Showing 45001 words to 48000 words out of 57158 words

Chapter 16 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt

07 Feb 2025

5528

muddin ta tambaya bai bata ba. Murmushi tayi musu kafin tace "Ku kwantar da hankalin Ku kukam Wlh da kanshi ya bani da hannun shi". Suka rike baki cike da mamaki suka ce amma ya akayi hakan? Hala dai Anty Lazeera bata gurin? Nan fa Fateema ta tintsire da datiya sai da tayi mai Isar ta sannan ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya musu, amma bata gaya musu batu na kissing d`inta da Yarima yayi ba. A ganinta da kuma tunaninta wannan iskanci ne sai dai ba yadda ta iya tunda halin shi ne haka, saboda son da take masa zata dinga rufa masa asiri na duk tabin da zai yi mata.




A Sokoto kuwa hankalin Iyayen Fa'eez ne a matukar tashe. Tsayayyen soja jarumi, wanda tun lokacin kuruciya ya taso da jarumtakar sa juriya da zurfin ciki. Amma sai gashi saboda yarinya d`aya ya rasa duk wad`annan Abubuwan. Tun daga lokacin da ya kira wayar Yaya Bashir, ya tabbatar masa cewa Fateema fa ta koma ma mijinta Yarima. To tun daga nan aka rasa kan sa, ya shiga damuwa da rud`u sosai, ba shikad`ai ba hadda Iayaye da kannen shi kai da duk wani makusancin sa




Yanzu ma kamar kullum zaune kawai yake kan kujera a falon d`akin shi. Yayi zuruu ya zurawa fankar dake ta faman juyi Ido kamar mai nazarin wani Abu gameda fankar. Momyn shi ta shigo da sallamar ta fuskar ta ba walwala, idonta akan fuskar d`an nata wanda bai ma san da shigowarta d`akin ba. Momy ta girgiza kai a lokacin da take zama kusa da shi idon ta fall da hawaye zuciyar ta cike da tausayin babban d`an nata. Tasaka hannu ta dafa kafad`ar shi a sanyaye ya d`ago da jajayen idon shi ya kalli mai dafa shi, ganin Mahaifiyar shi ce sai Ya koma sunkuyar da kanshi ba tareda yace komai ba sai wasu zafafan hawaye dayaji suna bin kuncin sa. Momy ta rungume shi a lokacin da kuka ya subuce mata. Cikin kukan ta fara magana "a'a son ba zai yiwu ba, sam bazan barka ka kashe kanka saboda mace ba. Ya kamata ka dawo hayyacin ka son, ka zama cikakken musulmi ka yarda da kaddara kayi imani wani ba zai Auri matar wani ba ka yarda Fateema ba rabonka bace"










*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍






*•263/264•*












Fa'eez ya fashe da kuka ya kankame Momy cikin yanayin sadakarwa ya fara magana "na hakura Momy, Wlh na hakura pls kar ki koma yin kuka kinji?" Ya fad`a yana share mata hawayen fuskar ta. Momy kuwa dad`i ne ya tirnike ta jin hakan daga bakin sa, ta raba jikin ta da nashi sannan ta zaro wani photon Kati ta Mika mishi. Ya karba Yana kallon photon da alamun tambaya a fuskar shi.




Tayi murmushi sannan tace "Sameera ce fa, baka gane ta bane?" Ta tambaya tana kallon fuskar shi. Ya Kara kallon photon da kyau sannan yai murmuhi yace "haba Ina kallon fuskar kamar na Santa, yarinyar ta bace min da gani, mortharn 5years." tace "eh kasan tana landan course din likita, kwanan nan ta dawo yau satin ta daya a garin" shiru ya ratsa d'akin na d'an lokaci Sameera yar'kanwar momyn shi ce duk a sokoto suke, satin ta d'aya da dawowa daga London inda ta dawo a matsayin cikakkiyar likita. Ya sake kallon ta yace "to Momy photon fa" tace "na kawo ka duba ne kafin kaje ku gana, nida hajja mun yi shawara akan had'a ku aure kai da Sameera". Ta takaita maganar tana kallon shi domin ta ga wane irin karba yayiwa maganar?. Ga mamakin ta sai taga yayi murmushi Yana sake kallon photon yace "duk yanda kuka yi da mu yayi Momy na, Ina son Sameera and nasan itama zata soni Allah yayi mana jagora" cikeda farin ciki Momy ta rungume shi "na gode yarona nagode Allah ya yi maka albarka" ta sumbaci goshin shi ta fice zuciyar ta fall da farin ciki.


acikin satin aka shirya komai kasancewar duka su biyun sun amince, da sati ya zagayo kuma aka d'aura aure masha Allah ansha biki abin Sai wanda ya gani Auren Soja da likita, abin Dai gwanin sha'awa a cikin abinda baifi wata d'aya ba Fa'eez ya fara saituwa kasancewar Sameera wayayya Mai ilmin boko dana addini ta iya tafiyar da namiji, cikin kankanin lokaci ta goge tabon da soyayyar Fateema tayi a zuciyar shi ta maye gurbin da d'inbin kaunar ta tuni yayi watsi da soyayyar Fateema ya rungumi ta matar da Allah ya kadarta Ita ce rabon sa, ya yarda da kaddara kuma ya karbe ta hannu bibbiyu. Sai Dai ya kudirta a ransa zasu cigaba da zumunci da dangin Fateema.




*Garin Gombe* Yarima ne kwance bisa lafiyayyen gadon shi, Sai sheka bacci yake cikin kwanciyar hankali a zahiri amma a bad'ini mafarke-mafarke ne yake tayi akan zaman takewar shi da matan shi duk wani wulakanci da tozarcin da yayiwa Fateema sai da ya gansu. Bangare d'aya kuma bautar dashi da Lazy tayi ita da mahaifiyar ta da Umman shi, har ma da dawowar Fateema gidan shi Sai da yazo inda ya bata kud'in nan ta fita da gudu yai firgigit! Ya farka Yana fitar da numfashi Mai sauti "Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'un" ya shiga Karantowa Yana waige-waige ba makawa tunnin Fahad ya dawo babu abinda bai tuna ba hatta fitar mahaifiyar shi daga gidan da kuma tafiyar Lazeera. Godiya ya yiwa Allah daya kasance ita Fateema tana gidan, da sauri ya mike ko brush baiyyiba ya nufi sashen Fateema. baiga kowa a falon ba, hakan ya bashi damar wucewa kaitsaye izuwa d'akin baccin ta.


Kwance ya sameta tayi share-share a kan gadon ta, baccin ta take cikin nutsuwa fuskar nan ta'ta kamar tana murmushi wani irin dad'i ne yaji Yana sakkowa tun daga ko'kon kansa har izuwa tafin kafar sa. Cikin gaggawa ya zube kasa a inda yake ya fuskanci alkibla yakai goshin shi kasa yai sujjada inda ya dinga kwararowa Allah (s.w.a) Yabo yana jinjina da kirari Yana Kiran sunayen sa tsarka'ka Yana gode mishi godiya marar adadi, ya rufe da salatin mazon Allah (s.a.w)


ya mike jikin shi har bari yake yi ya Isa gaban ta ya gurfane bisa guiwoyin sa ya zubawa kyakkyawar fuskar ta ido, a ransa Yana dad'a godewa Allah bisa wannan babban rabon da yayi masa na dawo mishi da Fateema wadda a kullam yakejin kanshi incomplete saboda rashin ta a kusa dashi Sai dai bashida damar tunawa ko kuma yin wani katabus na neman ta. ya d'an rankwafa fuskarshi ta dawo daf da ta'ta su na iya jin numfashin junan su Yana shirin Kai Mata sunbata tai firgigit ta farka daga baccin da take, ganin sa yasa tayi baya da sauri, nan fa suka shiga kallon-kallo da ita da shi.












*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍




265/266










Cikin in Ina tace "Yaya lafiya?" Ya kalle ta da wani irin kallo Mai d'auke da sakonnin da shi kanshi bai san adadin su ba, "barka da safiya My Princesses" ya fad'a da wata iriyar murya kamar mai yin rad'a. sai da ta d'an harare shi ta kasan ido sannan tace cikin karamar murya "yau kuma? Ko dai batan kai Yayana yayi yau?" maganar yarinyar ta ratsa shi, musamman da ya tuna irin zaman da ya yi da ita tun lokacin da ya aure ta. "a'a Fateen gwaggo, karki soma, pls kizama mai yafiya na roke ki." yayi folding hannayen shi yana kallon fuskar ta, Fateema tayi shiru tana kallon yanayin Prince. tabbas yayi laushi sosai alamu da yawa sun nuna da gaske yake yayi nadama sai dai a ganin ta ba cikin sauki haka ya kamata ta karbe shi ba, ya zama dole ya karbi hukunci. Duk da tana son Yarima hakan bazai hana ta ganar da shi yayi kuskure ba, duk kuwa da cewa ba a hayyacin shi ya aikata ba. Duk wannan dogon tunani da take *Yaya Fahad* yana nan gurfane a gaban ta, yayin da idon shi ya ciko tam da hawaye, yana jiran jin hukuncin da zata yanke masa. "pls Fateema" ya sake fad'a a mutukar sanyaye kamar mai shirin fashewa da kuka. tamkar wadda aka tsikara haka tayi tsalle daga kan gadon ta nufi kofa da gudu tana waiwayen sa. Yarima ya bita da kallon mamaki sam bai san lokacin da Fateema ta cika ta zama babbar budurwa haka ba, kayan bacci ne a jikin ta, rigar iya guiwa mai had'e da gajeren wando sun amshi jikin ta sosai fatar nan ta'ta tayi shar ga laushi ga alamun santsi kamar ta jinjirai tana gudu sassan jikin ta na motsawa tuni ta fice ta rufo mishi kofar amma idon shi na nan kyam akan kofar siffar ta da halittun jikin ta nayi masa yawo a kwakwalwa "huhhhh" ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jiki ba kwari ya mike ya ja kafa dakyar ya nufi d'akin shi dake cikin sashen nata, wanda rabonshi da ya shiga cikin sa tun lokacin da Lazeera tana bangaren. Amma ga mamakin sa sai ya tarar da d'akin fess da shi sai tashin kamshin kalolin tiraruka da yake yi, ya ja numfashi ya fitar cike da shauki. a ran shi yana tuna lokacin da Lazy take sashen, sam d'akin baya samun gyara haka. Ga wannan da ko shigo mata baya yi hakan baisa tayi wasa da gyara muhallin sa ba. "Allah ya albarkace ki Fateema" ya fad'a yana shafa kirjin shi wanda yake ji kamar a cikin sa Fateeman take. Ya nufi toilet zuciyar shi na dad'a yin nitso a soyayyar Fateema




ita kuwa tana fita daga d'akin ta shige d'aya d'akin ta saka key, ta shige toilet tayi wanka ta fito ta saka wata doguwar riga ash colour bata tsaya komai ba sai da ta fara gabatar da salla, sannan ta d'an gyara fuskar ta ta zaro wani karamin mayafi black ta d'ora ta fita kitchen dan sama ma cikin ta abinci. Ta samu an gama kammala komai suna ko'karin fita dasu zuwa danning ta tsayar dasu ta d'ebi iya abinda zata iya ci da drinks a babban tire ta nufi d'akin da take. Mintuna kad'an Yarima Fahad ya fito cikin shigarshi ta ya'yan sarakai fuskar nan tashi ba walwala ya nufi d'akin Fateema. Ganin bata d'akin yasa ya nufi d'aya d'akin da yake kyautata zaton can ta shiga da kuzarin sa ya tura kofar amma sai yaji ta a datse gam.




"Fateema" ya kira sunan ta a sanyaye hannun shi na rike da handle na kofar. "Fateema dan Allah kiyi hakuri ki saurare ni kinji, wlh nayi nadama Teema ina son ki, ina kaunar ki Fateema." ya saurara da maganar yana tunani ko zatayi magana amma shiru, ya kai mintuna goma tsaye a gurin amma ba ko alamar motsin Fateema. wadda yayi imanin cewa tana jin shi. Sosai yaso ya ganta amma ya zayyi? dole yaja sanyayyin kafafun sa ya fita ko breakfast bai tsaya yi ba ji kawai yayi yau ya tashi da matukar kewar mahaifiyar shi kuma kai tsaye gidan su ya nufa inda take. Umman tana zaune a falon kasa as usual hanunta rike da carbi tana ta yin lazimi, istigfari da hailala. sai ganin su tayi sun shigo a rikice ko sallama babu suka haye saman benen inda d'akunan baccin su suke. kallon mamaki ta bi bayan su dashi a ranta tana jinjina cewa duk abinda ya koro su haka mai girma ne, Wato Lazera da momyn ta. Tana cikin saka da warwara taji dukkanin su suna zunduma ihu sun nufo kasan a kid'ime, ta mike da nufin hawa saman domin ihun da suke bana wasa bane. a up tiers d'in suka had'u da har ta bud'i baki zata tambaye su lafiya suke wannan ihun haka? amma ina a bakinta kalmomin suka makale saboda ganin abinda ke faruwa a saman. gobara ce gagaruma ta taso wacce ta kama dukkan d'akunan bacci hud'u dake saman. rigegeniyar sakkowa sukayi dukkanin su a matukar tsorace suka nufi farfajiyar gidan suna kururuwar neman agaji direba da mai gadin gidan sune sukayi ta maza suka kira ofishin hukumar kashe gobara. domin duka matan ba wadda keda tunanin yin hakan Lazy da Momyn ta sai kuka suke suna ihun kiran duka dukiyar su ta kone domin wutar ci take tamkar ana bulbula mata fetir, haka tayi ta cin kayan dake d'akunan har zuwa lokacin da masu kashe wutar suka karaso, suka fara gudanar da aikin su an sami nasarar kashe gobarar ba tare da ta sakko kasan ba, sai dai a saman kam ta gama lashe komai ko tsinke bata rage musu ba. ganin hakan ya sanya Momyn Lazy kifewa a gurin tana borin hauka had'e da sambatu marar kan gado. A haka Yarima ya same su cirko-cirko a tsakiyar gidan kowa ya watse sai su kad'ai Momyn na ta zuba sambatu Lazy na ta faman kuka tana rarrashin ta Umma na daga gefe tana kallon ikon mabuwayi al'ajabin duniya ya cikata. shuru Yarima yayi daga inda yake yana sauraren maganganun dake fita daga bakin Momyn Lazy wayanda da yawan su duk akan cutar da sukayiwa shi Yariman da Fateema ne, Umma ma ido ta zuba mata domin wasu abubuwan bama da sanin ta ake yin su ba.












*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍








267/268







Jiki a sanyaye ya fito daga motar ya nufo inda suke, ganin shi ya basu mamaki dan ba wanda yasan da zuwan na shi.
Momy na ganin shi ta fisge jikin ta daga cikin na Lazeera ta isa gaban shi ta tsuguna bisa guiwoyin ta duka biyun tana shirin kama kafafun shi, ya d'an ja da baya yana mata kallo irin na tsana da ala'wadai.




Cikin kuka mai sauti ta fara magana "Fahad dan Allah kayi hakuri ka gafarce ni nayi kuskure d'ana wlh nayi nadama ka ceceni yace bazai barmu ba, gashi nan ya fara aibata ni ya saka min wuta a gaban idona ya kona min komai". Ta fashe da kuka mai tsanani "shikenan yanzu banida komai na rasa komai sai rayuwa, na shiga uku gashi yazo nan ma" ta fad'a tana nuna gefen ta da yatsa cikin yanayin tsoro, ta mike tsaye tana ihun wai ga aljanin nan yazo zai kashe ta tanayi tana neman mafaka. Lazeera ce tabi bayan ta cikin kuka ta riko ta tana lallabata, tun daga nan al'amarin ta ya dawo kamar hauka koda yaushe cikin sambatu take abu dai kamar ciwon hauka. Allah ya kyauta haka Fahad yace ya kad'e rigar shi ya isa ga mahaifiyar shi wadda tsananin kunyar shi da dana sanin abinda ta aikata suka lullube ta, ta kasa motsawa daga inda take. hawaye na bin kumatun ta tausayin kan ta ya kara kamata lokacin da ta koma kallon inda yayar ta'ta take, a ran ta tace yanzu da ita ce a wannan matsayin ya zata yi?,




godiya tayiwa Allah daya ceto ta kuma ya kare ta daga sharrin su. A fili tace "ya Allah ka kutubar da matan musulmi da suka raja'a da bin bokaye da malaman tsibbo, Allah ka ganar da su sudawo bisa hanyar gaskiya, haki'ka duk wani abin da zaka nema agurin wanin da ba Allah ba to kuskure ne babba" wannan gaskiya ne (Muyi tunani mai zurfi mu dawo hayyacin mu mata, Allah (s.w.a) shine yafi can-canta da mu kai kukan mu gareshi a duk lokacin da muke da bukata mu sanar mishi, mu roke shi shine mai bayarwa, kuma shine mai hanawa. Kisani yake yar'uwa mace zuwa wajen wani boka ko malami neman wata bukata la'lata imani ne. Kuma koman daren dad'ewa karshen ta bazai zamo mai kyau a gareki ba. Allah ya ganar damu baki d'aya). Taku uku Yarima ya kara ya isa gaban Umman shi wadda ta sunkuyar da kanta kasa saboda kunyar abin. "Umma" ya kira ta cikin sanyaya murya sannan ya tsuguna a gaban ta, daga aljihun shi ya ciro wani lallausan handkacip fari mai kamshi ya fara share mata hawayen dake fuskar ta zuciyar shi fall da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login