Showing 1 words to 3000 words out of 113548 words
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: DANA SANI
Writing by Amnah el yaqoub
1
Aguje na shigo gida, koda wasa bana kallan gabana, ko ina sa kafata nakeyi ,mama na tarar a
tsakar gida tana tankadan garin tuwo, da saurinta ta daga kai ta kalleni kawai ta girgiza kai tare
da fadin "Allah ya shiryeki,
" kafin taci gaba da abinda take anty na husna ta shigo Aguje itama, tanata faman haki, kasan
cewarta me Dan jiki, mama tace" husna menene?" Kafin ta Koro Mata bayani saida ta wankeni
da mari, aikuwa atake nasa kuka tare da bibbiga kafafuna,
" mama kin ganta ko" harara mama ta watsamin, husna tace" mama tsokanata tayi, har yaushe
zanci gaba da fada Mata cewa niba sa'arta bace, Amma taqi ji"
mama tace "ubangiji Allah ya shiryeku"
Ta dubeni tasake cewa "ke kuma jiki magayi,"
ta maida hankalinta Zuwa ga husna, "ina Aiken dana muka?"
Sai asannan husna ta kalli ledar hannunta sannan tabawa mama tattasanta, nide cike da haushi
nayi cikin daki ina harare harare.
Ma'u kenan koda wasa batasan raini, akwaita da San girma inde kana so ku shirya toka
girmamata, wnda nikuma bazan yi wannan ba, inde Fannin tsokana ne to bada ga nanba,
kasan cewarta me jiki shiyasa nake tsokanarta da suna lakekiya, kokuma Ma'u, ita kuma abnda
bata so kenan, tafisan husna, nikuma inde inasan wani Abu awajanta to anan zakaga ruwan
biyayya, anty husna kamr abakina aka radata
Asalin labari
Garin zaria gari ne me cike da dunbin albarka, mahaifinmu malam mu'az (principal) Dan Garin
ne, unguwar kofar doka jikin gidan firzin, iyayensa sun Dade da rasuwa, su biyu suka bari shida
kaninsa hassan suma su biyu ne yayinda hussainin yarasu awajan haihuwar su, Ammu hassan
baida aure yanade karatu ne ynxu, muna kiransa da Ammu ne kasan cewarsa qani awajan
mahaifinmu
Mama kuma sun hadu da Abba ne amakaranta inda aka turashi teaching practice daga zaria
Zuwa kano anan suka qulla soyaiya harta kaisu ga aure har aka samemu, ita din haifaffiyar
kano ce, kuma bafulatanar asali, haihuwar mama ta farko ta haifi yan biyunta Mata hassana da
hussaina, hassana ta rasu awajan qyanda saikuma hussaina ayanxu wadda nake kira da anty
husna, saikuma ni danaci sunan kakata ta wajan uba Nafeesa, Amma Ana kirana da FEENAH
Mrs usman ce
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: DANA SANI
Writing by Amnah el yaqoub
3
Anty maimuna ita tayimin komai muka shiga hostel ina ganin mutane da robobinsu Amma kala
ta banbanta suna tafiya Hall na amsar abinci, lebira yana binmu da kayana akansa, har mukaje
wani hostel inda naga ansa P.T.A HOUSE, wata yar tsohuwa muka gani fara da ita, ashe itace
me kula damu, naji anty maimuna tace mama yar yalwa ina wuni nima na gaida ta, anbani
kwana da komai nashirya kayana wasu kuma nasaka su cikin loka, daga nanfa nafada tunanin
gida, Allah sarki mama kome take yi yanzu? Dumin danaji a fuskata shiya tabbatar min dacewa
kuka nake, ga wani Abu danakeji a maqogarona, "sannu" naji anfada, wata matashiya ce
medan jiki na kalleta tacemin "kema new Comer ce? Nace" eh tace sunana Rabi'atu idan bazaki
damuba zanso mu zama qawaye ni nazo ne daga Hadejia, kefa?"
Uhm nayi ajiyar zuciya nace Mata" daga Zaria nake, "
Ido ta zaro tace" gaskiya daga nesa kike," ta sake cewa" kiyi hakuri kidena kuka ahankali
zaki saba muma da haka muka saba, kinga ni tun daga js 1nafara", Ido na zaro cike da mamaki,
nace "bazan iyaba," tacemin "dande ba'a kawokin bane, wanne bangare zakiyi karatun"?
" Arabic"
murmushi tayimin tace" gaskiya ni ina S.T.Q ne (Senior Tahfizul Qur'an) ss1,amma kirki damu
akwai qawata Zainab da take S.A.S (Senior Arabic School) zan hadaki da ita, batada matsala,
saiku dinga tafiya tare harkisan kan school din,"
godia nayi Mata, tace" ga gadona nan Opposite din naki idan kina buqatar wani Abu,"
nace Mata" to. "
Ta Mike Zata tafi sannan tacemin" baki fadamin sunanki ba,"
NAFEESA MU'AZ Amma FEENAH ake kirana, tayi murmushi "nice name"
" shukhran" nafada Mata,
Tace " iyeeee gaskiya ne kaji yan Arabic,"
murmushi na maida Mata, ni shaf na manta da larabci nafada Mata, kuma hakan yasamo asali
ne da musun da mukeyi nida husna agida, tayimin turanci in maida Mata da larabci, duk wanda
baijiba munyiwa kanmu, hawaye ne suka zubomin Allah sarki anty husna qawata yayata
abokiyar fadana
** *** **
"Wai bazakici abincin nanba tun dazu kinsa kwano agaba Babu abinda kike sai tunani"
husna tace "mama wallahi nafisa nake tunani Allah sarki ko yaya take yanzu"
mama tace "toya za'ai husna, jinake jiya jiyan nan kika Gama cewa garama ta tattara yanata
yanata tatafi," husna tace "to ai mama itace take tsokanata,"
"haka de kuka iya, inji mama, yi sauri ni kici kizo ki doramin kunun gyada babanku yakusa
dawowa, banaso ya tadda ba'ayiba yafara fada, daga kai husna tayi, tana goge qwallar idonta,
kallanta mama tayi, ita kanta daurewa kawai take Dan wani Abu takeji aranta kamar ta fashe da
kuka, toya za'ayi, nafeesa kwata kwata bataji, tafiyarta school din shine kwanciyar hankalinsu.
** *** **
Cikin wata daya na goge, nasaba da mkrnta, saide kewar su mama danake kwana da ita nake
tashi, kwanciyar hankali na shine ina tare da Zainab da kuma Rabi'atu, kokari na da kuma
yawan surutu danake dashi shiyasa nayi jama'ah duk inda nabi zakaji Ana Feenah Feenah ba
junior ba, ba senior ba, anty maimuna tunda na bata dubu dayan nan nace inji Ammu shikkenan
kullum saita yabeshi, babanku yanada kirki Feenah gashi Dan kyakykyawa, nide kawai jinta
nake ina Mata dariyar yaqe, to wanne kirki mutumin dayayi sanadin rabani dasu mama.
** *** **
Nayi suna sosai amakaranta har club nashiga na larabci wato Arabic Club, kuma hakan yaqara
temakamin wajan sanin larabci na, haka kuma suna ji Dani da suka fahinci inajin larabci sosai
yawan fitar da za'ayi kokuma wata drama to Dani aciki.
Ranar wata jama'ah muna dakinsu Zainab sani, nida Rabi'atu kaina Akan acinyar Zainab
tanamin tsifa,tace" Feenah kanki badai gashi ba, infada miki wani sirri?"
Nace Mata" fadi,"
tace" wallahi har darura nake kicemin inyi miki kitso sbd kan naki yayi tsawo", kallanta nayi
nace" lalle bakisan me tsawon gashi ba, tacemin "kamar ya" , nace wlh da kinga na husna
bazakice inada gashi ba, tafini gashi, Ido ta zaro tacemin "a hakan" nace" yes, "tace" kai
Feenah kinga fa gashinki"
nace" baby bazaki yarda ba sai kin ganta tukunta," haka sukai ta mamaki, muna firar club
dinmu ne Atu tace "nifa Feenah wlh idan kina larabci har birgeni kike, bari kiji inde kikasa abaya
kikai Rolling ko hmm kede kawai qawata "mafi kalam" (ba magana)" daria mukayi Gaba
dayanmu" wlh Atu Allah ya shiryeki," daga karshe muka tafi yawonmu kasancewar juma'ah ce Babu abinda ake, saida muka tsaya
awani bohol dayake gaban Dakin su Zeey wato Gumel house muka qaraci wasan ruwanmu
sannan muka tafi, mune Arewa house, su Hadejia house da kano house, kasan cewar duk
muna da friends acan sai wajan magrib muka tafi dakinmu nida Atu.
Mrs Usman ce
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: DANA SANI
Writing by Amnah el yaqoub
2
Babu abnda nabari daga kamannin mama tamkar photo copy, yayinda anty husna tayi kama da
abbanmu, ayanda mama take bamu labari itama hassanar anty husna suna kama da juna Sam
bazaka gane suba.
Nikam kamar maman nadauko Hali nede ya banbanta fara ce ni tas da dogon hancina, inada
yalwar gashin gira tare dana ido, ayayinda Dan qaramin bakina yake da taushi me launin ja,
inada gashi dede misali Amma na anty husna yafi nawa yawa
Gaba daya na fitini yaran unguwa banda wasu qawaye na kirki sai marasa ji irina, ni kenan
kullum cikin yawo tare dasu, qawata ta arziqi daya ce Amina yarinyar maqocinmu.
Shekara ta goma sha hadu matakin karatuna ynxu ne magana junior, ayayinda anty husna take
17years yanxu ne take shirin yin candy, ganin yanda na fitini yaran unguwa da jawa iyayena
magana hakan yasa Ammu yace akaini boarding school ko suma sa huta da wannan abin fadar
danake rabawa. Hakan ce ta kasance da'aka tashi sai aka rabani dama jihar Gaba daya akai nesa Dani izuwa
jigawa, bording school ta BABURA, kasan cewar tun muna yara nafi karfi ta bangaren Arabic,
husna boko shiyasa tayi science nikuma nake Arabic school, inada kokari dede misali
musanman ta Fannin larabci, kokadan bana maida hankali sosai Akan boko kawai nide larabcin
Nan nasa agaba, ayayinda husna kuma ko ta'al bata saniba saide ta tambayeni itama tafisan
bokonta.
Bamusha wahalaba Akan hanya kasancewar Ammu yasan jigawa kadan, hakan yasa muna
Zuwa babura muka dau hanyar dazata sadamu da school din, mun danyi tafiya kadan sannan
muka je gate din makarantar, dayake Ana kawowa dalibai shiyasa muma muna Zuwa aka Bude
mana gate din muka shiga, akwai tafiya medan nisa kafin muka shigo cikin makarantar, muna
Zuwa Aria class nafara gani sai kuma bishiyoyi dayawa, wadanda basuda cikar ganye, ina
juyawa hannun hagu na na hango wani gate din na daban, wasu yanmata nagani guda biyu
suna dosowa inda muke sukazo zasu wuce ta gabanmu, daya daga cikinsu ce take magana da
yar'uwarta, muyi sauri muje hostel kar abusa karbar lunch mu makara adakemu, anan nagane
kenan gate din hostel ne, Ammu ne yamusu tambaya su nuna mana office din da ake karbar
sababbin dalibai, Babu musu suka nuna mana wani office, Nan muka nufa, tagaban wani class
muka wuce naga ansa J.A.S 3B muka wuce mukaje office aka gamamin komai, hatta roba da
kofi sun bani sbd karbar abinci, anan malamin yahadani da wata prifet sbd ta nunamin inda zan
zauna da class dinmu, sunanta maimuna, Ammu yabani kudi yace indinga amfani dashi kafin
suzomin visit, yabani 1k yace inbawa maimuna ,yaqara da cewar bazai min fadaba idan na
musu laifi zasuci ubanane yaqara Gaba, daga nanfa idona yarena fata, ba uwa ba uba Babu
yar'uwata mai sona husna.
Mrs Usman ce
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: DANA SANI
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to Mrs Abdallah
4
Watana biyu mama Abba husna da Ammu sukazo ganina, nayi murna kamar ba gobe, kowa sai
nan nan yake Dani, Ammu kuwa fuskar nan ahade "ke baki iya gaisuwa bane" nace" sannu
Ammu ina wuni?" Bai amsaba
naje nakira musu qawayena harda anty maimuna suka gaisa, ina kallanta tana satar kallansa
shima haka, nan kuwa basusan uwar yan sa'ido tana hankalce dasuba, husna ta taboni tace"
autar mama nakusa candy fa,"
fari nayi da idona nace" wlh fadi ki qara nice farko nice qarshe," hararata tayi tace" a a kece
qarshen de yarinya", nace" ina lissafawa fa tare zakuyi candy da anty na," tace
" wace antynki bayan ni," nace "aike ta dabance, anty maimuna nake nufi,"
"Ok" tace,kallan su mama tayi taga hankalinsu baya kanmu tace" ke wannan boss dinfa naga
suna kallan kallo shida ita, koda wata aqasa ne? "
Nace" nima haka nagani," dariya tayi tace" intayi tsami maji," dariya mukasa harda tafawa,
kallanmu mama tayi, aranta tace" me Hali baya fasa abinsa. "
Dazasu tafi kuka nasa musu, ina kallan Ammu tagefen idona yana harara ta, niko ko ajikina,
Abba yayimin fadan karatu da fatan alkhairi, yayinda mama tayimin fada Akan cin abinci, tace"
nafeesa gashinan baki rasa komai ba, Amma duk kinbi kin rame saikace yar gidan kamaye
awun igiya, kinyi firit dake sai wani uban kwankwaso", dukanmu maganar mama tabamu dariya
bnda Abba da Ammu da hankalinsu baya kanmu, haka suka tafi inaji ina gani, sai kuma
kewarsu tadawomin sabuwa fil, Amma dana tuna saura befi wata dayaba muyi hutu sai naji
sauqi.
Haka muka Gama term din bayan munyi jarabawa nazo ta biyar, cike da murna nadawo gida,
kowa yayi farin ciki da dawowa ta, haka kuma su mama sunga canji atare Dani, mun baje afalo
ina tabawa husna labarin bording, Ammu yayi sallama take muka shiga taitayinmu, muna
gaisawa nabashi report dina, murmushi yayi yace yayi kyau saiki qara dagewa, "insha Allah"
nace, yasakai zai fita mama tace "ga abinci fa,"
yace "yana dawowa."
Allah sarki sai gashi ya dawo da leda ahannunsa ya miqo min, nakarba tare da fadin "nagode,"
"gashinan kyaci duk kin rame sai uban qashin wuya" mama tace" kaima de kafada nafeesa
batasan cin abinci. "
Araina nace" ai kaine ka ziga akaini school din," shide ya dauki abincinsa yayi waje, yana fita
muka Bude ledar, kaza ce babba sai maiqo take, kai nida husna munyi party ranar mama tace"
kamar Baku taba cin kazaba," husna a kace ai mama kazar Ammu daban take," tace "wato kun
raina babanku hmm zaku hadu dashi ai, jiki magayi."
Dazai fitane bayan yagama cin abinci yacemin "ya gajiyar hanya ya qawayen naki?" Nace "suna
nan kalau anty maimuna ma tace na gaida ka,"
be cemin komai ba yafice, aikuwa mukasa daria, nace" anaso Ana kaiwa kasuwa, "husna tace"
hmm damafa ita yakesan tambaya, shine aka wayance "ya qawayen naki" tafada tana
kwaikwayon maganar sa, dariya muka qara sawa.
Haka naci Gaba da karatuna a jigawa cikin kwanciyar hankali, Dan nalura da jihar akwai zaman
lafiya, a term dinmu na karshe su anty maimuna sukayi candy, nayi kuka harna godewa Allah,
tabani address dinta hade da number waya, nima nabata nawa, nayi kuka na rashin ta, danma
da qawayena yan Amana zeey da atu
Mrs usman ce
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: DANA SANI
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to Mrs Abdallah
5...
Rayuwa na tafia lokaci na sauyawa, harna shiga ss 3,yayinda husna tasamu gurbin karatu a A.
B. U zaria,tana karan tar "lab" a wannan lokacin kam, komai nawa yasake futowa, nazama
yanmata boobs dina dede misali yayinda hips dina suke acike, naqara haske nutsuwa tazomin
nikaina idan nayi kwalliya tsayawa nake ina kallan fuskata musamman idan naga nayi
murmushi kumatuna sun lotsa, (dimple), nida husna bazaka ce yaya da qanwa bane danna
tarota komai, nan kuwa tabani shekaru masu yawa kafin a haifeni shiyasa batasan raini.
"Zeey wai kukan nan be isabane, tun dazufa kike ta faman yi,"
"feenah Dan Allah kudena kuka,"
tafada tana goge kwalla itama, rabuwa kenan Babu dadi, anhadu daga gari mabanbanta gashi
ynxu za'a rabu, munyi alkawarin ko bayan mun rabu zamu dinga zumunci, haka muka rabu
kowa rai Babu dadi, munyi exchange din numbers tare da address, daga karshe akazo daukar
kowa muka rabu cikeda kewa Ammu ne yazo daukana shida wani abokinsa banma sanshi ba acikin abokan Ammu, muna
tafiya suna firarsu, munzo wani gari suka tmbyeni nafeesa inane nan, nace musu STK ne (sule
tankarkar) haka sukai ta tambayata garuruwa ina fada musu su Gumel dasu layin dazaka shiga
Dan zomo,, su gagarawa, munzo round na wani gari gujungu anan bacci yafara fizgata, bansan
kuma me suke tattaunawaba.
** *** ***
Kwance yake Akan bed dinsa qirar Italy, Dakin na kalla komai pink and blue ne, banga fuskar
wanda yake kwancen ba kasan cewar yarufe duka har fuskarsa da wani farin tattausan
blanket,yaya! Yaya!! Yaya!!! Tafada da karfi, dakyar ya Bude Zara zaran gashin idonsa,
yasaukesu Akan ta, "Saudat yaushe zaki bar mutum ya huta ne,"
Dan turo baki tayi, tace" yaya momy tace infadama break fast is ready"
"naji" shine kawai abinda yace yajuya yaci Gaba da baccinsa, sai wajan eleven yatashi, dama
haka yake, kasan cewar Babu abinda yake yi, bayan yayi wanka saida yagama shafe shafensa
kamar wani mace sannan yafuto, iyayansa yasamu a main falo bayan ya gaida su ne momy
tafara fadan data saba wato Akan rashin cin abinci da wuri, shafa kansa yayi cike da shagwaba
yace "momy zan dinga cifa"
, yan biyu ne sukasa daria Muslim yace "yaya na shagwaba kamar mu" , bukhari yace "ai shima
namiji ne shiyasa yake yi, dama maza ne sukeyi ko momy," harararsa tayi tace" ai sakarci ne
yasa sukeyi din ba komai ba, "
Muslim yace" yaya wai hakane? ", dalla kuyiwa mutane shiru kamar dasu ake magana," momy
bari inyi sauri inci abinci akwai inda zanje, abincin sa yakeci cike da nutsuwa dady yafuto da
shirin office bayan ya tsugunna ya gaida shine, yace " my son idan kagama abinda kakeyi kuje
ka raka saudat Zata duba exam dinta jiya tayimin magana nace tabari Zuwa Yau mugani,
kadaure kakaita banaso tana driving da kanta ne" , amsawa yayi cike da ladabi, bayan yagama
ne saudat ta futo sanye da atamfa Riga da sket, dinkin ya karbi jikin ta kasancewar ta fara, suka
yiwa momy sallama suka tafi.
Iyalan sanata muhd marzuq kenan, matansa biyu yana zaune a unguwar sharada, marzuq farid
Dan kasar masar ne balarabe ne na asali yana kasuwancin saida motoci daga masar Zuwa
Nigeria, kuma sosai harkar ta karbeshi, yana yawan zama a Nigeria da matarsa saudat
balarabiyar masar suna Nigeria Allah yabasu ciki suka reneshi a Nigeria har lkcin haihuwarsa
yayi suka samu muhd, bayan haihuwarsa da shekara ashirin ta rasu, haka marzuq yayi ta renon
muhd haryakai minzalin aure, bayan yaga hankalin dansa ya kwanta shine ya sake aure ya auri
wata balarabiyar mai suna bara'ah, Amma ita tafisan zaman masar tace bazata iya nesa da
iyayenta ba, shiyasa shima marzuq din zamansa yafi yawa