Showing 21001 words to 24000 words out of 91674 words

Chapter 8 - SALON SO SABON SALO COMPLETE Book by Momyn Fareesa.txt

10 Jan 2025

9074

burunta ya auri y'ar yarinya wacce zata chanjashi"ita kanta tasan sadeeq nata baya kula mata ko yayin mgn"amma abin mamaki yana biyewa noor suna shirme"ganin yayi shiru sai tace" shikenan ni ina ruwana tunda baza kayi sallama da itaba?"nidai ai nasami y'a"koda Abuja kayi zamanka banda damuwa....tamkar zaiyi kuka yace"wai mamy da gske kikeyi?"murmushi kawai tayi"ya mik'e tsaye yana kiran iro driver ta waya akan yazo ya d'aukar masa kayansa"mamy ta mik'e tsaye tana d'aura d'an kwalinta ta biyosa suka fito dg cikin d'akin"laure na parlourn tana turaresa"mamy tace"ina yarinyar nan y'ata laure?"tana kitchen hjy wanke wanke naga tanayi"mamy na murmushi ta kalli sadeeq"da ido ta masa alamar yaje suyi sallama"in bacin ganin ga laure dayayi musu"yanata wani shan k'amshi yanufi bakin k'ofar kitchen d'in yashiga"noor na tsaye gaban sink tana wanke wanke"k'amshin turarensa data shak'a yasaka taji fad'uwar gaba ta juyo da sauri....ta ganshi tsaye yana latsa waya"wanda ba haka bane"bayanta yaketa kallo daya shigo" yana ganin zata juyo yamaida idanuwansa kan waya....yaya sadeeq shine bbu ko sallama dan Allah?"har naji tsoro wlh"ta fad'a tana juyawa taci gaba da abinta takeyi"ya d'auki second 10 kafin yace"dama mecece ke inba matsoraciya ba?"sbd kinga mamy shine kikemun yadda kika ga dama ko?"to ai badauwama zanyi acanba zan dawo zaki san kin mun gwalo"d'an murmushi tayi tace"kainefa kaja yaya sadeeq"nidai Allah yatsare hanya yabada sa'a"sosai yaji dad'in addu'ar ta da yadda mamy ta yaba da ita sosai"dama shi tuni ya fahimci tanada tarbiyya shida ita rashin fahimta ne kawai aka samu"be amsa da Ameen ba afili sai cikin ransa"kamar an masa tilas yace"akwai abinda kike buk'ata ne?"batare data juyoba tace"bana buk'atar komai"dg haka taci gaba da aikinta sbd taji haushin be amsa addu'ar data masa ba"shikuwa kawai ya tsintsi kansa dason ko yaya su had'a Ido sannan yatafi"amma miskilin yarasa tayama zaiyi mgn harta juyo"kawai saiya juya ya fita dg cikin kitchen d'in"mamy kuwa jinsa shiru ranta yabata k'ilan warning yatsaya yima noor"saidai yadda taga fuskarsa asake yafito tayi mamaki....har bakin mota mamy ta rakosa tana masa fatan alkhairi sannan tadawo ciki"tasami noor har tagama wanke wanken tana goge kitchen d'in"sannunki da aiki noor"ke baki gajiya ne?"ah ah mamy ai zan sami lada ne"nasaba kafin ummanah ta tafi tabarni nice ke tayata aikin komai"Allah sarki wani waje ta tafi ne?"cewar mamy tana nuna kamar batasan komai ba alan noor"da Eh kawai noor ta amsa"mamy na cewa muje a Ida kitson muyi sallah ko?"dato ta amsa ta biyo mamy suka baro kitchen d'in.....
Acikin y'an awannin da noor tayi gidan ta gane mamy mace ce me kirki dason mutane"yyinda ita kuma noor mamy ke yabawa da tarbiyyar ta"abincima da aka kamata cewa tayi ta k'oshi"saida mamy ta nuna bataji dad'i ba harda fad'in zata kira sadeeq sanann noor taci abincin"ta gyarawa mamy kayanta dake cikin ward rope"bayan ta gama wajen k'arfe 3 suna a parlourn"noor kanta ak'asa tace"mamy me zan girka miki?"inaso k'arfe 4 natafi gida"Allah sarki da bari nayi saima 4 d'in na aza abu mai sauk'i tunda sadeeq baya nan"banaso ki rasa islamiya"ai yau friday ne"kuma yanzun da dare nake zuwa nadena zuwa ta rana"to shikenan dukda haka noor kinsha aiki da 4 tayi sai iro yamik'aki gida"gobe insha Allah sai kimun girkin"tana murmushi kanta ak'asa sbd bata cika son had'a ido da mamy ba"Ahankali tace"ai mamy nifa abincin gargajiya nafi iyawa"kamar dame dame kenan noor dan nima nafi yin irinsa?"kanta ak'asa ta lissafa kusan girki kala 10 na gargajiya wanda ta iya"masha Allah kin iya sosai"to gobe insha Allah zakimun alkubus d'in"sannan shima girke girken zamani zan yiwa habiba mgn(y'ar k'anwar mamy"tazo kuje skul nasu na week end datake zuwa"wato catering skul"kona wata d'aya ne ki koya"sbd arana girki kusan kala 5 suke koyawa"to k'arfe nawa ake zuwa?"10 zuwa 4 antashi duk asabar da lahadi"kodai in hak'ura mamy kamar yaya sadeeq bazai yardaba"murmushi mamy tayi tace"shida yana can inama zai san kinje"zuwa sadda zai dawo kinma iya abinda kika iya ko?"godiya sosai noor ta yiwa mamy"sai bayan sallar la'asar sannan iro driver yakaita gida"ranta fal mamaki wai ita ce sadeeq marafa yakai cikin family nasa"lallai abin da mamaki.....
Haka rayuwar taci gaba da wakana "acikin sati 3 zuwa 4 mamy ta gama yadda noor mutum ce mai amana kuma marar kwad'ayi"sannan ta fahimci yarinyar nada ilimi na addini"saidai kuma tana lura akwai wata damuwa dake damunta"kawai tabari sadeeq yadawo tasakashi shi yabinciki noor d'in yaji damuwarta"sbd ta fahimci noor najin nauyinta" shiyasa bazata tambayeta ba da kanta"kuma abin mamaki noor an k'ware wajen iya girki na zamani dana gargajiya"dan brain nata nada saurin d'aukar abu"gaba d'aya noor tayi haske da kyau sbd samun kulawa awajen mamy"dan har kayan shafa da kayan sawa sabbi mamy ta siyawa noor"gashi ta k'ara gogewa da wayewa sbd tana shiga cikin jama'a daban daban"especially a catering skul nasu"sosai takeyin tsabta da gayunta"aiki kuwa bama sai mamy tace tayi mataba"saidai kawai ita tayi"gashi mairo mai aiki ma tadawo gida tuni.....agidan Abba dahiru kuwa bbu wanda yasan Inda noor ke zuwa azatonsu wajen aikin take zuwa"sannan Abba na lura da yadda ta canza"saidai gidansu jummai bata b'oye musu komai ba"sbd kamar iyayenta ta d'aukesa"komai nata me amfani da kayan sawarta dana shafa duk suna can gidansu jummai....tunda sadeeq yatafi idan yakira mamy be tab'a cewa abama noor ba"itama kuma bata cewa agaidashi"sannan idan har taji yakira waya sai taji fad'uwar gaba"yanzun ita damuwarta shine tasamu taje wajen ummanta"gashi taji yace"idan yadawo zai sallameta"kuma yanzun take buk'atar aiki"gashi yadda ta shak'u da mamy bataso tadena zuwa gidan......
Afannin sadeeq kam duk yadda yaso yabasar da yawan tuna noor dayakeyi abin yaci tura"kuma ko nura bai sanar mawa ba tana zuwa gidansu"saidai kawai yabar abin amatsayin sbd yayi sab'o ne da ita"sannan yana tsintar kansa da jin haushin ko sau d'aya idan yana waya da mamy bata cewa abata su gaisa"ko kwanaki daya kira mamy yanajin surutunta da dariyarta"abin yak'i yabar ransa"sannan daya tuna dayace idan yadawo zai sallameta sai yaji wani iri"sbd yasan batada mantuwa tsab zatace yasallameta d'in....to ahaka sadeeq yayi wata guda a Abuja"duk abinda ke faruwa a marafa interprises tamkar agabansa akayi"domin suna communication ta waya sosai da ma'aikatansa.....


Ayau yakama satday"kuma ayau sadeeq zai dawo gida dan yanama hanya"so yakeyi zuwa 12 pm ya iso gida ,tunda ta jirgi ne zai tafo"tun wajen 8 am noor na gidan"sbd mamy tasanar mata ajiya gobe zatayi bak'i"batama sanar mata sadeeq neba"sbd taga dg noor d'in har sadeeq d'in bbu wanda ke tambayar d'an uwansa.....zagewa noor tayi tayi abinci kala 4 na zamani kala 2 na gargajiya kala2"wanda atare da mamy akayi girkin sbd Ayi sauri"sai wajen 12 d'in kuwa aka gama kusan awarsu 4 a kitchen"bayan angama mamy tace"noor kije d'akina kiyi wanka ki shirya akwai kaya na nan gefen bed"nasan kingaji saiki huta ko?"dato noor ta amsa tabar kitchen d'in"mamy kuwa da mairo suka gyara komai"kafin mamy tafara kwashe komai ta nufi dining area tana jerawa.....ahaka sadeeq yaturo k'ofar yashigo da sallama cikin k'asaitacciyar muryarsa"mamy na murmushi tace"d'an halak kak'i ambato"yanzun ka fad'o mun arai wlh"tafad'a tana nufo cikin parlourn"sadeeq na murmushi ya k'araso yana rungumeta yana fad'in I miss you so much mamy nah"nidai cikani dan Allah kai baka girma sadeeq"indai awajenkine bana girma mamy yafad'a yana cikata yanata kallonta cike da so irin na uwa da d'a"mamy nasameku lafiya?"yafad'a yana zama kan kujera"itama agefensa ta zauna suka gaisa"tana tambayarsa ya hanya?"dan gaba d'aya yayi kyau da alama abujan ta amsheshi"yayi haske yana sanye da k'ananun kaya ajikinsa"sai satar kallon ko ina yakeyi"kamar yace"ina noor? amma zafin kansa yahanashi ya tambaya"mamy tace"katashi kaci abinci saika bayar da key d'in agyara maka b'angaren ka ko?"dato ya amsa yana d'aukar wayoyinsa ya wuce dining area"iro driver yashigo da kayan sadeeq da tsarabar dayayiwa mamynsa"ita kuwa mamy bed room d'in ta koma sbd itama tayi wanka ta huta"tana shiga tasami noor tsaye tana yane kanta da veil d'in dubai abaya dake jikinta purple colour"tayi kyau kamar irin classic lady d'in nan"mamy datayi sallama tana kallonta aranta tace"masha Allahu"mamy sannu da aiki"sannunmu dai noor"nima ruwan zan watsa"dg haka mamy ta nufi bath room"noor kuwa hakanan taji fad'uwar gaba"ta d'auki baby nokia nata tayi hanyar fita"sbd ta zauna a parlour tabar mamy adakinta ta sake.......✍️


Tofa guys ga noor ga sadeeq marafa yadawo ko yaya game d'in zai kasance?


shin da gaske mahaifiyar noor tana agadaz kamar yadda Abba dahiru yafad'a??


yaya labarin zahida da hafsat zasu hak'ura da sadeeq ko kuwa suna kan bakansu??


shin Alh mansur zai hak'ura da noor ko kuwa zai koma kawo hari akaro na biyu"??


ga kuma Mohd shima yana dakon soyayyar noor


shin ogah kwata kwata wato sadeeq zai tsaya akan yadda yake ko kuwa zai canza ta hanyar ruftawa a soyayya?


Jin amsar wa'annan tambayoyin yana a paid grps in sha Allah😻🥰


Karki bari Ayi babuke qtafiyar" siyen nagari maida kud'i gida ne "bbu nadama ko cizan yatsa qtafiyar..... SALONSO yazo da sabon salo! zazzafar soyayya na'a paid grps🤪🤣


yi k'ok'arin biyan naki halal d'in ta wannan hanyar👇


wannan book d'in nakudine
Normal grp 300
Vip grp 1000
Special people 2k wato 3pages in a day


zaku biya kud'in ku ta wannan acc number👉2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina 08100084251
300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne


banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira❌


Y'an nijar kutuntub'i wannan n👉 +227 88 01 90 50
Normal grp 500f
Vip grp 1000f
Special people 2000f


dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba..........noor na dosowa cikin parlourn ta tsintsi kanta dajin fad'uwar gaba"sai kuma ta shak'i daddad'an k'amshin turaren *sadeeq marafa*"ta lumshe golden eyes nata tana k'arewa cikin parlourn kallo"yayinta zuciyarta ke bugawa.....kamar ance ta kalli dining area! idanuwanta suka hasko mata kyakykyawar fuskar sadeeq yanata cin abincin sa hankali kwance"tamkar besan ta shigo parlourn ba"wanda tun shigowarta da motsinta jikinsa yabashi itace"yamata kallo d'aya yana mamakin sauyawarta"saiya d'auke kansa yaga zata kulashi ko kuwa?"noor kuwa gabanta yakoma fad'uwa"ta tsaya cak! tana jin kamar ta koma bed room d'in mamy ko kitchen ko kuma ta fita"dan haka nan taji bataso yaganta"tunda be damu da itaba"bata gama wannan tunanin ba zahida ta turo k'ofar parlourn ta shigo.....atare gabansu yafad'i itada noor"kasancewar zahida tunda noor take zuwa gidan mamy basu tab'a had'uwa ba"d'an murmushi noor tayi tana amsa sallamar zahida" kafin ta nemi waje kan kujera ta zauna batare data koma kallon shashen dining area d'in ba"itama zahida kan kujera ta zauna tana cika tana batsewa"ada noor taso tayi mata mgn amma sbd ganin yadda takeyin haka saita shareta"tana danna nokia d'in ta dake hannunta....sweet heart sannu da hutawa! cewar zahida cikin jan hankali"sadeeq yayi kamarma ba dashi take mgn ba"noor kuwa mik'ewa tsaye tayi ta nufi dining area d'in batare data san idan taje meye zatace masa ba?"wanda tayi haka da gayya ne sbd ganin zahida na cusa kanta yana disgata"tana k'arasowa taja kujera wacce keda tazarar kujera2 tsakaninsu ta zauna"kanta ak'asa k'irjinta na bugawa tana addu'ar Allah yasa karya disgata itama"ina wuni ya hanya??"bana son gaisuwarki noorrrrrr! kin damu danine ko kin tab'a cewa mamy ta baki waya ki gaisheni?"ada ai komawa zakayi sbd kinga mak'iyin ki ko?"yafad'a yana tab'e baki ya ajiye spoon d'in hannunsa"subahanallahi yaya sadeeq! mak'iya na kuma?"Eh mana ko nayi k'arya ne?"yafad'a yana mik'ewa tsaye sbd yagama cin abincin"hakan yayi daidai da isowar zahida wajen azafafe"noor tayi saurin lankwashe murya tana fad'in nidai ba wannan ba ina tsarabata take?"kuma time d'in dazaka tafi na maka addu'a kak'i cewa Ameen ko?kallonta yayi suka had'a ido"k'asa tayi da kanta"zahida tayi saurin cewa wacece wannan baby?"dariya noor ta dingayi tana kallon sadeeq"noor kin rainani ko?"very soon zanyi maganinki Allah"addu'a dakikamun korafi ai na amsa azuciyata"yafad'a yana d'aukar wayoyinsa zai bar wajen batare daya damu da zahida ba"hmm! yaya sadeeq naga babba dakai ana cemaka baby ai dole abin yabani dariya....azuciye zahida tace"ke banza y'ar iska ki kiyayeni wlh"kinata wani iyayin banza da cusa kai....noor bata kulataba tabar wajen"sadeeq kuwa tsaye yayi yana kallon zahida har tayi shiru"tamkar an masa tilas yace"karki koma zaginta"sbd me?"bansaniba"noor dake zaune kan kujera tana sauraronsu sai taji sanyi aranta na yanuna damuwa da ita kenan"bata gama wannan tunanin ba taji hucin numfashin sa gab da ita"atsorace ta d'ago kanta"tagansa agefen ta ta duk'o"keys d'in parts nasa ya aza mata saman cinyarta yana fad'in kije ki gyaramun part nawa"yana fad'in hakan yamatsa dg kusa da ita"mamy data shigo parlourn tayi saurin cewa" ka bari mairo ta gyara sadeeq nida noor mungaji munsha aiki na girkin da aka maka....babu damuwa mamy zan gyara masa ai bangajiba"sadeeq beyi mgn ba yanufi k'ofar fita yana fad'in mamy saina dawo"Allah yatsare"abinda ta fad'a kenan tana kallon zahida dake cika tana batsewa"yyinda noor ta kalli mamy tace"inane d'akin yaya sadeeq?"kije upstairs"k'ofar dake kallonki anan ne"dato ta amsa ta tashi tabar parlourn"mamy na kallon zahida tace"yanzun kika zone?"kuka zahida ta fashe dashi tana fad'in wacece wannan yarinyar mamy?"y'atace adangina take"ko itace sukayi fad'a da hafsat?"bazan iya ganewa ba"kuma ke miye abin yin kuka"haba mamy! kamarfa yaya sadeeq yadamu da ita fa"shiru mamy tayi tana d'aukar remote ta canza channel"tana mamakin naci da rashin zuciya irin na zahida datak'i hak'ura da sadeeq bayan tasan baya sonta.....
noor kuwa tana isowa ta gwada key d'in tana mamakin meyasa sadeeq keta k'ok'arin sakata cikin komai nasa"ita ai ta d'auka bata kai matsayin dazata shiga part nasa ba.....wow masha Allah! Abinda ta fad'a aranta kenan"kawai sai ranta yabata kamarma sadeeq d'in na parlourn sbd k'amshin turarensa da parlourn keyi..."cikin minti 1 ta k'arewa parlourn kallo"komai fari ne amma gaba d'aya yayi k'ura sbd wata d'aya ba'a gyara ba"da hanzari tafara k'ok'arin karkad'e kujerun"ta nufi bath room anan taga abin goge goge dasu hypo, da klin da morning frash....parlourn ta gyara ta goge kayan kallo"sannan ta nufi bath room ta wanke"ta fito tana gyara bed room d'in"ta kalli agogo har 1:30 tayi"dan tayi kusan awa 1 cikin d'akin"da hanzari taci gaba da aikinta sbd gudun kar time d'in sallah yayi"komai anan ma k'al ta masa"batare data damu da abinda take gani a bed room d'in ba kota nuna k'auyanci"wajen 2 pm ta gama duk ta gaji d'an kwalinta har ya kwance" kawai saita yafa saman kanta ta bud'e k'ofar ta fita......gabanta yafad'i sbd ganin sadeeq zaune yamik'e dogayen santalan k'afafuwan sa masu cike da gargasan gashi a saman center table" magensa na a gefensa yana kallon tv"ya jingina jikinsa abayan kujera"ta k'asan ido yakalli noor ya fahimci ta gaji.... d'an ja da baya tayi da sauri tana fad'in mugunta bbu kyau dan Allah nidai ka rik'eta na fita"d'ago kansa yayi yakalleta"yana tab'e baki yace"wlh ko bini Ahankali kona wurgo miki ita ajiki"dan Allah kayi hak'uri ni dama gida zan tafi"ba 4 kike tafiya ba?"ai naga bbu abinda zanyi kuma kadawo ai"kizo ki zauna muyi mgn"kayi hak'uri muje parlourn mamy"kuma banyi sallah ba"shiru yayi ya rufe ido ita kuma ta fita da sauri"sbd bataso tana tsayawa waje irin haka dg ita sai shi"sadeeq kuwa hakan da noor tayi sai yaji ta burgesa"sbd hakan na nuna bata son kad'aicewar su kenan"amma yasan Inda zahida ko hafsat tasamu haka dad'i zataji"tashi tsaye yayi ya wuce bed room nasa yana kallon ko ina k'al"yaje bath room ma haka"gaba d'aya sai yaga shi ba'a tab'a gyara masa d'aki yayi kyau hakaba saidai ko in mamy ce ta gyara masa"sbd tasan beson masu aiki na gyarawa"laptop nasa ya d'akko a ward rope yazauna saman bed bayan saita komai yafara ganin abinda yafaru tun bayan tafiyarsa Abuja"yyi shiru ya rungume hannayensa a k'irji yana kallon komai"ta yadda noor ke taya mamy aiki ko tayi mata aiki"da yadda take girmamata"da yadda suke fira cikin raha da mutunta juna"da yadda noor ke kai da kawowa dg kitchen zuwa dining area duk saida yagani"anan yafahimci har catering skul tana zuwa"kuma.girkin d'azun itace ta masa"gaba d'aya sai yaji tausayin yarinyar"yana ganin kamar yadda yadinga takurata abaya da gaya mata maganganu masu zafi be kyautaba"rufe laptop d'in yayi"yana k'udurtar ayau zai tambayeta labarin family nata"kuma yakaita gidansu da kansa"sai kuma yatuna datace masa d'azun ina tsarabarta?"gashi mamy kawai yayima tsaraba.....ajiyar zuciya yasaki yamik'e tsaye yanufi wajen mirror"yajawo wata loka"atake yafiddo wata leda fara ta shoping"yazaro wani had'add'en turare me tsadar gske"wanda wancan zuwan nasa Abuja yasiyosa 50k"turaren na kaya ne kuma na mata ne"dan harda tsintuwar agogo da zobe aciki"kawai yaga yamasa a Inda yake siyo turaruka shine yasiyo da nufin yabama mamy"saiya mance be bataba"bayan yagama kallon turaren kamar mai yin nazari saiya mayar"ya nufi bath room"cikin nutsuwa yayi wanka yafito"yana shiryawa yanajin wayarsa na ringing"wani lallausan yadi ash colour yasaka"an masa aiki da bak'in zare"yasaka takalmi da agogo bak'i"amma kansa bbu hula"yataje bak'ar suman kansa dake kwance"masha Allah duk macen dataga sadeeq marafa" indai budurwace dole ta k'yasa....lolx!wayarsa ya d'auka yana bin kiran nura"bayan nuran ya d'aga sadeeq yasaki guntun murmushi yana fad'in "abokina dukda mommy ta aurar dakai amma bakayi hankaliba?"ka dameni da kira haka"dg d'ayan b'angaren nura yace"kaga mlm sbd na kira mu gaisa kake mun k'orafi"kai dake gwabro baka kiraba saini mai iyali nayi k'ok'arin kira"d'an iskan k'arya! cewar sadeeq yana kashe wayar sa yana tuna yaushe nura zai dena kiransa da gwabro ne?"da wannan tunanin yasakko down stairs d'in anutse"mamy da noor na zaune suna fira da alama noor d'in tayi sallah taci abinci"yyinda zahida bata cikin parlourn"kallonsa mamy tayi taga yadda ya wani d'aure fuska"fita zakayi ne sadeeq?"eh zanje office naduba wasu abubuwa ne dukda week end ne"amma sai nayi la'asar zan fita"noor dai kanta ak'asa koma kallonsa batayiba"mamy na satar kallon ta tana lura idan sadeeq na awaje bata sakewa"d'ago kanta mamy tayi da nufin tayiwa sadeeq mgn taga gaba d'aya noor yake kallo"hakan yasa tayi shiru ta mik'e tsaye tabar parlourn"sadeeq ya zauna kan kujera"shiru yad'an ratsa tsakani"noor dai kanta ak'asa tana wasa da yatsun hannunta"tasha alwashin bazata masa mgn ba saidai idan shine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login