Showing 18001 words to 21000 words out of 91674 words

Chapter 7 - SALON SO SABON SALO COMPLETE Book by Momyn Fareesa.txt

10 Jan 2025

9072

ban tausayi"gaba d'aya jikinta rawa yakeyi sbd tsoro da tashin hankali"yyinda sadeeq kallonsu kawai yakeyi"shi damuwarsa kar wani abu yasami y'ar mutane asanadinsa.....koka cikata mutafi da ita komu harbeta"ina zakuje da ita ne?"yafad'a afusace yana kallonsu"sbd ransa yabashi tabbas Alh mansur yaturosu"sbd yasanshi game da mata bunsuru ne"duk shegen dayake ganin yacika namiji ne ya ajiye bindiga yazo yajata ta k'arfin tsiya mana"yafad'a cikin zafin rai"sosai noor dake jikinsa take mamakin izzarsa"azatonta zai tsorata dasu amma taga yanayin abu kamarma yana a company d'in sa....acikin k'attin wani gadararre yamatso da bindiga a hannunsa zai fisge hannu noor"ahassale sadeeq yature noor yacukumesa yabashi wasu kyawawan punchers guda biyu a fuska"sauran k'attin sukayi k'ok'arin harbinsa da binga yakara k'aton suka harbesa"ana cikin haka body guards d'in sadeeq suka iso suka fara harbi da bindiga"gaba d'aya noor ta rikice"ta fice a hayyacinta saidai ta sulale ta sume awajen....sauran k'attin biyu suka gudu"aka bar guda 2 kwance an harbesu a k'afa"sadeeq yanufi wajen noor yaganta kwance asume"d'aukarta yayi yanufi cikin mota da ita yana sanarwa body guards nasa su kama k'attin da aka harba"dole yaje dasu Police station su fad'a masa ubanwa yaturosu?"back sit yasaka noor"sai kallon baby face nata yakeyi"she is very beautiful! yafad'a aransa"kafin ya d'auki wasu ruwa swan saura dake front sit yafara yarfawa noor afuskarta"yana kallon gashin gaban goshinta....sau 3 yana zuba mata ruwan kafin tasaki ajiyar zuciya tana salati"sadeeq ya d'auke kansa dg barin kallon ta sbd ganin zata bud'e ido"koda ta bud'e idanuwanta ta kallesa ta kalli kanta da motar"ta tashi zaune da sauri tana matsawa nesa dashi tana gyara d'an kwalinta"dan Allah abinda yafaru da gske ne koda wasa??"tafad'a tana kalle kalle"kafin sadeeq yyi mgn wani cikin yaransa yabud'e front sit yashigo yajasu"alokacin kuma la'asar tayi....motar ta d'auki shiru"sadeeq na latsa waya yana chats da nura yana sanar masa abinda yafaru...yaya sadeeq! kansa yad'ago yakalleta beyi mgn ba"turo baki tayi tace"dan Allah nidai na ajiye aikin nan bazan iya wannan tashin hankalin ba"kuma nika saka akaini gida dan Allah na rok'eka"idan sadeeq yace"no da wuya ya canza"sbd haka aikinki marafa interprises yazama dole"karma ki b'atamun rai da wasu korafi"Allah yaka mata ki gode mawa da komai yazo da sauk'i"idan kuma kinfi buk'atar ranki yab'aci bbu damuwa....shiru tayi tak'i mgn tanata tunani kawai"dg haka bbu wanda yakoma mgn cikinsu"gaba d'aya noor kunyarsa takeji sbd tuna abinda yafaru d'azun data dinga shige masa"gaba d'aya jikinta k'amshin turarensa yakeyi.....suna isowa company d'in driver yafita"sadeeq ya kalleta yace"zaman me kikeyi dabazaki fitoba?"to ai 4 tayi ko?"ki bari zan sakq ibrahim yakaiki gida"dg yanzun karki koma hawa adaidaita ko hawan motar wanda baki saniba"sbd kiyaye lafiyar kanki"dg haka yafito dg cikin motar"itama ta fito tabishi abaya"suka sami iro driver zaune gefen table d'in noor"sai zare ido yakeyi alamar yana cikin tashin hankali"yana ganin sadeeq yasaki ajiyar zuciya"yana k'ok'arin mgn sadeeq yadakar dashi gun cewa"kaje ka amshi key ka kai noorr gida idan da matsala ka kirani bana son jin komai"amma yaya sadeeq ni wlh tsoro nakeji karsu bimu"tafad'a cikin shagwab'a tana b'ata fuska"hakanan sadeeq yaji fad'uwar gaba da mutuwar jiki"be kulataba yanufi office"tanata b'ata fuska tabi bayan iro driver.....jikin sadeeq amace ya zauna kan kujera yana bin kiran mamy dayagani awayarsa"tana d'auka tace"sadeeq kana ina?"inafa office mamy"inane kukaje?"bbu Inda mukaje karki damu mamy"wani yasanar dake wani abu ne?"ajiyar zuciya tasaki tace"Allah yak'ara tsaremun kai sadeeq"ya amsa da Ameen "jikinsa na bashi mamy na binciken meke faruwa dashi kenan?"beso hakan ba sbd beso tashiga damuwa sbd shi"ajiye wayar yyi yanufi toilet yyi alwalah yafito"anan cikin office d'in yyi sallah sbd 4 ta wuce"gaba d'aya moment d'in daya faru tsakaninsa da noor amota yak'i barin ransa"sai jan tsaki yakeyi yanajin haushin tuna abin dayakeyi.....


Kamar yadda sadeeq yatsara aje da y'an daban police station"to haka akayi"aka kuma gane Alh mansur yaturo su sbd yanason kasancewa da noor"abin yatsaya aran sadeeq"amma dpo yace"abarshi akaro na biyu idan yyi k'ok'arin koma haka sai a hukuntashi.....noor kuwa washe garin da abin yafaru bataje gun aiki ba"hamisu yasakata wanki"wanda saida yadaketa sosai sannan tayi wankin tana kuka"sadeeq kuwa dagaya bata zoba ya d'auka taji tsoro ne"yasha alwashin kuma zai bari sati 1 yyi idan bata zoba zai d'auki mataki"sai yaga washe gari tazo"amma gaba d'aya bata son had'a ido dashi ko yawan masa mgn sai shiru shiru datakeyi"hakan kuma yabama sadeeq haushi"ya lura tsoronta yayi yawa......
Ahaka rayuwa taci gaba da wakana"Alh labaran be koma zuwa gidan mamy da zancen zai aureta ko sadeeq ya auri zahida ba"saidai yasha miyagun alwashi kan sadeeq da ita kanta mamy"yayinda hafsat da zahida na nan da soyayyar sadeeq aransu"shi kuwa basa gabansa"ayanzun haka Anyi albashi kusan 5 days kenan"abin mamaki 50k ne aka bama noor"ita azatonta kud'in basu wuce 20k zuwa 30k haka"taji dad'i ta masa godiya"dukda yanzun tarasa dalili be sake mata fuska"itama saita kasance haka"ko dariya takeyi taganshi saita gimtse fuska"idan nura yazo ta masa gaisuwa ta mutunci"yayinda tsakaninta da Mohd sai gani dg nesa"Alh mansur kuwa yana nan da son noor aransa konace sha'awar ta"duk hanyar dazai ganta yabi amma babu nassara aciki...
mamy kuwa kaf labarin noor saida ta tsare nura yasanar mata komai "har had'uwarsu ta farko da sadeeq da fara aikinta a company nasa"mamy taji dad'i takuma saka anyi bincike kan noor ,taji labarin komai nata da irin wahalar rayuwar da yarinyar ke ciki sbd maraici"ta tausaya mata sosai.....
Ayau yakama friday ne"wajen 7:12 am sadeeq yasakko down stairs cikin zazzafan wanka na farar shadda"tasha aiki da bak'in zare"agogo,hula ,takalmi duk bak'i yasaka"yayi kyau tamkar wani Ango"yanata zabga k'amshi"babu kowa amain parlour"kitchen yanufa Inda yaji motsin mamy"yashiga ciki da sallama "tana tsaye tana had'a break fast"mamy ke d'aya ke aikin ne?"eh yaron mamy"sai kace wanda zaije zance irin wannan gayu sadeeq"d'an murmushi yayi yace"kai mamy nidai bama wannan ba"ke kad'ai ke aikin ina mairo me aiki?wlh jiya taje k'auyensu an musu rasuwa" laure kuma sai anjima take zuwa"kaga Inda inada y'a mace agabana saita tayani aikin ko?"to sadeeq ka hanani rik'e yaran dangi"bana son asamu matsala ne mamy shiyasa banaso" anjima da k'arfe 2 pm zan tafi Abuja ta jirgi mamy"amma sati 3 zanyi sbd an bani wata kwangila acan"masha Allah! ubangiji yataimaka sadeeq"Ameen mamy nah nika d'ai"yafada yana murmushi"itama murmushin tayi tace"amma yanzun kabari hafsat ta dawo nankafin kadawo" kodan sbd tayani kwana ko?"laure ta dinga tayaki kwana mana"zan kawo miki noorr ta dinga tayaki zama mamy....haka nan mamy taji farin ciki dayace zai kawo noor d'in"amma a fili sai tace"wacece haka kuma sadeeq?"tamkar bazaice komai ba"sai kuma ya yatsina fuska yace" wacce sukayi fad'a da wannan yarinyar hafsat kwanaki"to shikenan batada matsala ko?"kema mamy kinsan Inda matsala bazanma kawo taba"kuma warning zan mata sosai"in kuwa tayi abinda ba daidai ba nida itane"kaga sadeeq nidai bana son haka ka kawota d'in anjima"dato ya amsa ya fita yana fad'in 12 zai dawo yyi break fast"mamy na murmushi tace"ja'iri garama ka kawota naganta naga yaya halayenta suke?"jikina na bani kamar akwai wani al'amari me girma da zai wanzu tsakaninku kaida ita....
noor na zaune kan kujera"da hijab yadin d'an katsina ajikinta dark yellow "d'inkin jalbab"hijab d'in har k'asa taka mata"yatsun hannunta sunsha lalle ja gwanin sha'awa"ta d'aure mad'aurin hijab d'in dg baya gashin ta yyi kamar tayi acuci"cikin second 30 sadeeq dake doso wajen yak'are mata kallo ya d'auke kansa"aransa yace"dan gulma shine yau tayi irin wannan dreess d'in"k'amshin turarensa yashaida mata isowar both d'in nata"ta d'ago kanta tasaci kallonsa"bbu wanda yatanka wani acikinsu" sadeeq yashige office yana rik'e da brief case nashi"noor tayi d'an murmushi tana fad'in su almasifatu yau ansaka kayan al'ada"ta fad'a tana nufar office d'in"ta tura k'ofar anutse tana sallama Ahankali" yana zaune ,iya lab'b'ansa ya amsa"ta russina tana fad'in ina kwana?"kamar yana jira yace" bana son ita gaisuwar taki"yaushe rabon daki gaisheni"ke kin waye ko??"to yyi kyau ai dama rabuwa da aikinki kikeso ko?"to zan tafi Abuja nayi sati 3 dana dawo zan baki albashinki kije Inda kikeso sai kiyi aiki"shiru tayi aranta tanajin dad'in zai tafi Abuja ta sarara tasha iska"gaba d'aya fuskarta tak'i b'oye farin cikin zai tafi"dukda taji zafin kalamansa" amma tafiyarsa yasaka bata damuba"saima k'arasowa tayi ta zauna tana fad'in da k'arfe nawa zaka tafi?"kuma zan cigaba da zuwa ne??"kingama murnan mugu zai tafi ki huta??da sauri noor ta d'ago kanta suka had'a ido tana mamakin taya yagane"harara ya zabga mata"ta turo baki ta d'auke kanta"ki saurari abinda zan gaya miki da kyau dan mai mahinmanci ne"anjima da k'arfe 12 zan tafi gida kuma dake zanje"zaki dinga d'ebema mamy nah kewa"karki bari na bincika acemun kinyi rashin ji ko wani abu ba daidai ba"ma'aika tana zasu cigaba da aikinsa bisa k'ark'ashin PA d'ina"ke kuma zaki dinga zuwa gidan mamy kullum da safe zuwa 2 ko 4 pm ki koma gida shine aikinki....amma yaya sadeeq idan ban aminceba fa?"hmm! yama zama dole ki amince tunda har na zauna na b'ata time nawa na miki wannan bayanin"ba kuma neman yaddarki nakeyiba umarni ne na baki"kamar tayi musu tayi dai shiru"sbd itama baza taso ta zauna gida sbd matsalar gidan"fatanta Allah yasa maman nasa nada kirki"in kuwa taga babu alamar mutunci wlh zata dena zuwa"ki tashi ki kamun coffee"batace komaiba ta tashi ta nufi Inda komai yake tafara k'ok'arin had'a masa"saidai tarasa meyasa takejin fad'uwar gaba?"kuma jikinta na bata kallonta yakeyi"amma data d'ago kanta sai taga yana danna laptop"ahaka nura yashigo office d'in"noor tayi saurin cewa"yaya nura ina kwana?"lafiya qlau ranki yadad'e"harara sadeeq yasakar masa yana tab'e baki"nura yyi murmushi yaja kujera ya zauna"noor tazo ta ajiye cup d'in yanata turiri"aka maka coffee ne yaya nura?"tafad'a tana satar kallon sadeeq"aikuwa ya d'ago kansa ya aiko mata da wata uwar harara bbu shiri ta fita tanajin nura na fad'in ya k'oshi...nura yajima acikin office d'in kafin yafito yana dariya sbd yakai sadeeq mak'ura da tsokana"shi kuwa nura cikin farin ciki yake sbd k'aruwar daya samu"matarsa na d'auke da juna biyu"sallama nura yayiwa noor yatafi"ita kuma tana anan bacci yafara d'aukarta sama sama"ringing d'in baby nokia nata yatayar da ita"tana dubawa taga bak'uwar number ce"anutse ta d'aga amma ank'i mgn"kawai taja tsaki ta kashe....wajen k'arfe 12 :5 pm sadeeq yafito dg cikin office d'in yarufe da key"fuskarsa ad'aure"noor data lura da yanayinsa sai tak'i tankasa"kawai ta tashi ta bishi suka nufi parking lot"driver sit yabud'e yashiga"hakan yasa noor itama ta bud'e gefen me zaman banza tashiga ta zauna"cikin nutsuwa yabama motar wuta kafin cike da izzah yace"ke y'ar kalan dangi " duk namijin dana koma jin kin kira da wani yaya wlh zan baki mamaki"amma kasan dai abokinkane be dace na fad'i sunansa atsaye ba ko?"kuma kai ai yaya sadeeq nake kiranka"kuma nasan banida wata alak'a dakai ta jini"shi mai yasa bakace nayi kalan dangi ba??"bansaniba"Allah yabaka hak'uri "ai daka dawo zaka sallameni kamar yadda ka fad'a"dg haka bata koma mgn ba"shima yayi shiru har suka iso gidan mamy....noor in bacin bataso yarainata datayi k'auyanci"sbd yadda gidan yamata kyau aljannar duniya"atare suka fito dg cikin mota"gabanta nata fad'uwa"ta tsaya bayansa"ya juyo suka had'a ido"sunkuyadda kanta ak'asa tayi"kinga banason gulma" muje mana"yafad'a yanayin gaba ta bishi abaya k'irjinta na bugawa.....โœ๏ธ


wannan book d'in nakudine
Normal grp 300
Vip grp 1000
Special people 2k wato 3pages in a day


zaku biya kud'in ku ta wannan acc number๐Ÿ‘‰2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina 08100084251
300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne


banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kiraโŒ


Y'an nijar kutuntub'i wannan n๐Ÿ‘‰ +227 88 01 90 50
Normal grp 500f
Vip grp 1000f
Special people 2000f


dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ




๐ŸŒน๐Ÿ’”SALON SO ๐ŸŒน๐Ÿ’“

(sabon salo)




๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ




It's rometic love story๐Ÿ’˜โคโ€๐Ÿ”ฅ




Story & written by mommyn fareesa

last free page๐Ÿ™Œ


Dedicate to all my y'an amanata๐Ÿ˜ป๐Ÿ˜ป


Free page 19&20


...........Cikin takunsa na izzah da k'asaita ya murd'a k'ofar parlourn yashiga da sallama"noor k'irjinta na bugawa itama ta shigo da sallama kanta ak'asa"mamy ta amsa tana tsareta da ido"itama tana jin fad'uwar gaba"saidai aranta masha Allah take fad'i"sbd baiwar kyau data gani atare da noor...yayinda sadeeq ya zauna gefen mamy yana wani turo baki yana fad'in mamy yunwa fa yaronki yakeji"noor kuwa tayi mamakin ganin yayi haka"fuskarta da d'an murmushi ta russina har k'asa tace"mamy ina kwana?"sosai sadeeq ke kallonta aransa yanajin dad'in yadda ta girmama mahaifiyar sa"yayinda mamy ta amsa fuskarta cike da fara'a tana yaba tarbiyyar yarinyar aranta"bata gama mamaki ba saida taga noor ta zauna k'asa kan carpet"ah ah y'ata tashi ki zauna kan kujera mana kinji?"Allah mamy nanma yayi"sadeeq ya wani b'ata fuska yana fad'in mamy nifa yunwa nakeji"ke kuma dallah ki zauna kan kujera kinata wani kallon mutane sbd gulma"noor batayi mgn ba tana murmushi har fararen jerarrun hak'oran ta suka bayyana"harara mamy ta aiko masa da ita tana fad'in noor kiyi masa dariya gashinan k'ato dashi yana shagwab'a....dg haka mamy ta wuce dining area"noor kuwa k'asa tayi da kanta tana dariya"maimakon sadeeq yaji haushinta aransa"ah ah sai yaji kamarma karta dena dariyar"saidai a fili ya d'aure fuska yana fad'in yaushe nafara wasa dake?"sbd kinga mamy ko?nifa yaya sadeeq bada kai nakeba"tafad'a tana kallon k'aton pic nasa dake parlourn wanda yazana kansa da kansa"banza yamata yana danna waya"ahaka katuwar magensa ta sakko down stairs aguje.....noor ta fasa k'ara tana mik'ewa tsaye atsorace"sadeeq yaja tsaki yana tab'e baki yace"dallah malama ki nutsu ko kuwa wlh na wurgo miki ita ajiki"yafad'a time d'in da magen ke hayewa jikinsa...wlh da gaske tsoronta nakeji dan Allah ka fidda ita ! ta fad'a tana mik'ewa tsaye"yadaka mata tsawa yana fad'in karki fita nace ko? sadeeq! mamy ta kirashi fuska ad'aure be koma mgn ba"ta dubi noor tana fad'in zonan y'ata kinji?"bazata miki komai ba"kisaki jikinki"kizo muje ciki ki barsa da kayarsa yayita jigila"sosai noor taji k'aunar mamy aranta"ta lura tanada kirki batada wulak'anci irin na wasu dg cikin masu dashi"babu musu ta nufi mamy dake nufar hanyar bed room d'in ta"kamar ance noor ta juya ta kalli sadeeq"aikuwa suka had'a ido ashe ita yake kallo"harara noor ta aiko masa da ita"sannan ta masa gwalo ta shige bed room d'in mamy tana dariya"sadeeq da kallo kawai yake binta"yama kasa ganin laifinta"asalima saiya jingina da jikinsa da kujera ya lumshe idanuwansa yana shafa gashin jikin magen....yakai kusan 5 minit ahaka kafin yajanye magen dg jikinsa yanufi dining area yafara break fast nasa"bayan yagama ya wuce part nasa sbd yayi shirin zuwa sallar juma'a"dg can bazai dawoba zai wuce Abuja.....yana wanka zuciyarsa na bujuro masa da tunanin noor"yana hango time d'in datake masa gwalo tana dariya"hmm !wlh zaki sani yarinya"yafad'a yana jan kwafa"sai kuma yaja tsaki daya tuna a toilet yake...bayan yafito ya shirya cikin shadda giznah kalar sararin samaniya"an mata aikin hannu da dark blue d'in zare"komai dark blue yasaka yama jikinsa wanka da turare"yayi kyau har yagaji dan har yafi d'azun yin kyau"sai sannan ya lura da troley nasa babba da mamy ta shirya masa kayansa aciki"fitowa dashi yayi "sannan yaje ya d'akko wasu k'arafa dayake exercise dasu, suma ya fiddo su ya ajiye a main parlour"laure nata goge goge"ta gaidashi ya amsa yana kowama upstairs d'in"haka kawai yaji yana son idan yadawo yaga yaya noor ta zauna da mamy?"hakan yasa yasaita CTV camera"dama tuni anyi wearing mamy batama san da itaba agidan"bayan yagama abinda yadace yarufe ko in na part nasa sannan ya sakko down stairs d'in"time d'in 1:30 pm"bed room d'in mamy yanufa.....kawai yasami noor zaune kan sofa" mamy na zaune k'asa kan carpet"noor tana yiwa mamy kitso suna fira kamar y'a da uwa"har noor d'in na murmushi"saidai tana ganinsa tayi shiru tak'i yadda ta kallesa"mamy ce ta amsa sallamar sa tana fad'in harka fito sadeeq?"yana daga tsaye fuskarsa ad'aure yanason su had'a Ido da noor tak'i yarda ya amsa da Eh mamy"sai kallon noor yakeyi"kasancewar da hijab ko mayafi yasaba ganinta"amma yanzun ta cire hijab d'in"ta d'aura d'an kwalin rigar material dake jikinta"saurin sakewa mamy kanta tayi ta mik'e tsaye"ina zakije ne noor?"cewar mamy"kanta ak'asa tace"zan jira a parlour kuyi sallama da yaya sadeeq ne"mamy na murmushi tace" to shikenan"noor ta fita"sadeeq ya zauna kan sofa yana wani cin magani yace"wai mamy dg zuwan yarinyar nan kin wani sake da ita haka"sannan gaba d'aya baki ta tawa ta tata kawai kikeyi....mamy na murmushi tace"idan na fahimceka kana kishi da y'ata noor ko sadeeq?"shiru yayi yak'i mgn"kasan Allah sbd wannan halin naka zan b'ata maka rai"yarinya na girmamaka kana mata tsawa"dama haka kake mata a office d'in?"bafa haka bane mamy"to ayadda na fahimta tanada kirki da tarbiyya"sanin kankane idan hafsat ko zahida ka shigo kasamu bbu wacce zatayi hankalin tashi tabamu waje muyi mgn"kuma duk sun girmeta"amma gashi ita mai k'ananun shekaru tafisu hankali"to wlh ka kiyayeni dayiwa y'ar mutane tsawa"tanada saurin sabo"muna fira yanzun nace ta iya kitso tamun ko yaya kaina yafi wata bbu kitso"shine tace mun tanadai koyo ne"saina ce tamun"sannan yaka mata kasanarwa iyayenta anan zata dinga zuwa kullum harka dawo"nifa mamy bansan kowa nata ba"kana nufin tana aiki a k'ark'ashinka bakasan komai akantaba?"eh mamy amma idan nadawo zan bincika"shikenan ai"Allah yatsare hanya yadawo dakai lafiya"yabada sa'ar abinda aka tafi yi"ka rik'e mutuncinka sadeeq nasan tarbiyyar dana baka nida mahaifinka(kasancewar indai zaiyi tafiya ta kwana saita masa wannan gargad'in"sbd gudun shaid'an dan ta yarda da tarbiyyar yaronta) kansa ak'asa yace"insha Allah mamy zan kiyaye"nasan zanyi kewarki sosai"dana sauka zan kiraki mamy nah"to Allah ya yadda sadeeq"noor na parlour kaje kuyi sallama ko?"mamy d'azun fa sbd ta ganki dariya da gwalo ta dinga mun"sbd haka ni bbu wani sallaman dazan mata bayan ta rainani....tunda yake mgn mamy ke kallonsa tana murmushi"aranta tana fatan Allah yasaka soyayya tsakanin noor da sadeeq"dan dama can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login