Showing 48001 words to 51000 words out of 57158 words
Chapter 17 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt
farin ciki domin hakan ya tabbatar mishi cewa Umman shi ta saduda. Kuka ne mai karfi ya kwace mata ta rungume d'an nata, "Son dan Allah kayafe min kai da Fateema kuyi min aikin gafara wlh son nayi nadama, ka yafe min kaji d'ana" Yarima ya d'ago ta yana kara share mata hawaye yace "babu wani abu a rai na Umma wlh na yafe miki, kuma su d'in ma na yafe musu nasan Fateema ma zata yafe musu. Ina sonki Umma na pls karki koma yin nisa dani kinji"
maganganun nashi sun kashe mata jiki sosai domin duk yadda take son zama dasu dole ta hakura tunda Mai martaba ya saketa kuma ya kore ta. ta koma fashewa da wani kukan ta kankame shi "a'a d'ana bazan maka wannan alkawarin ba tunda Abban ka ya koreni daga gidan sa ba yanda na iya, sai dai ka dinga kawomin ziyara kuma dan Allah ka nemamin gafarar Fateema da Abban ka kaji." "ki daina kuka hakan nan Umma pls banajin dad'in shi, Mai martaba ya koreki a lokacin da kike cikin kuskure, yanzu kuma kin gane gaskiya na tabbata zai karbe ki" ya fad'a yana kama hahhun ta suka mike tsaye tare. da kanshi ya gyara mata mayafin ta basubi ta kan komai ba ya sakata mota shima ya zaga ya shiga ya mata key suka fice daga gidan suka nufi gida
misalin karfe biyar na yammacin Hajiya Binta mai gyaran jiki ta amsa kiran da Fateema ta aika mata dashi. Sai da ta jira akayi mata iso sannan wasu kuyangi suka shigar da ita babban falon baki dake sashen bayan kamar mintuna biyu da zaman ta Gimbiyar ta fito "Masha Allah" inji hajiya Binta kasancewar basu da wani nisa tsakanin gidan ta da gidan sarauta yasa taji labarin had'uwa da kyawun matar Yarima a wurin matan dake zuwa gidanta koyon abubuwa amma sam bata d'auka kyan yarinyar da kuruciyar ta sunkai haka ba.
Ta d'auka zatayi jiji da kai sai kuma taga ba haka bane. Cikin saukin kai da sakin jiki Fateema tayi mata bayanin duk abubuwan da take so ta koya daga gareta. Hajya Binta ta gamsu harma ta karawa Fateen wasu na daban wayanda suma sunada muhimmanci sosai gare ta sun dai-daita maganar kud'i harma sun saka lokacin da zata dinga zuwa (sis hours) zata dinga yi a gidan tana koyar da ita abubuwan, sai dai tace zata na d'an leka gida lokaci lokaci saboda yara
*Yar'mutan Arkilla* β
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β.
*269/270*
Karfe goma da rabi Yarima ya shigo gidan sarautar d'auke da mahaifiyar shi Umma, wadda take ta d'ari-d'ari da shi tunda ta shigo motar batayi magana ba Sai ma shi da yake yi Mata magana jifa-jifa. Kai tsaye sashen ta suka nufa tana gaba Yana binta a baya, kuyangi da ma'aikatan gidan Sai zubewa suke yi suna gaishe su, idan suka wuce Sai abi bayan su da kallo masu masaniya akan barinta gidan su fara kus-kus-kus haka Dai suka ratsa sassan har suka Isa bangaren ta.
Jakadiya na ganin ta ta rangad'a gud'a ta shiga antayo Mata kirari da yabo tare da nuna farin cikin dawowar ta. Yanayin da take ciki yasa bata tsaya ta kanta ba, ta wuce uwar d'akin ta. Fahad yabi bayan ta, Sai da ya tabbatar ta zauna sannan ya fice ya nufi sashen mahaifin shi kasancewar time d'in fita fada bayyi ba.
Bai tsaya wani boyo ko noke-noke ba Kai tsaye ya sanar da Abban shi komai dangane da mafarkin da yayi, da kuma abinda ya faru a gidan su Lazeeran Sai kuma farin cikin shi daya bayyana wa Abban nashi akan dawowar Fateema gare shi ya tabbatar masa duka aikin asiri ne. yanzu ya dawo hayyacin sa kuma yana son matar sa. Mai martaba yaji dad'in al'amarin sosai har ya dinga sakawa d'an nashi albarka tare da addu'ar Allah ya kare gaba. Daga karshe Yarima ya rufe da rokawa mahaifiyar shi gafara ya sanar da shi cewa ya dawo da ita, kuma tariga tayi nadamar abinda tayi a baya, Yana da tabbacin bazata koma aikata maka mancin sa ba. Tunani mai zurfi dattijan yayi kafin ya d'ago yace na maidata Yarima taci albarkar ka Ina Mata fatan sabuwar rayuwa Mai kunshe da alhairai nan gaba. Yarima yaji dad'in hakan har cikin ran sa bai bar uban ba saida ya tasa keyar sa har sashen Umma suna tafe suna hira cikin raha da walwala ya dad'e rabon da ya rabi mahaifin nashi haka, haka shima Uban ya kyale shi ne kawai amma yaron Yana ran sa Sai yazamana dukkan su suna cikin farin ciki da wannan zaman nasu na yau. Umma kam da tayi ido biyu da Mai martaba Sai ta diririce kunya da takaicin aikin ta na baya suka baibaye ta. Amma dayake mijin nata wayayyen mutum ne Sai ya basar yayi Mata magana kamar wani Abu bai faru ba.
Haka Yarima ya barsu suna gaisawa bayan fitar d'an ne yayi Mata nasihohi masu karfi da sanyayar da jiki, Umma kam Sai kuka take tana rokon gafara kuma tace ya saka musu rana suje garin kukunba ta roko gafarar Baffa da Gwaggo. Yace wannan ba komai zasu je nan bada jimawa ba.
Zuciyar shi fari kall ya nufi gidan shi sashen Fateema da shigar shi sashen kamshi yayi mishi marhaba, da alama Ana had'a wani delicious ne inji zuciyar shi. Sai a lokacin ya tuna ko breakfast bayyi ba. Da sand'a ya nufi kitchen d'in kamar wani barawo domin yasan Fateema tana da masu aiki Yana so ya gani ne ita ce a kitchen d'in ko ma'aikatan gidan ne Dan magana ta gaskiya Yana so yaga matar shi kewar ta yake ji sosai. A d'an koridon hanyar kitchen d'in ya make Yana lekawa abin mamaki Sai yaga Fateema da wata mace suna shirya girke-girke ga dukkan alamu matar tana koyar da ita ne, farin ciki ya ziyarci zuciyar shi dad'i ya lullube shi. Ya dad'e tsaye a wurin domin kallon da yake mata yana faranta masa, gani yayi sun kammala komai suna shirin fitowa da sauri yabar wajan ya shige d'akin sa. Hajya Binta ta taimaka mata wajan jere kayan akan table wanda shima duk cikin horon ne, daga nan suka wuce d'akin ta inda ta saka ta shiga wanka da wani had'in turaruka na wanka wanda ta bawa Fateen ta had'a da kanta. Tana jin dad'in koyar da yarinyar abubuwa domin tanada brain, da sauri take haddace abu. gaban mirror ta zaunar da ita bayan fitowar ta daga wankan inda ta koya mata yadda ake amfani da hand drayer ta busar mata da gashin kanta mai tsayi da laushi sannan ta nuna mata irin kalolon mayukan da zata dinga amfani dasu a kan nata. daga nan sai aka zarce sashen make-up inda take nuna mata yadda zatayi tanayi da kanta kafin kace me fuskar nan ta d'auki sheki da walwali ga sihirtaccin turaruka sai zuba kamshi take. Suka koma gefen saka kaya nan fa tashiga nunawa Fateema had'in colours na kaya da mayafai, takalmi da jakunkuna ko wanne kalar kaya da kalar mayafi da takalmi da jakar da ta dace da shi. Tana kuwa d'aukar darasin sosai komai yana shiga kanta yadda ya kamata.
Doguwar riga ta saka ta wani tsadadde material mara nauyi rigar ta amshe ta matuka tun daga kalar ta data kasance marum ta d'aura mata d'ankwali na wani yadi mai kyan gaske porpul plat shoe ta saka suma porple ta manna mata d'aya daga cikin sarko'kin ta na zinari had'e da yan'kunne da warwaro cikin abinda baifi 30 minutes ba Fateema ta dawo asalin sunanta na tauraruwa (Zara) kyawun ta ya kara bayyana ita kanta Hajya Binta sai da ta bata snap, sannan tayi mata sallama ta tafi har kofar shigowa bangaren ta rakata tana ta yi mata godiya ta tafi. Juyowar da zata yi ne kawai sai ji tayi tayi karo da mutum tayi baya da sauri idonta a kan wanda tayi karon da shi Yarima ne ga dukkan alamu binta yake a baya. Ta tsuke fuska sannan tayi gefe zata raba shi ta wuce wani irin kamshi ya daki hancin sa, sai da ya lumshe ido, baisan lokacin da ya kai mata cafka ba ya kuwa rungumeta tsam a kirjin sa yana sauke numfashi tamkar wanda yayi gudun kilomita biyar. ta shiga kiciniyar kwacewa
"Yaya Fahad Allah ka sake ni bana So" ta fad'a tana cinno baki yayi murmushi *i miss you* Fateen gwaggo ya rad'a mata a kunne sai da tayi jim idon ta suka lumshe saboda wani bakon al'amari da taji a jikin ta. bai tsaya nan ba wuyanta ya shiga shaka yana shinshinar ta kamar tsohon maye, ya zagaye ta da hannayen shi ya mata kyakkyawar runguma ta mintuna biyar sai yaji kamar ruhin shi yana dawowa jikin shi wata irin nutsuwa yaji wadda rabon shi da jin makamanciyar ta tun lokacin da yake rabuwa da jikin Fateema. Ya koma sauke numfashi sannan yace "Alhamdulillah" sai z lokacin ya sake ta amma hannun ta yana rike da nashi yaja ta zuwa danning inda yaga an shirya abinci ba musu Fateema ta bi shi suka zauna da kanshi ya zuzzuba musu abincin ya zauna da spon d'aya ya ciyar da kanshi da kuma ita sam bata ki ba taci abincin sai da taji ta koshi sannan ta danne da drinks. Yarima Fahad kam ya raja'a da kallon kanwar shi kuma kyakkyawar matar shi Fateema wadda baya taba gajiya da kallon fuskar ta wani irin fari tayi mishi da ido baisan lokacin da ilahirin gabobin jikin sa suka saki ba kasala da mutuwar jikin suka dirar mishi lokaci d'aya yaji ya kwad'aitu da matar sa kuma abar kaunar sa Fateema sai dai kafin yayi wani yunkuri tuni ta raba jikin ta da nashi ta ruga aguje takai kofar d'akin ta sai a lokacin kuzarin sa ya dawo "Fateema" ya kira sunan ta da sauri murmushin mugunta ta sake mishi sanna ta shige d'akin ta ta leko kanta ta dalla masa gwalo tana dariya "a'a Fateema kar kimin haka pls" ya mike ya nufota da sauri ta datse kofar tamurza key ta barshi a jiki Allah sarki Fahad kuka ne kawai bayyi mata ba amma yayi magiyar duniyar nan taki ta bud'e d'akin dole ya hakura ya kwashi kanshi ya koma d'akin shi ya kife kan gado. Ya dinga matse filo yayin da zuciyar shi ke dad'a afkawa cikin kwad'ayi da sha'awar Fateema. Ita kam tsalle tayi ta haye gado aranta tana cewa "kad'an ma ka gani tukunna ai har marin da kayi min a rafin kukunba sai na rama wlh" ta kece da dariyar nan tata ta shed'anci (niko Nasmy nace anya Fateema bazaki tausayawa Fahad ba) to haka dai rayuwar gidan ta d'ore musu kullum cikin abu d'aya fiye da wata d'aya ya kasa samun Fateema, sai yaga kamar ya kama sai tayi escape. Umma ta roki gafarar ta kuma ta yafe mata yanzu zaman mutunci suke yi da mutunta juna Umma tanajin dad'in Fateema sosai sai yanzu ta fahimci yarinyar tana da kirki kusan kullum sai ta jewa Umma hurar dare wani lokacin hadda Yarima wanda idan suka had'u suna hira ba wanda zai ce da akwai wata damuwa a tsakanin su. Fateema ta kara gogewa ta zama wayayyar mace kimanin watanni biyu kenan tana d'aukar horo a gurin Hajya Binta yanzu ma har ta daina zuwa saboda d'alibar ta'ta ta zama malama ta gama kwarewa ta kowanne fanni tazama tauraruwa a gidan sarautar kuyangi da bayi da ma'aikatan gidan sunajin dad'in ta sosai. Mai martaba na ji da ita kusan fiye da kowa a gidan. Sai da ya tabbatar zaman su yayi dad'i komai ya dai-daita a yau yace musu su zama cikin shiri gobe zasu tafi kukunba, dukkan su sunji dad'in maganar tafiyar amma basu kai Fateema ba wadda tayi kewar gidan su matuka tunda tazo gidan bata koma ba haka suma tunda suka zo sau d'ayan nan suka tafi ba wanda ya dawo sai dai sukanyi waya kodayaushe kasancewar itama yanzu tayi wayar kanta farin ciki ne zallar sa a ranta yau sai rawar kai take ji take kamar anbata kyautar zuwa hajji hatta Fahad yau ya shaidi hakan domin da suka koma bangaren su tsalle tayi ta d'ane bayan shi tana ihun murna Yarima kam ji yayi kamar su dawwama a hakan bisa kuhera ya sauke ta tanata dariya shiko sai kallon fuskar ta yake baki a sake bakaramin kyau dariyar take kara mata ba sai da tayi mai isarta sannan ta tsagaita ta kalke shi "Yaya Fahad, kaima kanajin yanda nake ji ko?" "eh" yace yana kare mata kallo baisan yaushe Fateema zata daina yaranta ba. "Nasan yau kina cikin farin ciki, Fateema dan Allah ki tsaya mu fahimci juna kinada iliminki dai-dai gwargwado shin bakisan akwai hakki na a kan ki ba?" kasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannun ta hakika wasu lokuta Yayan nata yana bata tausayi. Ita kanta daurewa kawai take yi amma tanajin dad'in zama a kusa dash. A ranta tace ya kamata ta tausayawa mijin ta abinda takeyi sam bai dace ba ta d'ago ta kalle shi "kayi hakuri Yaya na insha Allah ya wuce zamu zauna kamar yanda kake so amma fa sai ka cikamin burika na guda biyu tareda bani amsar tambaya d'aya" da sauri ya d'ago ya kalleta
*Yar'mutan Arkilla* β
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*271/272*
"Meye wad'annan burikan naki Fateema? Wlh zan cika miki su, mece ce tambayar ki? Fateema zan amsa miki" bakin shi har ruwa yake idanun shi a kan ta. tayi murmushi "da fari dai kaga ina son cigaba da karatu, zaka nema min admission ka barni in cigaba" ta tsagaita tana kallon fuskar shi. Murmshi yayi mata sannan ya kai hannun shi ya shafi gefen fuskar ta yace "amma inaga ai kin san dokar ko Fateema?" Kin sani sarai ba'a irin wannan fice-ficen a gidan sarautar nan" Fateema ta bata fuska tana shirin mikewa tsaye yayi saurin rikota ya zaunar da ita "ina son ki Fateema, zan iya yin komai saboda faranta ranki, amma me kike So ki karanta?" sai a lokacin ta saki fuskar ta "ina da muradin na zama likita ne abinda zan karanta kenan, dan Allah Yaya ka taimaka min kaji?" Janyo ta yayi saida ta mannu da kirjin sa yace " I'll do anything for your happiness Teema na, zakiyi karatu amma fa kisani ba dai a gombe ba dole sai in kin lamunta mubar kasar nan da sunan zanyi wani cours kinga sai kiyi karatun ki cikin kwanciyar hankali ko" batasan lokacin da tayi mishi kyakkyawar runguma ba. "Thats my yaya" ta fad'a lokacin da ta kwantar da kanta bisa kirjin sa, shi kuma sai yaji kansa kamar bai taba rungumar wata macen ba sai ita kad'ai. Sbd dad'i da sanyin da yaji a rayuwar sa. Ya d'ago fuskar ta yana fad'in "naji bukatar ki ta farko Fateema, mene ne na biyun?"
ita kanta sai da abinda yake ranta ya sakata dariya kafin ta koma d'aure fuska tace "gobe zamuje kukunba, ko zaka iya tuna marin da kayi min a hanyar mu ta dawowa daga rafi?" Yarima yai shiru yana tunani can ya d'ago yace "eh na tuna, lokacin da kika ce kina sona ko?" Ya tambaye ta yana sosa kyeya cike da jin nauyin abin. tayi murmushi "to shi zan rama, kuma a dai-dai inda kayi min a can zan rama" ya zuba mata ido cike da mamakin ta a zatan shi wasa take, amma a fuskar ta sam bai ga alamar wasar ba. hannu ya saka ya tallafo kumatun ta suka fuskanci juna "Fateema, da gaske kike zaki iya marin Yayan ki?" Cike da yaran ta tace "eh ai kai ne ka fara Allah yaya sai na rama" ta karashe maganar cike da shagwaba "to naji na yarda zaki rama, meye abu na ukun?" "uhum dama zan tambaye ka ne akan anty Lazeera ance min ta tafi, shin meye gaskiyar maganar?" Shiru sukayi duka na yan mintuna kafin ya fara magana, ya kwashe duk abinda ya faru ya sanar mata, daga karshe yake shaida mata ya riga yasake ta saki d'aya, kuma shi da wata macen ma hayatan-hayatan har Γ bada yana kallon fuskar ta yace "in dai har kika yarda dani kika So ni Fateema to zan zama naki ke kadai har karshen rayuwa, wallahi yanzu ina son ki Fateema fiye da wanda kike yimin dan Allah ki yarda dani ki daure ki karbe ni amatsayin mijin auren ki" ya fad'a lokacin da ya zame daga kujerar ya tsuguna a gaban ta. Tausayin Yarima da mamakin rayuwa suka kama Fateema
Wai yau ita ce *Yaya Fahad* yake bibiyar ta yana barar soyayyar ta, Allah sarki rayuwa ba shakka maganar magabata gaskiya ce (mahakurci mawadaci ne wata rana) zuwa yanzu Fateema tariga da ta goge da ilmi na soyayya da sanin makamar namiji.