Showing 36001 words to 39000 words out of 57158 words

Chapter 13 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt

07 Feb 2025

5533

ne aka kuma turo qofar da sallama wannan karon su waxirin sarki ne da shamaki dakuma mai fada. Wayannan sune manyan mutanenda mai martaba yake shawara dasu kafin ya yanke duk wata shawara data shafi fada, ganisu yasaka jikin umma da danta yarima yayi sanyi bashiri tanemi guri taxauna. Suma suka xaxxauna suna sauraren mai martaba






Yafara magana Ahankali kamar bayasanyin maganar bakomai bane yasakashi yin hakan saidan tsananin mutuwar jiki da nauyin bakinshi dayakeji adalilin wannan baqin cikin da yarima da mahaifiyarsa suka haifar masa , yace " Ayau kuma awannan lokacin agaban wayannan mutanen masu daraja da mutunci a idona, Na cire yarima fahad daga rayuwata na yafeshi duniya da lahira, sannan na haramta mishi gadon sarautata kobayan rayuwata bana buqatarshi kusada gawata in fact ina buqatar yabarmin gidana dashida mahaifiyarshi sunisanta dani dakuma masarautata ayau basai gobe ba.............innalillahi wa inna ilaihi raji,in abinda gabadaya mutanen dake wajan suke ambato kenan






Yarima kuwa baikoma jin komaiba kamar yadda yadaina ganin komai adalilin daukewar da ji dakuma ganinshi sukayi lokaci daya, wani irin bugu xuciyarshi tahauyi kamar xata fallo qirjinshi tafito waje, kanshi yahau sarawa da qarfi




Umma kam awurin tasuma daga xaunen datake




Fateema ta qara fashewa da kuka




Baffa kam miqewa tsaye yayi ya isa gaban yayanshi "haba yaya haba yaya mekake shirin aikatawa haka? Me yarima da hjya sukayi wanda yakai kayanke musu wannan dayen hukunci?




Mai martaba cikin daga murya yace "Auren damuka daura masa yasaki tunbaishiga dakin amaryar ba, dan uwana yarima yasaki fateema harma ya auri wadda yake So duk bada saninmu ba




Baffa da goggo suka dauki salati shamaki dasu waxiri ma haka,


Jikinsu yayi sanyi matuqa yaya bashir kuwa wani mugun kallo yashiga bin yarima dashi dan yariga ya cuci yar,uwarsa qanwarsa ya bata mata suna agari wanda hakan xai iya xama silar rasa mijin aure gareta
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *yaya*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *fahad*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ’“
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *Nawa*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *ne*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ‘―πŸ’“πŸ‘―


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍




*Assalamu Alaikum masoya na, masoyan "yaya fahad" novel barkarmu da dawowa hutun salla. Da fatan dukkanin ku kunyi salla lafiya, Allah (s.w.a) ya karbi ibadodin da mukayi.*


*Fans kumin afwa da rashin dawowa bakin aiki da wuri, hakan yafaru ne a dalilin matsalar dana samu nayi jinya sosai amma yanzu kam Alhmdllh naji sauki kuma insha Allah zan kawo muku karshen labarinku har ma mushiga sabo daku.*
*Ku kasance dani u will always been in happiness guys, keep smiling πŸ˜€ masoyan Yar'mutan Arkilla* ANA TARE 😍🀝






*β€’231/235β€’*




Fateema kuwa tana can saman bene daga d`akin mai martaba tana kallon duk abinda ke wakana, tana kallo Fa'eez da iyayen sa sukayi sallama da kowa suka shiga motar, Fa'eez shine na karshe a shiga motar dan tsayuwa yayi yana nazari kamar mai jiran wani abu kai da gani kasan bayason tafiyar ko kuma wani abu ne yake bukata kafin ya tafi, daga karshe dai bisa dole ya shiga motar direba ya tayar suka fice. Sam bataji dad`in kaucewar fuskarshi daga ganin ta ba, a wannan halin da take ciki ta tabbatar a yanzu babu SO a ranta sai dai ta yarda kallon fuskar yaya Fa'eez na d`aya daga cikin ababen dake rage mata rad`ad`i da zogin abinda yarima yayi mata. Tayi nisa sosai a cikin tunanin da take saiji tayi an dafata ta baya juyowar da zatayi sai taga Bilki ce d`aya daga cikin kuyangin dake mata hidima idan tazo gidan. hakan yasaka ta fad`ad`a fuskarta da murmushi domin ta saba dasu sosai "Bilki ya dai, ina Rukayya? " ta fad`a cikin ko'karin ta na boye damuwar da take ciki. Bilkin ma murmushin ta mata kafin tace " ranki ya dad`e wlh ni kad`ai nake kuma wurinki nazo zamuyi magana kafin su goggo su dawo" Fateema ta kalleta cike da mamaki ta ce "magana Bilki?, to ina jinki Allah dai yasa lafiya" Bilkisu ta karayi kusa da Fateema sanna tayi kasa da muryar ta ta fara magana a hankali cikin rad`a tace " wlh anty fatee yarima na matukar kaunar ki, Fateema ta d`ago da sauri dan ko kusa ba abinda tayi tsammanin ji kunnen ta yaji ba. kamar zatayi magana sai kuma Bilki ta katseta ta hanyar cigaba da cewa " wlh yana sonki sai dai an riga an fi karfin sa, alamun mamaki karara a fuskar Fateema take kallon Bilkisu. tace "eh wlh fin karfin sa akayi dan asiri akayi mishi Umma ce da Hajiyar Lazeera ke harma da Lazeeran, anty Fatee nida nake nan nizan gaya miki komai yanda yarima ya tsani anty Lazeera da can wlh ko gunda yake zaune bata isa ta raba ba, idan ya ganta ji yake kamar ya kasheta saboda sha'shanci da rashin kamun kanta." Nan dai Bilkisu ta kwashe duk abinda ta sani ta shaidawa Fateema. Allah sarki hausawa suka ce sauran SO yafi sauran KIYAYYA domin kuwa cikin kan'kanin lokaci tsanar da Fateema ta yiwa Fahad ta juye ta zama tausayi


Jikin ta yai sanyi matuka tausayin yayan nata ya kamata soyayyar shi kuma ta dawo sabuwa fill a zuciyar ta, cikin zubda hawaye ta kalli Bilkisu tace "na gode Bilki da kika sanar dani wannan sirrin kafin nabar garin gwambe tabbas ba inda zani har saina ceto d`an'uwana kuma miji na daga wannan halin da yake ciki, na gode da kika gayamin tana shirin rabashi da gidan nan ina tabbatar miji cewar bata isa ba, wannan gidan namu ne, masarautar gombe tamu ce, kuma *YAYA FAHAD NAWA NE* na rantse miki saina karbo Abina" ta fad`a tana share kwallar dake fitowa daga idanun ta. zuciyar ta ta riga da ta dake ta rika hannun Bilki dan su koma babban falon



Juyawar da zasuyi sai sukayi kicibis da duka iyayen nata Baffa da Mai martaba Goggo da yaya Bashir dukkanin su sunyi jugun-jugun alamu sun nuna ba abinda basuji ba daga hirar tasu. "Ya Rabbi" Fateema ta fad`a tare da sunkuyar da kanta kasa Bilki kam tsoro ne ya baibayeta.


Mai martaba da kanshi yaja hannun Fateema tareda cewa Bikkisu "kema biyo ni" yayi gaba su Baffa suka rufa masa baya kafin Bilki itama tabi su sumi-sumi




*Yar'mutan Arkilla* ✍
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *yaya*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *fahad*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ’“
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *Nawa*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *ne*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ‘―πŸ’“πŸ‘―


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍




*β€’236/240β€’*


_Wannan shafin sadaukarwa ne gareka fasihi matashin fikira,fasaha, da d`inbin basira dole muyi alfahari da kai autan writers_ *KING BOY ISAH* _Allah ya kara baiwar brain kuma ya kara d`aukaka *ZAMANI WRITERS*πŸ™






Bai tsaya babban falonshi da suba har d`akin baccin shi ya kure dukkanin su suna biye da shi a baya. haka yaje ya zauna a wata kayatattar kujera dake d`akin sannan ita ma Fatee ya zaunar da ita gefen shi, su Baffa ma zaman suka yi a matukar rauna ne saboda maganar da suka ji ta gama kashe ilahirin lakar jikin su. Mai martaba yayi hmgyaran murya sannan ya kalli Bilkisu yace "shin ki tabbatar abinda naji daga bakin ki gaskiya ne?" Bilki cikin rau'rawar murya tace "eh-eh Allah ya taimake ka, wlh gaskiya ne ba'abinda na dad`a wlh inajin su kuma sau tari ina gani suke aikata wasu sirrukan. tayi shiru, iyayen suka cika da al,ajabi ya yarda dan yasan halin Umma sosai kawai kawar da kai yakeyi a zama da ita kasancewar shi mai sarautar babban birni sakin Aure ba nashi bane, yau d`in ma dan ta kaishi kwano ne. tunani ya shiga yi da nazarin abinyi, d`akin yayi tsit ba abinda ake ji sai karan (a.c)


Idan ka d`auke Fateema da Bilki kowa a wurin tunani yake yi na hanyar da za'a bulluwa lamarin, Faeema kuwa tun kafin su shigo d`akin ta samu way out a zuciyar ta, hakan ne yasaka batayi kasa a guiwa ba wajen sanar da iyayen nata sai dai kafin tace wani abu Baffa ya rigata da cewa "to kaji fa yaya yanzu yaron nan duk abinda yakeyi ba bisa hayyacin sa bane, gashi ka yanke masa tsatstsauran hukunci". Goggo tayi caraf tace "to yanzu yaza'ayi kenan meye mafita akan wannan lamarin?" Shirun da taji Mai marta yayi shine ya bata damar amayar da abinda ke zuciyar ta, sai da ta sunkuyar da kanta kasa sannan ta ara magana cikin ladabi da sanyaya murya tace "Ya'baffa tunda abin hakane ni inaganin kayi hakuri kawai kamaida aurena da yaya fahad, kuma ka hanashi barin gidan nan sai afara nemo masa magani da abubuwan karya asiri, ni kuma nayi muku alkawarin zan shanye duk wani wulakanci da cin zarafin da zasu yimin har zuwa lokacin da zamu samo hankalin sa, domin ni a ganina wannan ce hanya mafi sauki dazamu bi mu ceto rayuwar shi. Mai martaba ya kafe yarinyar da ido tsananin tausayin ta da hakuri da kuma zurfin tunanin ta sun burgeshi. Ahankali yayi gyaran murya sanan ya fara magana "Fateema Allah (s.w.a) yayi miki albarka irin tunanin kinan shine ya zomin a zuciya ta sai dai ina nazarin yanda zaki d`auki lamarin keda iyayen ki idan na furta, sai gashi kin fad`a da kanki ba abinda zan ce saidai Allah yayi miki albarka kije d`akin ki zamuyi magana dasu waziri".


Fateema ta mike zuciyar ta cike da was'wasin abinda ta ballowa kanta anya zata iya kuwa? haka dai ta fice Bilkisu na take mata baya. Kai tsaye sashen ta ta nufa inda ta fara tarewa har takai ga ko'far Bilki tayi saurin riko hannun ta, tajiyo da sauri a d`an razane Bilki tace "ki gafarceni anty a yanzu Yarima da Amaryar sa ne ke rayuwa a d`akin ki na da kiyi hakuri kishiga d`ayan part d`in tunda shima akwai komai a ciki gyara ne kawai wancan yafi dayan dashi". Wani shu'umin murmushi Fatee ta sake wa Bilki kafun tace " Ai wannan da kika gani shine asalin gida na saboda ni aka gyara shi, kuma ni nafara tarewa cikin sa saboda haka babu wanda ya isa ya hana ni zama a cikin sa, bata jira me Bilkisun zata ceba. kawai saita kunna kai a babban falon dayake shine farkon shiga gidan, subhanallah! Tafad`a da karfi a dalilin abinda idon ta yayi arba dashi ta kawarda kanta gefe Bilkisu kam waje ta koma da gudu tun Yarima bai ganta ba, Yarima ne da Lazeera suketa shagalinsu har sun fara barin duniyar da suke ciki sai yar karar da Fateema tayi ce ta dawo dasu hayya cin su, cikin kad`uwa da mamaki Lazeera tamike zumbur tazubawa Fatee ido taga yarinyar tayi fresh ta goge fuskarta fayau ba make-up amma hakan bai hanawa sihirtaccen kyawunta bayyana ba. Yarima kam kusan d`aukar abin yayi ba gaske ba dan a tunanin shi daga inda yabar ta bazai koma ganin ta ba. Dukkan su dai sunyi nisa


Fateema tayi murmushi ganin yanayin data jefa su a tashin farko. Lazeera ce ta daure ta kauda shirun cikin dakewa ta dakawa Fateema tsawa "ke jaka meki ka zo yimin a gida?" Wani irin juyi Fatee tayi da idonta tace gidan ki ko gida na? Ba Laxee kad`ai ba hatta Yarima sai da maganar ta girgiza shi, Lazeera kam zuciyar ta tagama rufewa me wannan yarinyar take nufi? Juyowar da zatayi sai ganin Fateema tayi zaune akan kujera ta d`ora kafa d`aya akan d`aya tana jijjigawa har Lazee ta d`aga baki zatayi magana sai Fateema ta tari numfashin ta da cewa "kinga malama idan kinada abin da kikazo da shi nan to kiyi gaggawar d`auka ki fice dan mai gidan ta dawo shi wanda ya aurekin bashida wani wajan da zai ajiyeki ne? Mintuna biyar su na baki ki tattara kibarmin gidana" ta karashe zancen cikeda gadara da rashin tsoro. Cikin d`aga murya Lazeera tace "kan uban can lallai yarinyar nan kin rainani wlh kuwa yanzu zakiyi laushi a gidan nan" ta daka tsalle tayi kan Fateema da nufin dukan ta sai a lokacin Yarima ya motsa da sauri yasha gaban Lazee yace haba my dear yanzu akan wannan yarinyar zaki wahalar min da jikin ki?, Noo ba sai ke ba barni da ita kawai


Ya juya ya fuskanci Fateema yace "ke me kikazo yi a nan d`in? Ko bakisan mata da miji ne suke rayuwa a nan ba? Bai jira amsar taba dan yasan batada abun cewar ya ci gaba "tashi ki kifita" ya fad`a yana nuna mata hanya banza tayi da shi kamar bada ita yake ba, taci gaba da jijjiga kafar ta "keee! Ba da ke nake magana ba" Ya daka mata tsawa saida ta razana a zuci amma bata yarda ta nuna a fuska ba Fahad ya gama cika da takaicin ta dan ya tsani a kawo masa raini a lamuran sa shima dai kanta ya nufa da nufin d`aukar ta ya wurgata waje Tsoro ne ya dirar mata taji kamar ta ruga waje kafin ya iso gareta amma inaaa zuciya ta dake ko gezau batayi ba, baifi taku uku ya rage ya isa gareta ba suka jiyo sallamar Sarkin gida a kofar falon






*Yar'mutan Arkilla* ✍
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *yaya*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *fahad*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ’“
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *Nawa*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *ne*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ‘―πŸ’“πŸ‘―


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍




*β€’241/245β€’*






Wannan shafin kuma naki ne kawa ta gari abar fahari sis *AMA ALHAJI KABIR* U mean more than a friend to me, u are nown my sister. keep trying sis I believe one day our dream will be come true *INSHA ALLAH*






Tsayawa yayi cak ! Sannan ya juya ya nufi kofar ba tareda ya amsa sallamar ba. Daga inda suken suna jin naganganun da sukeyi shida Sarkin gida sako ne daga Mai martaba cewa yazo yanzu yana son ganin sa, ai kuwa kaitsaye yabi d`an aikar suka tafi tare. Nan akabar Fatee da Lazeera suna kallon kallo kafin Kazeerar taja dogon tsaki ta bar falon ta shige bedroom d`inta ta bankowa Fateen kofa, Fateema tabi bayanta da murmushi mai d`aukeda sakon zaki fito ne


Tana shiga ta d`auki wayar ta ta dannawa lambar hajiyar ta kira, ringing biyu a na uku aka d`aga wayar da "hello Doughter na" cikin shagwaba ta amsa "momy wai meke faruwa ne Fateema nagani a sashena wai hadda cemin infita in bata gidan ta, badai ta dawo gidan Fahad ba?" Momy tayi shiru na d`an lokaci sannan ta ce "ki kwantar da hankalin ki Fahad kam yanzu ai naki ne sai yanda kikayi dashi yanzu gayamin me ya faru?" Nan ta kwashe duk yanda akayi ta gaya mata. Tace to banda abinki inma dawowar tayi ke ina ruwanki tunda miji ake yiwa kishi kuma yana hannun ki kedai kawai ki dage ki cigaba da amfani da nagungunan da boka ya baki kinji" ta amsa da "to Momy Nah lov u bye!"


A d`akin Mai martaba kuma manyan mutane nan ne wayanda ya tara su daga farko dasu Baffa sai Fahad daya shigo daga baya ganin taron ya tuna mishi da abinda ya faru tsakanin shi da mahaifinshi d`azu take idonshi suka kawo ruwa ya nemi guri a d`an nesa da uban ya zauna hawaye nabin kuncin sa. Mai martaba yayi gyaran murya ya kira sunan Fahad ahankali Yarima ya d`ago idonshi tam da kwalla ya kalli Abban nashi tareda cewa "na'am Abba" Mai martaba yace "nasan bakasan dalilin kiran danayi maka ba" ya d`aga kai alamar "eh" yace "to na kiraka ne akan abinda ya faru na hukuncin dana yanke maka d`azu shine zan janye amma abisa wani sharad`i guda d`aya" da sauri Yarima ya d`ago kai bakinshi har rawa yake yace "nagode Abba kafad`i sharad`inka nayi alkawarin zanbi shi ko mene ne shi mutukar bai saba sharu'ar Allah ba" dattijan ya gyara zama sannan yace "to madalla auren ka zan mayar da Fateema wato matarka zata koma gidan ka bayan saki d`aya da kayi mata, kuma inaso kayimin alkawarin zaka rike yar'uwar ka amana zaka zauna da ita ba cuta ba cutarwa, kar ganin hakan yasa ka wulakanta min yarinya Yarima muddin ka tozarta Fatee babu ni babu kai har abada". Gabad`aya d`akin suka d`auka "subhanallah" Yarima cikin kuka yaja guiwa ya isa ga mahaifin nashi kayimin afwa ka gafarceni Abba na wlh bana son bata maka kasani fushinka akaina ba alkhairi bane, nayi alkawari zan rike amanar Fateema Abba xanyi iya ko'karina wajen yin hakan" yana kaiwa nan ya fashe da kuka Mai martaba ya shafi kansa yace Allah yai maka albarka tashi ka tafi. Yarima ya mike ya koma gun Baffa ya tsuguna bakinshi har rawa yake yace "kayi hakuri Baffa ka yafemin wlh har ga Allah ina son Fateema bansan meke damu na ba dazarar naganta sai inji na tsaneta Baffa ka taimake ni kar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login