?"sadeeq ya dubeta yana fad'in nidai kika shammata haka ko?"ita dai kanta ak'asa batayi mgn ba"yamik'e tsaye yana ajiye mata keys d'in part nasa yace"ki gyaramun zanje nadawo"dg haka yabaro dining area d'in"yayima mamy dake zaune a parlourn sallama yafita"sbd dama police station zaije.
yana isowa police station d'in...✍️
wannan book d'in nakudine idan kina buk'atar siya serious normal grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Ki turo shaidar biyanki ta what's app number d'ina 08100084251
Idan kika karanta mun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba........ sadeeq yana isowa police station d'in kai tsaye office d'in DPO ya wuce wanda case d'in yake a hannunsa"time d'in da akaje da sadeeq yaga hamisu saida ya tausaya masa"sbd sun masa duka na fitar hankali da k'yar yake motsi"yana kwance magashiyan"sadeeq yatab'e baki yana tuna ai bashida matausaya tunda yadoki mace"kuma k'aramar yarinya kamar noor"bbu laifin data masa saidan cin zalin"komawa yayi office d'in DPO yazauna aka tura jami'an tsaro sukaje suka tafo da Abba d'ahiru"wanda yayi bala'in tsorata daya gansu" sbd azatonsa ko shima kamashi za'a yi"sadeeq na anan zaune aka shigo dashi"jikinsa na kirma ya dubi sadeeq dake zaune yana latsa waya yace"yaro mena maka da zafi haka daka zab'i ka tozartani?"me noor tasanar maka akaina??ba wannan yasaka aka ce kazo nan ba"ka zauna Ayi mgn"cewar DPO"Abba bece komaiba yazauna kan kujera suna furkantar juna da sadeeq"k'amshin turaren sadeeq nata kaimasa kofofin hancin Abba ziyara"atak'aice sadeeq yafara mgn kamar haka"wannan bawan Allah k'anin mahaifin yarinyar ne"amma suna cutar da rayuwarta tason yab'ata mata rayuwa" sbd yana aminta da mazan banza mararsa mutunci da tsoron Allah na zuwa wajenta"yakuma tursasata akan ta kulasu"ayanzun dole yayi signing ruk'onta yafita a hannunsa zata koma gun kakarta"wato mahaifiyar babanta marigayi"sannan muddin d'ansa yafito dole yakiyayeta yadena cin zalin nata ko kuwa nasaka ab'atar dashi har abada....."duk ita noor d'in ce ta fad'i ina mata haka?"banza sadeeq yayi masa"Abba yasaki ajiyar zuciya ab'oye dayaji ba'a yi zancen mariya ba"wani file DPO yaturo ma sadeeq yayi signing sannan aka bama Abba shima yayi"kafin DPO cikin kakkausar murya yace"ba sadeeq yabamu umarnin hukunta yaronkaba "ah ah muna bimata hakk'inta ne amatsyinta na y'ar k'asa kuma marainiya"baza muce kacire hannunka akantaba"sbd kana nan amatsayin uba gareta"amma ruk'onta yafita a hannunka"yaronka bashida ikon hukuntata sbd akwai zalinci ahukuncin nasa"zamu rik'esa tsawon sati 2 agidan yari idan yaladabtu zamu sakesa"dg k'arshe muka koma kamaka da cutar da marainiyar Allah"ko kayi k'ok'arin had'ata da mazan banza" zamu manta kai babbane a d'auki hukuncin daya dace akanka.....dpo na dasa aya azancensa sadeeq yadubi Abba yace"shikenan zaka iya tafiya"bece komaiba yamik'e tsaye yafita aransa yanajin zafin abinda noor taja aka masa shida hamisu...yakumasha alwashin bazai k'yale noor ba" har gidan innar zai tura hamisu yayi mata fyad'e yagudu yabar gari"idanma wannan d'an gayun sonta yakeyi ai dole yafasa yafita rayuwarta yatsaneta"ta hakane kawai itama zai gama da ita kamar yadda yashafe shafin babin labarin rayuwar mariya.....
sadeeq kuwa sai wajen 1:15 pm yabar police station d'in"suka tsaya ahanya sukayi sallar azahar"kafin suje wani babban shago yasiyowa noor waya sabuwa dal me tsadar gske iphone 11 +"kafin yanufo gida yana tunanin k'ilan yanzun tagama yi masa gyaran d'akin.....
noor kuwa bayan fitarsa itama acikin parlourn ta dawo"mamy na lura da ita tana jin nauyinta"hakan yasa ta dinga janta da fira harta d'an sake"kafin can tace"dama mamy zan gyara b'angaren yaya sadeeq"to shikenan noor kin hutashsheni"dama beso masu aiki suna gyarawa sai yace" saidai ni ko kuma idan week end ne yagyara da kansa"dg yanzun indai ina nan zan dinga gyara masa mamy"yauwa noor kin kyauta"Allah yayi muku albarka"akunyace ta amsa ta wuce upstairs"kusan awa d'aya da wasu mintina tayi tana gyara ko ina"dan part d'in 6days kenan rabon da agyarashi"sannan har jallabiyoyinsa ta wanke kala2" da vest kala3 farare data gani an jik'a da klin"time d'in data gama ta fito a parlourn tasami mamy na jera lunch"tana a tsaye kanta ak'asa tace"mamy sannu da aiki"yauwa noor"kema sannu nasan kinsha aikin gyarawa sadeeq ko ina"akwai wani aiki ne?"ah ah wlh bbu ki zauna ki huta kinji?"mairo da laure duk suna nan kowa kuma aikinsa yakeyi"to shikenan mamy zan tafi gida"ke noor na lura yanzun gaba d'aya bakyason sakewa agidan nan"ki bari kici abinci mana"lahh na k'oshi mamy"inaso naje gida nayi wankane"meyasa bazakiyi anan ba?"cewar mamy tana baro dinning area d'in"tazo ta zauna kan kujera"noor dai na tsaye tana wasa da yatsun hannunta"mamy nata satar kallon ta"ita kanta tasan muddin sadeeq ya mallaki noor amatsayin matar aurensa ta dace da suruka ta k'warai"gaba d'aya yarinyar ta lura batada kwad'ayi da son abin duniya"bazaki jira sadeeq yadawo ba?"d'an murmushi tayi sbd dama akansa zata tafi bataso yana yin abinda zataji kunya agaban mamy"ai mamy zanje nadawo ne"murmushi mamy tayi domin ta fahimci kunya takeji sadeeq yazo yasameta anan"batayi mgn ba takira gudan driver gidan ta waya tace"ga noor nan yakaita gida"bayan sun gama wayar"noor ta mata sallama ta fita....bayan sun iso anguwarsu ta sauka ta masa godiya"cikin gidan Abba dahiru ta shiga tayi sallama"halima na tsakar gidan da inna saratu suna girkin rana"ke banza y'ar iska shine kika saka kwartonki yasa y'an sanda suka kama yaya hamisu ko?cewar halima tana bin noor da wani mugun kallo"inna ta k'arbe zancen da cewa"aiko yanzun dg wajensa take sun gama aikata fasik'ancinsu ta dawo gida"amma ita munafukar Allah tana nuna ita ta Allah ce ko?"kuka noor ta fashe dashi tana fad'in wlh zargina dakukayi kuda Allah"yaya sadeeq ba mutumin banza bane....zanci ubanki ko kimun shiru"cewar innah"noor batayi mgn ba tashige d'aki da sauri"duk abinda tasan natane"ta kwashe tasaka cikin wata babbar ghanah"sbd dama kayanta masu kyau suna gidan su jummai"tana rik'e da ghanar ta fito tsakar gidan tana goge hawayenta"tanajin suna zaginta da fad'in Abba ma yana can police station d'in" muddin shima aka rik'esa saita sani"banza ta musu ta fita"gidansu jummai ta shiga"kasancewar duk abinda yafaru duk mutan anguwar sun sani"to suma gidansu jummai ansani hamisu na hannun hukuma"dukda jummai na skul kasancewar part time ne take zuwa"wanka noor tayi ta canza kayan jikinta"umma ta zuba mata abinci tana mata nasihar tayi hak'uri da abinda rayuwa tazo mata dashi "bayan taci ta k'oshi ta had'a komai nata"ta sanarwa umma acan gidan inna zata koma"agayawa jummai da Abba idan sun dawo"kafin ta fito ta tari nafef ta nufi gidan kakarta......
Noor ko minti 10 da fita batayiba sadeeq yashigo"yana rik'e da ledar da kwalin wayar ke aciki"mamy ta amsa sallamar sa yazauna agefenta yana k'arewa parlourn kallo sbd bega noor ba"mamy ina noor take?"ta tafi gida yanzun nan"fuska bbu walwala yace"shine tak'i bari nadawo ko?"kuma mamy kika barta ta tafi?"to yazanyi da ita sadeeq?"tunda tanaso taje gidan ai bazan tursasata ba ta zauna ko?"sanan na lura tanajin kunya ne"d'an murmushi yayi yace"damafa haka take"d'azunma dazamu shigo haka ta dingajin kunyar ta ganki"ai haka akeso ga y'a mace dan kunya ado ce"kai kuma na lura ba itace dakai ba"shiru yayi yana sosa k'eya"saiya mik'e tsaye yana fad'in zanje ciki mamy"dato ta amsa yanufi upstairs"ta bishi da kallo tana mamakin sadeeq"saidai tasan dama YAU DA GOBE ta wuce wasa"tana aiki kan kowa tana kuma canza kowa"sadeeq na doso parlourn sa k'amshin air fresheners da turaren wuta yadaki hancinsa"ko ina k'al"wayar yasaka chargy"kafin yawuce ciki yarage kayan jikinsa yanufi bath room.... murmushi yasaki dayaga kayansa da noor ta wanke ta shanya"Allah sarki my baby noor"ada nayi fushi dake kin tafi baki jiraniba"amma yanzun na huce"yafad'a duk cikin zuciyarsa yana wankan cike da nishad'i"bayan ya jima aciki sannan yafito"yayi tsaye gaban mirror yana d'aure da towel iya k'ugunsa "ko mai be shafaba yad'auki wayarsa yafara k'ok'arin kiran layin noor......sai gab da zata tsinke sannan noor dake k'ok'arin fita dg cikin nafef ta d'aga wayar"sadeeq yasaki ajiyar zuciya yana kallon kansa ta cikin mirror d'in"Ahankali noor ta masa sallama"ya amsa yana lumshe idanuwansa kafin murya can k'asa yace"nazata bazaki d'auka ba?"yaya sadeeq baka gajiya da neman mgn"to meyasa bazan d'auka ba?"nasan ko kina tsoron nasaceki ne?"tunda gashi kink'i jira nadawo naganki na mayar dake gidan da kaina"bafa haka bane wlh"wanka naje nayi"nima yanzun shinayi ai"turo baki tayi tana fad'in nidai bbu ruwana gani nan zan shiga gidan innah"kaje kaci abinci"ta canza topic"kema ai baki ciba"wlh naci yaya sadeeq"to shikenan na yarda my noor"idan nagama shiryawa zan kiraki kibani address d'in gidan nazo zamuyi mgn da ita innar"to shikenan amma nidai dan Allah kaci abinci sosai"kinsan Allah nina gaji da abincin dakike ta lodamun ko kice naci"bayan ke bamaki iya cin abinci agabana"yanzun haka banajin yunwa noor sbd abincin dakika bani d'azun"nidayin lunch sai 4 gsky.....bekai ayaba takashe wayar"murmushi yasaki"yana jinsa cikin nishad'i"ahaka yashirya cikin manyan kaya"voile ne bak'i yasaka"da hula da agogo duk bak'ak'e"yanata zabga k'amshi"yayi kyau sosai" wayar ya d'akko yasaka acikin kwalinta , yarik'e ledar a hannu ya sakko down stairs"dan zai fara zuwa amasa gyaran fuska saiya wuce wajen noor"mamy dake zaune ta dubesa yana danna waya"lunch d'in fa sadeeq?"d'ago kansa yayi suka had'a ido da mamy"yana b'ata fuska yace"nidai sai 4 pm mamy"noor ma tadameni da rigimar wai naci abinci ?nace mata sai 4"murmushi kawai mamy tayi dan sosai soyayyar sadeeq da noor d'in ke burgeta"fatan adawo lafiya ta masa yafita atare da iro driver"bayan angama askin yayi sallar la'asar"ya d'auki wayar zai kira noor"anan yaga ta turo masa text na address d'in gidan"bbu b'ata lokaci suka nufi gidan inna...
Ab'angaren noor kuwa tana rik'e da jakar kayanta tayi sallama ta shigo tsakar gidan"inna na zaune kan tabarma bakin k'ofar d'aki"tana sanye da glass"yayinda goggo saude(k'anwar Abban noor)ke duk'e tana wankin kayan inna"amsa sallamar ta sukayi"inna na fad'in sallamar wa nakeji kamar ta takwarata??"nice inna da kaina"b'atan kai kikayi kenan?"tunda nasan d'ahiru be barinki zuwa gidan nan"to wai inna koshi yaushe rabon dayazo gidan balle yace ita tazo?cewar goggo saude tana k'ok'arin shanya kayan kan igiya"noor dai na murmushi ta gaishesu"kafin ta zauna kan tabarma bayan takai kayanta d'akin inna"atak'aice ta musu bayanin azabar datake sha agidan Abba dahiru"inna kuka taka mayi"goggo saude kuwa batayi mamaki ba sbd tasan mugun halin sa"kuma dama tana samun labarin wahalar da noor kesha sama sama awajen y'an gulma"noor kuwa tasanar dasu labarin sadeeq da zuwan dazaiyi ayau"tasa nar musu uban gidantane tana aiki a company nashi yana biyanta"beda matsala yana tausayin talaka shinema yasaka aka kama hamisu kuma yace"tadawo nan da zama"saidai ta b'oye musu gidan mamy datake zuwa.....sosai inna da goggo keta sakawa sadeeq albarka"noor dai na murmushi"kafin ta tashi taje ta share soro tas"ta wanke sumuntin ta goge ta shimfid'a sabuwar tabarma"ta zauna tana turawa sadeeq address d'in gidan....ko zaman minti 15 batayiba wayarta tayi ringing"saida taji fad'uwar gaba dataga sunan yaya sadeeq akan fuskar wayar "dama d'azun daya kirata da my noor ta dinga mamaki"gashi sai taji tanata yawan tunasa"shiryawar nan tasu ta yau ita kawai tasan irin farin cikin data tsintsi kanta aciki"anutse tayi sallama bayan ta d'aga kiran"sadeeq yace"gani nan bakin titi kizo kitafi dani"dato ta amsa tana kashe wayar"ta mik'e tsaye ta gyara mayafin dogowar rigar jikinta"kafin ta fito k'ofar gidan"murmushi shimfid'e asaman baby face nata ta iso bakin titi"sadeeq da tunda ya hangota yaketa kallonta babu ko k'iftawa yanajin fad'uwar gaba"fitowa yayi yatsaya gaban motar"suka had'a ido da noor"sosai yamata kyau"jitakeyi aranta inama ace sadeeq sonta yakeyi"saidai ita aganinta mutuncine kawai atsakaninsu "kuma ita tana y'ar talakawa ina ita ina sadeeq boloniya.... mayen k'amshinsa yadaki hancinta"ta d'ago kanta suka had'a ido"wani tsadaddan murmushi yasakar mata yana fad'in kina guduna ko my noor?"shiyasa kika tafi d'azun"bafa haka bane yaya sadeeq"hmm! ga sak'onki sai muje ko?"sak'on miye?"tafad'a batare data amshi ledar ba"wayace babba na siya miki sbd kidinga d'ebe kewa"kuma da dare inaso mudinga chats ko vedio call dake"saidai ban aminta ba bayan ni kiyi mgn ko chats dakoma waye"yafad'a fuska bbu walwala"noor dai natsaye tayi shiru tana mamakin kalamansa na k'arshe"sannan tana ganin hidimarsa agareta tayi yawa....tunanin gulman zakiyi ko amsar wayar?"kinsan dai banason musu ko?"nidai gsky yaya sadeeq kadena mun hidima haka sbd Allah"sannan indai tanada tsada bazan amsaba"tafad'a cikin shagwab'a tana turo baki kamar wata k'aramar yarinya"gaba d'aya sadeeq kallonta kawai yakeyi"cikin cool voice yace"fad'amun gsky shekarunki nawa?"d'an juya idanuwanta tayi kafin tace"18yrs fa"kawai ada nace maka 20 yrs sbd karka mun kallon y'ar yarinya ko?"murmushin gefen baki yasaki yana fad'in to mecece ke yanzun inba yarinyar ba?ni Allah babbace yaya sadeeq"to yanzun nikin san shekaruna?"d'an