Showing 9001 words to 12000 words out of 57158 words

Chapter 4 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt

07 Feb 2025

5524

tambayar lfyrki sqi kuka ina yanxu kikace mana kinji sauqi, ya dora wayar akunnenshi inajinka yaya




Mai martaba yace kuhada mata kayanta anjima xan turo dan,uwanta ya daukota akaita asibitin nan garin koxaifi nacan din to allah yakaimu Allah yabar xuminci yadada girma da daukaka mai martaba ya katse wayar xuciyarshi cikeda damuwa




Yafara kiran layin fahad wanda alokacin yake hanyar xuwa turakar mahaifin nashi domin ya gaisheshi, yadaga wayar da sallama yace yarona kana ina? Ina hanyar xuwa wajanka abbana to shikenan bari kaxo din ya katse wayar




Da isarshi kuwa bayan sun gaisa mai martaba yasanar dashi buqatarshi tayaje kukunba yadauko fateema akaita asibiti anan yace Allah yakaimu yatashi yafita xuciyarshi cikeda tunanika barkatai shida yake shirin fita garin yau koxai sami dai dai dashi da agaskiya kwana biyunnan haqurinshi yafara gaxawa yanada buqatar mace jiyamadaqyar yayi bacci




Qarfe goma shabiyu yarima da yan rakiyarsa fadawa suka isa gidan angama shirya mata komai goggo harda kukanta tanatayi maata addu,a bayan sungama gaisawa yace afitoda ita sam fateema batayi wani farincikin gqninshiba goggo ce ta riqota fuskarta yakalla sqidaya tsorata ganin yanda ta kumbure suntum shidagani yasan kuka tasha bawani ciyoba yayi mata sannu ta amsa batareda ta kalli inda yakeba,


Nanfa goggo taqara tsorata da wannaj ciwon na fatee tabbas. Baqaramin ciwo bane ace ga yarima gabanta amma ko kallon inda yake batayiba


Hakadai tariqota har bakin motar aka bude ta sakata abaya yarima ma. Yaxaga yashiga sukatafi baffa ne yani goggo da rarrashi aiciwo ba mutuwaba addu,a yakamata muyi mata ba kukaba,




Qarfe daya suka isa gombe kaitsaye memorial prvt hospital ya nufa da ita asibityn families dinsi kenan daxuwa aka shigarda ita bayan yan gwaje gwaje likita yakira yarima xuwa office dinshi yagaya mishi qanwarshi fa daftake da kamuwa da ciwon xuciya saida yadan firgita doctor for what? Likitan yace bansaniba amma dai damuwar axuciyarta ne ba mamaki akwai aninda takeso bata sameshina ko kuma bataso ake takurata cikin biyunan dai dole akwai daya sbd haka maganinta badaga garemu yakeba kune xaku gyara inkuma bakusan damuwarta ba toku tambayeta tasanar daku sannan kuyi qoqari da gaggawar sadata da abinda takeso kafin wannan muunan abin yasameta,




Yarima ya gama rikicew ya diririce yarasa abinda xaice da dr miqewa yayi yafita yakoma dakinda fateen take xuciyarshi cikeda rudani wannan wacce irin masiface? Yarinya qarama tadauki damuwa ta dorawa rayuwarta yanxu idan takamu da ciwon xuciya tadalilinshi in abbanshi yasani yaxayyi kenan? Bashakka xai tsaneshi
Innalillahi




















👉 *Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯














*5 star's ✨✨ online writer's association*👌








*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍


















*•61/65•*




























Tana xaune abakin gadon inda likita yabarta qofa take kallo qkma yana shiga dakin ta dauke kanta tamayar gefe, abinda yanashi haushi kenan wato batama son ganinshi kenan? Lallai yarinyarna wato shibaiji haushintaba itace xataji haushinshi uhum




Batareda ya kalletaba yace mata tashi mutafi, baijirata miqeba yayi waje wani irin qololon baqin cikine yatokare wa fateema a maqogwaro tamiqe daqyar tanabin jikin bango harta fita a mota tasameshi sai shan qamshi yake kamar wanda akama wani abu, aka bude mata motar tashiga driver yatayar suka tafi cikin qasaitar nan tashi yaceda driver xamu sayi magani a venga pharmacy, ok sir driver ya amsa cikeda ladabi suka faka a wani makeken pharmacy nan yafita ya siyo dukkanin magungunan da likita ya rubuta mata




Da isarsu gidan yafice yayi cikin gida yabarta a motar ahankali ta tako qafarta ta fito daqyar take takawa saidai xuciyarta tagama yanke hukunci akan yarima tafe taje tana cixon lebe, hmmm kawai baisan fatee
Bane jina yakeyi wlh dan kawai banida lfy ne amma bari in warke xan nunamishi asalin kala ta, duk a xuciyarta take wayannan maganganun lokacinda take tafiya xuwa cikin gidan sarautar


Dayake tasan gidan sosai da mutanen cikinshi suma sun santa tana tafe suna gaisawa da hadiman gidan harta isa sashen gimbiya umman yarima kenan akayimata iso umma tace tajirata anan tana xuwa


Takai 20mins bata fitoba dukda angaya mata wadda taxo din can fateema harta fara gyajgyadi tafito cikin takunta na isa da qasaita laxeera na biyeda ita dawasu damammun kaya riga da sket kanta ka dankwali babu, suka iso falon yayinda umma ta hakimce akan doguwar kujera laxeera kuma taxauna a qaramar kujerar dake gefenta fateema tadan xame daga kan kujerar tagaida umman ta amsa da dan kulawa hartana tambayarta su goggo ta amsa mata da lfyrsu qlau,




Tace akace bakida lfy keyake daminki? San danki xuciyarta tafada a gajarce, afili kuwa cewa tayi eh wlh yanxunma daga asibiti muke amma da sauqi


Laxeera dakejin haushi da tsanar wannan kyakkyawar yarinya takalleta a tsawace tace ke dan iyayenki baki iya gaisuwa bane kobqn isa kigaidani ba? Sosai fateema taji xafin xagin harcikin ranta takalli umma koxatace wani abu amma bataceba, saima cewarda tayi kigaisheta man fateema yayarki ce, itadin yar yayatace




Fateema tayi qasa dakanta ina wuni taceda laxee kamar baxata amsaba saican tace lfy




Umma takira jakadiya tace takai fateema dakinda xata xauna taceto tqyi gaba fatee tabita a baya van tatsinkayo muryar laxee tanacewa hmm qauyawa kenan anyi marmarin miyar nama, yitayi kamar batajitaba tawuce axuciyarta kuwa cewatake lallai wannan kin tsokalo tsuliyar dodo yoni ko a garimmu ma an isa axageni inqyale balle a birni inda mutum yakeyin yanda yaso tayi qofa xamu hadu ne wlh baxanbar gidannan ba sainayi maganinki yar iska karuwa jibi kayan dake jikinta




Dai dai nan suka isa dakinda akabata jakadiya ce takarbi kayanta tabude wardrobe tasaka taja hannunta yaki yata tabude bayin dake cikin dakin ta nunnu na mata yanda ake amfani da komai sannan suka fito


Fateema tace ngd jakadiya tace bakomai yata fatee Allah dai yabaki lfy tafita tareda ja mata qofa fateema tasauke ajiyar xuciya taxauna a bakin gadon tafara qarewa dakin kallo yayi mata kyau sosai tanashirin kwanciya jakadiya tayi sallama tashigo dawasu matasan bayi mata gudabiyu abayanta kowacce daukeda faranti ahannu dayar kayan abincine akai dayar kuma kayan lemuka da yayan itace wato pruits, jakadiya tace ga qanwar yarima nan dagayau kuxaku cigaba da kulada ita har ranarda xata komgida bayin suka russuna gareta bayan sun ajiye kayandake hannunsu sukace angama rankishi dade,




Sannan tajuya ga fateema tace mata wannan sunanta ummi wannan kuma xaleeha suxasu riqa xama dake suna debe miki kewa duk abinda kikeso ki sanar dasu xasu kawo miki, tamiqa mata ledar magungunan ta tace gasunan idan kinci abinci kisha kowanne daya haka da darema, Allah yabaki lfy tafita tabarta dasu ummi da xalee wayanda dukkausu kusan sa,anninta ne, suka xuxxuba mata abinci da abinsha sukabata tanaci suna mata hira






















👉 *Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯














*5 star's ✨✨ online writer's association*👌








*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍














*•66/70•*












To dayake itadinma ba bayaba haka suka dinga hira cikin qanqanin lokaci tasaba dasu ummi wayanda suka taimaka sosai wajan rage damuwarta hankalinta yakwanta da yamma suka hada mata ruwan wanka ummi takalleta kai rankiya dade kibani dama in tsefe miki kanki mana kinada gashi sosai amma xai baciidan bakya gyarawa




Fateema tai murmushi dama tanason gyaran dakantane dai baxata iyaba dan agidama goggo ce ke tsefe mata takunce kai suka hadu suka tsefe matashi, suka wankemata da mayukan wankin kai nandanan gashinta yayi fess sai sheqi da walwali yake yaqara baqi ga wani qamshi dakeyi itakanta taji dadinshi


Sukabarta a bayin tayi wanka tafito sanyeda hijabinta suka bata towel sukace tagoge jikinta takuwa goge ba musu tashafa mai daya tafita saigata tadawo kata dawata doguwar riga mai kyau da daukar ido rigar pink ce sai akayimata adon red stone sababbin pant da bra suka kawo mata tafara sakawa sannan tasaka rigar masha Allah


Ummi ce maiyimata make,up yayinda xaleeha ke taje mata kanta sannan ta busarmatashi da hand drayer masha Allah watabarakallahu ahsanal khaleqeen, fateema tadawo kaman ba itaba, dukda tadauki xubo gashi a gadon baya iskanci ne yau kam tayarda iskancin nayimata kyau sosai jinkanta tayi kaman balarabiya ga kwalliyarda bata tabayin irintaba ga wannan gyaran gashi da aka mata yasha mai sai sheqi yake fuskarta tayi luwaui luwui kaman ta jarirai




Kawai saita tuna da wannan laxeeran data xageta daxun, wani shu,umin murmushi naga tayi (nace tofa real fatee ta dawo bari in ruga incewa laxeera ta gudu)




Afalo nasami laxee tayi dai dai akan kujera tana cin pruit salad, a yangace tana wani lumshe ido, tashar xee tv take kallo kanaganinta kasan tana cikin farin ciki, wanda ayanxu xaman jiran fitowar yarima fahad takeyi awurin,


Ahankali fateema ta tako ganin har tashigo falon laxee batasan da itaba yasa ta buya a bayan kujerar da laxee take kai, dayake kujerun irin dima dima dinnan ne saitashige qarqashinta ahankali tafara xila hannunta tana shafo qafar laxee tun tana dan kada qafar hardai tamiqe xaune amma bataga komaiba, takoma tq kwanta tana mamakin abinda ke tabinta adai lokacinda fateema tasami dan tsinken stick ta tsula matashi aqafa da qarfi tayi ihu ta miqe tsaye amma bataga komaiba ga qafarta sai xogi take mata wurin kaman ya fiddo jini


Tafara tsorata nan tashiga dube2 tana qoqarin duqawa qasan kujera ta leqa fateema tayi gaggawar cannja muryarta xuwa kakkaura ta maxa adan tsawace tace karki kuskura ki ganema idonki abinda xai xamo ajalinki ke kin isa kiyi ido biyu da autan jinni


Laxee jikinta yahau qyarma dan tunda take bata tabajin irin wannan muryarba aiko ihu bata iyayiba takwasa dagudu harta bige kanta da qofa amma bata tsayaba tabar falon arikice


Da gudu fateema ta fito tayi dakinta tahaye gado kaman bata fita ba, dariya tahauyi hadda riqe ciki tana dukan gadonta


Jin motsin qofar dakintane yasa tayi shiru su ummi ne dama abinci suka fita kawo mata tayi lamo kaman maison yin bacci xaleeha tace ayya ranki yadade badai bacci xakiyi yanxunba? Ai baccin yamma babu kyau


Ummi tace ai warrware baccinnan kitashi yau aljanune a gidannan tadan waro ido alamar tsoro tace aljanu? Eh haka yaya tace gasucan afalo antaru wai anan aka tabata kuma har magana aljanin yayi mata


Fateema ta miqe da sauri tafita falon tana ware ido kaman dai batasan komaiba haka suma sukabita abaya fapo cikeda ma aikatan gidan anata dube2 laxee natsaye hannunta riqeda umma sai xare ido take dariya tasota kufcewa fatee amma saita kanne ta isa gareta yaya waidagaske aljani kika gani wata muguwar harara ta wurga mata fateema tayi shiru, maganar datayin yadawo da hankalin mutanen gurin kanta


Nanfa sukafara santin kyawun datayi akabar maganar aljani kowa a gurin cewa yake kai masha allah fatee kinyi kyau sosai banda umma da laxeera da abun yayi matuqar qona ransu




Ummance tadaka musu tsawa abinda kukaxo yi kenan? Dalla kufita kubani guri nandanan suka fashe jiki na rawa kowa Yakama gabansa yarage dagasu sai fateema a falon laxeera ta qwallawa ummi kira tadawo dasauri ta rusuna a gabanta gani yaya, tace acikinkunnan wacce shegiyarce tayimata wannan adon tareda bata kayan gidan sarauta? Duk sukayi shiru fateema ta daga kai takalleta sannan ta taka xuwa gabanta cikin gadara da rashin tsoro tace nice nan ni ja buqaci suyimin duka wayannan abubuwa laxeera ta kalleta cikeda tsananin mamaki




Tamarasa tayanda yakamata tahukunta fateema, hannu tadaga ta sharara mata mari wanda saida yasa ta tangadawa kaman xata fadi ta tirje ta kalli umma dake gefe batacewa laxee komaiba


Aikuwa itama cikin shammata da baxata tadaga nata hannun ta wanke laxee da mari har guda biyu




















👉 *Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯














*5 star's ✨✨ online writer's association*👌








*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍


















*•71/75•*
















Tsananin kamakin dataji yafi xafin marin yawa umma tasaya salati yau mexan gani? Ke fatee laxeeran kika mara? Cikin tsananin fushi laxee ta nufo fateema gadan gadan itakuma ko aranta dan batasan tsoroba jirakawai take ta iso gareta su dambace




Muryar yarima sukaji daga bayansu inda yadakawa laxee tsawa karki yarda kitaba ta, cikeda mamaki umma takalleshi kasan abinda tamata ne? Laxee kuwa tsayawa tayi tana cixon yatsa


Eh ainaga komai agabana akayi baiqara cewa komaiba ya wucesu yakama hannun fateema yakoma sashensa da ita, kallon mamaki umma da laxeera suka bisu dashi kafin umma tajuya takoma sashenta laxeera tabita tana share qwalla baqin ciki kaman ya kasheta




A dakin yarima kuwa fateema taqara xama asalin haqauya domin yanda aka tsara dakin dole akalleshi yaxaunar da ita bakin gadonshi shima yaxauna tanakallon tsarin dakin shikuma yana qarewa halittar ta kallo, ashe haka yarinyarnan ta hadu? Hmmm wani iri sha,awa ya qara xaburo mishi sanda idonshi yasauka a lips dinta nandanan idonshi suka sauya yafara shiga yanayi


Fatee yakira sunanta lokacinda yakama hannunta yariqeshi acikin nashi ma,am ta amsa batareda ta kalleshiba ta hada rai tajuyarda kanta gefe, hmm yai murmushi mai fidda sauti fushi kikeyi dani qanwata? Tayi mishi banxa ok shikenanma tashi kitafi dama kayan sakawar ne naga yakamata asiyo miki naki kihuta dashan gori, yafada tareda sake hannunta


Allah sarki quruciya dasauri tajuyo takamo hannun nashi Allah yaya inaso pls kasiya min yanda tayi maganar cikin farin ciki saiyaji dadi aranshi yajanyota jikinshi yarungumeta tsam dukkaninsu saida sukaji sauyi ajikinsu yawwa qanwata karki koma fushi dani kinji? Taceto, yaushe xaka siyomin kayan? Yace ko yanxuma tasakeshi tamiqe tahau tsalle yeeeeee wayyo dadi xak xama yar birni kuma wlh yaya inada kyau da irin kayan nan kalleni fa taxo gabanshi tasaya tareda kama qugu abin yabashi dariya yai murmushi hmm kinyi kyau sosai jeki dauko mayafi mutafi da gudu ta fita tana ihun murna




yabita da kallon mamaki waiharta huce kenan hmmm


Agurguje yashirya xuciyarshi fall da farin ciki wanda shikansa baisan dalilinsa ba, yasandai badan xai fita da fateema bane


Saidai abu daya daya bashi mamaki gameda ita shine duk tsanani yanayin sha,awar dayake ciki runguma daya yayi mata yaji duk sha,awar tafita akanshi saiyajishi warwar




Madalla da fatee nankam yaji dadinta sosai dole yai mata siyayya sosai manyan kaya naji da fada












*fans kumin afwa yauba yawa wlh yau banajin dadi kawai dankar kujini shiru ne* _gobe xanmuku dayawa insha allah_ 😘






👉 *Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯














*5 star's ✨✨ online writer's association*👌








*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍














*•76/80•*


















Yana cikin saka botiran rigarshi tashigo, mayafin rigar ne tadauko batayi rolling ba tadai yafa akanta ne sannan ta jefa dayar jelar baya gashinta kuwa ummi tasaka mata ribon tadaure mata shi waje daya saitaqara kyau fuskar taqara fitowa das das,




Kai yaya haryanxu baka shiryaba? Tayi maganar cikeda shagwaba tana yanqwane fuska kamar xatayi kuka, hmmm aranshi yace wannan yarinyar akwai shagwaba


Rigar takama ta taimaka mishi wajan saka botir din na qasa, suka kammala suka fito tare ajere tamkar wata da xara, kana ganinsu kasan sun mutuqar dacewa da juna abinda haryau fahad yakasa fahimta kenan, haka suka keta gidan fadawa nata xubewa suna gaishesu harsuka isa inda ma,ajiyar motocin take, wata farar farado ya nufa dagudu fadawa biyu suka rugo suka bubbude bayan motar driver yashiga gaba gefenshi kuma wani bafare daya fahad yayi murmushi kuyi haquri nikadai xanfita nida qanwata




Dasauri sukafito sunafadin Allah yaba yarima haquri bamusani ba, adawo lfy yakarbi kakullin motar yashiga gaba itama yace tashigo gaban ba musu tashige ayau tanacikin farin ciki irin wanda bata iya kwatantashi jitake kamar su tabbata ahaka itada yayanta




Yatayar da motar suka fita fadawan na daga musu hannu dan ladi yakalli lawal yace kai amma wannan fateeman akwai kyakkyawa kuma wlh sun mutuqar dacewa da yarima inamadai............baiqarasaba lawal yace kai dan ladi akwai gulma ashedai kaima ka hango abinda na hango sukayi dariya suka tafa




Laxeera kuwa sakin labulen window tayi takoma kan gadonta taxauna xuciyarta namata tafasa kamar wuta aka rura acikinta, kasancewar daga inda taken tana kallon fitowar su yarima har sanda yasallami fadawa yashiga mota daga shi sai ita suka fita, to me hakan yake nufi? Kardai yarima son yarinyarnan yake? Taf him aiko daya sakata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login