Showing 18001 words to 21000 words out of 57158 words
Chapter 7 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt
tunaninta da saninshi akayi auren kasancewar tagani da idonta yanda yake bawa yarinyar kulawa a gida
Xaune yake a farfajiyar filin gidan nashi bisa wata lallausar center carpet, kalolin lemuka kusan biyar ne a gabanshi saidai yakasa shan ko daya ya qurawa kyawawan furannin dake xagaye dashi ido kaman mai naxarin fulawa
Ahankali naga ya matse ido π³ fans kunsan me? Qwalla nagani tam a idon yarima kafin ingama tsinkewa saigasu yana matsowa wasu saunabin wasu hawaye sharr kamar wani qaramin yaro abinda baitabayi da wayanshiba, duk kuwa yanda ranshi yakai maqura da baci baya yin kuka yau gashi yanayi a inda bashida mai share mishisu, wai akan mace kacenma qanwarshi fateema yaqara matso ragowar hawayen abin tausayi
Ahankali ya kai hannunshi kan wayarshi dake ajiye agefe number mai martaba yayi dialing kai tsaye yaukam ba kodar a xuciyar sa tariga ta dake bashida sauran haquri ko kadan duk yagama qarewa
Ringing biyu ana uku aka daga wayar..........................................
*Nasmy ce*π
Yar mutan arkilla love you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*5 star's β¨β¨ online writer's association*π
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’121/125β’*
Sai qanwar goggo dake riqeda hannun ta, Fateema sai kuka take tana waiwayen qofar gidansu yaya bashir taga yana mata murmushi yashiga gabaj motar dake gaban tasu, suma suka shisshiga nandanan xugar motocin suka dauki hanyar gombe
Qarfe biyar daidai suka isa gombe fadar tacika tinjim irin cikarda ta dade basuyi ba, wani sashe na musamman aka xarce da fateema wanda yasha gyara da tsari irinnan qasashe waje, kowa ka kalla makaki ne xaka gani qara a fuskarshi cikin wayanda suka kawo amaryar saboda irin tsarin gidan fatee nimadai nace tubar kalla
Har quryar daki muka raka amarya aka xaunarda ita bakin narkeken gadonta wanda duk mai kartaba ne yayi matasu, sashen cike yake da bayi kota ina sune suketa hidima da mutane, dattijawan dasuka kawo fateema sunyi mamakin bakowa acikin dangin mahaifiyar yarima bawanda yaxo yataresu koyayi musu maraba haka suka daure suka dauki fateema da taimakon wasu kuyangi biyu suka gane sashen mahaifiyar tashi suka gaisheta haka ta amsa ba yabo ba fallasa suka gabatar mata da yarta akaryar danta dan kar afahimci yanda tadauki lamarin saita janyo fateema jikinta tace fateema ai gida kuka kawota nan dacan duk daya ne ba banbanci Allah dai yabasu xama lfy suka ce ameen suka ja hannunta suka ooma sashenta da ita kasancewar mai martaba yana fada
Tsakanin gidan fateema dana iyayen yarima tafiyace mai dan tsayi drivers dinda sukawo yan kai amarya suka turo mutanen sufito amaidasu dan kar,suyi tafiyar dare haka duk manyan matan suka tafi suna qara yiwa faeema nasiha tareda jadda da mata tayi babban dace da auren yarima nan akabar qawaten ta duka sabida ansanar musu da akwai deenar qarfe shida
Shiru yaratsa dakin nayan daqiqu qawayen fateema na kukunba sun baxama cikin gidan wajan bawa idonsu abinci wato kalle2 na tsare2 gidan wasu har kitchen wasu bandaki wasu kuma danqaramin lambun dake gidan suka nufa
Innawuro ce kadai take xaune da fateema tana bata baki dan har yanxu. Kukaj takeyi sanannin kuyanginta ne su ummi sukashigo da sallamarsu suka xube a gaban fateema suka gaisheta cikeda biyayya sannan sukace ranki yadade uwar dakinmu daga yau mune amintattu kuma bayi mafi kusanci gareki wayanda xasu ringa bawa qananan bayi masu kulada bangaren nan umarnin aiki dakuma isar da saqonninki aduk sanda kika buqaci hakan ahankali tadago ta kallesu saitaji tana murmushi kai kawai ta gyada musu dan muryarta tagama disashewa
Dayar tace Allah yataimakeki yanxunka ance mugyara miki adonki sbd lokacin fita deenar yakusanto dagama fadar hakan dayar tamiqe tasga toilet dinda ke dakin ruwan wanka ta hada mata tareda turarukan qamshi nawanka tafito nahada ruwan wankan anty ba musu fateema tamiqe ahankali ta taka tashiga yauten duk wani iri takejin kanta tarasama tunanin daxatayi gameda rayuwarta da auren yarima
Itako innawuro kallon sha,awa tabita dashi aranta tace dama nice, Allah yasakamu a danshinki qawata kekam tauraron rayuwarki mai haskene
Mintuna kadan fateema ta fito nandanan suka shigoda wasu bayi guda biyu,sukuma aikinsu kenan yakata kwalliya qwararri ne awannan fannin nandanan kuwa suka kama aikinsu
Qarfe biyarda rabi girginsu Prince yayi landing a gombe state international airport, shikanshi saida yayi makakin irin tarbar daya samu ta musamman wadda kusanma xai iya cewa baitaba samun irinta ba, kusan mota biyar dasukaxo tariyarshi duka sababbine fil kowacce daukeda sunan masarautar gombe an daddaura musu balons sai qyalli suke ga manyan abokanshi wayanda yasan ko waya bayyi yasanar musuda xuwan nashiba tunda shima baxata ne akq kirashi amma saigasu dayawansu sunxo tarbonshi hakadai sukayita bashi hannu sunacewa congrats aboki yadai daure yashiga motar da sadiq yake ciki suka tafi
Baiqara tsinkewa ba saida akafara shiga masarauta yaga ko ina anyi sabin pentee ga gyara na musamman da ko,ina yasha kuma daxuwa abokan nash suka jashi xuwa sashenshi wanda yaga ko ina nagidan ansauya tsari da furniture's daxuwa sukace yayi wanka mai martabq yakirasu yasanar musu inya iso yashirya dakyau xasuje neman aure
Nandanan yarima yaqara washewa yafada wanka yasan kukunba xasu tafi dafitowarshi yafara shiri agurguje Sam baidamu da gajiyar dayake tattare da itaba wasu skayblue suit suka dauko mishi yasaka aka saka mishi net da safa da shoes nandanan yafito real Prince gashinan aka tajeshi yakwanta su sadiq sai tsiya suke masa suka fita
Yawan jerin motocin dayagani yadan tsoratashi yakalli sadiq wannan shirin haka ina abban nawa? Baice komai ba yanuna mishi wata baqar endofdiscotion sabuwa fill ya bude mishi bayan yashiga yaxauna sadiq yarufa qofar
prince kusan mutuwar xaune yayi ganin fatee a gefenshi cikin wata shiga ta alfarma dabai taba tunaninta a haka ba tayi kyau kakarda fenti akamata make-up yasaki baki yaxuba mata ido yayinda itama taxuba mishi nata amatuqar tsorace
Saiyafara tunanin kodai gixo fateen take mishi tabbas kuwa yayi nisa a SO tunda har yafara ganin mahaifinshi a kamannin fateema
Kafin yayi yunqurin wani abu motocin sukafara tafiya
*Nasmy ce*π
Yarmutan arkilla love you allπ
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*5 star's β¨β¨ online writer's association*π
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’126/130β’*
Irin kallonda yatsareta dashi ne yaqara jefata cikin tsananin tsoro tunawa tayi da wancaj lokacin data sanardashi tana sonshi ya falla mata mari har guda biyu, aranta tacr to yaukuma dayaga andaura masa aurena Allah ne kadai yasan abinda xaimin
Nandanan hawayendq ke maqale a idonta suka fara fitowa sharr sunabin kuncinta alamun tsoro qara a fuskarta tahada hannayenta guri daya tafara roqonshi dan Allah yaya kayi haquri wlh bansan komaiba kawai jinayi andaura aurena dakai yaya baffa ne dashida baffa kuma wlh ban gayamusu ina sonkaba bawanda ya tambayeni kawai sukq daura auren taqarasa da kuka mai dan sauti
Shikuwa yarima hakan yafitar dashi daga waswasi yatabbatar fateeman ce agabanshi kuma a matsayin matarshi wato harma an daura aurensu wani irin dadine Wanda baitaba jin irinshiba yaxiyarci xuciyarshi kyakkyawar runguma yakai mata cikeda marari da xanqi farinciki Mara misaltuwa ya mamayeshi yayinda idonshi yaciko da qwalla lallai abbanshi yayimishi gata mafi girma da daraja a rayuwarshi
Ahankali yafara magana cikin digar rarrashi stop crying my teema wlh nayi farin ciki da wannan hadin fiyeda tunaninki ubangiji Allah yasakawa iyayenmu da mafificin alkhairinshi bisa taimako da ceton rayukan dasukayi fateemq nima nakamu da matsanancin sonki ina qaunarki fiyeda tunaninki yaqara sassauta murya yarada mata akunne ina sonki fateema
Fateema da jikinta yayi mata wani irin nauyi takasa cewa komai tunda yafara maganar ta dasqare sai takeji kamar a irin mafarke2 datake dashine ba,axqhiri ba,
Fahad yafahimci hakan yadagota suka fuskanci juna yace dagaske nake ina qaunarki fateema wlh nayi farin ciki sosai da auren nan
Kawai sai fateema tafashe da kuka ta rungume yayanta wanda ko a mafarki bata taba tunanin xaisotaba waiyau itace yake furtawa so haka yaqara dagota yana shafa nayanta tareda umartar ta datayi shiru
Dai2 nan motarsu tayi parking yadago yakalli wurin dasuka tsaya mamaki me yai mishi dirar mikiya ganin makeken hotonshi rungumeda fateema anrubuta happy married life son murmushin jindadi ne ya subuce masa yajuyo yakalli fatee kigyara fuskarki mun iso nantarasa yanda xatayi dan nataxoda kayan make-up ba yai murmushi sannan yaciro wani lallausan handcuff daga aljihunshi yabata ba musu ta karba ta share hawayen sama2 fuskarta tadawo nrml tamayar mishi handcuff din yakarba yasaka a aljihun rigarshi fadawa ne suka bude musu motocin suka fito fuskarnan ta Prince yau kaman gwanar auduga yaxahaya yariqo hannun flower sa fateema abinda yaburge daukacin mutanen dake gun kenan hannayensu sarqe har suka isa maxauninsu namma saida yafara xaunar da ita sannan yaxauna atashi kujerar wurin yafarke da tafi raf raf raf. Kujerunsu suka fuskanci wasu manya2 kujeru gaban fahad yayi mummunar faduwa alokacinda idonshi suka sauka kan mahaifiyarshi ta watsa mishi wata harara nanfa yashiga tuno laifinshi ga umman tashi yadade bata daga wayarshi to balle kuma yanxu daya dawo qasar bai nemeta ba yayi qasa dakanshi tareda sake hannun fateema
Kallo daya dayaiwa umman mashi saiyaji yafara tsanar fateema yafara wani harare2 xuciyarshi yaji tafara yimishi xafi da xogi akan auren da akayi mishi da fateema yasake kallonta saiyaji wata irin tsanarta ta dira axuciyarshi inannalillahiπ³
Jiyayi kamar yatashi yabar wajan saidai yasan hakan baxai yuwuba kasancewar abbanshi yana gun nandanan fuskarshi ta canja yanayinshi yadawo daban da wanda yashigo wajan dashi
Ganin nayi umman yarima ta kalli gefen da yayarta da yarta laxee suke xaune suka sakewa juna murmushi tareda kanne ido
Tafaπ€
Fateema kuwa kanta na qasa batasan abinda kefaruwa ba hatta canjin fuskar fahad bataganiba balle abinda sukayi
Maijawabi ataran sukaji yafara magana a mike yafara koro bayanai da maqasudin taruwarsu agun wanda iyayen amarya da angon ne suka shirya musu nandai aka cigaba da gudanarda bikin iyaye da abokanin ango sunyi nayanai dayawa tareda tarin addu,oi da nasihohi ga ango da amarya daganan biki ya watse qarfe bakwai na yamma kowa yakama gabansa aka dauki ango da amarya kamar yanda akadauko su aka maidasu gida
Fateema tayi mamaki qwarai yanda talura da sauyin fuska daga yarima tundasuka shigo motar ko kallonta baiyiba balle yayimata magana haka dasuka iso gidan baiko waiwayetaba yanufi sashensu
*Nasmy ce*π
Yar mutan arkilla love you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*5 star's β¨β¨ online writer's association*π
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’131/135β’*
Kai tsaye dakinshi nacikin sashen fateema yanufa wani babban daki danaga aj rubutawa master room yanufa yasaka key dindake jikin qofar yabude yashiga ansauya komai na dakin yayimishi kyau sosai sabon tsarin ya burgeshi saidai har yanxu xuciyarshi tuquqi take mishi da quna
Yaxauna a bakin gadanshi yabude wata bedside drower yadauko juice na bost mai sanyi yadaga yashanye qaramar robar duka amma hakan baisa yaji sanyi ko sauyi na xafin xuciyarshiba mahaifiyarshi ce tayomishi sak ga rayuwarshi yamiqe dasauri kamar ana ingixashi yanufi sashenta
Dukkansu ukun sunacan sunqure a uwar dakinta wato itada yayarta dakuma yarsu laxeera sai murna suke da farinciki maganin boka yafara aiki akan yarima fahad dama bokan yace musu daxarar ya hada ido da dui wadda tashafa kwallin toxaiji yatsani yarinyar gabadaya daga nankuma duk abinda suka umarceshi xaiyi, ti shinefa ummamshi tashafa ta kalleshi kasancewar tasan acikinsu ba wadda xaiyi saurin hada ido da ita samada ita
Hajya takalli umma tace toyakika gani yar,uwa ba fada ba tada jijiyoyin wuya gashi yaro yaxo hannu ai nagaya miki fada da husuma banaku bane kudai kurum kuyi biyayya ga dukkanin umarnin boka
Umma tayi wani qayataccen murmushi tace wlh nayarda yaya ai shiyasa akace duk abunda babba yahango yaro koyahau rimi baxai hangoshiba
Laxee tai karaf tace toyanxu momy ni meye matsayina banji kunyi maganata ba
Ummanta ta harareta kaji shashasha duk wannan fadi tashin damuke danwa akeyi badan keba
Harxata kumayin wata maganar sallamar fahad ta katseta tsit tayi shiru sai manyan dasuka wayance da canja xance suka amsa sallamar sai ummanshi ta miqe xatabar dakin bayan ta daure fuskarta tamau dasauri yarima yasha gabanta sannan yakama hannayenta duka niyu yariqe da nashi ya tsuguna akan guiwowinsa duka biyu a gabanta
Ahankali cikin murnar tausayi yafara magana dan Allah ummanq kitsaya ki saurareni kar kiyi fushi dani kiyimin rai pls ya qara marairaice murya, anan umman laxee tayi magana haba kekuwa yar,uwa karkiyi fushidashi mana musamman idan kika duba auaren nan dole akamishi komai bada saninshi akayiba
Dasauri yaruma ya cafe maganar wlh kuwa umma Allah banason yarinyar nan dole kawai xaisa naxauna da ita amma wlh bana sonta dan Allah umma kiyi haquri idan kikayi fishi dani yaxanyi dawanne xanji?
Umman tayi wani irin murmushin mugunta tadago yarima ta miqar dashi suka fuskanci juna tace cikin kissa da iya tuggu son tayaya kakeso inyarda dakai bayan kai namijine ba maceba taya kake tunanin xanyarda auren dole aka maka bana soyayya ba? Naga indai hakane to kanada damar rubuta takardar saki kabawa yarinyar nan
Dukdacewa fahad yana cikin sarqaqiya ta asiri da aikin tsibbo amma dayaji ummanshi ta furta kalmar sakin aurenda mahaifinshi ya daura mishi saida yatsorata ainun. Ya kalleta a raxane saki umma?
Nanfa takoma tamke fuska tabita gefenshi fuuuuu xata wuce dasauri yasake shan gabanta a karo nabiyu yaxube akan guiwowinshi dan Allah ummana kiji tausayina wlh xan iya rayuwa babu kowa amma baxan iya rayuwa babu keba kifada duk abinda kikeso xanmiki umarninki nakejira mahai fiyata
Umman tajuya tayiwa yayarta signal da ido nandanan hajya tabude jakarta taciro wata farar takarda da biro ta taso ta damqawa umma dama can sunshirya wannan umma takarba tamiqaw fahad hannunshi har karkarwa yakeyi yakarba yasake kallonta saki nawa kikeso inmata ummana? Hajya tayi caraf tace uku saki uku xakamata dasauri umman shi tace a,a yar,uwa inyayi uku ai xaidawo sontane kayimata saki daya kace intasami miji tayi aure kawai ya isa
Hannunshi na qyarma yana karkarwa yarubuta kaman yanda aka umarceshi sannan ta karba taduba tayi murmushi ta ninke takardar tabashi kayi qoqarin nata ita yau dinnan dan banaso taqara kwana a masarautar nan amatsayin matarka tajanyo hannun laxeera takawo gabanshi wannan yar,uwar taka itace matarka kasaka aranka laxee ce matardatafi dacewa dakai
Gamsuwa sosai fahad yaji akan maganar nandanan yaji laxee tasami masauki axuciyarshi yaji wani irin sonta take alokaci daya suka kalli juna suka sakewa junansu murmushi
Nanfa yaji gwara yaje yasallami fateema tabar gidan danshi ayanxuma baiqi a daura auranshi da laxee ba
Nagode ummana nagode da wannan kyautar dakika min bari naje nasallami waccan yarinyar dan wlh xamanta a gidannan yana dada dagamin hankali baijira cewar taba yajuya yafice da takardar sakin fateema ahannunshi yanufi sashen su
*Nasmy ce*π
Yar mutan arkilla love you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*5 star's β¨β¨ online writer's association*π
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’136/140β’*
Dafitarshi dakin suka fashe da dariya da murnar samun nasara hajya tace menagaya miki ai wlh ni nayarda da wannan bokan sha yanxune magani yanxu (wa iyaxu billa) suka hadu harda yar suka tafe hannaye itako murna take sosai yau yaya Prince yaxama nata har godiya yake anbashi ita ta rungume iyayen nata harda qwallar farin ciki tace I really lovo you my mamys baxan taba mantawa dakuba kun ceci rayuwata dan wlh dana rasa yaya Prince da mutuwa xanyi inasonshi ina qaunarshi fiyeda tunaninku sukayi murmushi dukkansu
Fahad kuwa yana isa farfajiyar fada yaji ankira sallar isha nanfa yatuna ko sallar magrib bayyiba kaitsaye masallaci yanufa yafarayin magrib kafin akatayarda isha yayi tareda jam,I ciki kuwa hadda abbanshi mai martaba ganin abban nashi yadan karyar mishida xuciya saidai kome xai mishi dolene yasaki fateema dan baya buqatar xama da ita hasalima ayanxun ko sunanta bayasanji ballantana ganinta
Baibari sun hadu da mahaifin nashiba suna kammala sallar yafice gidanshi yanufa dashigarshi saiya nufi dakin fateema baikaiga qarasawaba yafarajiyo muryoyinsu natashi itada qawayenta yan kukunba wayanda akabari a gidan sunata hire hirensu suna dariya haka yabude dakin yasamesu cikin farin ciki wani mummunar faduwar gaba yaji da idanunshi suka sauka akan fateema dasauri yakauda kanshi daga kallonta duka yan matan suka gaidashi cikin girmamawa suka fice dakin yarage dagashi sai fateema tatsuguna har qasa tagaishe shi bai amsaba itakuma bata dagoba saidai gabanta dataji yatsananta faduwa shikuwa wani irin xafi da quna yakeji na kasancewarshi da ita a daki daya takardar dake