Showing 54001 words to 57000 words out of 57158 words

Chapter 19 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt

07 Feb 2025

5534

ta bayyana ta feshe jikin ta da had'ad'd'un turarukan ta ta kimtsa wurin ta nufi kitchen a can ta Sami Rukayya da Bilki wayanda yanzu sune Masu kula da abincin gidan ta duk da ita take girkawa amma suna taya ta. Yau kuma ganin bata gidan yasa suka d'ora Mata. "Sannun ku da kokari yan'mata" ta fad'a cike da zolaya "Kai anty Fatee, Wai yan'mata sannun Ki da dawowa" suka gaisheta duka ta amsa cikin sakin fuska "yau na barku da aiki ku kad'i" "banda abin Ki anty ai aikin mu ne, Kin Sami mutanen gidan lafiya?" "lafiya lau na same Su Sai alkhairi" Bilki ta canza maganar da cewa "Kai anty Faty tubarkalla wlh kullum Kara kyau kike yi, kin gan Ki yau kuwa?" Tai murmushi "zaku fara ko?" sukayi dariya "ai fad'ar gaskiya baya zama laifi". Ta kyale Su ta shiga duba abinda suka girka. Tuwon doya ne da miyar agushi ta sha kifin hausa busashsshe Sai farfesun kaji daban Sai kuma soyayyen naman shanu Wanda yaji had'in yaji na gargajiya, ta yaba ma aikin Su sannan ta saka plate kowanne ta d'ibi kad'an dai-dai da bukatar Su tace Su d'auki sauran suje Su ci kar Su baci sukayita godiya ita kuma ta d'auki babban tiren da ta jere Kayan ta nufi d'akin Yarima. Bata sameshi a d'akin ba amma taji motsin ruwa a bayi alamar Yana wanka. Hakan ya bata damar Kara gyare d'akin ta feshe shi da turare a cikin wardrobe d'in shi ta d'auko mishi kayan sakawa wasu na Shan iska mara nauyi ta ajiye Su gefen gado bayan ta feshe Su da kalar turaren daya ke amfani da shi. da fitowar shi yayi tozali da ita cikin irin shigar da yafi so a jikin ta Sai da ya lumshe ido yayi godiya ga wanda ya bashi Fateema sannan ya Karaso gare ta inda ta tare shi kamar ba ita ba sosai ta bashi mamaki domin da kanta ta tsane mishi ruwan jikin shi ta shafa mishi Mai da turaren jiki ta taje mishi gashin kan shi ya kwanta yayi luf-luf sannan ta bashi kayan da zai saka sannan ta d'auki Wanda ya cire ta kaisu cikin wata drower inda suke tara Kayan wanki.




Ya bi ta da kallo lokacin da yake saka kayan ganin Kayan abinci a d'akin shi yau ya tabbatar mishi cewar da gaske take ta canza komai cikeda zumud'i ya gama saka Kayan inda ya sameta bisa lallausar garass capet dake tsakiyar d'akin tana zuzzuba musu abincin ya zauna daf da ita ya rad'a Mata wani Abu a kunnen ta bansan me ya gaya Mata ba naga Dai tayi murmushi sannan ta ajiye abinda take ta manna mass kiss a gefen kumatu " *I love you* " ta fad'a kanta a sunkuye farin ciki ya Kara lullube Fahad haka Fateema ta zama? ya Tambaya a ransa "Alhamdulillah" ya koma fad'a a fili. Abincin suke ci amma dukkan Su ba Su maida hankali ga abincin ba domin dama ba yunwa suke ji ba wasannin Su suke da tsokanar juna haka dai har suka kammala zuwa lokacin an fara Kiran sallar isha yashiga bayi ya d'auro alwala ya tafi masallaci ita ma tashin tayi ta harhad'a kayan abincin ta mayar kitchen ta kimtsa wurin sannan takoma d'akin ta tayi alwala tayi sallar farilla




tana addu'a ya shigo ya zauna gefen ta lokacinda ta shafa addu'ar ta mike domin yin nafila shima ya mike ya shiga gaban ta Yana fad'in "yau jam'i zamuyi Ni da mata'ta" ba musu ta bishi sukayi bayan sun kammala ya koma umartar ta suka mike sukayi wasu guda biyu Inda suka d'auki lokaci Mai tsayi suna godewa Allah bisa barin Su tare dayayi dakuma neman zaman lafiya Mai d'orewa a tsakanin Su daganan Yarima ya fara janta a jiki. da wayau ya kaita bayi da rigima da komai ya rabata da kayan jikin ta ya sake musu ruwa Masu sanyi wanka na farko da ya taba yi tare da Fateema Sai yaji kamar kar Su fito amma daya tuna da muradin shi a yau Sai kawai ya d'auko ta cancas bai direta ko Ina ba Sai bisa gadon ta a lokacin sanyi take ji sosai Sai kudundunewa take a jikin shi shikuwa dama haka yafi so ya shiga sarrafata cikin salo da kwarewa tun suna gano kan Su har suka yi nisa da wannan duniyar suka daina gane komai (ganin hakan yasa na had'a Yan papers d'ina nace bari inabawa yarima guri domin cike burin rayuwar shi, a kunne na rad'awa Fateema asuba ta gari lolz)












*Yar'mutan Arkilla* ✍
💞💞💞 *yaya*💞💞💞
💞💞 *fahad*💞💞
💞💓💞
💓
💞💞💞 *Nawa*💞💞💞
💞💞 *ne*💞💞
💞💓💞
👯💓👯


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*




*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍. . *280* *The* 🔚.










Washe gari misalin karfe hud'u na asuba ta farka domin Yarima kam ko baccin bai samu ba tunda ya Sami Fateema bai koma gane komai ba Sai bayan yasami nutsuwa Sai a lokacin ya lura da halin da take ciki da Tsanani wuya da galabaita hankalin shi yayi mutukar tashi sai kuka take mishi tana kiran Goggo, cikin Daren ya Kai ta bayi ya gasa Mata jikin ta bayan ya tsaftace Mata shi har ya kwantar da ita bata daina kuka ba yashiga aikin rarrashi da bata baki Yana lailayeta da hannayen shi a haka yasamu bacci Mai nauyi ya d'auke ta a cikin baccin ma tanata shesheka da sauke manya-manyan ajiyar zuciya Allah sarki Fateema Sai tausayin ta ya mama shi tsananin so da kaunarta suka Kara bin sassan jikin shi, tun da tayi baccin yake makale da ita idon shi kyar akan ta ya kasa bacci har izuwa yanzun da ta farka. Ganin idon shi tamas ya tabbatar Mata da bai rintsa ba tausayin shi ya kamata tana shirin janyo shi jikin ta Sai ta tuna da abinda ya faru a Daren jiya. da sauri ta sake shi sannan ta kudundune fuskarta a mayafi yayi murmushi "feel free Teema na, a yanzu ke cikakkiyar mace ce, ina tayaki murna na samun nasarar kawo budurcin ki gidan mijin ki. Fateema ke babbar mace ce wadda irin ta ke wahalar samu a wannan lokacin, zanyi iya kokarina wajan ganin ban koma rasa kiba kece rayuwar Yarima Fahad" ya fad'a yana had'ata da kirjin shi lokaci d'aya taji duk wani ciwo da rad'ad'in da take ji dun kau, soyayya da kaunar mijin ta suka mamaye ta ta rugume shi tsam Tana hawayen farin ciki da godiya ga Allah da irin tsare-tsaren da yayiwa rayuwar ta. hakika abin farin ciki ne ga kowacce mace ya kasance her first love been her husband. Yarima ya mike ya d'auki matarshi suka shige bayi sukayi wanka suka fito tare suka gabatar da sallar nafila sannan ya fita masallaci ya barta Tana shirin kabbarta farilla. A wunin ranar ko tsinke bai barta d'agawa ba shine ya wuni yimata hidima yana tarairayar t. Bayan kwana biyu yazo mata da passport na barin kasa ya tabbatar mata maganar zuwa aikin hajjin nan ce ta taso kasancewar an fara d'aukar mahajjata an riga angayawa su Baffa suna can suna shirye-shirye. tayi marin cikin jin hakan bayan kwana uku aka kira su su duka suka tafi Mai martaba da Baffa, Yarima da yaya Bashir da Umma da kuma Fateema abin dai sai wanda ya gani. A daddafe ya samu aka gama aikin hajji suka dawo gida domin yayi kewar matar shi matuka ita kuwa ko ajikin ta yanzun ma da suka dawo d'akin Umma ta sauka ganin Goggo a gidan ta sauka kafin gobe a kai su kukunba Yarima sai zagaye yake ya rarasa yadda zaiyi ya sami Fateema bayanda ya iya haka ya hakura ya koma ya kwanta can cikin dare ya ji shigowar ta Umma ce ta korota tace taje gidan ya hakannan da sand'a ta shigo dan tun da suka iso ta lura da take-taken sa. Hmmm bata san idabshi biyu ba ta shige bayi tayi wanka ta fito Tana sand'a saida ta murje jikin ta da mai da turarukan ta sannan ta kwanta a silale azaton ta Prince bacci yake sai ji tayi an rungume ta ta baya ido waje ta juyo Tana kallon shi cike da tsoro sai ta bashi dariya ya kuwa yi mai sar sa sannan yace "yi hakuri kanwata ki taimaka min wlh a hanu nake, kuma bazan miki irin na wancan karon ba i promise" hawaye ne suka ciko idon ta "Allah yaya ni tsro nake ji" ya shiga share mata hawayen yana rarrashinta da haka har ya cimma abinda yake So. Washe gari da kwarin ta ta tashi ba kamar wancan karon ba karfe tara sukayi breakfast suka shiga gida dan gaida iyayen su suka gaishe su. Sun d'an taba hira a nan kafin ya tashi ya fita fada saboda masu zuwa gaisuwar barka da dawowa. Ya barta nan tare da gwaggo da Umma suna shan hira. Karfe uku na yamma aka kai su Umma kukunba. daga ranar Hajiya Fateema da mijin ta suka zama irin masoyan nan da basa son rabuwa ko kad'an, bata so yarima yayi nisa da ita haka shima a nashi bangaren ga wani irin so na Fateema dake kara mamaye ilahirin sassa da gabobin jikin shi jin ta yake kamar ransa tattali da kulawa kam sai wanda ya gani. haka satuttuka da watanni suka shud'e wata shida da dawowar ta su Fateema ta fara laulayin ciki Allah sarki Yarima Fahad sai ya kara zama wani abin tausayi ko motsi tayi sai ya tashi koda kuwa a cikin bacci ne, farin ciki ya lullube iyayen kasancewar Yarima kad'ai suka haifa a duniya. gata na duniya kam Fayeema ta same shi bayan watanni tara ta santalo d'an ta, fari sol mai kamada Uban sa. Farin ciki kam ba'a magana duk inda ka duba yan taya murna ne ga d'aukacin iyalan mai martaba. A ranar suna kuwa mai jego tazama tauraruwa abar son kowa, d'aukacin mutane mota biyu aka ciko daga kukunba na yan'uwa da abokan arziki ina aka sha biki naji da fad'a ilahirin membres na Nasmat novel duk sun halarci bikin haka ma na King boy Isa novel, (King hadda bada babbar jaka yace Hadiza hadi ta ciko masa da kayan makulashe lolz 😝) haka membres na Ama Alhaji kabir novel, ga yan gidan Asmart &deeyart ga na Maryam Ameen kai gaskiya su Yarima sun ga baki yaro yaci sunan Aliyu taron suna kam ya kai taro garin gombe ma ya shaidi hakan. Tun daga wannan ranar alkhairai suka kara kunno kai a gidan sarautar. Bayan shekaru Uku dana koma gidan a falon Umma na sami Aliyu yaron Fateema yanata kiriniya yana wasa da Umma. A sashen Fateema kuwa akasin hakan ba tarar domin samun su nayi suna ta jibga kaya a jakunkunan tafiya kallo d'aya nayiwa fufkarta na gano Tana d'auke da karamin ciki suka gama had'a kayan suka fito cike da annuri a fuskokin su dai-dai kofar fita daga sashen nasu suka tsaya tare suka kalli juna suka saki murmushi ya sanya hannayen sa duka biyu ya tallafo kumatun ta cikin sigar soyayya ya fara magana "Yau na kudur ta aniyar cika miki burin ki matata ina yi miki albishir da cewa lokacin da kafarki zata koma tako nan gidan to kin zama cikakkiyar likita" tayi murmushi Tana fad'in "kai cikakken namiji ne yaya na, na tabbata zaka iya duk abinda kayi niyya, godiya ga Allah daya bani miji mai riko da alkawari sakallahu bi khair" "na gode da yabon ki matata sai alkawari na biyu dazan miki shine na bayar da aikin gina miki babbar asibiti wadda na tabbatar kafin mu dawo an kammala ginin filin yana nan bayan mu direct za'a fitar miki da kofa daga cikin sashen nan zuwa cikin asibitin ki ina kaunar ki matata" farin ciki ya lullube Fateema ta rungume mijin ta cike da murna "wayyo Allah Yaya na na gode Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa Allah ya biyaka da mafificiyar aljannar sa" "Ameen Teema na Allah ya sauke ki lafiya " yaja hannun ta suka isa sashen Umma da shigar su yaro Aliyu ya rugo gun su da gudu "oyoyo dady na momy ina zaki?" Yarima ya kalle dhi cike da mamakin wayo irin na yaron kamar ba d'an shekaru uku ba ya tsuguna dai-dai tsayin yaron yace "inda nace maka zamuje mana boy, ko ka manta ne?" "Oh na tuna dady, inda zakayo corse kazama babban lacturer ko?" "thats my boy nasan bazaka manta ba" Umma ta fito daga d'aki Tana fad'in "a'a matafiyan har sun fito?" "mun fito Umma" inji Yarima Umma tayi musu addu'a da fatan alkhairi tareda fatan Allah ya bada abinda zaije nema (kamar yanda ya gaya musu zaije wani course ne na shekaru bakwai amma zasu dinga zuwa hutu lokaci-lokaci) shine fa Umma ta dage bazai d'auke mata Fateema kuma ya raba ta da Aliyu ba dole ya bar mata d'aya hakan ne yasa zasu bar Aliyun gida tun jiya sukayo sallama da mutanen kukunba tare da rakiyar mai martaba aka kaisu filin jirgi a gaban iyayen da d'an su jigin su ya tashi suka bar kasar haihuwar su zuwa Ijeep neman ilmin matar sa. A kasar ijip sun sami tarba mai kyau da kyakkyawan masauki gidane sukutum aka mallaka musu dukayi sati d'aya suna hutu a sati na biyu ne ya nema mata admission a wata babbar jami'a wadda aka gina ta musamman domin karantar likitanci duk fanni da mutum yake da bukata Yarima kuwa makarantar horar da malamai ya shiga domin ya samu gogewa akan lacturing bayan yan watanni karatu ya kankama na kowannen su sai dai a bangaren Fateema Tana fama da d'awainiyar ciki cikin da yariga ya tsufa dai-dai lokacin ne kuma suka sami hutun karshen shekara. Sosai taji dad'in samun hutun na watanni hud'u hutun bai Kai sati d'ayaba ta haihu inda Allah ya azirtasu da ya'mace a nan ya d'auko wata likita ta Riga kula da Fateema da babyn ta Su kad'ai suka aha suna inda yarinya taci suna Ameena mutanen gida kam sundai ga baby a photuna da vidio call, yarinya Meena Tasha gata da tattali Sai suke jinta kamar yar'fari bayan watannin hutu baby ta fara kwari yar raino aka samowa Fateema wata dattijuwa musulma Mai suna Aysha raward. Ita ce Mai kula da Meena kafin Umman ta ta dawo daga school karatu kam Fateema ta dage babu kama hannun yaro shine ma yasaka ko hutun shekarar farko basu Sami zuwa ba a hutu na biyu ne suka je Nigeria inda suka sha tattali da tarairaya yaron Su Aliyu ya Kara girma da wayau har an sakashi nursery yaro d'an 5yars soyayyar Fateema da Yarima Fahad kam sai wabda ya gani kullum idan ka gansu Sai kayi zatan ko saurayi da budurwa ne, haka hutu ya kare suka koma egeep rayuwa tacigaba da tafiya satika suna ture watanni su kuma suna ture shekaru hausawa Dai sun ce komai yayi farko zai yi karshe yau Dai Allah ya kawo karshen karatun Fateema Allah yayi ta kammala suk kuma dawo gida Nigeria inda suka zowa da Familyn da wani sabon al'amari wato Fateema ta zama cikakkiyar likitar Mata abin mamaki da al'ajabi bangare d'aya kuma abin fahari domin an kammala ginin asibitin ta Mai suna (Mrs. Yarima women hospital) shi kanshi Mai martaba bakaramin dad'in al'amarin yaji ba gagarumin biki ya shirya musu inda yan'uwa da abokan arziki suka zo taya murna ta Sami cikakkun takardu na shaidar zamanta likita Mai zaman kanta tunda suka dawo busy suke kullum cikin shirye2 suke komai na dangane da Kayan aiki sun gama had'uwa hatta wayanda akayo order sun iso, an gama Diban ma'aikata horses da wasu likitoci Mata Alhamdulillah yau itace ranar da aka kebe domin fara aiki a asibitin Dr Fateema masha Allah jama'a kamar jira suke asibiti ta cika ta tamgatse ayau burin Fateema ya cika a rayuwarta babu abinda ta tsana kamar ta ga Mata musulmi a hannun likita namiji Wanda akasarin Su ma ba musulmi bane. Yau gata ga yan'uwanta Mata Masu neman agajin mace yar'uwar Su. idan tana ganin Su a gabanta Sam bata jin kasala ko lalaci aiki takeyi tukuru Yarima tun Yana damuwa Yana cewa ta huta har ya gaji ya barwa Allah yanzu yaran Su uku Aliyu (littlePrince) yanzu ya zama matashi Mai shekaru goma sha d'aya Sai kanwar shi Meena yar shekara takwas Sai karamin Su Al'amin d' an shekara hud'u yara Yan gata ta gaba da baya duk inda suka yi dad'i da gata suke sha fannin iyayen Su ko na kakanin Su baremma in sunje hutu a gidan kakanin su na kukun ba ko kuma in anclule Fa'eez d'in Su yaxo daga sokoto dashi da yaran sa da matarsa Anty Sameera wadda yanzu kawabce ne Mai karfi tsakanin ta da Fateema haka Yarima da Fa'eez da kuma yaran Su duk da ba koyaushe ake had'uwa ba Su Fa'eez d'inma sune Masu yawan zuwa garin gombe kam sun more sun mance matsalar ciwo takai Su ga likitoci maza sadai jarumar Su Mai burin share kukan Su *Dr Fateema* tammat bi hamdallah dukkan yabo da kuma godiya sun tabbata ga Allah (s.w.a) daya bani dama da ikon kawowa karshen wannan labari na *Yaya Fahad Nawa ne* labarin dake d'auke da sakonni daban-daban jigo acikin Su shine








*HAKURI* musamman gare mu mu yan'uwa Mata ma dage mu zama Masu hakuri domin shine solution na kowacce matsala ta duniya duk wani kalubale da zaki fuskanta Ki saka hakuri a gaba Wanda ya jarabce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login