Showing 90001 words to 91674 words out of 91674 words
Chapter 31 - SALON SO SABON SALO COMPLETE Book by Momyn Fareesa.txt
k'arasowa taff idanuwanta k'wallah"ayya my princess nima yaka mata nayi haka"kinga anaso arabamu ko?"ni kuma abinda bazan lamun taba kenan wlh"zo kiji tawan"yafad'a yana mik'a mata hannunsa"babu musu ta iso ta fad'o ajikinsa"ya rungumeta yana shafar jikinta da tambayarta bbu Inda ke mata ciwo? ta sanar masa bbu kafin tace"wlh yaya sadeeq ban tab'a zaton haka akeshan wahalaba wajen haihuwa"to ai my noor ananma ana ganin me sauk'i ke kikayi"sbd mamy dana fad'a mata kin haihu k'in yarda tayi Saida na rantse mata"to nidai gsky bazan koma haihuwaba tunda dai yara 2 ne ko?"lallaima yarinya to saura 10 ki gama sbd yara 12 nakeso ki haifamun"kika san koma kina gama wanka nakoma yimiki wani cikin?"yafad'a yana sakin dariyar tsokana"noor ta turashi tana kukan shagwab'a"yadinga yimata dariya"ta sauka dg jikinsa tafara d'akko baby boy d'in"dafa macen zaki fara bamawa my noor sbd itace k'arama"nidai shizan fara bamawa sbd yana kama dakai"Allah sarki noory nah"nima nafison macen sbd dake take kama"kuma bata da sunan daya wuce Amina (zamu yimata alkunya da meemee)namijin kuma haruna zamu masa alkunya da (affan)Allah yasa su amsa yaya sadeeq"ina alfahari dakai Allah yabarmu tare"Ameen yah Allah matata uwar y'ay'a nah"yafad'a cikin tsantsar farin ciki"tana murmushi yataimaka mata ta zaro maman jajir dasu sun ciko"sadeeq yatsaresu da ido yanata kallo"noor tayi bissimilah tafara bama yaron maman"tanata rintse ido sbd zafi"sadeeq nata yimata sannu"bayan tagama bama namijin ya amshesa tafara shayar da macen"ahaka su mamy suka dawo"sunata kallon sadeeq da noor cike da burgewa"mamy na k'wallar farin ciki tace"Allah na godemaka daka nunamun wannan rana naga yaran sadeeq aduniya"in sha Allah duka duk zaki ganin mamy nah"ko yanzun my noor tace"sunanki za'a sama macen ai"kai Alhmdllh noor naji dad'i Allah yayi muku albarka yabarku tare"insha Allah ke kad'aice matar sadeeq har aljanna"noor tayi dariya cike da kunya tana ansama....kwanan noor ukku da haihuwa suka tattara komai nasu suka dawo gida nigeria ana basu kulawa ta musammun itada yaran"kuma a part d'in su suka koma"sbd sadeeq yakafe bbu me rabashi da matarsa"itama noor azahiri ta nuna bata son rabuwa da mijinta"hakan yasa mamy tace a barsu"goggo saude na gidan sai anyi suna zata koma gida"ga me raino da sakq ruwan wanka duk sadeeq yadaukarwa noor"sosai suke samun kulawa itada yaran"sai gashi kafin Ayi suna noor tayi dumur dumur da ita"tayi haske gwanin sha'awa"ranar da aka kawo kayan barka aranar noor har kukan farin ciki tayi sbd yadda taga sadeeq yakashe mata dukiya itada yaranta"akwati 12 yamata, yaran kowa akwati 12 macen harda gwal"abin saidai ace masha Allah"ranar suna yara sukaci sunansu ana musu kara da meemee da affan"an sha buduri da shagali iri iri bbu kama hannun yaro"y'an jarida sunyi fira da sadeeq yanuna musu irin tsantsar farin cikin dayake aciki"nura da khairat sunsha hidima sosai"yyinda jummai sune k'irjin suna itama tana nan tayi nauyi"zahida kuma laulayi takeyi"duk abinda ke wakana idan tagani sai taji inama itace tasami wannan damar"hafsat ma tayi aure duk dasu akayi hidimar komai ta haihuwar noor"wanda noor na lura dasu jikinsu yayi sanyi"saidai kawai tayi murmushi domin tasan komai daular da mutum yake aciki sai yasha wahala yake samun ta"tasan taci wahalar rayuwa! taga jarabawa, dg k'arshe Allah yayaye mata yabata miji na k'warai"wanda shi kansa sadeeq d'in shima yasha wahalar rayuwa bayan mutuwar mahaifinsa dg k'arshe Allah yayaye musu"ita rayuwa duk abinda kayi hak'uri dashi zai zama tarihi da yardar Allah awata rana.......washe garin suna dg noor har yaran duk basu tashi da wuriba sbd gajiya"sai wajen 9am sukayi wanka suka shirya"masu raino suka goyasu"noor ta gyara bed room d'in ta"ta fito tana kwashe kayan break fast na sadeeq sbd taje ta kai masa"komai acikin tray ta zuba ta d'auka ta nufi parlourn sa"ajiyewa tayi asaman center table"ta tura k'ofar bed room d'in"sadeeq na kwance rigingine dg shi sai guntun boxer yanata bacci"da alama dayayi sallar asuba yakoma"ahhhhhhh yaya sadeeq munma rigaka tashi"tafad'a tana haurowa saman bed d'in ta haye ajikinsa tana jan karan hancinsa"yabud'e idanuwansa dasukayi jaa sbd bacci"wani killer smiling yasakar mata"tana shafa kansa tace"tashi muje kayi brush yaya sadeeq sai kayi break fast ko?"wai haka time yaja my summy?"yafad'a yana kallon agogon dake manne jikin bango"eh muma mun makara ai"hakane to yanzun an sallami bak'i da yara sai azo asallami big baby"wato daddyn twins ko?"yafad'a yana matseta ajikinsa"ta kwantar da kanta akirjinsa tana murmushi tace"yanzunma gudowa nayi na kamaka break fast nagaisheka yaya sadeeq"banaso anemeni"my noor romance kawai zamuyi ba wani abu ba"kusan 10days kenan rabona dake kin sani kuma ai yaka mata ki tausayamun ko?"yafad'a cikin kwantar da murya yana lalubarta"ta d'ago kanta da nufin tayi mgn yahad'e bakinsu awaje d'aya yana bata hot kiss"noor ta biye masa bbu wani d'ar....kimanin mintina 45 sadeeq na yamutsarta yak'i ya barta"yana ganin kiran mamy yashare yana hidimarsa"saida yasamu gamsuwa sannan noor ta mayar da kayanta shi kuma yashige bath room"da nufin idan yafito yayi break fast d'in"noor na fitowa dg bed room d'in sadeeq taji motsin za'a bud'e k'ofa da sauri takama kakkab'e kujeru"mamy ta turo k'ofar ta shigo fuskarta ad'aure"da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da mamy"dama kina nan anata nemanki?"ayya mamy ban jimaba anan"break fast naka masa bema nan"shine na gyara masa bed room yanzun ina gyara parlour"naga an kwana biyu ba'a gyara ba"ajiyar zuciya mamy ta saki tana fad'in ki barshi zuwa anjima kya gara noor, kije ki basu mama ki kwanta ki huta"ko lunch da break fast karki komayi zan dinga kamuku har kuyi 40 "kanta ak'asa ta amsa dato"aranta tana yiwa Allah godiya daya bata mami amatsayin suruka"atare suka fita itada mamy ,noor na dariyar k'aryar data shirgawa mamy"sai bayan tagama shayar da yaran ta hau online suka fara chats da sadeeq dake yin break fast"take sanar masa yadda akayi"sunata dariya da k'aryar da noor ta shirgama mamy.....
*Bayan shekara 5*
Rayuwa ta lulama sadeeq da noor"wata ran Ayi farin ciki wata ran akasin hakan"baffa dahiru shekaransa guda kenan da fitowa dg gidan yari"yayi nadama sosai musammun "da yaji mutuwar hamisu"yana kuka yarok'i gafaran noor"wacce saida sadeeq ya amince sannan ta yafe masa"kuma yak'i taimakama Abba dahiru da komai sbd yamasa wata iriyar tsana"noor nason ta taimaka masa da kanta sbd tana kasuwancinta"amma tsoron sadeeq ya hana"super market sadeeq yabud'e mata"dg k'arshe dai ta rarrashi sadeeq yabari tabama Abba dahiru jarin 200k sbd be siyar da komai gidan inna yake cin abinci"dukda innar ma bbu lafiya haka dai take"sosai yaji dad'in kud'in yafara siyar da cefane"yayinda matarsa saratu da sauk'i tama dawo gida suna tare"saidai duk ranar data tuna mutuwar halima tofa aranar zata yini sabbatu"saidai Abba dahiru yayi shiru yana kallon ta yana tuna rayuwa"acikin haka innah Allah yayi mata rasuwa" wanda noor taji mutuwar sosai" tasha kuka kamar babu gobe"dan inna itace komai nata adangin ubanta"ita kanta mariya tazo gaisuwa da yaranta biyu duk maza"Abba dahiru daya ganta yaraina kansa" yasaka noor ta masa mgn da ummanta"bayan tazo yana kuka yanemi gafararta"wanda tace tuni ta yafe masa"saidai ta gaya masa maganganu masu ciwo da zafi.....ayanzun haka dai noor yara 4 take dasu"haihuwa 3 yara hud'u ,ga kuma ciki na hud'u ajikinta harma yafara tsufa.......
Ayau yakama monday"anutse sadeeq marafa yayi parking agaban get d'in wata private hospital"kasancewar indai shida noor zasu fita shine ke driving ba driver ba"twins na skul"Ahmed da mohd na wajen mamy"noor tayi shar da ita an zama manyan mata y'ar kwalisa"sadeeq na murmushi yace""gsky za'a bincika awajen scanning yara nawane zaki haifamun?"fatana ace triple zaki haifamun my noor"haba yaya sadeeq ka tausayamun ai"in bacin yaran nan gaba d'aya suna wajen mamy ai wlh da bazanyi wannan jikin ba"yayi murmushi yana fad'in bbu damuwa saina kawo amary...be samu damar karasa zancen saba noor ta murd'e masa red lips nasa"yayi murmushi yana kallon ta"fuskar ta ad'aure tace"auranmu na zobe ne bbu kishiya"zaka koma zancen yin Amarya?"ta fad'a tana murd'e masa kunne"tuba nakeyi mrs sadeeq marafa"amma meyasa shi nura yak'ara aure last 3 month??"ni kuwa taya zan game yaya sadeeq?"kaine yaka mata ayima wannan tambayar sbd kana amininsa"shiyasa har yanzun bana sakar masa fuska naji zafin kishiya dayayima khairat wlh"okay bara na kirashi nasanar masa"ta gallah masa harara"yaja hancinta yana fad'in saina tuna ranar dakika watsamun sob'o ajiki my summy....dan Allah adena zancen yaya sadeeq kunyama zanji"ni kaina bansan meyasa nakamayi maka dariya ba alokacin?"SONE( book d'ina idan Kika bari ya wuceki kinyi missing) yasaka kikamun dariya"yafad'a yana kama hannunta suka fito dg cikin motar"yayi lock nata"suna k'ok'arin shiga cikin get d'in asibitin"Alh mansur yafito dg ciki"yayi bak'i yayi rama"kamar bashiba"sadeeq ya d'auke kansa yana k'ara godema Allah daya yishi mutum na k'warai"dan yasan tabbas mugun halin Alh mansur yakaisa ga haka"sbd tun kwanakin baya dayaso yabashi rancen kud'i ya hanashi"yasami labarin yafita waje an zuk'e masa jini"anxuba masa wsni"tunda yadawo gida nigeria tattalin arzik'in sa yakarayin k'asa"yanzun haka kasuwanci yakeyi bbu aikin compony"matansa duk sun gudu sun barsa"ga ciwon kanjamau nasa yanata tashi"ko yanxun ganin likita yazoyi....da sauri Alh mansur yace"dan Allah sadeeq ka tsaya ka saurareni"atare noor da sadeeq suka kallesa"ita noor batama ganesaba"amma shi sarai yasan noor ce yarinyar dayaso yaraba da sadeeq beyi nassaraba"sadeeq yadubesa yana fad'in bani acc detail naka"jiki na kirma yashiga bashi"bayan yarubuta atake yamasa transfer d'in million guda"Alh mansur na godiya yana washe baki yana tuna irin sharrin daya yimasa arayuwa.... "sadeeq da noor suka wuce ciki.....ni kuwa nace Allah karabamu da ciwon hassada sbd babban ciwo ce......!
Tamat bi hamdilillahi🙏🏻🙏🏻 Allah nagode maka daka bani damar fara rubuta wannan book dg farko har k'arshe lafiya"kuskuran danayi aciki yah Allah kayafemun🤲
Tsira da amincin Allah sutabbata ga shugabanmu Annabi S A W"
Ina mik'a d'inbun godiyata agareku mutanena Allah yabar tare sai mun had'e asabon book d'ina nan bada jumawa ba.....
wannan book d'in na kud'ine! duk wacce takaranta bata biyaba tasan meta karanta" bazan tab'a yafema wanda yacutar daniba har duniya ta tashi.....
Na sadaukar da wannan littafin ga yarana fareesa&fatima da Ana's Allah ya albarkaci rayuwarku data sauran yaran musulmi baki d'aya🤲
MEENA VIP GROUP HAUSA NOVEL DOCUMENT for more information contact on
WhatsApp ONLY
+234 7014979567