Showing 30001 words to 33000 words out of 57158 words

Chapter 11 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt

07 Feb 2025

5527

baxan iyaba tafada cikin disheshiyar murya kafin tasilale daga jikin momy tararrafa ta isa gaban dady ta tsuguna wlh danayi tunani irin wannan daban yanke shawar barin gidanba dady xama xanyi duk abunda xa,acemin ace koma menene xan jura amma baxan iya jurar ganin mutuwar iyayena sbd wani banxan tunani nawaba








Tafasheda kuka nagode dady nagodewa Allah daya qaddara xuwana hannunku tabbas ku iyayene kuma nagari nagode dady momy nagode sannan ina neman alfarmarku akan gobe ku maidani gida xanje in rayu da iyayena gatana kuma farin cikina






Dady da momy suka kalli juna sukayi murmushi alhmdllh inji momy madalla da yarinya mai sauqin kai da xurfin tunani insha Allah gobe dakaina xan maidaki gidanku kiyi shiru ki kwantarda hankalinki kinji
Allah yayimiki albarka






Damn! Yaji saukar maganar a xuci tamkar an buga mishi guduma aqirji yakafe iyayen nashi da ido jiyake kamar yace musu abinda xaku aikata ba dai dai bane wato baya goyon bayan tafiyar fateema




















*Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all😘
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *yaya*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *fahad*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ’“
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *Nawa*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *ne*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ‘―πŸ’“πŸ‘―














*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐
⭐






*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍












*β€’196/200β€’*




















Momy tamiqe idonta tam da hawaye ta isa ga fatee takama hannunta ta dagata tanufi dakinsu da ita tana qara lallami da kwantar mata da hankali suka fice






Fa,eex yabi bayansu dakallo saida suka qurewa ganinshi wani irin xafi da qunq yakeji na daban a qirjinshi Wanda baya tunanin yatabajin irinshi a duk tsayin rayuwarshi wata nannauyar ajiyar xuciya yasauke alokacinda yaji andafa kafadarshi yadago saiyaga mahaifinshi tsaye akanshi xai saukarda da kanshi qasa dady yasaka hannu yatare tahanyar riqe habarshi ya qura mishi ido kafin yace yau mexan gani arayuwata? Son hawayene a fuskarka abinda bantaba ganiba son meye matsalarka me ka sirranta aranka gameda wannan yarinyar maimakon yayi magana saima ya fasheda kuka tareda rungume dadyn nashi ikon Allah nanfa dady hankalinshi yakuma tashi






Fa,eex yakira sunan dan nashi ahankali cikin sassarqewar murya meye wannan mekefaruwa ne? Cikin muryar kuka fa,eex yafara magana dady inbaxaka mantaba nidakai baxamu iya qirge adadin lokutan dakake sakani agaba kace infitar da matar daanakeso ba, amma haryau bantaba kawo maka koda maganar mace ba dady yanumfasa sannan yace dady wlh bantaba ganin wadda tamin din bane tunda nake arayuwa bantaba arba da macenda nakeso kuma naji nakamu da santa alokaci daya irin wannan ba, dad kwanan mu daya da ita amota amma inaji kamar da ita jafara rayuwata dady inasonta kuma ita kadai ita kadai nakeso dadyna wlh baxan iya bahu ita ba ya kuma fashewa da kuka rairas kamar qaramin yaro






Dady yakai maqura da rikicewa yadago fa,eex daga jikinshi suka fuskanci juna tabbas yaronshi akan gaskiyar xuciyarshi yake fada aawayar idonshi yagano hakan, a yau dady yagama sallamawa SO ya ajiyeshi a matsayinda dacan baikaishi ba agareshi tabbas SO daban ne dan tundayake tun fa,eex yana matashin shi baitabayin kuka agabansuba koda yanayi din, duk yanda akakai ga bata mishi rai saidai kaga idanun nan sunyi jajir amma ko hawaye baitaba xubdawa agabansu ba, kai hatta kakaninshi iyayen dady dasuka mutu rana daya tahanyar hatsarin mota fa,eex baiyikukaba




Dady yaxubawa dan nashu ido kawai yakasa cewadashi komai tabbas wannan shi ake kira ga qoshi ga kwanan yunwa domin kuwa inda sauran wani abu dayaragewa dady wanda yakeso yayi adujiya kafin mutuwarshi to baifi yaga babban yaronshi yakawo mishi wacca yakeso dakanshi ya daura aurensu ba, to ayau gashi fa,eex yakawo yarinyar saidai yasan ayanda yaji lbrn fateema ya tabbatar tana komawa iyayenta xasu iya maidata gidan mijinta dukda cewa ba santa yakeba amma yalura da iyayen masu son hada kan yayansu ne hmmmmm yasauke numfashi rigiji gabji kenan






Momy dake tsaye aqofar dakin tana saurarensu taqaraso dakin jiki ba qwari takama hannun dan nata taxaunar dashi kan kujera itama ta xauna dadyma yaxauna gefensu momy tashafa kan fa,eex kayi haquri yarona kuma ka kwantar da hankalinka babu abinda yagagari ubangiji kakai kukanka gareshi mumanan dukanmu xamu tayaka da addu,a son nikaina inamaka kwadayin samun fateema hankalina ya kwanta da yarinyar kuma insha Allah xanyi iya qoqarina naganin kasameta muddin da akwai rabon aure tsakaninku




Da ire iren wayan maganganun ne. Suka dinga rarrashin yaronsu har suka samu yafara sakkowa


Fateema kuwa aranar kuka takwana tanayi baji ba gani su saj sunata aikin rarrashi dan momy tagaya musu komai


Haka fa,eex ma aranar shima bai samu yarintsaba yanayiwa mayarda fateema ga iyayenta kallon wata hanya daxata yanke duk wata alaqa dayake qoqari qullawa da ita






Abirnin gombe kuwa amasarauta wato gidansu yarima hankalin mai martabane kadai yatashi da batan fateema sukuwa iyayen aikin ko ajikinsu saidai shima yariman yanacikin damuwa akan lamarin dominkuwa yaga hacin ran dabai taba ganiba a idon mahaifinshi akan lamarin har marinshi yayi alokacinda yace shibaxaije nemanta ko inaba, mari yasha abinda baitaba tsammaniba mahaifinshi da ko yatsa baitaba daga mishiba wannan ne dalilin damuwarshi aranshi yana jinjina abinda xai faru idan mahaifinshi yaji yasaki auren daya daura mishi da fateema




A kukumba kuwa kusan dimuwa ce takama iyayen fatee jin wai tabar gidan bada sanin kowaba duk dacewa bawanda yasanda lbrn sakinta yarima yayi, amma mahaifiyarta goggo tayi amanna cewar fateema baxata bar gidan abanxaba kasancewar ba auren dole suka mata ba




Agari kuwa lbrn yaxaga ko ina cewa fateema ta gudu daga gidan mijinda tafi SO fiyeda kowa arayuwarta, wannan ne yasa mafi yawan mutanen qauyen suke fadin wataqila da akwai wata maisonshi acan ita tamata asiri ta fita, dan aganinsu banxa baxata raba fateema da gidanba kuma dayawa sunyi amanna da hakan din wato batanta yashafi asirine wannan ne yasaka duk wani ko wata masu sonta a qauyen suka duqufa dayimata addu,a
















Hmmmmm nikam dai ina tsakiya, kome readers sukuma xasuce akan wannan?πŸ€”πŸ‘€
































*Nasmy ce*😍
Yar mutan Arkilla love you all 😘
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *yaya*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *fahad*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ’“
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *Nawa*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *ne*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ‘―πŸ’“πŸ‘―














*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐
⭐






*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍










*β€’201/205β€’*












Washe garin ranar takasance assabar agidan mai martaba kowa da abinda yakeyi wato mai martaba yanacikin damuwa da tashin hankali na batan yar dan,uwanshi inda abangare daya hjy umma mahaifiyar fahad itada yayarta momyn laxeera suka saka ranar amatsayin ranar daura auren yarima fahad da laxee misalin qarfe tara nasafiyar wanda sam ba,a shiryashi dasanin mai martaba ba a wani babban hotel suka dauro auren tsakanin iyayen laxeera maxa dakuma wasu dai daikun manyan mutane najikin mai martaba wayanda aka gayyata asace




Su shida ne suka qure a babban dakin umman yarima wato da ita da yayarta dakuma ita laxee din dawasu qawayenta uku wayanda basa rabuwa, shawarwari sukeyi akan tarewarta da fahad dakuma yanda xa,a gudanarda shagalin bikin tunda komai cikin sirri akeso ayishi sunfiso yakasance saita xauna dashi xamana mata da miji kafin mai martaba yasan da auren yanda bayanda xaiyyi koda yasani sai haquri tunda mai afkuwa tarigada ta afku




Dukda cewa suna aikinsune da tsifface tsufface ne da asiri amma umman yarima amatuqar tsorace take sbd gudun abinda xaifaru ranarda mai martaba xaiji wannan lbrn na tayiwa fahad aure batareda saninshiba




Momyn laxee ce mai kwantar mata da hankali cewar ta kwantar da hankalinta wannan duk mai sauqi ne idan angama wannan suka tare xasuji da mai martaba ba,abunda ya isa yayi takuwa amince nan suka yanke sutare ayaudin kawai inyaso daga baya idan komai yabayyana ayi shagulgulan bikin




Laxee jitake ayau bawanda yakaita murna da farinciki itada uwarta nagani cikar burinsu yaxo kusa, gurin gyaran jiki sukawuni itada qawayenta da yamma aka saka jekadu da qawayen umma dana momy suka kaita sashennan da aka gyarawa fateema acan ta tare yarima kuwa bashida katabus saidai yanda akajuyashi nashi bi ne kawai dukdacewa yanajin wani daci da tuquqi a qasan xuciyarshi amma baya iya tsallake umarnin ummanshi da yayarta ballatana na sabuwar amaryarshi laxeera




Qarfe tara dai dai ango yashiga dakin amaryarshi wadda yakegani tamkar tauraruwa idan ya hada ido da ita jiyake tamkar bayan ita din babu wata mace aduniya wannan kuwa yana daga cikin tasirin aikin bokansu, kqmar waina haka taita jujjuyashi domin yanaganinta ya xare buqatarta yake a haukace saida tagama garashi sannan daga bisani tabiye mishi tinda dama abinda takeso kenan dan qarasa mallakeshi gabadaya




Fahad haukacewa ne kawai baiyiba daya sadu da laxeera sbd tsumin asurinda boka yayimata dakanshi na wuni daya xaune acikin ruwan tsafi, daganan abubuwa suka fara rincabewa diminkuwa yarima bayaji kuma baya ganin kowa sai laxee


Dasafe tayi waya da uwarta take sanar mata yanda abubuwa suke tafiya dai dai momynta tayi farin ciki sosai nanfa tafara bawa yar tata target daban daban nikam danaji saida naxubda hawaye araina nace lallai rashin sani yafi dare duhu domin kuwa hatta wadda sukayi komai da ita basu bariba wato umman yarima sungama shirya makirci da tuggun daxasu rabata da dan nata gabadaya dama shi suke buqata da abinda ke hannunshi


TofaπŸ™Š






Gabaki daya wunin ranar yarima bai iya fitaba koda masallaci kai sallarma rabonshi da yinta tun wadda yayi kafin shigowarshi gidan yanan maqaleda laxee ko kadan baiso yadaga kota daga bayaso ta bacewa gajinsa haka kuma inya ganta baya iya haqura saiyajita ajikinshi (tirqashiπŸ€”)
Hakasuke nane da juna gidan






Qarfe hudu na yammacin ranar ne wata danqareriyar mota qirar jip tashiga qofar fadar bayan angabatarda gajeren bincike akansu mutane hudune a motar sukaxo sukafaka daf dawata farar mota dake fake agurin alokacin bakowa afilin farking din alokaci daya matanenda ke cikin motar suka firfito ikon god! Fateema ce da abban fa,eex da momy dakuma shi fa,eex din masha Allah dukdacewa suna cikin tashin hankali amma kallo daya xakayi musu dole kace tubarkalla


Sam fateema batayi kuskuren shiga gidan kaitsaye amatsayin yar gidan ba, iso suka nema akayimusu gun mai martaba tareda bayanin sunxoda fateema ne yarinyar da aka saka cigiyarta agidan tv ai dagudu bafaden yanufi qofar fada har yana hadawa da tintibe badan komaiba sai dan sanin yanda mai martaba yatada hankalinshi akan natan na fateema


















*Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *yaya*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *fahad*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ’“
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *Nawa*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *ne*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ‘―πŸ’“πŸ‘―














*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐
⭐






*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍










*β€’206/210β€’*






















Bajimawa yafito tareda wasu mutane daganinsu kasan manya ne masu fada aji afadar daxuwa suka gaisa da dady cikeda karamci da girmama baqo irin na gombawan asali su sukayimusu jagora xuwa dakin baqi na musamman na mai martaba




Kusan tare suka isa da mai martaba dan taqofar ciki yabi dashigarshi kuwa idonshi suka sauka ga abin nemanshi fateema tana rakube abayan momy kamar marainiya mai martaba dakanshi yayi tattaki ya isa gareta cikeda farin ciki ya rungumeta wasu hawaye masu sanyi suka kwararo daga idonshi yata fateema! Yafada yana sauke numfashi ina kika tafi fateema? Meya fiddaki daga gidan abbanki? Lock yadagida fuskarta yace kosaceki akayi fatee? Kigayamin gaskiyar abinda yafaru dake yata kinjefamu acikin tashin hankali Mara misaltuwa gayamin yafada lokacinda ya tsareta da ido ko qiftawa babu




Fateema kam kuka ne ya qwace mata takoma rungume baffan nata tace kuyi haquri yaya baffa dan Allah kumin afwa abisa kuskuren danayi nufin aikatawa cikin rudewa damuwa da rashin tunani kugodewa Allah baffa kuka kugodewa wannan bawan Allah dashida iyayensa tafada tana nuna yaya fa,eex da iyayensa, sai alokacin idon mai martaba yasauka akan kamilallun mutanen yasake hannun fateema ya isa gaban dady ba girman kai yamiqa mishi hannu cikeda sakin fuska sukayi musabaha dady yayi mamakin hakan tabbas wannan sarkin ba girman kai akanshi yadinga kwararo musu godiya da sa albarka akan wannan alkhairin nasu da baida abinda xai biyasu akan hakan




Kowa yanutsu aka xaxxauna aka kawo abinci da abinsha ga baqi fateema kam tanacan maqale agefen mai martaba fa,eex sai satan kallonta yake ahakan saiyaga taqara haskakawa xaman nata gefen mai martaba yaqara fitoda asalin martabar da yadade yanagani a idonta cikin dabara yafitoda wayarshi kamar maiduba wani abu yaita daukarsu photo kasancewar kujerunda suke kai suna fuskantar nasu mai martaba




Bayan kamar mintuna talatin sudady sun dan tsakura kadan daga abubuwan ci danasha da aka jibge musu kowa ya nutsu mai martaba yakalli yarshi fateema yace inajinki yata gayamin menene dalilin fitarki daga gidan nan? Karkisake kimin qarya koki boyemin wani abu dukda nasan ba halinki bane




Falon yayi tsit nantake abubuwan dasuka faru tsakaninta da *yaya fahad* sukafara dawo mata aqwaqwalwa hawayene suka farabin kuncinta kafin takwashe duk abunda yafaru tagayawa mai martaba sannan tadora mishi dalilan dasuka sakata tunanin barin gidan dakuma rufin asirin da Allah yayimata na hadata da fa,eex dayayi






Subhanallah subhanallah innalillahi wa inna ilaihi raji.in abinda suday da manyan mutanen dake gun suka shiga ambatowa kenan fateema kuwa dafe kai tayi tashiga karanto addu.oi da sambatuj rikicewa cikin harshen fulatanci




Nikaina danasan hakan xata faru dana hana fateema sanarda mai martaba cewan *yaya fahad* yasaketa domin kuwa mimmiqewa yayi dagakan kujerar jikinshi yahau karkarwa da qyarma hannu da bakinshi duk motsi sukeyi saidai ba.ajin sautin maganarshi da alama magana yakesonyi amma babu damar hakan cos muryarshi bata fitowa kwata kwata daganan kuma saiya shide ya suma yadaina numfashi innalillahi wa inna ilaihi raji.un addu,a suka dauka Dukkansu sukayikan mai martaba cikin kidima da matsanancin tashin hankali
















*Nasmy ce*😍
Yar mutan arkilla love you all 😘
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *yaya*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *fahad*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ’“
πŸ’žπŸ’žπŸ’ž *Nawa*πŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’ž *ne*πŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’“πŸ’ž
πŸ‘―πŸ’“πŸ‘―














*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
⭐⭐ ©(Z.W.A)⭐⭐
⭐






*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_✍










*β€’211/215β€’*






















Su waxiri da mai fada ne suka yi gaggawar kinkimarshi hankalin kowa awurin yatashi fateema sai rusa uban kuka take kukanda fa,eex yakejinsa kamar ana gugar qahon xuciyarshi da wuqa, suka shigardashi awani qofan daki dake cikin falon akan wani lafiyayyen gado suka kwantar dashi kafin daga bisani sukayiwa likitanshi waya, tsawan mintuna talatin likitan yayi akansa kafin yasaki nasarar dawowar numfashinsa yabawa mutanen dake gurin umarnin barinshi yasami hutu na awa daya




Dady da momy dakuma fa,eex da fateema kaitsaye sashen gidan waxiri aka kaisu kafin cikar lokacin hutunda likita yabuqaci abawa mai martaba dama can matar gidan tasan fateema basu fuskanci wata matsalaba antaresu cikin girmamawa da karamci part daya aka ware musu mai daki biyu da babban falo kowanne daki yanada bayi acikinsa




Afalon sukafar yada xango nanma aka koma gabatar musu da kayan abinci dana sha harmada maqulashe kasancewar aqoshe suke yasa basuci wani abin kirkiba suka bige da hira ta jajanta yanda lamarin ya kasancewa mai martaba lurada iyayen sukayi yaronsu yana buqatar ganawa da fateema yasa suka miqe sukashige daya dakin dake gidan sukabar subiyun afalo




Hakan yasa falon yaxame masu shiru dan acikinsu bawanda yakoma magana tsawom daqiqu fateema kanta yana sunkuye aqasa fa,eex yakasa haqura domin kaikawo da xuciyarshi take masa abisa tunanin dayayi naganin yau xuwa gobe xasu rabuda fateema rabuwarda yakeganinta kamar shine ganin qarshe daxai mata gashi har yau bai isar mata da saqon xuciyarshi ba,




Shine yaqatse shirun tahanyar yin gyaran murya yace fateema! batareda tadago kaiba tace na,am saikuma yakoma yin shiru kafin yadorada fateema kiyi haquri kiyafemin baxan boye miki sirrin xuciyata ba tundaga waccan ranar danafara dora idona akanki naji nakamu da qaunarki xama damukayi dake nakwana daya amota jinsa nayi kamar rayuwata ce tafaro daga wannan lokacin nakamu da sonki fateema, sbd hakanan bbu irin tunanin da banyiba naganin kinbaro gidanku a yanayi da shekarunki sai wata xuciyar tabani kamar kin aikata wani mummunan laifine yasa kika gudo daga gidan iyayenki dukda hakan ban iya rabuwa dakeba saboda tsananin qaunata gareki fateema




Saida yadan ja numfashi kafin yacigaba wannan ne dalilin dayasa nadage da bibiyqrki har saida nakaiki gidan mu sannan nasami kwanciyar hankali da nutsuwa fateema tunda aka haifeni banyi soyayya ba nikwata kwata bansan soba saida Allah yahadani dake bayyanar gaskiyar lbrn dakika bamu ayau yaxamo wata iska da taqara rura wutar so da qaunarki axuciyata ina sonki fateema kidaure kisoni kisakani a xuciyarki, idankikayi hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login