Showing 51001 words to 54000 words out of 57158 words

Chapter 18 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt

07 Feb 2025

5532

hannayen ta duka biyun ta mika mishi ya rika su cike da farin ciki ta jashi izuwa kan kujerar daf da ita ya zauna idanuwan shi akan fuskar ta. murmushinnan nata ta koma yi mishi hannayen ta na rike a cikin nashi idon su na sarke suna yiwa junan su wani kallo tace "Yaya Fahad a yau kuma a wannan ranar nake yimaka albishir cewa duk wani shirme ya kare, ni Fateema har yau ina son ka kuma zan ci gaba da son ka har izuwa karshen numfashi na, ina son ka yaya na" ta karashe zancen da lumshe ido hawaye suka gangaro daga idon nata da sauri Yarima Fahad yakai harshen sa kan kumatun ta ya lashe hawayen nan tas batare da yabari ko d'aya ya sauka a kasa ba.




"Na gode miki Fateema, na kuma godewa Allah daya nuna min wannan rana. Allah ya albarkaci rayuwar mu kuma ya bamu zuriya ta gari". Fateema kam har zuwa lokacin idon ta rufe suke gam tana jin kanta Kamar yau ta fara rayuwa a duniya. hakan ya bawa Yarima damar manna bakinshi a nata yana tsutsar leben ta ahankali ji yake kamar yana shan wata madara wadda bai taba jin mai d'and'anon ta ba lokaci mai tsayi suka d'auka a hakan kafin ya d'auketa cancas ya shige d'akin shi da ita. Suka zube kan lafiyayyen gadon shi Yarima ya shiga wasanni da sassan jikin Fateema wadda ta kwanta lif ajikin na shi ko motsin kirki batayi sam bata hanashi abinda yake yi ba sai ma ta tsinci kanta da jin dad'in yanayin da suke cikin




A kunnen ta ya dinga rad'a mata wasu dad'ad'an kalamai na soyayya wayanda ko a mafarki bata taba kawowa zataji su daga bakin Yaya Fahad ba, hakan ya zaburar da ita batasan lokacinda ta shiga mayar mishi da martanin kalaman nashi ba a ranar dai haka suka kwana cikin farin ciki da faran tawa juna, duk da cewa babu wani abu daya shiga tsakanin su amma fa sun shayar da junan su madarar So da kauna washe gari da safe haka suka tashi cikin fari ciki sai tarairayar junan su suke abin dai gwanin birgewa. haka sukayi shirin zuwa kukunba karfe goma na safiyar Mai martaba ya aiko yace su fito Masha Allah haka kowa yake cewa lokacinda suka ratsa tsakar gidan sarautar Yarima da Gimbiyar shi sun sha kyau kamar yau suka fara yin ado da kayan sarauta. Suka shiga sashen iyayen nasu inda suka tarar da Mai martaba da Umma cikin shiri da ado na kasaita. Suka zube suka gaida iyayen suka amsa cikin farin ciki suka sakawa yaran albarka sannan suka mike suka shige gaba yaran na take musu baya suka nufi farfajiyar gidan inda motoci suke a fake an riga an gama shirya komai.










*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍








*273/274*










Masha Allah abinda kowane bafade ke fad'a kenan tun bayan auren Yarima basu taba fita irin wannan ba. kana'nan motoci guda biyar ne aka shirya domin tafiyar. d'aya ta Yarima da Matar shi, d'aya kuma ta Mai martaba da Umma. Ukun kuma na security da fadawa ne sannan aka tanadi hillous guda biyu wayanda aka cika su da kayan tsaraba tun daga kan kayan abinci har izuwa kayan sakawa turamen zannuwa da shaddodi da yaduka. bayan duka sun shiga motocin aka tayar suka fara tafiya. Fateema ta kalli mijin ta wanda tunda suka shiga motar bai d'auke idon shi daga kallon ta ba. "to kallon fa?" Ta fad'a Tana kallon shi, Yarima Fahad ya saki lallausan murmushin nan nashi tsadadde ya janyo Fateema zuwa jikin shi yai mata kyakkyawan mazauni a kirjin shi. "Ina kaunar ki Fateema, dan Allah ki daure kiyimin matsuguni a zuciyar ki, ki so ni Fateema, dan Allah ki kaunace ni." mamaki ya cika Fateema jin saukar hawayen Yarima bisa kumatun ta. da sauri ta tashi ta zauna da kyau Tana kallon shi tabbas kuka yake Innalillahi.




Hannayen ta ta saka ta tallafe kumatun sa "Haba Yaya na, meyasa zaka yimin asarar hawayen ka akan abinda kake da tabbacin ka samu? Yaya, na so ka tun bansan miye so ba, na kaunace ka tun bansan kaina ba, to meyasa zan ki ka yanzu da na mallaki hankali na? na tabbatar zuciya ta bazata taba aikata wannan kuskuren ba" ta rungume mijin ta Tana share mishi hawaye dad'i da farin ciki suka lullube Yarima "cikin farin ciki yace "na gode Fateema nayi miki alkawarin zama bawa gare ki a wannan rayuwar, na zama rakumi kuma na hannunta miki akalar Fateema *ni naki ne* , ki taimake ni ki cigaba da kasancewa kusa dani kamar haka. dan Allah kar ki koma yin nisa dani kinji" "bazan koma barinka ba *Yaya Fahad* Ina son ka" suka koma rungume juna kowannen su najin dad'in sabuwar rayuwa da sabon yanayi na kusanci da suka tsinci kan su a ciki dai-dai nan suka ji motar ta tsaya ya d'aga ta daga jikin shi sannan ya karbi jakar ta ya ciro bandir-bandir na kud'i guda biyar ya zuba Mata a jakar ta, ga wannan ki rabawa mutanen kukunba Ki tabbatar musu yanzu ke gimbiya ce Matar Yariman Gombe, sauran kayan tsarabar suna mota anjima za'a fito dasu" hawaye ne suka ciko idon Fateema "na gode yaya na, ubangiji Allah ya bani ikon binka in maka biyayya kamar yanda addini ya tanada" ya share Mata hawaye kiyi farin ciki Fateema, ni naki ne har abada" shine ya fara bud'e motar ya fito lokacin ne wani security yazo da sauri zai bud'e gefen da Fateema take Yarima yayi gaggawar d'aga masa hannu, mutumin ya koma baya Prince ya taka da kanshi ya bud'ewa gimbiyar shi ta fito.




Sai a lokacin ta fara karewa kauyen nasu da kofar gidan su kallo Mai martaba ma tsaye yayi kamar wani bako Yana kallon gidan d'an'uwan nasa. Sauye-sauye kam kauye ya samu sannan gidan su Fateema an canza mishi gini daga yanda yake da zuwa katafaren gida Mai zagaye da fulawoyi hadda gate d'in mota. Ga manyan shaguna guda biyu a gefe, inda suka hangi yaya Bashir Yana fitowa daga cikin su ya nufo su da saurin shi ya tsuguna Yana gaida Mai martaba. daga cikin gidan kuma Baffa ne ya fito Yana lale marhabi da zuwan su. Farin ciki Mara misaltuwa ya lullube Fateema. da hanzarin ta ta Isa inda suke ta tsuguna har kasa ta gaida Baffa da yaya Bashir suka kalle ta cike da kulawa suka amsa Baffa ya kalli Mai martaba cikin harshen fulatanci yace "yaya yar'ka fa ta girma da alama ta nusu, yau Fateema a kukunba duk dad'ewar nan ba ihu ba tsalle?" dukkan su sukayi dariya har ita d'in hakan yayi dai-dai da isowar Yarima inda suke, ya tsuguna gaban Baffa ya gaishe shi ya amsa cikeda kulawa Yana tambayar shi "yaya hanya" yace Alhamdulillah" Mai martaba ya kalli Baffa "d'an'uwa wannan sauyin gida haka ba sanarwa?" Baffa yayi dariyar su ta manya yace "hana ni akayi yaya, aikin Yarima ne, duk shi yayi komai kuma yace kar in sanar maka Wai duk randa kazo zaka gani" sosai Mai martaba yaji dad'in lamarin domin hakan ya kara tabbatar mishi yaro ya dawo hayyacin sa, Kuma ya d'auki Matar shi da daraja. Umma da Baffa suka gaisa sannan suka d'unguma zuwa cikin gidan inda suka tarar da kyakkyawar tarba daga Goggo tsabagen murna da farin ciki tarasa inda zata saka Fateema taji dad'in yanda ta ganta yarinya tayi jajur da ita ga yadda jikin ta yayi kyau ko manafuki ya kalle ta yasan tana cikin kwanciyar hankali. aka gabatar musu da kayan abinci kala-Kala dad'i da farin ciki sun cike zuciyar Fateema soyayyar mijinta ta dad'a ninkuwa a zuciyar ta gidan su yayi matukar kyau ciki da waje kamar tana cikin Masarauta haka take ji.




An dad'a yawan d'akuna a gidan an zuba masu taya Goggo aiki yan'mata guda biyu an kafa fanfuna da ababen more rayuwa a kowane lungu da sako na gidan ....












*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍










*275/276*










A babban falon gidan aka sauke su inda suka ci mai dad'i suka sha mai dad'i, a nan ma Fateema ta gano cimakar gidan su ma ta canza, an Sami ci gaba sosai. Bayan sun kammala cin abinci da gaishe-gaishe ne Umman Yarima ta fara rokon gafarar iyayen Fateema tana dad'a basu hakuri akan abinda ya faru a baya. Suka ce ai komai ya riga ya wuce, baya-baya ce yanzu kam Sai dai a fuskanci gaba. Taji dad'i sosai Sai jan Goggo a jiki take ita kuma ba saban ba har yanzu d'ari-d'ari take da ita Yarima Sai kallon Fateema yake ta koma can nesa dashi ta zauna ta d'ora kanta a cinyar Goggo. Sai yaji Ina ma a cinyar shi ta kwanta ya shiga ayyana yanda zai ji. Su Baffa da Mai martaba suka mike suka koma d'akin ajiye baki na kofar gida Wanda shima yanzu an kawata shi da lundum-lunduman kujeru da Kayan kawata falo irin na manyan mutane. d'akin ya rage saura Goggo da Umma, Yarima da Fateema Dan Yaya Bashir kam tun d'azu aka Kira shi waje za'a sayi Abu a shago yanzu ya zama d'an kasuwa domin shi Yarima ya ginawa shagunan kuma ya cika mishi su da Kayan business na bukatun al'umma.




Yarima ya mike Yana sosa keya yace "Ina son zaga garin nan gashi bansan ko Ina ba, ga yaya na kuma shago ya rike shi". Iyayen sukayi dariya Umma tace "to ai ga Matar ka nan, Sai ka sakata gaba ku tafi" Fateema kamar jira take tayi zumbur ta mike tsaye "yawwa yaya muje, kaga daga can sai ka cika min alkawari na ko?" "haka ne fa" ya fad'a Yana fita daga d'akin ta bi shi a baya. Iyayen suka girgiza Kai suna murmushi cike da Jin dad'in yanda yaran suke tafiyar da rayuwar su. dai-dai kofar gidan sukayi karo da Innawuro (kawar Fateema) da gudun ta tazo kamar zata tashi sama, tana ganin Fateema ta kankameta sam bata damu da Wanda ke gefen ta ba. Itama ihun murna ta saki suka rungume juna cike da murnar sake had'uwa Yarima kam gefe ya matsa Yana kallon yaranta. Suka saki juna Innawuro tace "Kai Fatee kin ganki kuwa?, ya Salam!,wayyo Allah Fateema wlh kinyi kyau kamar ba ke ba. Wayyo Fatee na" ta koma rungume ta. Fateema tace "kedai bari yanzun ma ta gidan ku naso biyowa in mun dawo, fita zamuyi da yaya" ta fad'a tana kallon inda yake.




Sai a lokacin ta lura da Yana wajan ta rusina ta gaishe shi ya amsa da fara'a yace "Ki shiga ciki yanzu zamu dawo" "to" tace ta shige ciki tana cewa Faeema "kar fa ku dad'e Adda tana jira na a gida" "kekam Ki shiga ciki yanxu zamu dawo" ceear Fateema tana washe baki yau dai kam farin cikin ta ya kasa boyuwa dad'i takeji sosai a ran ta. suka fice ita da Yarima a jere suka ratsa garin kukunba duk inda suka bi sai a bi su da kallo samari da yammata duk Wanda ta sani idan ta ganshi sai ta tsaya sun gaisa ta bud'e jaka ta ciro kud'i masu yawa ta basu. da haka har suka Isa dai-dai wurin da Yarima ya mare ta taja ta tsaya cak "yaya a nan ne fa" ta fad'a tana kallon shi Sai a lokacin ta lura da canjin da fuskar shi tayi kamar ran shi ya baci maimakon ta damu sai ta fashe da dariya




"kaga yaya da wayau,borin kunya da wayau zaka yi min? Allah ni fushin ka bazai hana ni rama mari na ba". da karfi ya fisgo ta, ta fad'a jikin shi yayi amfani da d'aya hannun shi ya matse bakin ta sai da taji zafi batasan sanda ta saki Kara ba "kaga mugu wani ma zaka dad'a akan wancan? Allah shima Sai na rama" cikin bacin rai ya fara magana "ban damu ba kiyi ta mari na Fateema, amma Sam bazan lamunci ganin kina gaisawa da katti kamar haka ba, shin kin manta da matsayin Ki ne? Kefa Matar aure ce kuma gimbiya Matar d'an sarki ya kamata Ki kula kusan mutuwa nayi lokacin da kike musu murmushin nan" mamaki ya mamaye Fateema lallai ma Yarima wato abinda ya bata mishi kenan tayi rau-rau da ido sai hawaye shar akan fuskar ta da sauri ya sassauta Mata rikon da yayi Mata "meye abin kuka kuma Fateema?, no pls ya Isa haka kiyi hakuri amma Ki dinga tausaya min kinji mata'ta" ta gyad'a Kai tareda cewa "to" ya raba jikin shi da nata suka fuskanci juna yace "gani gaban Ki kuma na baki dama ki rama marin da nayi Miki Fateema" tayi murmushi lokacin da ta d'ora tafin hannun ta bisa lallausar fatar fuskar shi "bazan taba iya marinka ba Yaya na, ka sani na kawo ka nan ne domin ka tuna ranar da na fara furta maka so da kuma tsayin lokacin, Yaya ba ranar na fara son ka ba, na so ka tun banida wayau da wannan nake tabbatar maka bazan taba barin son ka ba" ba karamin dad'i kalaman Fateema suka yi mishi ba ya kasa cewa komai sai dai janta da ya koma yi ya manne ta da kirjin shi "na gode Fateema da wannan nake Kara tabbatar Miki ni *Fahad naki ne* ciki da waje kin kulle ko Ina kanwata"




lokaci Mai tsayi suka d'auka a hakan kafin ta raba jikin ta da na shi ta rike hannun shi suka kama hanyar gida zuwa lokacin gabad'aya garin ya d'auka sarki yazo gida da shi da iyalan sa, hakan yasa Mai gari da mutanen garin fitowa domin kawo gaisuwa ga Mai martaba sarkin gombe. An rarraba tsaraba sosai ga yan'uwa da makota harma da mutanen garin sannan aka cika store na gidan fall da kayan abinci Fateema ta bawa Innawuro kaya niki-niki da nata da na Umman ta da kuma na sauran kawayen su sannan ta kara musu da kud'i. Suka yi ta godiya sukayi sallama. Bayan ta gama rabe-raben ne ta kirga ragowar kud'in dubu d'ari uku da arba'in duka ta bawa Goggo su tace ta ajiye ita ma ta fara wata sana'a Uwar tayi ta godiya da d'inbin alkhairi domin nata manyan turamen zannuwa ma daban aka kebe Mata su.




Karfe biyar suka yi sallama da kowa suka kama hanyar gombe zukatan Su cike da farin ciki. Tun a mota Fateema ta fara yiwa Yarima godiya akan irin gyaran da yayi wa gidan Su ya rufe Mata baki Yana fad'in "karki d'auki abin da banbanci Fateema, Ki tuna matsayin Baffa gareni ya fi karfin wannan a gurina. a shekarar nan ma duk tare da Su zamuje aikin hajji insha Allah" ta kwantar da kanta bisa gefen kafad'ar shi a hankali tace "ka tare ko Ina da ko Ina yaya na, Ina kaunar ka" yayi murmushi ya shafi fuskar ta "nagode Teema na" lokacin da suka iso fada magariba ta kawo Kai shiyasa Yarima da Mai martaba suka nufi masallacin fada, tareda mutanen da suka tarbe Su. Fateema da Umma ko cikin gidan suka wuce inda suka yi Sai da safe kowacce ta nufi sashen ta














*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍












*277,278*










Yau kam gaba d'aya rayuwar Fateema fess take, ji take kamar ma bata taba jin farin ciki kamar na yau ba kamar yadda take jin soyayyar mijin ta na tafasa a zuciya da sassan jikin ta kamar dai wannan shine farkon soyayyar inji (Nasmt 😉) da shigar ta d'akin ta rage Kayan jikin ta ta shige toilet tayi wanka da had'in turarukan ta sannan ta d'auro alwala tazo ta fara gabatar da salla bayan ta d'auki lokaci Mai tsawo tana roka musu zaman lafiya da kwanciyar hankali ita da mijin ta tare da neman kariyar Allah akan duk wani Mai nufin Su da sharri. Ta mike ta zauna gaban madubi cikin kankanin lokaci ta rangad'a kwalli fuskar nan tayi shar da ita, kyawun ta da kuruciyar ta suka Kara bayyana a lokacin da ta d'auko wata doguwar Riga ta roba ta saka rigar yar ficik ce mara nauyi irin Masu bin jikin mutum d'innan, tayi wa gashin kanta wani style a gaban sannan ta zubo ragowar baya sai ka rantse baindaya ce.




Kasancewar yanzu Fateema take tasowa gabad'aya albarkatun jikin ta sun cike kyakkyawar surar ta Mai fizgar imanin duk wani cikakken namiji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login