Showing 27001 words to 30000 words out of 57158 words
Chapter 10 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt
dai dai nan driver yayi horn
*Nasmy ce*π
Yar mutan arkilla love you allπ
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
ββΒ©(Z.R.A)ββ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’176/180β’*
Itakuwa fuskarshi tabida kallo tareda ayyanawa aranta baqaramin kyau murmushi yake yimishiba takafeshi da ido haka shima ya xubamata nashi suka sakewa juna wani sabon murmushin batareda sun saniba
Wata kyakkyawar budurwa ce madaidaiciya baxatafi sa,ar fateema ba tabude qofar motar dasaurinta cikeda xumudin ganin yayanta nanfa sajida tacikaro da ya fa,eex da fateema sunqurawa juna ido fuskokinsu daukeda murmushi mai wuyar fassarawa jinqarar budar motarne yadawo dasu daga wannan yanayin dasuka shiga fa,eex dai fuskewa yayi ya wayanceda wani kalar murmushin na musamman yace oyoyo my sajjj really miss you yafito daga motar tareda hogging sistershi wadda ta raja,a da kallon kyakkyawar yarinyar da ya fa,eex yaxo musu da ita, itakuwa fateema saitaji abin wani banbarakwai cikin sanyin jiki ta lalubo akwatinta tafito
Sajida taxare jikinta daga ja yayanta ta isa gun fateema da murnarta takamo hannunta sannudaxuwa sis ijamiki barka tareda jinjinawa kyawawan dabi,u da halayyarki wanda haryasa kikasami gurbin xama axuciyar dan,uwana jarumin qasata wanda yan,matan qasa da qasa ke daka wawa akansa a gaskiya sis kin........... fa,eex ne ya katseta tahanyar wurgamata da wata irin harara data tilastata yin shiru ba shiri dai dai nan ayarin members na familyn suka qaraso garesu
Wani babban mutum ne akan gaba wanda da kallo daya xaka iya tabbatarwa kanka cewa shararrene kuma hakshaqin attajiri mai fada aji a qasarnan alhaji ma,aruf affan kenan fitaccen more ministan ilmi na nigeria kuma sanannen dan kasuwa mai gaskiya da adalci adukkanin al,amiranshi
Yana gaba yaranshi yan mata guda biyu suna bayanshi fuskokinsu cikeda annuri kaidagani kasan suna cikin farin ciki dasauri yanufi mahaifin nashi danufin ya rungumeshi saidai sam baisami wannan damarba dan yan matan twins din dasukayi mishi rufff suduka biyun suka rungumeshi oh ya fa,eex munyi kewarka dayawa yai murmushi sannan yashafi kawunansu nima nayi kewarka my sisters fatandai nasameku lfy atare sukace lafy qlau ya barkada sauka yace yawwa
..
Ahankali yaraba jikinshi danasu ya isa gun dady dake gefe yana kallonsu cikeda sha,awa ta irin qaunar dasuke nunawa junansu, sukuwa suka wuce inda sukaga anty sajida tsaye da wata pretty acewar sajj, suka yanyameta suna yaba kyauda sa,arta tasamun ya fa,eex dansu atunaninsu budurwarshi ya kawo itakuwa fateema duksaita diririce takasa koda magana saidai murmushi kawai aranta kuma tana godiya ga allah dabai hadata da wanda xai cutar da ita ba, saitaji kunya na irin daukar datayi mishi a fari
dady yayimishi side hog yace barkada dawowa son inafatan kadawo lfy alhmdllh dad amma yabanga momyna ba? Dady yai murmushi tace tana fushi dakai acewarta bakiyi kewarmu ba tunda bayan ka kammala abinda xakayima motar haya kabiyo dankar kaxo da wuri wai dankaga ta damu dakaine dashida dadyn duka suka saka dariya dai dai nan su sajjj da yanbiyu safeenah da safeeyah suka qaraso wajansu saj tana riqeda hanun fateema safeenah kuwa akwatinta ta dauko
Sai alokacin idon dady yakai kan fateema cikeda mamaki yakalli fa,eex yace ah son baquwa mukayi? Kafin yayi magana saj tayi karaf eh wlh dady budurwar yaya ce yaxo mana da ita dady yaqara fadada murmushin shi yaqara tambayarshi akaro na biyu dagaske take kuwa ?
Fateema tadago da Saudi danjin irin amsardaxai bayar akanta shidinma saida yakalleta kafin yamaida kallonshi ga dady yace...........................................
*Nasmy ce*π
Yar mutan Arkilla love you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
ββΒ©(Z.R.A)ββ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’181/185β’*
No dad yar,uwa dai nasamo musu ku kuma ya' dady yakalleshi kallona rashin fahimta daneman qarin bayani amma fa eex saiya fuske tareda jan hannun dad din suka nufi hanyar daxata sadasu da wannan tamfatsetsen gidan su saj nabinsu abaya sai murna suke su adole yqyansu yayi budurwa abinda aka dade Ana jira
Ababban falon suka saketa sai faman xarya take takasa xaune takasa tsaye tanason ganin gworxon danta jarumin qasa babban yaronta fa,eex tayi kewarshi sosai wannan ne dalilin dayasa taji haushin rashin hawo jirgi dayayi saiya biyo mota aganinta kawai dan kar yaxo da wurine
Suna shiga falon sukayi arbada ita farar mace kamila mai yawan murmushi saidai tana ganin shigowar tasu saita juya danufin barin falon xuwa dakinta na sama dady yakalli fa,eex da murmushi shikuwa cire dasauri yasha gaban momynshi tareda tsugunawa a gabanta yakama kunnuwanshi ya marairaice fuska kaman xaiyi kuka pls mom inkikayi fushi dani mutuwa xanyi dan Allah kiyi haquri wlh ban aikata hakan dan kiji haushinaba wannan ikone na ubangiji kinganta yanuna fateema rabon kusameta shiyasaka naji nafi sha,awar hawa motar akan jirgi acan muka hadu da ita na lura tana buqatar taimako rarrashi irin naki kafin musan asalin wacce ce ita, kinji dalilin mom pls karkiyi fushi dani yaqarashe kaganar hade da langwabar da kai gefe kaman mai shirin yin kuka
Momy datake kallon inda wadda ya nuna mata yake saitajuyo gareshi fuskarta daukeda murmushi akasin yanda suka sameta baxan iya fushi dakaiba son kawaidai nayi kewarka dayawa and I know you do as I do ko tafada lokacinda take dagoshi daga tsugunon dayayi sukayi hogging din juna dadi fall a xuciyar fa,eex haka ma mom kafin tajanyeshi ta isa ga yan matan takamo hannun fateema da kanta yake qasa tanawasa da yan yatsunta tadago da dara daran idaninta suka kalli juna itada mom momy tasake matamurmushi haka kawai taji yarinyar ta kwanta aranta haka fateen ma sosai dattijuwar ta burgeta kai dukkansuma familyn yayimata saitaji inama itace take tareda iyayenta cikin farin ciki irin wannan? Allah sarki saita fara tambayar kanta koya suke ayanxu? Ko lbrn batanta da sakin da yaya fahad yayi mata yariskesu yanxu? Wayyo nawanda tafi tausayawa kaman goggo tasan irin sonda take mata saikawai taji idonta sun fara sirnano da hawaye mom ta qura mata ido kaitsayetagano yarinyar tana cikin damuwa tajata xuwa jikinta cikin dabaru irin nasu namanya tasharewa fateema hawayen sannan tadagota barkada xuwa ya'ta kuxo muxauna tariqe hannunta gefe tariqo na fa,eex kaha tanufi dining dasu inda dady yake xaune yanmatansu suka rufa musu baya
Saida momy taxaunar dasu akan kujeru dasuke passing juna kafin itama taxauna kusada dady haka yan biyu ma sajida ce tayi serving dinsu taxuxxubawa kowa abincin sukafara ci amma bamda fateema wadda ayanxu gidansu da iyayenta kadai take tunani momy ce tadafa kafadarta kici abinci kinji ya'ta jitayi baxata iya yimata musuba dan itama matsayin uwa takejinta aganin farko, batareda tayi maganaba tadauki spon tafara cin lafiyayyan abincin wanda qamshi shi kadai ya isa ya qosarda mutum
Harsuka kammala ba wanda yakomayin magana saida suka gamane sannan taga mom dakanta tamiqe takama hannun danta tanacewa son muje kayi wanka kasamu ka kwanta ba musukuwa ya miqe sannan takalli sajida tace saj kitafida yar uwartaku can dakinki itama tayi wanka tace to tamiqe takama hannun fateema suka tafi dagudu yanbiyu suka bisu
Dady yadan daga murya yace umman twins haka xakumin ko? Shikenan saiduk kutafi kubarni jikadai aishiyasa nace kibari akawa miki qanwa wadda xata ragemiki dawainiyar gida yaqarasa maganar da yar dariya dan dama danufin tsokana yayi maganar yakuwa tsokano dan saida tajuyo ta dalla masa hararan wasa sannan tashige wani daki riqeda hannun fa,eex suna murmushi dady kam dariya yayi sosai
Haka su fateema sukashiga dakin saj na riqeda hannunta fateema a ranta tanajinjina irin kudinda aka narka akowanne fanni nagidan agefe daya kuma soyayya da kulawar da iyalan gidan keyiwa junasu ita tafi burgeta
Haka suka sakata tayi wanka tafito tasauya kayan jikinta ixuwa wani material mara nauyi dataxo dashi yayimata kyau sosai taxauna agaban madubi gakayan make-up nan irin wanda takeso kala kala saidai batada kwanciyar hankalin daxatayi kwalliyar fateema tanason ado sosai wasu mayuka datagani a wurin sukadai tashafa tagyara kwantaccen gashinta daya dan hargitse takoma tufkeshi da ribon dindake kanta, yan biyu da yayarsu saj sunagefe suna kallonta tanaburgesu sosai danta hadu acewarsu
fateema takalli tsararren lallen amarcin da akayimata nanfa tashiga tunano abubuwanda suka wanxu tsakaninta da yayanta fahad burin ranta kuma muradinta mutumin data so tunbatasan kantaba ballatana tasan wani abu na rayuwa takoma tunawa da irin jankunnen da goggo tasha yimata akan son yarima hawayene suka wankemata fuska tacigaba da tuna kalamanshi naqarshe a gareta saikawai ta fasheda kuka yammatan duka sukayi kanta cikeda mamaki na dalilin kukanta
*Nasmy ce* π
Yar mutan arkilla love you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
ββΒ©(Z.R.A)ββ
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’186/190β’*
Saj tadafata cikin kidima tace yar uwa lfy kuwa? Allah yasa bamu muka batamiki raiba fatee tadago takalleta saitaji tausayinta yakamata yanda tashiga damuwa danganin tana kuka
Tashare hawayenta bakomai yar uwa wlh ba abinda kukayimin tace to meyasaki kuka? Fateema tayi shiru safeenah tace pls anty karki kumayin kuka baya yimiki kyau saleema ta karbe allah kuwa amma bakiga yanda murmushi yake yimiki kyauba fatee batasan sanda murmushi ya dubuto mata ba saisuma duka sukayi mata murmushin saj takalleta yar uwa yasunanki? Tadago danufin bata amsa saidai kafintafada saitaji daga qofa ance fateema!!!
Dammm gabanta yafadi ya akayi momy tasan sunanta fateema takalli mom din da mamaki qarara a fuskarta suma yaran haka saj ce tafara magana momy dama kinsanta ne bata amsataba ta isa ga fateema xonan ya'ta takama hannunta suka fice daga dakin fateema kam hankalinta a tashe yake bin momyn kawai take harsuka isa wani qayataccen falo ba wanda suka sauka daxuba ganin dady xaune ya harde kan babbar kujera two seeter yasata fahimci wannan falonshine hotunanshine birjik a falon mafu yawancinsu tareda ya'yanshi yadauka wanda sukayi da fa,eex sunfi yawa Kuma sunyi kyau sosai
Mom taxaunar da ita gefe akan kujera sannan itakuma ta isa kusada dady taxauna suka fuskanci fateema ahankali taxame daga kan kujerar taxauna dai dai akan capet falon yayi tsit dadyne yafara magana yakira sunanta kamar wanda suka dade da saninta fateema! asanyaye tadago kai tareda amsawa dan amatuqar tsorace take a ina sukasan sunanta? Wannan ba lokacin tunani bane dan kafinma takoma tuno wani abin dady yajeho mata wata dakakkiyar tambaya data kadata tareda raxana qwaqwalwarta waccce ce ke? Mekuma ya fuddoki daga gudanku masarautar gombe?
Wannan karon tsoronta ya bayyana qarara a fuska bakinta har rawa yake amma takasa furta komai sai hawayen dake kwaranya daga idonta falon yayi shiru bakajin komai sai sheshsheqar kukanta
Fa,eex dake gefe yagama quluwa da ita wata raxananniyar tsawa yadaka mata. Dalla malama kiwa mutane shiru kibasu amsar tambayar da aka miki fateema ta fashe da kuka sosai mai tsuma xuciya duk sukayi shiru kowannensu yakasa magana
(Abinda fateema bata saniba shine yanxu yanxunnan aka sako tallan cigiyarta a t'v alokacin dady yana kallon news momy kuma tana xaune a gefenshi kwatsam sai sukaga ankatse labarun ansako cigiyar fateema tareda nuna hotunanta wanda take tareda mijinta wato yaya fahad yariman masarautar gombe ana cigiyarne akan tafita a ranar farko data tare agidan mijinta anaroqon duk wanda yaganta daya taimaka yamaidata masarautar gombe domin itadin ya'ce kuma sarakuwar mai martaba)
Saida tayi kukanta mai isarta sannan tatsagaita tafara sheshsheqar kuka Allah sarki tausayin yarinyar yakama momy ta tashi daga inda take taje har gaban fateema ta dagota tareda jan hannunta xuwa inda take xaune taxauna sannan itama taxaunar da ita gefenta tafara rarrashinta saida tayi shiru ta nutsu sannan Momy ta fara yimata tamayar cikin sanyi da alamun tausayawa lokaci mai tsawo tadauka kafin tafara magana cikin sanyi da tsantsar rashin kuxari yanayinta abin tausayi tace:
Tabbas sunana fateema kamar yanda kukaji kuma dagaskene ni matar yariman gombe ce a da kafin farawar qaddarata wasu hawaye masu xafin gaske suka silalo daga idonta taja hanci sannan tacigaba shidin yayana ne dan yayan mahaifinane tunda aka haifeni nayi wayan sanin mutane bantaba son kowa samadashiba tun ina yar qanqanuwata nake sanarwa iyayena da yan garinmu dangi da maqota gayamusu nake yaya *fahad nawane* haka nataso tunbansan so ba har Allah yakaimu ga girma nasan so kuma nafahimci anayin aure ga masu son junansu nanfa naqara matsa lamba naqara girmama soyayyar yaya fahad araina lokuta dayawa mahaifiyata na nuna damuwarta bisa irin sonda nake nunawa inayiwa yaya fahad saidai fau niban damuba bankuma tabajin sonshi ya ragu a xuciyata ba dukdacewa a lokuta dayawa idan muka hadu yana nunamin alamu na tsana da rashin so kai akwaima lokacinda yacemin bayya sona kuma sam banyi kamada irin matan da xai iya so ba, amma dayake sonda nakeyimishi ajinina yake bantaba jin xafi ko ganin aibun abinda yake nunamin dinba haka rayuwarmu ta dore har xuwa lokacinda iyayenmu suka yane hukuncin hada aurena dashi*****************************************************************kaf fateema takwashe duk abinda yafaru tundaga lokacinda aka daura aurenta da fahad harxuwa ranar tarewarta da abinda yayimata dakuma dalilinta nabaro gidan wato kunyar da xatasha da habaici da gorace goracen mutanen qauyensu da qawayenta dakuma mahaifiyarta wadda saudatayita kwabarta akan abin tunkan yagirma amma tanace batasan da wane ido xata kaleetaba
Tanakaiwa nan takuka fashewa da kuka tarungume momy tsam dan Allah momy kutaimakeni wlh banaso banason komawa garesu dan Allah kubarni inrayu daku nawani lokaci
Jikin kowa awurin yayi sanyi shiru yaqara ratsawa hatta dady yakasa cewa komai ballemma gogan fa,eex dajikinshi yahau bari sosai yakejin haushin fahad a lbrn nan dayaji kawai saiyaji tsanarshi ta dira axuciyarshi kaitsaye yayi godiya ga Allah dayasanya lbrn fateema yaxama haka baixoda qaxanta ba, abangare daya na xuciyarshi kuma yalashi takobin kare haqqinta dakuma tabbatarda taxama tashi mallakinshi wato matar aurenshi hukuncin dady sukejiranji dukkansu akan fateemar dan hatta momy data fara ganinta yau tashiga ranta sosai tanaji aranta batason rabuwa da ita
*Nasmy ce*π
Yar mutan arkilla love you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
ββ Β©(Z.W.A)ββ
β
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*sallama da fatan alkhairi gareku masoyan nasmat masoyan yaya fahad novel yaudai ga nasmat Allah subhanahu wata,ala yadawomuku da ita cikin qoshin lfy, ina miqa godiyata mara adadi agareku a bisa irin kulawarku gareni tundaga kan masu kirana a waya har ixuwa masu turomin saqonninsu wayanda na mayarwa da wayanda bansami damar yin hakanba nagode ubangiji Allah yabar qauna nasan KUNA TARE DANI kamaryanda nima nake tare daku be with me u will always been in smiling love u all*πππ
*β’191/195β’*
Falon yayi tsit! Banda qarar a.c da shesheqar kukan fateema ba abinda ketashi a wurin jiki asanyaye dady yadago yakalli fateema sosai yarinyar tabashi tausayi wanda damacan halinshi ne koda baitana sanin mutum ba idan yaji yaxo dawata damuwa ko yagani saiyaji abin tamkar a ahlinshi ne Allah sarki
Fateema yakira sunanta ta amsa itama asanyaye xuciyarta cikeda fargabar hukuncin da farin dattijan xai yanke akanta gabanta sai dukan uku uku yake dady yace tabbas kina tattareda damuwa dakuma tashin hankali wanda yagirmi shekarunki fateema ke qaramar yarinya ce wadda baxata taba tunani irin na manyaba kisani nimafa ubane nahaifa gasunan bamkuma san ya qarshen rayuwarmu xata kasance ba sbd haka yata ke nasan damuwarki baxata bari kiyitunanin yanda iyayenki xasuji alokacinda wannan mummunan lbr nafitarki ya riskesu ba amma ni xan iya sani sbd nima uba ne
Yakike tunanin xasu rayu alokacinda suke tunanin kinshiga duniya kina wajanda bakisaniba sam xuciyoyinsu baxasu taba hutawa da tunani ba shin wane hannu kika fada? Waishinma kina raye kokin mutu? Baxasu taba fidda wayan nan waswasi axukatansu ba har abada wataqila ma tunanin yaxame masu sanadin kamuwa da ciwon xuciya ba mamaki waninsuma yarasa rayuwarshi akan hakan
shin kin tanadi amsar daxaki bawa mahaliccinki aranar alqiyama alokacinda xai tuhumeki daxama silar mutuwar iyayenki? Dady yafada yana kallon inda take
Fateema jikinta yayi sanyi sosai banda xubda hawaye ba abinda takeyi, ahankali tafara girgixa kai a ah a....ahh....dady