Showing 3001 words to 6000 words out of 57158 words
Chapter 2 - YAYA FAHAD NAWA NE COMPLETE by Nasmatu Muhammad .txt
out you. Yakai hannu yashare hawayen nata baisan ya akayiba yanajin Sonia harcikin ranshi itadin dabance da duk wata budurwar da yataba mu.amila da ita bandir din dollars naga yadamqa mata guda biyu take care, baijira komaiba yashige motar Dan kallon hawayen Sonia na Dada karyar mishi da xuciya dama driver yana ciki tayarwa kawai yayi suka tafi Sonia tabi bayan motar da kallo tabbas Rayuwa ba Prince baxata mata dadiba jiki a sanyaye takoma cikin Gidan dama anan xataci gaba da xama harya dawo tunda Gidan da yan.aiki
*gombe state international airport*
Mai martaba ne dakansa tareda rakiyar fadawansa da xugar motoci sukaxo tarbar yarima fahad a brnin gombe
Basufi mintuna biyar datsayuwa ba jirgin ya sauka inda ahankali passenger's dindake cikinshi sukafara fitowa har akaxokan kyakkyawan matashin Wanda yatara abubuwan alfahari dayawan gaske nafarko yarima kyakkyawane na bugawa a jarida, ga isa da qasaita ga kudi ga mulki sanye yakeda sweats yayi red nic dinshi fari haka takalmin qafarshi yayi kyau sosai fuskarnan na daukeda wannan murmushin nashi sumar nan ta fulanin asali tasha gyara ta kwanta sai qyalli take da daukar ido
Farin ciki ya lullube mai martaba alokacinda yayi arbada Dan NASA shekara biyar kenan saidai suganshi a video call
Dagudu fadawa suka taroshi suka karbe jakar dake hannunshi suna kwasar gaisuwa ya isa ga mahaifinahi sannan ne shima yaxube qasa yakwashi gaisuwa gun mai martaba da kecikin wadataccen farinciki ganin yanda yaron nashi ya girma ayanxu yarima yakai cikakken namiji
Yadago yaron yarungumeshi Allah yayi maka albarka yarona , ameen babana nasameku lfy , lfy qlau yarona
Daganan suka dunguma xuwa gida wato fada gidankam cikeyake tam da al umma , maxa da mata duk Wanda ka kalla xaka gano asalin farinciki sbd murnar dawowar yarima fahad, kasancewarshi mutum ne mai sanyi a garesu dayawan kyautuka
Koda motocin suka tsaya tuni mutanen dake ciki sukayo waje, masha Allah kyakkyawar mace CE fara sanye cikin farar alkebba tasha ado da kuyangi Masu yawa a bayanta , gefenta kuma wata budurwace wadda baxa,a kirata kyakkyawa ba dukda tana cikin Hutu da jindadin Rayuwa itamadai shiga tayi ta alfarma balaifi Kayan dai sunyi kyau amma fa wadda tasakadin π· laxeera kenan laxee, yar yayar mahaifiyar yarima fahad CE, dagudu taxo tayi hogging dinsa welcome home yaya prince we miss u a lot,
yayi murmushi yajanyeta daga jikinshi shima ya isa ga mahaifiyarshi yayi jogging dinta dukkansu suna murmushi welcome home son we miss you miss you too my mom
Itace taja hannunshi suka shiga Gidan gabaki dayansu har mai Martaban
π *Nasmy ce*π
Yar mutan Arkilla love you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*5 star's β¨β¨ online writer's association*π
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’21/25β’*
Awani qayataccen falo mai fadi da yawan ado na hidan darauta traditional ko ina kaduba akan wata lafiyayyar darduma suka xube wadda akan laushinta har qafar mutum ke nutsewa idan yataka ta, an cika dakin da ita ba kujera ko daya sadai mamya manyan titimmai na sarakuna masu kyau da laushi
Bayan sun xauna sai dukkan kuyangin sukayi waje yarage daga mai martaba sai matarsa gimbiya usaina sai yarima fahad dakuma laxeera dakeaqale a gefenshi jerin kayan abici ne dana sha agabansu kala kala laxeera ce tayi saving dinsu cikeda yanga da iyayi
Bawanda yayi magana har suka kammala cin anincin wanda baqaramin dadi yayiwa yarima ba, yayi kewar abincin Hausa sosai mai martaba ne yafara magana cikin muryarnan tashi mai dadin sauraro mai tattareda hikima da mulki yace inaqara yimaka barka da xuwa my son tareda fatan kamaida hankali wajan abinda kakeyi acan yarima da kansa yake qasa yadago sosaima kuwa abbana insha Allah saikayi alfari da ilmina, masha Allah Allah yasa hakan
Ameen inji mom laxeera kuwa langabe kai tayi gefe yaya Prince mekaxomin dashi saida yayi murmushinan yace abubuwa dayawa qanwata
Tayi murmushi yawwa yaya na godiya nake,
Mai martaba yace Allah dai yasa a tsarabar yarima bai manta da qaramar qanwarshi ta kukunba ba,
Gabanshi ne yafadi damm! Sannan afili yaqaqaro murmushin daya xamemishi jiki yace taya dan,uwa xai mamta da yar,uwa rabin jikinshi kaf fa a duniyar nan namuda wasu kamarsu dangi na jini, yafadi hakan ne badan yayo mata tsarabar ba, saidan yasan mai martaba yana mutuqar jin dadi idan aka nuna soyayya ga dan,uwanshi baffa da iyalanshi, Allah yayi maka albarka cewar mai martaba
Fateema ta girma xuwansu yakai uku itada baffanka kuma duk rigimarta ce take kawosu wai ita yakawota taga koda photonka ne, kai daga qarshedai saida aka bata photonka daya ta tafi dashi sannan aoasami xaman lfy
Yarinyar ta damu dakai sosai
Yakoma yin murmushi sannan yace Allah yaqara maka nasara haka nima na damu dasu duka nayi kewarsu sosai. A qasan xuciyarsa kuma cewa yake ai kam dole ta damu dani tunda gashinan ta hanani kwanciyar hankali badan ita jinina bace danace ko mayya ce ita
Maganar mai martaba ce tadawo dashi inda yakecewa wannan yana qara amintar dakai axuciyata nuna so ga ahlina yana dada tabbatarmin cewa kaidin jini na ne, ina alfahari dakai yarima yaji dadi harcikin ranshi dan arayuwa bashida wani burin dawuce yaga ya faranta ran iyayensa musamman mai martaba wanda yafi shaquwa dashi fiyeda mahaifiyarshi domin shi yakasance mai yawan jan yaro ajiki da nuna mishi qauna da kulawa
Nagode abbana badan nagaji dayawa ba da ayau xanje na gaida baffa na nayi kewarsu sosai mai martaba yaqara jindadi aranshi wanda hatta fuskarshi saida ta nuna yace bakomai yarona kabari kahuta xuwa gobe dan nasanar musu da dawowarka tun shekaran jiya, duk da bada. Xuciya daya yace xashiba amma yaji dadin farin cikin dayajefa a xuciyar mahaifin shi,
Mamanshi tayi murmushi wato mu anmanta damu nida yata ko? Mai martaba yace mun isa? Mantawada uwar gida ai saidai in rai yayi halinsa, tayi murmushin jin dadi yarima ya miqe bari inshiga xanyi wanka indan huta xuwa anjima xan fito
Ok afito lfy Allah yayi maka albarka ya karemin kai daga sharrin mutum dana aljan ameen ya amsa cikeda jin dadin addu,oin ya fita laxeera ta miqe dasauri tabi bayansa iyayen suka bisu da murmushi
Duk inda suka gifta bayi da fadawa xubewa suke suna kwasar gaisuwa har ya isa part dinsa ko ina tsaf angyare komai an goge, yaji dadin hakan abakin gadonshi yaxauna sannan yakalleta yadai sis? Ta wani shagwabe fuska tsarabata mana yaya Prince, hmmm haba laxee saikace wata baby baxaki bari indan hutaba kinga xuwa anjima sai in baki
Sanin halin yarima yasa tace ok ahuta lfy, dan tasan yatsani ayimishi musu arayuwa, saida takai qofa tajuyo ba,abinda kake buqata,? Yace bakomai sannan ta fice
Shikuma yarage kayan jikinshi sannan yashige wanka
*Asalin su*
β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’
π *Nasmy ce*π
Yar mutan arkillalove you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*5 star's β¨β¨ online writer's association*π
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’26/30β’*
Malam usman ummar shine asalin wannan ahli kuma uba ga mai martaba sarikin gombe bello, da dan uwansa malam aliyu na kukunba, wato asalin su duka a qauyen kukunba ne na qaramar hukumar dukkum ta jihar gombe
Shidai wannan qauyen garine mai dimbin tarihi da al,ajabi maxauna cikinshi kuma fulanine xalla babu bare ko wata qabila a garin duk fulani ne masu tarin arxiqi na dabbobi sosai ba dan kadan ba, kowannensu a jeji yake ajiye shanunsa domin yawansu ya wuce ayi kiwonsu gida ko qofar gida, baremma gidan malam usman umar kaf garin ba wanda yayi arxiqinsu na dabbobi dana noma wanda shine aikin mutanen garin rani da damina
shidai malam usman ummar shine mai anguwar qauyen awancan lokacin yayinda baffanshi dan,uwan mahaifinshi ke sarauta a birnin gombe, ranan sai Allah yayiwa baffan nashi rasuwa kawai baxato bayan angama kwana ukun, rasuwar margayin mutane suka xowa da malam usman ummar da maganar sunyanke shawara shi xasu nada sarautar gombe sbd can cantarshi bayanda ya iya dasu haka aka nadoshi daga can koda yadawo gida mutane sukayita mamaki dukda cewa ya cancanci hakan,tunda baffan nashi bashida yaya nakanshi
Nan yayiwa al,ummar kukunba nisihohi da kuma sabon shugaba daya nada musu wani attajirin bafulatani mai kirki, yayanshi maxa guda biyu kuwa bello da aliyu suna samari alokacin yayiwa kowannesu aure agidanshi na qauye yace baxaiyuwa yakoma birni dasuba al,amarin kiyo da gwanakinshi xai tabarbare yace suxauna nan da iyalansu sucigaba da kula da dukiyarsu, sannan yadauki mahaifiyarsu da rakiyarsu data mutanen gari yakoma nirnin gombe yacigaba da sarauta, yaran kan xiyarcesu lokaci xuwa lokaci
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah matar malam bello ita tafara haihuwa Allah yabata da namiji ranar suna mahaifinsu mai martaba yaxo yaradawa yaro suna fahad, sannan itama matar qanin tahaifo nata akarada mishi suna bashir
Sukacigaba daxaman lfy wayannan yan,uwan malam bello da aliyu suna matuqar son junansu, saida fahad yakai shekara goma sha biyu aduniya sannan Allah yaqarawa matar malam aliyu haihuwa inda tahaifo yarta mace ce itama ranar sunanta mai martaba yaxo yarada mata suna fateema
Fateema kyakkyawace ta gaban kwatance asalin gulani Allah yayi mata baiwa iri iri, saidai ita takasance irin yarannan ne masu qiriniya batajin dadi inbatayi tsokana ba kamar yanda bata yafe abu idan akamata badaidaiba saita rama haka ta taso tundaga quruciya har girma
Shekarar fateema daya a duniya Allah ya yiwa mai martaba malam usman umar rasuwa dashi da matarsa asanadiyyar hatsarin mota aranar mummunan saqo yaxowa al,ummar kukunba ansha kuka babu kamar yayanshi dan sunsan sunriga da sunyi rashin da bayada kama, bayan kwana uku nan ma al,ummar fada sukayanke shawarar nada babban dansa malam bello, aka yi nadi lfy aka rakoshi sallama da yan,uwa
Tun alokacin ba yanda bayyiba da dan,uwanshi akan yabiyoshi birni shi xai kawo wayanda xasu dinga oularmusu da gwanaki dakuma dabbobi, amma fir malam aliyu mahaifin fateema yaqi yace sam baxai kauce fadar mahaifinsu ba, dole ya haqura yadebi iyalinsa suka tafi, hakan baikawo tangarda ga xumuncinsu ba sukan xiyarci juna lokaci xuwa lokaci, dakomawar su yabiyawa fahad babbar makaranta anan yafara primary
Aqauyen kukunba kuma ansami sauyi sosai mai martaba bello ya gina musu makarantu na primary da secondary da islamiyya, tareda xuba qwararrun malamai ya inganta musu ruwan sha, da qaramar asibiti,
Gidan dan,uwansa kuma ba,abinda suka rasa najin dadin rayuwa gida maikyau ya gina musu ginin xamani yaxuba musu kayan amfani da gadaje hatta fateema dakinta daban dakuma lafiyayyar katifar ta, kayan sakawanta iri iri shiyake dinko mata daga can tun tana qaramarta har yanxu datakeda 15years
Soyayya ta xahiri da badini yakewa dan,uwansa da jama,ar qauyensa, yarima fahad kuwa tunda yabar qauye rayuwar birni ta shigeshi yamanta da qauye kuma yatsaneshi dole yake xuwa badan yanasoba,
Kawai dan mahaifinsa yaji dadi haka mahaifiyarsa dake itama iyayenta sun rasu yarage daga ita sai yar,uwarta itama abirnin gomben take Auren wani mai kudi itace mahaifiyar laxeera umman yarima tace tadawo Gidan ne a wannan dawowar daxaiyi koxasu daidaita yasota Dan taji maimartaba na maganar yimishi aure wannan xuwan nashi
.
*wannan kenan*
.
π *nasmy CE*π.
Yar mutan Arkilla love you allπ
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*5 star's β¨β¨ online writer's association*π
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’31/35β’*
*Cigaban labari*
_washe gari_
Aqauyen kukunba malam ne dakanshi yaketa fama da fateema da innawuro ta biyomata suje makarantar boko
Amma fir tace ita baxataba dan kar yaya fahad yaxo har yatafi basu dawoba, tunda baixo jiyaba to tasan dole yau xaixo, kinaji autan goggo tashi kitafi inyaxo nidakaina xan tura bashir yakiraki kinji
Shiru taqarayi shimadai shurun yayi dan yafara quluwa gashi ance test sukeyi a makarantar, haryadago daxafinshi saita rigashi magana
baffa awadi alkawal tu,awari anoddayam? Tayi tambayar kamar xatayi kuka, Allah sarki saita bashi tausayi wannan yariyar lallai tadamu da fahad sosai take qaunarshi, dan,uwa mai dadi Allah yasa kudore haka,
Saida yatausasa murya tukun yace eh nayi alqawari xansa akirakin. Idan yaxo din, sannaj tamiqe a sabule tashiga dakinta ta canxo kayainta xuwa uniform masha Allah kayan sun mata kyau sosai darkgreen colours ne riga da wando sai dan matsakaicin hijab dinta fari, fuskarnan fayau babu digon kwalliya wannan dabi,arta ce batasanyin kwalliya tace to muntafi kumana addu,a test mukeyi wanda dagashi sai final exam, baffa yai murmushi Allah yabada as,a fatee ainasaj kinada qoqari saidai inkinsaka shashancinki. Dan malamanku nagayamin kinada qoqari sosai maida hankaline nakyayi
Batace komaiba taja hannun innawuro suka fice, giggo tai murmushi kaga waitayi fushi sukayi dariya yace fateen kenan ai nibansan inatadakko wannan halinna badamar amata magana saita sille wai tayi fushi bari inatashi inkira bashir yaqara gyara babban dakincan kekuma dunda ta tafi tashi kidora kinsan tafiyar wuri sukeyi kuma tareda yaya xasuxo tace to ta miqe tanufi madafinsu shikuma yafita
Qarfe goma darabi angaka komai anshare ko ina, gidan yayi fess dashi sai qamshin turarukan wuta ketashi goggo nagani tanufi dakin waje na saukar baqi da qaton tray itamadai ya cancana adonta daidai gwargwado
Qarfe shadaya motocin gidan sarki sukafara parking a qofar gidan mota uku daya yarima ne da mai martaba, sai driver sunyi kyau sosai dukkaninsu suna sanyeda kaya na gidan sarauta na alfarma,
sauran kotoci biyun kuma duk yan rakiyane da fadawa
Malam aliyu naxaune aqofar gidan yataso dasauri yagaida sarki cikeda girmamawa shikuwa mai martaba farincikin ganin dan,uwan nashi yaqi boyuwa fuskarnan faran faran yarungumi qaninshi nayi kewarka dan,uwana fadawama sukafara miqa gaisuwa, saida suka gama tukun yarma ya isa garesu harqasa yatsuguna gaban baffa yana gaisheshi baffa yadagoshi yamiqar dashi alokacinda yake amsa gaisuwar masha Allah, yaronmu shima ya girma ixuwa babban mutum, dai dai lokacinne hashir ya iso wajan dasallama yaje ya suguna yayi gaisuwa a gaban sarki mai martaba ya jashi xuwa jikinshi yawwa yarona yakake ina yar,uwarka? Yakalli baffa banga yata ba, wadda kullum naxo ita nake fara gani?
Baffa yace ta tafi makaranta kai bashir jeka kirata bata tafiba saida tasa nayimata alqawari xankirata in yayanta yaxo, damn! Gabanshi yayi mummunar faduwa danyanxu yagano wadda suke magana, yarinyarda take takurashi tahanashi saqat aduk sanda yashigo garin daqyar yake rabuwa da ita, jiyayi ana cewa yarona shigo daga ciki mana saida yadan xabura koda yadago saiyaga kowa yaqarasa cikin dakin baqi da aka. Bude musu saishi kadai awaje
Qasa qasa yai tsaki sannan yaqarasa ciki shima yanemi guri yaxauna goggo tashiga suka gaisa sannan ta gabatar musu da abinci da abinsha tafita suka bubbude abincin balaifi anyi tsari maikyau tuwan sakwarane da miyar agushi mai wadataccen kifi, sai lemuka da aka siyo musu
Suka faraci suna dan taba hira, ankaiwa fadawa nasu awaje
Dagudu tashigo dakin bbu ko sallama saidata taka qafar yarima ta wuce ta isa ga mai martaba data gani kusada baffanta, tafada kanshi kamar qaramar yarinya wayyo Allah yayabaffa, ina yayana yake? Inadai tare kukaxo? Haushi ya tirniqe fahad amma shi mai martaba sai murmushi yake yashafa kanta Allah yayi miki albarka yata taremuke gashinan bayanki sai a lokacin tajuya idonta yasauka akan kyakkyawar fuskarshi wani mahaukacin ihu tatsala takuwa yo kan yarima dagudu
π *Nasmy ce*π
Yar mutan arkilla love you all π
πππ *yaya*πππ
ππ *fahad*ππ
πππ
π
πππ *Nawa*πππ
ππ *ne*ππ
πππ
π―ππ―
*5 star's β¨β¨ online writer's association*π
*Writing by*
_Nasmatu Muhammad_β
*β’36/40β’*
Jiyayi kamar yayi waje kafinta iso gareshi amma ina badamaryin hakan dole yagyara karbarta karta fadar dashi, aikuwa jikinshi tafada da qarfi ta qanqameshi kai yaya fahad lale lale barkada dawowa
Murmushin dole ya qaqabo sannan ya dagata yaxaunar da,ita gefe yakama hannunta yariqe a nashi barkadai qanwata nasameku lfy? Lfy qlau saidai kewarka wlh ba dadi tsayin shekarun nan da bakanan kullum sainaji kamar inbika gabaki daya iyayan sukayi dariya mai martaba yace dan,uwa kenan mai dadi, da yardar Allah kune xaku gajemu dan lura kunadan junanku kaman yanda mukesonjunanku nida dan,uwana, sukayi murmushi dai dai lokacinda fadawa suka yiwa mai unguwar qauyen da yan rakiyarsa iso sunxo su gaida sarki, fateema ta kalli fahad yaya taso muje mudan xaga gari mana kafun su gaisa nafayi kewarka sosai. Jiyayi kaman ya falla mata mari tsabar ta rainashi wai suxaga gari kaman wani sa,anta jinyayi shiru yasa malam cewa haba fatee yanxu daxuwan mutum ko hutawa baiyi