Showing 42001 words to 45000 words out of 57158 words

Chapter 15 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt

07 Feb 2025

5530

Binta ko?" Tace "eh" cikin zumud`i tana murmushi suma murmushin sukayi kafin Rukayya ta kama kunnen ta ta rad`a mata wani abu


Fateema ta d`ago fuska a raunane ta kalli Bilkisu dake gefe tace "anya zan iya kuwa?" Bilki ta d`aga mata kai "zaki iya mana"


Lokaci mai tsayi suka d`auka suna karfafa mata guiwa sannan ta mike tasaka wasu hills shoe da suka fiddo mata ta fice daga sashen tana rike bango Wai kar takalmin su yaddata. Kai tsaye sashen dake fuskantar nata ta nufa, kuyangin dake hidima a farfajiyar gidan sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa


Da sallama ta shiga falon sai dai ba wanda ya amsa mata kasancewar falon shiru ba kowa. Bata jira komai ba ta nufi kofar da zata sadata da d`akin, shima dai tana murd`awa kofar ta bud`e idon ta fess akan su dai-dai lokacin da Lazeera ta doshi bakin Fahad da nufin sumbata tana kwance bisa kirjin shi akan gado. Wani uban ihu Fateema ta saki tayi tsalle ta hankad`e Lazeera daga kan Yarima tana rafka salati


Hatta Yarima sai da ya tsorata ya mike a razane yana kallon ta tareda mamakin abinda ya shigo da ita nan kuma. Fateema bata damu da halin daya shiga ba ita kam Lazee take kallo cikin ido cike da mamaki tace "lallai Anty Lazeera bakida imani yanzu saboda Allah da kika danneshi haka kashe shi kike so kiyi?"


Lazeera da ta gama kuluwa ta kalli Fahad dan ganin wane mataki zai d`auka akan Fateema? Ga mamakin kawai sai gani tayi yana murmushi








*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍




*•255/256•*








Shi gaba d`aya yanayin yarinyar sai ya bashi dariya. Itafa a tunanin ta yanda Lazeera tayi akan shi zai iya cutar dashi, Fahad da baya dariya yau sai gashi yana kyelkyetawa, al'marinda yayi matukar kona ran Lazee ta juya ga Fateema "ke" ta daka mata tsawa "me kika zo yi nan bangaren?" Fatee da ahalin yanzu take jin haushin ta sai da ta murgud`a baki sannan tace "ina ruwan ki? gurin ki na zo?" cikin kuluwa Lazee tace "gurin wa kika zo?" "Gurin miji na" ta bata amsa a takaice


"Kutumar uban can" Lazeera ta fad`a lokacin da tayi tsalle da nufin shako wuyan Fateema. Yarima ne yayi gaggawar shiga tsakanin su ya rike Lazeerar "meye haka? dukan ta zakiyi?" "Eh ko zaka rama mata ne?" ta fad`a a tsawance tana kallon shi cikin ido Fateema tace "he ai Wlh in gaya miki ba'a ramawa Fatee duka, da ya barki ki gani hmm" ta juya musu baya tana wani girgiza da karkad`a kafa (ni kuma Nasmy nace "yan iskan kauye sun motsa Liz)


Yarima yabi bayan ta da kallo yanajin wani Abu na yawo a ziciyar shi, sai ya tsinci kansa da sha'awar yadda take lamuranta cike da kurciya. Shi kanshi ya san tsanar da yake mata ta ragu a ransa. A hankali cikin sanyin nan nashi ya raba jikinshi dana Lazeera wadda keta faman huci tana jifan Fateema da mugun kallo, ya zaunar da ita bakin gadon ba tareda yace komai ba yaja hannun Fateema suka fice fallo


Tirkashi a wannan lokacin Lazeera ji tayi kamar numfashin ta zai yanke, zuciyar ta ta hau bugawa da matsanancin karfi. Fateema kuwa sai da suka kai kofa ta juyo ta dalla mata gwalo. Ta rumtse ido da karfi jitayi kamar an yanki naman jikin ta tabisu da kallon takaici na rashin abinyi ta san Yarima sarai ta kuma san halayen shi, dole ta zauna badan ran ta ya so ba.


A falon kuwa sai da ya zauna sannan ya saki hannun Fateema wanda yaji kamar yaci gaba da riki shi, kujerar dake daf da tashi ya nuna mata yace "zauna" ba musu ta zauna tana mai tilasta idon ta barin kallon Yarima ta maida su kan yatsun hannun ta da take murzawa, a ran ta kuwa sake-sake take da tunanin taya zata tambaye shi kud`i?. Yarima Fahad ya zuba mata ido yana mata wani kallo da shi kanshi baisan dame zai fassara shi ba shin so ne, ko sha'awa? Tayi mishi kyau sosai kamar su dawwama yana kallon ta. Zaman shirun yayi mata yawa "Yaya" ta kira sunan kaman mai ciwon baki, shiru bai amsa ba hakan yasa ta d`ago da nufin yi mishi magana karaf idonta suka had`e da nashi daya kafe ta dasu da sauri tayi kasa da nata zuciyar ta na zarya akan lamari na soyayyar *Yaya Fahad* cikin kankanin lokaci jikin ta ke fara shock idan ya tsareta da irin kallon nan take take rasa tunanin ta


Ginin girma zai fad`i yasa Yarima ya Kauda kan shi ga barin kallon ta. cikin kasaitar shi yace "kin ce gurina kika zo kuma kinmin shiru" Fateema tace "eh dama kasan ni ban iya komai bane na girke-girke da sauran abubuwa na nan, to shine su Bilki ke gaya min da akwai wata Hajiya mai koyarwa sai dai suka ce zata bukaci kud`i da yawa. Yanayin yadda take maganar ma abin kallo ne baice komai ba ya mike ya shiga bedroom d`inshi bai jima ba ya fito hannun shi rike da jakar hannu ta maza wato briefcase yazo ya zauna kan kujerar daya tashi ya bud`e jakar nan cike take makil da kud`i yan dubu-dubu layi-layi ya mayar da jakar ya rufe duk abinda yake tana kallon shi ta gefen ido


Bazato taga ya mika mata gaba d`aya jakar yace "gashi ki ajiye a hanun ki duk abinda kika bukata kiyi, idan suka kare kimin magana"










*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍




*•257/258•*








Fateema tabi jakar nan da kallo ido waje. Sannan ta d`ago ta kalle shi "Yaya meye zanyi da duk wannan kud`in?" Tana maganar tana zare ido hakan ya burge shi sosai yanayin yarantar ta na bala'in burgeshi, ya kuwa zuba mata ido yana murmushi, a ran shi yace "Wato ita a komai ma haka take" yace "Fateema ai ke yar'uwa tace ko ba komai ai kinfi karfin wannan kud`in a wurina" maganar shi ta shigeta ba karamin dad`i takejiba idan Fahad na magana. itama dai cikin sanyin jiki ta zame daga kujerar tazube kasa tace "na gode Yaya Allah ubangiji ya biya kuma ya saka da alkhairi..."




"Shiiiiii ya katse ta ta hanyar d`ora yatsa a baki "No Fateen Goggo" duka hannayen sa biyu yasaka ya tallafo kafad`un ta ya mikar da ita tsaye suka fuskanci junan su a lokacin da idon su suka had`u "huhhh!" Suka sauke wata nannauyar ajiyar zuciya a tare, cos dukkan su ba wanda baiji wani sabon al'amari ba ta dalilin kusanci da had`uwar da idon suka yi. Yarima ya kasa jurewa tunanin shi ya fara dawowa tsohuwar soyayyar Fateema ta motsa masa bai san lokacin da ya kaiwa bakin ta cafka ba ai kuwa yafara tsotsa da tand`a kamar wanda ya sami lollipop, Fateema kam sandarewa tayi a wurin tamkar busashshen itace.




Hakan yayi dai-dai da fitowar Lazeera cikin fushi janye da trolley a hannu da nufin barin gidan as tayi fushi zata gidan su. Ai kusan fad`uwa tayi a dalilin abinda idonta yaci karo dashi "Ya Prince" ta fad`a da karfi tareda kolalo duka idanuwan ta waje, da sauri Yarima ya saki Fateema ya maida kallon ahi ga Lazee wadda idon ta yake fess akan shi, kome tayi mishi sai kawai ya tsinci kanshi da fad`uwar gaba tareda jin nauyi da shakkar Lazeera. Fateema kam yana sakin ta ta suri jakar kud`in tayi waje da gudu. bawai dan jin tsoron Lazee ba a'a kawai ganin abin tayi kamar aafarki, tana tafiya tana tuno wani lokaci daya wuce a baya kamar dai haka daya faru yanzu yasha faruwa tsakanin ta da Yarima a babban lambun gidan inda suke zama da yamma a lokacin nan datayi zama gidan.


Lazeera kuwa matsanancin tashin hankali ne ya riske ta zuciyar ta kamar zata faso kirjin ta ta fito saboda tsananin bugun da take mata, "me ke shirin faruwa dani ne?" Ta tambayi kanta a fili "inaaa" ta fad`a cikin d`aga murya "this will never be" ta fisgi jakar tayi waje daga ita sai wata tsinanniyar riga doguwa ce amma ta d`ame ta sosai ba ko mayafi haka ta fice


Suka bar Yarima tsaye kamar wanda aka dasa shi a gurin, tunanin shi duk ya hargitse yarasa abinyi shikan shi ba zai iya gane abinda yake yiwa Lazeera ba shin So ne ko tsoro? Bakaramin d`aga mishi hankali tafiyar ta'ta tayi ba. Hannu yasaka ya shafi kanshi a hankali ya furzar da wani iska mai zafin gaske. Dakyar ya iya Jan kafa'fun shi ya shiga d`akin baccin shi da zuwa ya zube kan gadon cikin mutuwar jiki ya d`ora hannu akan goshin shi dake yimasa rad`ad`i ya lumshe ido abin uwa na masa yawo a kwakwalwa


Lazeera kuwa ikon Allah ne kad`ai ya kaita gidan su, saboda tukin gangancin datayi. Da isarta ko dai-daita parking batayi ba ta fita da gudu ta shiga gidan a babban falon kasa tayi kicibis da Umman Yarima zaune a kan kujera tayi zugum abin duniya duk ya ishe ta tun ranar da ta baro gidan Mai Martaba tasan asalin wace ce Yayar ta, dakan ta ta zauna ta fed`e mata biri har wutsiya akan muguwar manifar su akan tilon d`an ta Yarima da dukiyar gidan sarauta harma da ita kanta sarautar, ranar Umma tasha kuka har ta gode Allah ta kuma yi nadamar goyon bayan data basu suka asirce d`an ta, jitayi a ran ta inama da wata hanya dazatabi ta fad`akar da Iyaye masu hali irin na ta akan su gyara su nisanci duk wata hanya ta asiri da bin nakaman tsibbo domin babu wani alkhairi a cikin ta, hanyace mara billewa itakam tayi nadama yanzu adu'a take baji ba gani akan Allah ya ceto d`anta su kuma ya toni asirin su, tun ranar ita da Hajiya ba mai shiga sabgar wani kowa na bangaren shi ko had`uwa sukayi banda mugun kallo da harare-harare ba abinda keshiga tsakanin su


Wani mugun kallo Lazeey ta wurga ma Umma sannan ta haye up tiers tayi saman Umman ta tana kwalla mata kira








*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍






*•259/260•*








"Momy! Momy!! Mo....." Bata karasa na ukun ba dan ganin wadda take kwallawa kira d`in tsaye a gaban ta, a razane ta fito saboda jin muryar Lazeera da kuma irin kiran da take mata. Tana ganin Uwar ta wurgar da jakar hanun ta ta tafi da gudu ta rungume ta sannan ta fashe da kuka. "Ke lafiya meya same ki? Ina mijin naki yake?" Hajiyar ta ce mai yimata tambayoyin cikin kad`uwa ita kuwa sai ta kara tsananta kukan tareda kankame momyn "Umma na shiga uku yarinyar nan zata kwace min mij......." Da sauri ta kai hannun ta ga bakin Lazeey ta toshe ta hanata karasa maganar a hanzarce ta ja hannun ta suka kure Uwar d`akin ta.




Ta kalli yar zuciyar ta na harbawa tace "me kike so ki gaya min Lazeey?". Sai sa taja hanci tace "abinda kunnenki yajiye miki Momy wallahi asiri ya karye ya'Prince ya koma son Fateema" Umma ta koma kallon ta cikeda rashin yarda don tariga ta yarda da Bokan su, samada shekaru Goma suna mu'amala dashi ta harkar asirai amma ba'a taba samun matsala ba da zarar yayi musu aiki kamar yankan wuka haka suke cewa, to baremma wannan da ta tabbatar mishi yafi duk ayyukan da ya saba yimusu muhimmanci kuma ya gamsu harma ya tabbatar musu da babu wata hanya da Fahad zai koma had`uwa da Fateema saboda tsan-tsan tsana da kiyayyarta da akasa Aljanu suka dasa masa a cikin zuciyar shi




Tace " to wanne dalili kake dashi wanda ya tabbatar miki da haka?" Nan da nan Lazeey ta bayyane mata duk abinda ya faru tsakanin Fateema da Fahad a d`akin ta. Take jikin Momy yayi sanyi kalau tace "inko haka ne ai zama bai same must ba maza tashi muje mu gurin Boka" ta fad`a a lokacin da ta mike tana ciro mayafi a wardrobe. Lazeey ma mikewar tayi tabi bayanta suka fice




Zaune suke a gaban Bokan nasu sunyi shiru bayan sun gama koro mishi bayanin abinda ya faru, shi kanshi Bokan yayi mamakin jin maganar dan a yanayin aikin da yayi musu hatta inda Fahad yake Fateema bata isa ta kusanci gurin ba. Ba tareda ya ce musu komai ba ya bazama ga buga kasa da surkullen tsafin sa. Can kuma sai ya had`e fuska cikin sigar fushi ya fizgo wani d`an karamin shantu baki wulik yana rataye a jikin bangon d`akin ya dire shi gaban sa, ya shiga karanto wasu surkulle na d`alasimman tsafi. Nan da nan d`akin ya kaure da hayaki tareda kuka da kururuwar Aljanu take d`an shantun nan yai bindiga ya fashe ji kake d`uuuu- d`uuuu




Hajiya da Lazey suka shiga ihu da bankaura suna gwara kanun su, A gigice Bokan ya daka musu tsawa "Ku asararru marasa nasara maza ku tashi ku fice kafin in hallaka ku, mahaukatan banza kunje kun jangwalo mana masu riko da addini gashi kun saka tsananin addu'ar su ya illata min Aljanu gashi duk sun tarwatsa min fada ta. To kusani wayannan mutanen ayanzu sun riga sunfi karfin Ku babu wani asiri da zai iya tasiri akan su. Haka kuma duk wanda kuka shirya abaya yanzu ya la'lace kutashi Ku fita" yafad`a da wata iriyar murya mai rugugi da gudu suka fice suna had`a hanya




Boka kuwa cigaba yayi da sambatu yana cewa "kuje zaku sani na tabbatar idan kowa ya barku Aljani Auhal ba zai barku ba, wannan bakar azaba dayasha saboda aikin ku"








*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍






*•261/262•*








Abinda su Hajiyar basu saniba shine tun ranar da Mai Martaba ya gano al'amarin na asiri ne, sai yasaka kullum sai an sauke Alkur'ani mai girma tareda manyan addu'oi, sannan a yanka babban bujimi ayi sadaka kuma har yau ba'a daina ba. Addu'oi ake baji ba gani, ba dare ba rana. ana nemawa Yarima da Matar sa tsari da kariyar Allah akan duk wan sharri, na mutum ko Aljan.


Wannan kenan








Cikin su ba wadda ta kalli ko inda motar su take, da gudu suka nufi hanyar da zata sadasu da babban titi, suka tare napep suka shige. mota kam a gurin suka barta




Fateema na shiga sashenta su Rukayya suka mike dan tariyar ta da kuma son ganin ko tayi nasarar samo kud`in?, Sai da ta zauna sannan ta shiga maida numfashi dakyar kamar wadda tayi gudun kilomita biyar.




A hankali ta bud`e lumsasun idon ta, wani irin farin ciki takeji Mara misaltuwa, sabon yanayi, sabon Al'amari, mikewa tayi ta rungume Bilkisu cike da farin ciki tace "Allah ya biya wadda takawo wannan shawarar, da badan wadda ta kawo wannan shawarar ba da zaman nisanta da takatsantsan na shirya zanyi da yayana, saboda tunani na yana bani baya sona, amma a dalilin wannan zuwan da nayi gareshi na gano har yau akwai tsagwaron so da kauna ta a ransa. Tsabar tsoron da yakewa Anty Lazeera shi yake hanashi isarwa ko bayyanawa"




Bilki tayi murmushi tace "Alhamdulillah yanzu kinga kin kara samun kwarin guiwa na neman horo da gogewar da zaki iya gogayya da kowacce irin mace saboda mijinki"




Fateema tace "sosai ma kuwa" ta fad`a tana gyad`a kai, kyakkyawar fuskarta d`auke da murmushi. Rukayya tace "to kud`in fa, an samu?" Bata bata amsa ba ta mika musu jakar kud`in data shigo da ita. Suka kurawa jakar ido cike da mamaki Bilki ce takai hannu ta zuge zip d`in, ai suna d`agawa suka rud`e tare suka kalli Fateema baki na rawa Rukayya tace "A..Anty Fatee baki yayi ko d`aukowa kika yi?, Tayi mata wannan tambayar ne saboda dalilai guda biyu.




na farko saboda ganin yawan kud`in da ta yi, na biyu kuma saboda sanin halin kiriniyar Fateen da ta yi, ko a gaban shi zata iya d`auko su ta gudo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login