Showing 24001 words to 27000 words out of 57158 words
Chapter 9 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt
datake ciki tanaci tana xubda hawaye abinda yayi matuqar daurewa fa,eex kai kenan yatabbatar wannan cin dole kawai take ma abincin
Ya jijjiga kai yakoma kan kujerarshi yaxauna xuciyarshi cikeda tausayin yarinyar tabbas damuwa ba dadi yatabbatar wannan tana cikin tsananin damuwa to Allah dai yasa ba mummunan tunanin danake akanta ne ya tabbata ba wato tayi cikin shege ne aka kirota daga gidansu
Suna cikin wannan halin motar ta tashi fateema ta kammala cin abincin ta window din motar ta wanke hannunta
Misalin qarfe biyar na yamma suka shigo babban birnin jihar sokoto (tashehu birnin samu gagara gasa garin malamai da waliyan Allah) a babbar tasha aka saukesu tunda motar ta taso fa,eex bai koma kula fateema ba haka itama tunda dama bata damu dashiba shine yaji yagani
Passengers sukafara sauka ahankali duk wanda yaxo wucewa saiya miqawa kondostan dake tsaye a qofar motar dahaka har akaxo kan fateema wadda keta faman raba ido ganin mutane na miqa kudi gashi kuma ita batada su kana kallonta xaka tabbatar da batada gaskiya taxo tatsaya a qofar kondastan ya miqo hannu yaji shiru na,a damqa mishiba yadago ya kalleta yaga ko alamar dauko kudin batayi
Ranshi yabaci sisai amma ahakan yadaure yace malama kudinki xaki bayar fateema tarasa ta inama xata fara saikawai tace kayi haquri wlh banidasu wani mugun kallo kondastan ya watsa mata bangane bakidasu ba? Kinsan bakida kudi kika hau motar haya? To wlh saikin bayar tunda motar bata ubanki ceba, banxa irinku ne masu shiga mota dan axo anata rigima to wlh saikin biy.................ai bai qarasa maganarba yaji saukar wani lafiyayyen mari a kumatunshi na hagu
Saida abadaya hankalin mutanen dake gun naciki dana waje yaqara dawowa Kansu kowa a wurin yacika da tsananin mamaki tareda jinjinawa iskanci irin na wannan yarinya ke baki biya mutane kudinsuba sannan ki wanke dan tahaliki mari, hatta kondastan kallon mamaki yake binta dashi yqyinda kowa a gun yaxuba ido dan ganin matakin daxai dauka akanta
Taf nimadai nasmat tashi guduwa nayi dan ganin fateema ta debo mai xafi lolx
*Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯
*5 star's ✨✨ online writer's association*👌
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•161/165•*
Harna juya xan gudu naji hayaniya ta kacame dasauri najuyo dan ganewa idona sainaga wuri kam yacika da mutane amma kondastan nan yakasa daga hannu yamari fateema sbd tsorata dayayi dagudun ace yar wani babban mutum ce anan danganin yanda ta iya dqga hannu ta mareshi batareda jin ko dar ajikintaba gakuma yanayinta da shigarta sun isa su tabbatar cewa ba daga qaramin gida tafito ba
Shiyasa baiyi gaggawar marinta ba saiyafake da baraxana nikika mara ko? Cikin tsiwa da daga murya tace an mareka kaidin banxa wayekai dahar xaka dqga baki kaxagi ubana to wlh kull ina gargadinka ubana ya wuce axageshi gaban idona duk kuwa wanda ya aikata wannan kuskuren to yaxama dole in ganar dashi kawai dan nahau motarku banida kudi
Alokacin drivern motar ya qaraso wurin lokacinda kondastan yake mayar mata da eh din bakyasan xagi meyasa xakici kudin mutane
Fa,eex dake gefe ya harde hannaye yacika da mamakinta yaqara gyara tsayuwa kumafa tun kafin su qaraso tashar akaxo daukarshi amma yaqi yatafi dan yayiwa kanshi alqawarin saiyaga inda tadosa dakuma abinda yakawota garin to gashi kuma wai ko kudin mota bata dashi kuma ahakan harda qarfin halin marin masu mota hmmm waishin wacce ce wannan? Ya tambayi kanshi
Ai baikaiga nemo amsarba yaqara tsurewa da al,amarinta dan akwatinta yaga ta xuge taciro daya daga cikin sarqoqi na xinarin dake gefe ta miqawa mai motar tace kayi haquri banida kudin motar ne shikuma wancan da baisan darajar iyayeba saiya xageni abinda ya batamin rai kenan a rayuwa natsani xagin iyaye kusayarda wannan ku fanshe kudinku
Daga bayanta taji ance mayar mata sarqarta malam juyowar daxatayi saitaci karo da wannan mayen kamar yanda ta liqamishi shine mai maganar ya isa gaban mai motar yaciro kudi dagaaljihunshi yabashi yakarbi sarqar yamayar mata batacedashi komaiba ta karba nagode tace sannan tajuya ta nufi hanyar datagani tafita daga tashar badan tasan ida xata nufaba
Fa,eex yabi bayanta da kallo yana mamakin yanayinta da sauri2 yabi bayanta dan harta fita daga harabar tashar
Tana futowa taga wasu manyan motoci baqaqe guda biyu dawata hilows mai kalar kayan sojoji bayanta yana cikeda sojoji nanfa gaban fateema yashiga dukan uku uku jikinta yahau bari gar gar gar kamar maxari tunda take bata taba ganin sojoji ido da ido hakaba. Saidai a litattafan karatu na makaranta kokuma a jikin jaridu udan sun siyo qosai a gombe ma ba irinsu take gani a gidan sarkiba
Kowannensu na daukeda dirkekiyar bindiga ahannu daqyar ta iyabi tagabansu tawuce takai bakin titi tayi tsaye tarasa yadda xatayi kokuma inda xataje aranta tace komadai yaxanyi yakamata inyi nesa da wayannan makasan mansaniba ko kasuwar sukaxo tashi
Haka tadinga tafiya daukeda akwatin ta tayita bin gefen titi ahankali
Fa,eex kuwa yana fitowgabadayan sojojin nan sukayi sahu agabanshi suka sara mishi yai musu murmushi tareda cewa thanks dafatan nasameku lfy sukq amsa da lfy yallabai yaje gurin motocinnan yaduba bamai tarbonshi kodaya daga gidansu direbobi ne kawai da ma,aikatan yai murmushi watodai fushi akeyi dashikenan?
Ya umarci daya direban dayakoma tareda dayan ya amshi motar yace sujirashi nan yabi bayan fateema
Tundaga nesa ya hangota xaune ajikin wata bishiya dake gefen titin tasaka kanta tsakiyar cinyoyinta tana kuka saida yadan wuce inda takedin sannan yafaka yafito daga motar yanufi inda take
Jin alamun mutum tsaye akanta yasa tadago dasauri da jajayen idonta dakuku ya canjama clour takalleshi cikeda mamaki meyasa wannan yakebinta tane? Ta tambayi kanta
Shikuma gogan tsayen kawai yayi yaharde hannaye ya xubamata ido kamar mai naxarin wani abu akan fuskar tata
*Nasmy ce* 😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯
*5 star's ✨✨ online writer's association*👌
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•166/170•*
Alamomin tsoro ne qarara afuskarta xumbur tamiqe tsaye tasuri akwatinta danufin barin wurin fa,eex yayi hanxarin shangabanta abisa dole taja ta tsaya
Har ixuwa lokacin baiyi mata maganaba hakan yasa ita tafara maganar cikin raunaniyar muryata wadda tasha kuka tace dan Allah kayi haquri kafice agabana in wuce naroqeka karka cutar dani kabarni da damuwata ma ta isheni
Tana kaiwanan tajuya daya gefen dan cigaba da tafiya kidakata da akwai tambayoyin danakeso nayi miki kuma dakin amsamin su dai dai xanbarki kitafi
Fateema bataso tsayawar ba amma saita tsinci xuciyarta da son tsayuwar dominjin wane tambaya xai mata tabashi amsar kawai ta huta dashi, koxai barta tajida abinda ke gabanta saita tsaya batareda ta kalleshi ba tace inajinka
Saida yayi taku biyu ya iasa gabanta suna fuskantar juna saida fateema tadan jada baya yai murmushi sannan yace kafin kiji tambayoyin daxan miki imaso kiyimin alqawarin baxakiyimin qaryaba dafatan dai kinsan girma da darajar mutumin dake cika alqawari awajan Allah
Fateema tadanyi shiru tana tunanin inda xai dosa to meyasa yakeson quretane? Taya xatayimishi hakan bayan batasan wacce irin tambaya xai mataba? Duk tsayin lokacin nan bawanda yayi magana acikinsu saican tadan juyo tace inajinka saida yakafeta da ido sannan yace kinyi alqawarin? Jitayi qwarjininshi yacika mata ido naxata iya musa mishiba daqyar tayi qasa da kanta tace eh xan fadamaka idan har abinda katambaya wanda nasani ne
Fa,eex yanisa yace wacce ce ke? mekikaxoyi a sokoto? Ko ince wurinwa kikaxo? Kinada yan uwa anan ne? Meyasa kikaxo bakida kudin mota? Mekuma yasa kikaxo nan kika xauna kina kuka?
Danasani tafarayi axuciyarta akan alqqwarin datayi mishi nafadamishi gaskiyar abinda xai tambayeta domin koda wasa bata xaci xai mata tambayoyin ne danganeda abinda yashafi rayuwarta ba
Axatan ta ko wani wajan xai tambayeta saitagaya mishi itama baquwace ba inda tasani
To ashe ba haka bane
Saitayi shiru tana naxarin abinyi taya xata dauki sirrinta tasanar ga mutuminda bata saniba kuma baisantaba
Saikuma taji kira
dagacan wani sashe na xuciyar ta yanacewa to amma aikin riga kinyi mishi alqawari xaki gayamishi indai abinda kika sani ya tambayeki nannauyar ajiyar xuciya tasauke kafin wasu xafafan hawaye sukafara xarya akan kumatunta
.
Takalli fa,exx wanda yakafeta da ido yanamata wani irin kallo wanda sam batasan ma,anarshi ba idonta jage2 da hawaye tace sunana fateema haifaffiyar jihar gombe bansan kowa anan ba ina nufin banida kowa a sokoto asalima bantaba xuwanta ba sai yau maganar kudin mota kuma bantanadesuba kasancewar tafiyar taxomin a baxata
Takoma kallonshi wannan karon harcikin ido takalleshi tace inafatan nagama amsa maka tambayoyinka kamar yanda kabuqata to dan allah kabarni hakannan naroqeka katifi abinka bana buqatar kusanci da kowa
Tana kaiwa nan tajuya tayi gaba anan tabar fa,eex yasandare dominjin abinda fateema tafada aranshi yace kenan xarginshi akanta ya tabbata babu makawa cikine da ita wato cikin shege tayi aka koreta daga gidansu wani irin haushi da takaicinta suka mamaye xuciyarshi saiyaji xuciyarshi tacigaba da raya mishi karya barta ta tafi wata qila wannan dinma tsautsayine tunda ga yanayinta bawanda xai mata kallon yar iska kartaje tafada wani mugun hannu kota ida xama cikakkiyar karuwa
Koda yadago saiyaga fateema harta danyi nisa dashi sosai tama wuce inda yafaka motarshi da sauri yabi bayanta yanaxuwa yashiga motar yatayar yaqarasa inda take yamaxuwa yayi blocking gabanta da motar hakan yasa ta tsaya cak a inda take fa,exx yafito daga motar ya tsaya agabanta
Itakuwa ganinshi yahaifar mata da mummunar faduwar gaba axatan ta sun rabu kenan tunda tabashi amsoshin tambayoyin dayayi mata
Hasbanallahu wa ni imal wakil abinda tashiga ambato kenan dan ita ayanxu tafara tsoraya sosai da lamarin mutumin nan
Shikuwa fa,eex wani irin kallo yakemata dan ayanxu haushinta yakeji kamar ya rufeta da duka aganinshi tariga ta banxartar da rayuwarta nikuwa nasmy nace anya wannan ba kishi bane? Hhhhhh
Saiyaji haushin kanshima na bibiyarta to meyasa baxai qyaleta ta tafidin ba? Sai wata xuciyar tace dashi ai wannan taimakon muslumci xakayi dan ba makawa wannan idan tayi gaba rayuwarta xata qara tabarbarewa
Yanxu kuma ina kuka nufa? Tambayar daya wurga mata kenan takalleshi da mamaki saitaga yanayin fuskarshi ya canja sosai dukda bawani sani tamishi ba amma ta hango tsanani bacin rai afuska dakuma qwayar idonshi abinka da riqaqqen soja, nanfa hankalinta yatashi tabbas wannan mutumin mugu ne abinda xuciyarta tashiga raya mata kenan
Saita farahawaye wlh nima bansaniba amma naroqeka dan Allah karka cutar dani Allah xaibani wajan da xan xauna dan Allah kabarni in tafi wata irin tsawa yadaka mata da wata irin muryar dataji kamar ba daga bakinshi ta fitoba dalla malama shiga mota kina wani kiran Allah kamar kinwani saninshi dakike nunamin tsoro mekike tsoron? Meye baki saniba? Ko meye baki iyaba Wanda kike tsoron a koya miki? Cikin qunan rai yake maganganun wanda kodaya fateema bata fahimtaba kawai abinda tasani shine yau kwanakinta sunxo qarshe a duniya saita fasheda kuka jikinta sai qyarma yake ta tsuguna har qasa danufin ta qara roqonshi amma saiya sake daka mata wata rikitacciyar tsawa wadda tasakata yin fitsari a wando batareda yasake kallontaba yajuya yaxagaya dan ita tuni tafada cikin motar a rikice
.dashigarshi saiya tayar ya cilla motar a kan titi itakuwa tana qudundune a guri daya kuka take sosai kamar ranta xai fita nadamace da danasani qarara a xuciyarta saiyanxu ta tabbatar barin gidan datayi shine mafi girman kuskure data tafka a rayuwarta
daida nan fa,eex yafaka inda yabar sojojin nan yai musu Horn sannan yasake fisgar motar yayi gaba suka mara mishi baya har ixuwa lokacin fateema bata daina kuka ba shikuwa gogan ko ajikinshi saima qarajin haushinta dayakeyi
*Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐©(Z.R.A)⭐⭐
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍
*•171/175•*
*aslm my lovely fans fans of yaya fahad inafatan xakuyimin afwa abisa rashin jina kwana biyu wannan yafarune Bisa wasu dalilai dasukasha gabana* _farin cikinku shine asalin nutsuwata ku kasance dani xakuyi farin ciki , keep smiling_😍
Sam fateema batasan iya tafiyar da sukayiba balletaga ta inda akebi da ita dan tunda sukafara tafiya kanta yana qasa tana rusa uban kuka tadaiji alamar tsayuwar mota sannan yabude bangarenshi yafita baice da ita tafitoba amma dakanta tasan batada xabin dawuce hakan tabude ta fito hannunta riqeda akwatinta hawaye nacigaba da kwaranya daga idonta duk dacewa tatsayar da kukan na bayyane amma takasa tsayarda hawayen dake ambaliya afuskarta
Wani tangamemen wurine tagansu wanda xa,a iya kwatantanshi da kamfani kokuma wata ma,aikata ayarin sojojinda tagani biyedasu yaqara tsorata ta matuqa haryanxu jikinta qyarma yake sosai fa,eex kuwa ko waiwayenta bayyiba tafiyarshi yake cikin qasaita da kwanciyar hankali
Ta lura duk wanda tagani awurin da kakin soja ajikinshi wasun kuma da wandunan ba riga wasu kuma babu kodaya hakan yasa ta tabbatar nan gidansu ne wato head cotteer su, tafiya sukayi maidan tsayi cikin farfajiya dakuma layukan dake wurin sannan suka isa ga wani jerin wasu sojojin inda suka jeru suna jiran isowarsu yanaxuwa ya qame ya sarawa mutanen dake gabanshi wani dan madaidaicin dattijo wanda babu kakin soja ajikinshi naga yafito fuskarahi daukeda wani qayataccen murmushi a fuskarshi hannunshi na riqeda wata sarqa wadda ke qyalli kamar da gold aka qerata ajikinta anyi wasu manyan rubutu da black colour kamar haka: canal fa,eex,ma,aruf, ya sakawa fa,eex awuya yayinda gabadaya wajan suka koma sara mishi harshi wanda yasaka mishi din
Fa,eex dinma ya sara musu wannan farin dattijo yafara magana cikin ixxa alhamdllh canal fa,eex rundunar sojoji ta jiha dama ta qasa baki daya tana alfahari dakai inamaka barkada dawowa amadadin duka sojojin qasarnan tareda tayaka murna akan gagarumar nasarar daka samu a wannan tafiyar bincikenka yayi fa,eex ina alfahari dakai, da wannan nakecewa kaje kahuta na sati daya kafin kadawo kacigaba da aiki ahuta gajiya lfy
Hmmmmm saiyanxu na tabbatar da fa,eex dinnan miskilin mutum nenaqarshe dominkuwa duk wannan yabo da girmamawar da general yayi mishi baiyi magana ba sai wani keeler smile dayayi mishi da rabin lebe sannan ya sara mishi yawuce gaba kaitsaye office dinshi ya nufa
Fateema na tsaye taga duk sojojin dasukaxo tare dinnan ba wanda yabi bayanshi hakan yasa itama taji tsoron binshi saita tsaya a inda take rakube agefe daga dan nesa dasu harma tanaji kamar tace suroqa matashi yabarta ta tafi saidai aganinta ai duksune gakuma lura datayi duka kamar sunabinshi ne watodai shi babba ne anan dinma
Koya akayi yasan bata bayanshi? Oho saigani tayi yajuyo tareda watsa mata harara ai bashiri tabi bayanshi har tintibe takeyi wata qofa taga yabude yashiga hakanyasa itama tayi shahada tabi bayanshi wani qayataccen office ne wandayasha ado na kayan alatu da more rayuwa kai kace ba aduniya kakeba idan katsinci kanka a wannan wajan abinkada quruciya nanfa fateemq tamanta da damuwarta tashagaltu sosai wajan kallon irin wannan tsari da akayiwa office to inaga gida wajan xama? Ta tambayi kanta saidai kafin takaiga bawa kanta amsa sai jitayi yadaka Marat sawa araxane takalli inda yake yana tsaye aqofar office din dawani babban file ahqnnunshi da alama harya kammala abinda xaiyi yafita amma fateema batasaniba sbd nisa datayi wajan qarewa gurin kallo
Batareda yace mata komaiba yaja dogon tsaki yayi waje dasauri tafusgi akwatinta ta rufa mishi baya
Wannan karon driver je yake tuqa motar fa,eex da fatee a kujerun baya kanta yana sunkuye aqasa dan ayanxu tsoron mutumin nan takeji sosai shikuwa gogan ya tamke fuskarnan kaman baitaba yin dariya ba,
tunanine barkatai axuciyar fateema ko ina xaikaita yanxun? Asace tadago ta kalleshi gabanta yakoma faduwa yaukak nashiga uku tafada axiciyarta wlh wannan sam bayyi kamada masu imaniba ya Allah ka kawomin dauki wani irin kallo ya wurgo mata kafin yace waye baiyi kamada masu imaniba? Fatee ta warwaro idonta duka tq xarosu dan ita asaninta axuciyarta tayi maganar Sam batasan ta bayyana ba yaqara tambayarta nine ko? Tace cikin ina ina wlh bakaibane king nake nufi😂 shikanshi fa,eex saida ya waro ido dan yanayinda tayi maganar yaso yabashi dariya daurewa kawai yayi yace waye kuma King? Bashiri tafara sambado mishi bayani itadai burinta karya fahimci dashi take
Tace wani marubucine bashida kirki ko kadan saida yafaro mana lbr maidadi sannan yaxo yabari sunan littafin ma *mijin aljana* amma inaga xaidawo dashi dandai kam yanada qoqarin rubutu sosai
Tunda tafara maganar fa,eex yake murmushi badan yasaniba, dukdacewa yariga yasan qarya kawai take xirara mishi amma yanayinta dayanda take maganar abin sha,awane musamman gareshi
Baice komaiba sai murmushi dayayi mata cos yariga yasan dashitake ba dawani King ba dai2 nan motar tatsaya aqofar wani katafaren gida mai tananin kyau da ado na furanni