Showing 6001 words to 9000 words out of 91674 words

Chapter 3 - SALON SO SABON SALO COMPLETE Book by Momyn Fareesa.txt

10 Jan 2025

9070

mgn da tsokana"k'awarta guda data shak'u da ita sosai itace jummai anan mak'otansu take"tunda ta fara girma burunta shine ta zama nursing"kuma iyayenta ma haka"saidai gaba d'aya maza sukayiwa noor caa"ita kuma bata kulasu dukda tanada karancin shekaru alokacin"har takai 16yrs anan kyawunta yak'ara bayyana"time d'in tana SS3"Abba dahiru yafara bama Abbanta shawara karya barta tayi karatu yasamu wani me kud'i ya aura mata sbd tanada kyau"Abbanta yakama fad'a dan be goyi bayan saba"ahaka noor tafara exams harta gama ta kammala SSCE nata"ana zaman jiran sakamako saita cigaba"dan yarinyar gifted ce tanada k'ok'ari sosai"wata ranar Alhamis da marece aka kawo gawar mahaifinta dg kasuwa kawai anga yafad'i"fad'in tashin hankalin da suka shiga itada umma b'ata bakine"bayan Abba yayi 40 days Abba dahiru yanuna son ya auri mariya sbd wai zata rik'e noor "in kuma bazata aminceba tofa zai amshi noor dg wajenta"badan tasoba ta amince da auren"amma ta zauna agidanta"kusan shekara guda da auren"wanda umma tayi dana sanin auren"baya basu abinci itace ke ciyar dasu a y'ar sana'arta"gashi tanaso noor ta koma skul"amma bbu hali tana zaune dai"ita kanta noor tasan Abba dahiru hak'uri kawai mahaifiyarta keyi dashi dan batajin dad'in zama dashi"gashi Allah yamasa son abin duniya da hange"da an aiko ana sallama da noor zaije yaga talakane ko mai kud'i"idan talakane yakoresa in mai kud'ine yabarsa "hakan na yiwa noor ciwo da umma"gaba d'aya taji tama tsani soyayya bata kula kowa"duk kuwa tarin masoyanta"dan da wuya ta fita wani bai tsayar da itaba"tun bayan zuwan mariya bauchi bata koma zuwa kasarsu ba hakama wani nata be tab'a zuwa ba....wata ran da marece noor zata tafi islamiya umma ta sanar mata idan ta dawo ta jirata agidansu jummai zasuje wata anguwa itada Abba"da wannan suka rabu"noor na dawowa dg islamiya tasami gidan bud'e"tana shiga tasami Abba zaune yana matsar k'wallah yabata takarda"yana fad'in gashi inji mariya tace"abaki ita ta tafi agadaz"bazata iya rayuwar wahala da talauciba"gaban noor na fad'uwa tace"Abba shine ta tafi ta barni? bayan bansan kowa nata dake agadaz ba" tab'e baki yayi yace"ki manta da ita mana tunda itama ta manta dake"nima na saketa ai"kuka noor ta fashe bata karanta takardar ba"tana kallonsa tace"gobe nima zanje agadaz d'in"kije gidan ubanwa?"k'asar da kud'in mota dubu 200 ne"kina yarinya dake kije wata uwa duniya kinsan hannun dazaki fad'a ne?"to dg nan gida zan wuce dake ki zauna wajen saratu"tunda gasu halimatu dasu hamisu saiki zauna da y'an uwanki ko?"dan dangin uba sune d'a...wani kukan noor ta koma fashewa dashi"yaja tsaki yace"kiyi kukan jini tunda tabi uwa duniya ta manta dake ai be kamata kituna taba"sai kuma noor tayi shiru tana ganin ai da gske ne"saidai kuma noor tayi mamaki meyasa umma bata d'auki kayantaba da zata tafi?"saidai kawai tayi shiru adaren ranar Abba dahiru yatafi da ita gidansa"yanada mata 1 da yara 3"hamisu , halimatu da Abbas......sosai inna saratu ke gallazawa noor sbd tana kishin uwarta"kuma tana goranta mata uwarta ta gujeta"sannan ba'a bata abinci wadatacce agidan"yayinda halimatu zasuyi sa'anin juna amma noor bata d'aukar raini agunta"danko dambe sukeyi noor ke bigeta"hamisu kuwa tantirine na gidan gaba"yana shaye shaye da y'an d'auke d'auke"duka shekarunsa 25"amma ya k'ware wajen b'ata y'ay'an jama'a"noor ma yana harinta Allah ne be bashi sa'a ba"ita kuma rashin kunya da tsiwa take masa koda yasakata aiki batayi"Abba kuwa maza yadinga turowa noor kuma y'an iska wad'anda badan Allah suke sontaba"ita kuma bata kulasu"ga rayuwa ta mata zafi"abinda ada tafi k'arfinsa yanzun yafi k'arfin ta"hakan yasa jummai k'awarta tabata shawara tasami sana'ar yi kota sami abinda zata rufawa kanta asiri"shine ta amince mahaifiyar jummai tasaka yayarta tasamarma noor aiki gidan Alh salis kaita"shine tafara aiki tana samun abinci da y'an kud'inta suma wani lokaci Abba ya amshe tasha kukanta"tunda tafara aiki gidan Al'ameen keson jan ra'ayinta su aikata sab'on Allah"kuma yasanar mata yana sonta da gske"kawai su huta dg baya saiya aureta"aranar noor tasha kuka ta kuma yadda duniya ta lalace"kullum addu'ar ta shine Allah yamata canjin alkhairi acikin wannan rayuwar datakeyi"sannan Allah yabata ikon zuwa k'asar agadaz ko taga mahaifiyarta da danginta......
Noor ba doguwa bace ba kuma gajera ba"batada kuma k'iba"amma sbd tanada manyan breath da hips ake mata kallon me jiki"tanada dogon gashi bak'i na buzaye"yayinda take da siririyar murya "inta gadama kuma ta juyata zuwa tsiwa" bata son raini haka yasa bata raina kowa kuma bata yadda araina taba"tanada dimple da wushirya atsakkiyar hakoran ta na k'asa"tanada d'an mitsitsin baki me lips brown"idanuwanta basu cika girma ba"amma tana yawan lumshesu"tsabar cikar da gashin girarta tayi harya kusa hadewa da y'ar uwarta"noor ta had'u sosai"saidai yanayin yadda ba hutu da nutsuwa da kwalliya takeyiba shike b'oye ainahin kyawunta"saika zauna ka nutsu kana kallonta zaka gane ita kyakykyawar gaske ce........


cigaban labarin.....


sallama noor tayi ta shiga cikin gidan babu kowa sai Abbas dake zaune kan kujera y'ar tsugunne yana cin tuwon dare"d'akinta da bbu ko k'ofa anan ta shiga ta cire hijab ta b'oye kud'inta"sannan ta fito ta wuce bayi tayi alwalah tazo tayi sallah"bayan ta idar ta fito tsakar gidan" ta duba kitchen amma bataga abincin taba alamar bbu kasonta kenan"tana k'ok'ari nufar d'akin ta Abba yashigo ya kalleta yace"ke ina kud'in nan sbd jiya akayi albashi ina lissafi"eh jiya akayi yau aka bamu" amma sunce mu dena zuwa sai sun nememu..... k'arya kike munafukar Allah"in ma baki nema ba damuwarkice"ki d'akko kud'i ki bani"nidai ba wata uwa zan dinga miki ba ta kaina nakeyi"tunda bak'in ciki ya hana ko maza ki kula kisami me kud'i ki aura ko nima na huta"amma Abba ina gidanmu da Abbana yabari?"na siyar na kashe kud'in ko akwai abinda zakiyi ne?"tana k'ok'arin mgn inna ta fito dg cikin d'akin ta tana fad'in"hmm! mlm wlh kana bani mamaki da yarinyar nan ke neman ta gagareka.....kuka noor ta fashe dashi aguje ta nufi d'akin ta"yabita acan ya amshe 10k d'in yayi gaba"noor kuwa bayan tayi shiru barin gidan tayi taje gidansu jummai takai ajiyar 40k d'in ta" sbd tanaso ta dinka y'an hijabai da kaya ko kala 3 ta siyi kayan shafa da takalmi"acanma taci abinci"mahaifiyar jummai na tausayin halin da yarinya k'arama ta tsintsi kanta aciki"duka yanzun 18yrs noor gareta amma dubi yadda rayuwa ta tafi da ita"anan umman jummai ke yiwa mai gidanta bayani bayan tafiyar noor d'in yace"insha Allah zai samar mata aiki ko a restaurant ko wasu ma'aikatu insha Allah bazata tozartaba.....


wajen k'arfe 9:30 pm sadeeq yashigo cikin gidan"bayan yasaka anrufe ko ina ya wuto main parlour anutse"kai tsaye dining area yanufa"yaja kujera ya zauna"sbd yasan yanzun dai mamy tayi bacci"coffee d'in ya had'a yafara sha yana chats a face book"nura yai masa mgn yamasa banza dan mugun haushin sa yakeji"yyinda fuskar noor takasa goguwa azuciyarsa"har haushi yaji dayaga message d'in nura domin abinda yafaru d'azun yafad'o masa arai"kashe wayar yayi yabar wajen cikin sand'a yanufi upstairs sbd yaje yayi wanka ya kwanta..... sadeeq idan ka gama gewaye gewayen kazo zamuyi mgn"yaji muryar mamy abayansa.......โœ๏ธ


Labarine daya tamkar da dubu mai saka zuciya nishad'i da tunanin yaya za'a kasance akowane page๐Ÿ˜ป acigaba da bi zak'in labarin na'a gaba....


wannan book d'in nakudine
Normal grp 300
Vip grp 1000
Special people 2k wato 3pages in a day


zaku biya kud'in ku ta wannan acc number๐Ÿ‘‰2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina 08100084251
300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne


banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kiraโŒ


Y'an nijar kutuntub'i wannan n๐Ÿ‘‰ +227 88 01 90 50
Normal grp 500f
Vip grp 1000f
Special people 2000f


dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ




๐ŸŒน๐Ÿ’”SALON SO ๐ŸŒน๐Ÿ’“

(sabon salo)




๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ




It's rometic love story๐Ÿ’˜โคโ€๐Ÿ”ฅ




Story & written by mommyn fareesa


Dedicate to raudah mohd sokoto๐Ÿฅฐina yinki over tawan๐Ÿ’“๐Ÿ’”


Free page 7&8


............Cak sadeeq yatsaya batare daya juyoba yana sosa k'eya alamar rashin gsky"mamy dai na b'oye dariyar ta tanemi gefen kujera ta zauna"shi kuma yanata wani cin magani da shagwab'e fuska yajuyo ya sakko down stairs d'in"mamy pls dare fa yayi bacci nakeji kibari saida safe mayi mgn tunda week end ne ko?"yafad'a cikin muryar shagwab'a kamar wani d'an yaro yana kallonta yayi tsaye"wlh sadeeq zan b'ata maka rai"shin sakarcin d'an fari ke damunka ko kuwa shagwab'ar autanci kakeji??"yanzun Inda kanada mata ai baza kayi wannan shirmen ba.....atake sadeeq ya had'e rai"bece komaiba dai yazo gefenta ya zauna"ina so na tambayeka,kuma tambayar k'arshe game da zahida"shin kana sonta ko baka sonta??"b'ata fuska yayi yana fad'in sau nawa zance bana sonta mamy?"indai zancen tane pls adena"sannan mutumin nan yaka mata mamy ki nutsu kiyi hangen nesa ki fahimci badan Allah yakeso ya aurekiba!sai dan sbd wata manufarsa"kuma ni najima da sanin manufar tasa"koda bashida manufa gsky banaso ki auri kowa?"d'an jim mamy tayi kafin tace"sannu ubana me bani umarni"toko jiya yaya mukhatar (yayanta)yamun zancen yaka mata nayi aure shekara 10 kenan da rasuwar mahaifinka"zancen Alh labaran ni kaina naji ban amince da auren saba"sbd haka zan sanar masa yyi hak'uri"ita kuma zahida Allah yabata wanda yafika"ba zanso na maka auren dole ba"nasan wannan halin naka na miskilanci kaje ka cutar da y'ar mutane kana samun zunubi gara ka auri wacce kakeso"ajiyar zuciya sadeeq yasaki yana d'an sassauta murya yace"hakane mamy komai ai yanada lokaci ko? aure dai zanyi karki damu"d'ago kanta tayi ta maka masa harara tace"wace yarinya ce jiya naji kace nura ya hanaka ka hukun tata?"mamy a office take amma na maida ita bakin aikinta ai"hmm kawai ta fad'a sbd bata yadda da abinda yafad'a ba"tasha alwashin kuma zata binciki nura taji"sadeeq bazan koma yimaka zancen ka fito da matar aureba saidai zan baka mamaki kawai....mamy pls ki fahaimceni mana"kinsan yaran ne bbu wata tarbiyya sai a hankali"yafad'a yana tab'e baki"murmushi tayi tace"oh yarama ba y'an mata ba?"Allah ya shirya mun kai sadeeq"dan Allah ka rage wannan zafin ran"inba hakaba k'ilan bbu wacce zata zauna dakai kana wannan d'aure fuskan haka"ko kuma in kaje tad'i ace tsoho ne tunda kazama tuzuru"duk yarinyar datace mun tsoho ai wlh saita sani mamy"hmm Allah ya tsare mun kai yabaka ta k'warai sadeeq"kaje ka kwanta amma kayi addu'a dan Allah"insha Allah zanyi mamy nah"tayi murmushi tanata kallon sa"aranta tana cewa mutum har mutum amma bbu iyali"tashi yyi ya haye up stars"k'ilan mace ta canzaka sadeeq"nafiso ka auri wacce kakeso take sonka"ta haka zaka samu farin ciki"bana so ka auri wacce kakeso bata sonka"ko wacce ke sonka kai baka sonta"Allah dai yyi maka zab'in alkhairi"ta fad'a tana mik'ewa tsaye tabar wajen......
Ahankali yatura k'ofar bed room nasa yashiga"yafad'a samqn bed d'in ya lumshe golden eyes nasa yanajin dad'in yarabu lafiya da mamy"nura yatuna da damuwarsa"yatab'e baki yace"k'ilan anwuce wajen"yana mamakin wasu mazan"dan yasan shidai ba haka yakeba"da wannan tunanin yatashi yafara rage kayan jikinsa yanufi bath room"yana wanka yana tuna noor yarinyar dako sunanta be saniba"idan yatuna yadda take masa mgn cike da tsiwa kuma nura ya hana ya d'auki mataki saiyaji kamar ya had'iyi zuciya"jiyakeyi inama ace yasan Inda take hmm! da wannan yanayin ya fito zuciyarsa acunkushe"yafi 30 minit yana shiryawa kafin ya kwanta dg shi sai guntun boxer ajikinsa"yyi addu'a ya rungume pillows"ahaka bacci yayi awon gaba dashi dan agajiye yake....


*7 days ago*
kimanin sati 1 kenan da haduwar noor da sadeeq" kuma haka yayi daidai da dena aikinta gdn Alh salis kaita"wanda in bacin kud'in nan data ta gayyara sosai"wanda babu laifi ta siyi duk abinda takeda buk'ata na amfani"akuma yau monday Abban jummai zai kaita Inda aka samar mata aiki"kasancewar ta san da zancen" tun jiya"yau ko kari batayiba tafara k'ok'arin shiryawa"mutanan gidan nadai kallonta bbu wanda yatankata ko tambayarta Inda zataje"danko tarbiyyar yaransu dasuka haifa basu kulawa da ita balle wata noor kuma"wacce yanzun burunta kota fara aikin ta tara kud'in zuwa agadaz ta gudu dg bauchi"kota huta da azabar datake sha wajen Abba dahiru da family nasa"shiryawa tayi cikin material me zanan bak'i da brown d'inkin bubu"tasaka plate shoes brown da hijab jalbab yadin d'an katsina"shima brown colour"fuskarta babu make up"powder da kwalli kawai ta shafa"amma ba k'aramin kyau noor tayiba"wanda atake inna saratu taji zafinta sbd tafi y'arta halima kyau da farin jinin samari"y'ar post ce a hannunta da sauran kud'inta aciki"tanata k'amshin turare me k'aramin kud'i"ta dubi inna saratu tace"zan tafi wajen aiki inna"damuwarki ba nawa ba"aikin share share da wanke wanken dazakije shine zaki d'auki gayu haka?"uffan noor batace ba"tayi ficewarta dg gidan"a k'ofar gidan tasami Abba da mai nafef"ta russinah ta gaishesa"babu b'ata lokaci suka shiga gdn baya"harga Allah Abba yanajin tausayin noor kuma shima talakane me rufin asiri"yaga gara kota wannan aikin yataimaka mata tasamu"ko tabar garin nan ta koma wajen dangin mamanta"dan zamanta a anan , dahiru zai iya wargaza rayuwar yarinyar"nasiha mai shiga jiki yamata game data rik'e mutuncin ta"ta tsaya iya matsayinta"sannan dg k'arshe yace"zamuje dake *marafa interprises*...... hakanan gabanta yafad'i"kina jina?dama wani abokina ne ke aiki acan"zamuje yanzun wajensa zai kaiki shashen da aka baki aiki"kiyi abinda yakaiki sumayya"k'arfe 2 yace ko 3 ake tashi"insha Allah Abba"ta fad'a gabanta nata fad'uwa tanajin wani irin mugun tsoro"ita kanta in bacin bbu hanyar da zata sami kud'i wlh da bazatayi irin wannan aikin ba"ta ayyana haka aranta"bayan sun iso Abba yakira mlm audu ta waya" bayan yafito suka gaisa yagabatar masa da noor"sannan ya musu sallama ya tafi"mlm audu yace"muje ciki yarinya"zamuje dake wajen ogan namu gaba d'aya"sbd ki bada sunanki da address naki da acc n naki ta Inda za'a dinga turo miki kud'in albashinki"sannan zamuje shashen masu goge Inda anan kike....dato ta amsa kirjinta nata bugawa bata san daliliba......


Anutse yabud'e yafito dg back sit"sanye yake da mint blue d'in shirt me long sleeves da cufflinks"se dark blue d'in jeans"yana sanye da takalmi sawu ciki bak'i da bak'in agogo na dimon"


wani sanyanyan"fitinan nan k'amshi me tsayawa arai da zuciya natashi ajikinsa"duk Inda ya gifta sai yabar k'amshin sa"
fuskarsa tamau babu annuri ,hakan ba k'aramin kyawu yak'ara ma doguwar kyakykyawar fuskarsa ba"yana rik'e da break case d'in sa" *sadeeq marafa* kenan da akema kirari da yaro da kud'i.....


Cikin izzah had'e da shan k'amshi yake tafiya" body guards nasa na take masa baya da wasu masu buk'atar ganinsa"gaba d'aya yayi hanyar office nasa....
Anutse ya danna wani bottom, k'ofar yyi scanning nasa "bayan antabbatar baya d'auke da makami"sannan wata k'ofar tasake bud'uwa"anan take mutanan cikin ginin suka bayyana"mata da maza kowa nata aiyikan gabansa....wajen tsit babu hayaniya"kai tsaye yanufi office nasa"dg bak'in k'ofar an rubuta *CEO office*
sosai office d'in yatsaru komai tsab dashi ga wadatattun kayan aiki"bayan ya zauna ya d'auki telephone da nufin yakira suleman (sakatarensa)kawai Alh mansur yashigo cikin office d'in"yana wani shan k'amshi babu ko sallama"sadeeq kuwa tsabar zafin kansa be kalli wanda yashigoba"yakuma sanarwa suleman kar yabar kowa yashigo masa office saida saninsa"shine yabar wannan mutumin yashigo"ajiye telephone d'in yayi yajawo laptop"yana saita tsarin CTV camera dake a company d'in" *mr sadeeq marafa* yaka mata ka girmama bak'onka ko?"sadeeq yad'auki kusan second 15 kafin cikin ko in kula yace"kaje kayi sallama sannan kadawo ka fad'i komai kake son fad'a....dariyar rainin hankali Alh mansur yasaki kafin yace"na wuce wannan matakin sadeeq"karka manta kai abokina ne bbu wata izzar da zaka mun"uffan sadeeq bece ba"Alh mansur na tsaye"ahaka nura yyi sallama yasha gayunsa cikin farar shadda yashigo office d'in"Alh mansur yatab'e baki be kalli nura ba yafice dg cikin office d'in"mlm miye had'ina dakai daza kazo kamun zaune?"cewar sadeeq batare daya kalli nura ba"hmm ! kaidai kasani marafa"naga kak'i dena fushi dani nace bara nazo mugaisa na wuce office"kasan abin mai iyali tanata rigima na fito"tsaki sadeeq yaja bece komaiba"nura na murmushi yace"bayan gaisuwa kuma nazo na maka godiya domin shwaranka tayi..... sadeeq yad'ago kansa da nufin yyi mgn suleiman ya shigo da sallama"aladafce yace"both ga mlm audu nan da wata budurwa na neman iso......kallon da sadeeq yamasa yasaka yasha jinin jikinsa"miye dalilin dayasa kabar mansur yashigo mun office?? yafad'a murya adake.....cikin daburcewa sulaiman yace" wlh both na masa mgn yajira"na masa iso amma yak'iya yana zagina yabar body guards nasa awaje yashigo"okay to bakin aikinka tunda kanajin tsoron wani akan aikinka"shi kuma mlm audu kace yashigo"yana fad'in hakan yamaida attention nasa a fuskar tv dake jikin bango" wacce yasaita CTV camera da ita.....atake fuskar noor data mlm audu ta bayyana da kuma isowar suleiman wajensu yana mgn da mlm audu......da k'arfi sadeeq yabuga table d'in gabansa yana mik'ewa tsaye.......โœ๏ธ


zazzafan sharhi guys ko aji shiru๐Ÿ˜Ž


wannan book d'in nakudine
Normal grp 300
Vip grp 1000
Special people 2k wato 3pages in a day


zaku biya kud'in ku ta wannan acc number๐Ÿ‘‰2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina 08100084251
300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne


banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kiraโŒ


Y'an nijar kutuntub'i wannan n๐Ÿ‘‰ +227 88 01 90 50
Normal grp 500f
Vip grp 1000f
Special people 2000f


dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ




๐ŸŒน๐Ÿ’”SALON SO ๐ŸŒน๐Ÿ’“

(sabon salo)




๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ




It's rometic love story๐Ÿ’˜โคโ€๐Ÿ”ฅ




Story & written by mommyn fareesa




Dedicate to zee h wada๐Ÿ˜ป๐Ÿ˜ปina yinki totally tawan acigaba da zazzafan sharhi๐Ÿ˜‚


free page 9&10


..........da sauri nura yadubesa yana fad'in lafiya dai marafa?"sadeeq beyi mgn ba yana kallon dai tv still"sai kuma yayi saurin zama kan kujera yana sakin wani irin mugun murmushi "yana fatan Allah yasa wannan yarinyar anan zatayi aiki"yyinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login