Showing 105001 words to 108000 words out of 113548 words
Momy? "
Momy tace" ai shine labarin danace zanbaki ansa ranar bikin nanda wata daya shida qawarki
nafeesa"
"Dan Allah Momy, wayyo dadi"
Momy tace "wallahi ansa rana jiya,"
saudat tace "to Allah yakaimu kice zuwanade bai fasu ba," 橙提
Momy tace "a a Zuwa bai fasu ba, ga qawa da yaya"
"Allah sarki sister ashe sun dedeta"
Momy tace "haka de ahmad din yace sun dedeta, ai yarinyar tayi masa halacci, a wannan
lokacin Mata da miji ma suna rabuwa a dalilin rashin haihuwa, Amma ita taji tasan baya
haihuwar ta amince Zata aure shi ahaka, ai kinga kuwa tayi kokari,"
saudat tace "gaskya kam Momy hakane, Allah yasaka Mata da alkhairi,"
Momy tace to saikunzo, ki gaida farouq din, sauda tace Momy zasuji ki gaida su mami dahaka
sukai sallama sauda sai murna take
** *** **
After one week
"Biki yarage sati uku, wai feenah miye haka kin wani je gida kin maqale, sai nemanki muke,
Allah idan kika yarda nazo zaria dake zan taho, kafata kafarki"
Nace "maida wuqar Zahra, kinga yanzun nan nagama hada kayana anjima kadan zan taho,
akwai wanda nake jira ne"
"Banganeba feenah wakike jira, keda kike Gab da shiga gidan wani"
Nace "oh Zahra, me kike tunani akaina, kinsan de bazan kula kowa ba"
Tace "to wakike jira da bazaki taho ba, kokuma ahmad dinne yazo ne?"
Ajiyar zuciya nasauke nace " Zahra kenan ni wallahi rabona da ahmad ma nadade, tun lokacin
dayazo ya kitsa karya da gaskya, ko gidan nan bai sake Zuwa ba, ke Kiran nawama dayakeyi
yadena yanzu橙提"
, Zahra tace" tofa, to Allah yasa lafiya"
nace "amin, yanzu ma Ammu ne yazo suna magana ne shida Abba, to shine yace injirashi
saimu tafi tare,"
Zahra tace "Toshiknn Allah yakawo ku lafiya sai kunzo"
nace " to"
** *** **
Direct gidan Ammu muka sauka saida naci abinci nahuta, sannan ya kaini gidan kalatynmu
muka gaisa, daga nan yadau hanyar gidan husna, nace
" Ammu ai agidan kaka zan sauka, husna bayau zanje ba,"
Ammu ko magana baimin ba ya wuce gidan kaka, saida yashiga suka Dan taba fira tsakanin su
sannan yayi mana sallama yatafi, har wajan mota narakashi ina Ammu Allah yakiyaye, amin
kawai yace, araina nace kaji dashi, kaima wani baqin miskilin
Ina dawowa na miqe akujera, nadora kaina acinyar kaka, muka dasa fira, kaka sai nan nan take
Dani
** *** **
"Uncle kaga baby ko, ta dakeni banyi Mata komai ba,"
janyo hannun ta yayi yace "mama kiyi hakuri kinji, bazata sakeba,"
Momy dake gefe itada mamy suna kallansa
Da gudu ta taho itama tana hawaye, bata tsaya wajansu Momy ba kai tsaye wajan ahmad ta
nufa cikin kuka tace "uncle kaga baby ta shanyemin ice cream dina, kuma ta dakeni,"
goshinsa ya dafe da hannun sa ya janyo ta jikinsa yace "mima, yanzu me kikeso"
tace "Allah saita biyani," 橙提
Yace " to kiyi hakuri nizan biyaki kinji,"
nan da nan ta goge hawayen ta tayi shiru, tace "uncle nicefa mama kake tacemin mima" 橙提
Mima ma datake gefe tasa daria tace "nima haka yacemin mama" 橙提
Ahmad yace "koma de menene ai nace kuyi hakuri ko" 橙提
, Momy ta daga murya tace "oh wato kai bazaka iya Rama musu ba, saide ka dinga aikin bada
hakuri
Allah ya shirya, wataran ai kwa tsokano maiyi muku shegen duka"
Murmushi ahmad yayi baice komai ba, mama tace " uncle Yau kace zaka kaimu gida mu tafi
kaji,"
Mima ma tace " eh wlh"
, Babu yanda ya iya, dole yasa aka dauko musu kayan su, baby tana musu bye bye, suma
sunayi Mata, haka suka rabu da qawar fadan nasu
** *** **
"Mama wai nikam har yanzu basu isobane?"
mama tace "ai Kuwa tun dazu munyi waya tacemin sunje, tana gidan mama,"
husna tace "OK to nasa Tahir yaje yataho da ita, ninakirata wayar Bata shiga," mama tace "Ok"
Falo tafuto dawayar ahannunta, tana Zuwa falon su mama suka taho da gudu suka rungumeta,
husna tace
" oyoyo sannunku da Zuwa," tadubi Ahmad tace "sun gajiyar dakai ko,"
Ahmad yace "a a babu komai, yanzu ma sunata rigima ne saina dawo dasu shiyasa muka
taho,"
tace "sannunku da Zuwa," Tahir ta duba da zuwansa Kenan tace "my hero ko zaka dauko min
auta ne agidan kaka,tazo dazu Kuma nasan bazata zo da wuri ba, nasan halinta, may be tace
Sai gobe, nikuma nayi missing dinta wallahi"
Tahir yace "ok karki damu yanzun Nan zanje nakawo Miki ita shikkenan?"
Ahmad yace "a a, am kagane Tahir Bari kawai naje na daukota
babu damuwa bani address din gidan dama inasan ganin kaka"
Tahir yasaki murmushi aransa yace "shege Ahmad"
, fada masa address din yayi, shikuma Ahmad yajuya yatafi, Yana sakarwa Tahir wani shu'umin
murmushi Wanda su kadai ne suka San ma'anar sa
Mrs usman ce
[5/4, 3:48 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹
Writing by Amnah el yaqoub
Wannan shafin nakune masoyan wannan novel, Ina yinku sosai踫潤蕃
63
Magana ta gaskiya gabansa faduwa yake, kawai de daurewa yake Yana driving, nafarko yanaso
yaga kaka, ashe dama wannan unguwar tadawo shiyasa naketa haqilon nemanta, sannan ita
kanta feenah inasan ganinta saboda inji meda me take tsarawa, idan nayi sa'ah tagama fishin
nata saita fadamin Yana wannan tunanin Har yazo, wasu samari yagani agefe suna zaune, sallama yayi musu
yaqara tambayar su, suka tabbatar masa da gidan ne, Dan haka babu Bata lokaci yasa kansa
ciki
Abakin kofar falon yatsaya yanata sallama, muryar kaka yajiyo tana amsawa daga nesa, yace
" inshigo?"
Kaka tace " yau naji ikon Allah shigo mana"
Yana shiga, kaka tafuto daga daki, murza idanuwanta tayi da kyau tace "wanake gani Kamar
amadu?"
Cikin murmushi yace "nine kaka"
Matsowa tayi takama taba fuskar sa tashafa kansa, tace "yauwa yanzu nasan ba mafarkin dana
saba bane, yanzu amadu kana duniyar Nan, muka nemeka muka rasa,"
Sai kuka Kuma
Cikin sauri yace "a a kaka kiyi Hakuri, kiyi shiru," tace "ashe zamu sake ganinka "
Yace "eh wallahi"
kaka,tace aure Kuma yazo kusa
Murmushi yayi baice komai ba
tashi tayi tace "lalle yau inada babban baqo Ina Zuwa" ,
hanyar kitchen ta nufa
Shikuma ya zauna akujera
Yana juyowa hannunsa na dama yaganta akwance tana baccinta Cikin kwanciyar hankali
Gashin kanta yabazo Mata Har fuska, dan qaramin bakinta ya kallah, bazai manta dandanon
wannan bakin ba, idonta ya kallah, Gashin idonta daya hadu da dan'uwansa saiya qara yimata
kyau, Kamar tasaka gashin ido
Ahankali yatako Yazo Har inda take, agaban kujerar ya tsugunna
Yasa hannunsa yagyara mata gashin kanta
Matso da fuskar sa yayi gab da tata,
Cikin baccinta taji qamshin turaren da bazai Iya gogewa a qwaqwalwarta ba, murmushi tasaki
taji baccin yaqara mata dadi, danhaka tasake gyara kwanciyar ta taci gaba da bacci
Murmushin datayi shine yaqara shagalar dashi, baisan lokcin da dayakai hannunsa Kan Dan
qaramin lips dinta ba, Ahankali yake shafawa Yana hurawa idanunta iska
Jitake Kamar numfashinta Yana haduwa da wani, kasancewar kusanci da fuskar su tayi,
Ahankali ta Bude idonta, aitana ganinsa tatashi tana zare ido
Kenan ba mafarki takeba shine akusa da ita, meya kawoshi gidan Nan? Waye ma yace masa
Ina gidan? take tambayar kanta
Murmushin sa Mai tsada yasakar mata, yace
" kinata baccinki nikuma kin barni Sai gadinki nake"
, harararsa tayi tatashi tayi daki, bayanta yabi da kallo yanda hips dinta yake juyawa yayi bala'in
tafiya da imaninsa, aransa yace wayyo Allah wannan yarinyar zata kasheni
Toilet tashige tayi brush tasake gyara kanta sannan tafuto falon, Ahankali Kamar bataso tace
masa "Ina yini"
Da sauri ya kalleta, saboda baiyi zaton hakanba
Yana Murmushi yace
" lafiya amarya"
Harararsa tayi, tabi kaka kitchen
Kaka tanata kimurtun hada abinci ita kadai, tana ganin feenah tace
" yauwa alhamdulillah dauki wannan kikai masa, Ina Zuwa da lemon Nima"
Babu musu taje ta tsugunna a gabansa ta ajiye abincin, Ahankali Cikin nutsuwa take zuba
abincin
Kuskus ne da miya dataji naman sa Sai ganyaiyaki dangin su salat
Tsugunna war datayi ne yabashi damar ganin abinda yake Cikin rigar ta, Cikin ransa yace
masha Allah, bulbul dasu farare gwanin sha'awa
Ya shagala a kallan wajan baisan tagama zubawa ba, saijin tashinta yayi
Ba yabo ba fallasa tace
masa "Ga abinci"
Muryarsa ashaqe yace
" bazaki bani ba?"
Shiru tayi masa tana kallan wani wajan
"Ungo"
Abinda yace mata Kenan, takai dubanta gareshi taga yabata hijabi, Shima kawai ganinsa yayi
Akan kujerar baisaniba nata ne kona kaka, shikam koma na Waye
Gara tasaka inba hakanba Kuwa gaskya saide kaka tarufe idonta
Yana Bata hijabin still idonsa ba akanta yake ba, Yana kallan wani wajan, idanunsa tabi da kallo
taga ya zubawa kirjinta wani mayan kallo, danhaka Cikin sauri takarbi hijab din tasaka, Cikin
ranta tace wannan kallo haka Kamar za'a cinye mutum
Yana cin abinci kaka takawo masa lemon juice
Sai surutu take masa na Bayan saduwa
Haryadanci kadan, tace
" amadu wannan cin abinci Naka Kamar na yar taku"
Shiru yayi Yana Sosa kansa
Daga baya yadinga Bata labarin irin zaryar daya dinga yi atsohon gidanta, kaka tace "wallahi
adamu ne yadawo Dani Nan shida ma'azu
Wai sun dawo danine kusa dasu, saboda can din yayi Nisa Kuma ni kadai"
, Ahmad yake "eh gaskya wannan haka yake,
Ashe shiyasa naketa Zuwa bakwa Nan qarshe ma akacemin ansaida gidan,"
kaka tace "eh wallahi Nan na nadawo, ai Ina yawan tambayar ka awajan nafi, tace min katafi
masar shiyasa baka Zuwa"
Da sauri ya Kalle ta, wato boye laifinsa tayi, lalle yau yaqara yarda feenah tana sansa
Kaka taci gaba da cewa,
" to itama Kuma adamun yanema mata scholarship tatafi Sudan, saidata dawo ne nakejin
labarin komai awajan ta Har abinda yafaru
Nace Toya za'a yi ai haka ubangiji ya qaddara, saide muce Allah mungode Maka daya bamu
ikon cin wannan jarabawa amadu
Allah Kuma yayafe mana, yakore shedan azaman auren ku "
Ahmad yace " amin kaka
Yanzu ma naje gidan Tahir ne saiyace min zaizo yadauki nafeesa shine Nace kawai zanzo
indauke ta, daga Nan ma naganki, Naga gidan da kike "
Kaka tace" a a ka kyauta babu laifi kayi kokari
Allah yamuku albarka"
Saida muka dade muna fira da kaka, Dan dole na nadauko kayana muka tafi, Ahmad kudi ya
ajiye Akan hannun kujerar dayake zaune, aqallah zai Kai dubu hamsin, yace "kaka gashi kyasai
goro"
Kaka tanata ruwan godia muka tafi, nikuwa naci hijabi Kamar matar liman
Muna tafiya amota narufe idona Kamar me bacci
Shiru ne yabiyo baya, shi Yana shakkar yimata Magana ita Kuma tanaso tana basarwa
Kamar daga Sama taji yace "Ina tsarabata?"
Still idonta arufe tace
" aibana Bawa irinku, kaga babu amfanin tambaya Kenan"
Cikin ransa yace "dama nasan za'ai haka"
Danhaka yace
" toshikkenan, yasu mama da Abba"
Agajarce tace "lafiya"
Daga haka babu Wanda yasake Magana acikinsu, sunyi tafiya sosai yatsaya awani waje, yace
"Ina zuwa,"
Fita yayi yashiga wajan, baidade ba yadawo, suka Ci gaba da tafiya, Shiru Kamar wasu kurame
Sunzo kofar gidan Tahir Ana Kiran sallar magrib, fos dinta tadauka tace
" barshi ananma ya isa," tafara kokarin Fita, tana budewa taji kofa arufe
Juyowa tayi tana kallansa, yace "Amma my feenah Magana nakeso muyi, sannan koba hakaba
kema kinsan Bazan barki awaje ba dole saina kaiki Ciki, sonake mugama Magana saimu
qarasa Ciki"
Itafa batasan Zaman motor Nan tsakaninta da Ahmad 橙提
Gabana Yana faduwa cikin rawar murya nace
" nide banasan Zaman motor Nan, muje Ciki saimuyi koma wacce irin Magana ce"
Shi maganar tatama saita bashi Daria, yace
" my feenah ki yarda Dani babu abinda zanyi Miki"
Kuka ne yazomin naba gaira babu dalili, nace "ai abayama haka kace"
Yace "OK, OK, naji toyi Shiru banasan kukanki," Bata zataba taji tattausan hannunsa afuskarta,
yashare Mata hawayan, yace "Muje"
Atare suka futo, takama kiciniyar daukar jaka
Sunkuyawa yayi, yace
" bani,"
tace "a a barshi zan Iya"
"Allah idan baki baniba zan daukeki daga ke Har jakar"
Sanin zai Iya aikata hakanne yasa tasaki dasauri
Kawai fos ce ahannunta, shikuma yadauki jakar, ahaka sukaje Har falon husna, suna zaune
dukansu suna kallo, yaran suka taho da gudu suka rungumesu, Tahir yace "man, sainajika
Shiru,"
Ahmad yace "maine yaqare mana ahanya"
Feenah cikin ranta tace
" haka de ka Iya" 橙提
Waje suka samu suka zauna, husna tanata tambayar ta Yan gida, suna firar gida abinsu gwanin
sha'awa
Tahir ma Yana wasa dasu mama,
Shikuwa gogan Yana zaune Yana yiwa feenah pictures, Kamar danne danne yake
text ne yashigo wayar Tahir
Anutse yadauko wayar zai duba, yayi tunanin wani abune muhinmi
"Yaya Tahir please please kabani aron qanwarka inaso muyi Magana da ita kafin natafi "
Abinda yagani Kenan, yakai kallansa wajan Ahmad
Tashi yayi yadauki mama da mima afili yace "dole aceda mijin Iya baba" 橙提
Ahmad Sarai yasan dashi yake
Yana Tashi yace "muje nakaiku wajan ummi ko"
Yadubi feenah yace "auta, kaimuku abinci falon baqi mana, kisamu ladan wannan gwauron"
Husna tace "yau Kuma Kaine kake masa,"
Ta kalli yaran tace "mima, mama saida safenku ku gaida ummi,"
taja jakar feenah tayi Ciki
Nima kitchen nanufa, nadauko lemo da kofuna, nace masa muje
Ina gaba Yana bina abaya
Bayan munzauna nazuba masa lemon namiqa masa, maimakon ya karba saiya hada hannun ta
da cup din yariqe gaba daya
Kaina na sunkuyar qasa, yace "matsoraciyar Mota"
kawai, inajinsa nayi Shiru
Sakin hannun yayi, ya ajiye lemon batare dayasha ba
Yace "kiyi hakuri feenah, nasan nayi Miki laifi, nafadawa su Abba da daddy Cewa mun daidaita
tsakaninmu Bayan bahaka bane, kiyi hakuri Dan Allah kinji?"
Kaina nadaga alamar to
Yace "kin hakura?"
Sake daga Kaina nayi
Nace "Bari in koma Ciki, nagaji dayawa zan kwanta,"
Ina fadar haka namiqe nafara tafiya
Kawai jinayi anfuzgoni, Har munajin hucin numfashin juna, ido nazuba masa, Shima haka, yace
"nafeesa meyasa kike San wahalar Dani Wai?
Narasa yanda zanyi Miki bayani ki fahinceni
, feenah inasanki, Ina sanki, Ina sanki feenah"
Abin mamaki hawaye kawai nagani Yana zuba a idonsa
Hannuna yaja yadora Akan kirjinsa saitin zuciyarsa, yace "kinji yanda zuciyata take bugawa a
dalilin kaunarki, nafuskanci wahala feenah, a dalilin sonki hawan jini ne yakamani feenah,
banda ciwon zuciya Shima dayake gab da kamani
Dan Allah naroqeki kiyi hakuri kiyafemin feenah"
Durqusawa yayi agabana
Tare da kama Hannayena duka biyun yace "please! Please!! My feenah"
Yana Magana hawaye Yana zuba a idanunsa, wani kukane ya kufcemin, dasauri yatashi tsaye
Yace
" shikkenan yi hakuri nadena, Bazan sakeba kinji"
Hannu yasa zai sharemin hawayena
Banyi wata wataba nafada jikinsa ina cigaba da kukana
Bayana yafara bugawa alamar rarrashi Yace
" shikkenan yi Shiru banasan kukanki"
Dagowa nayi ga hawaye a fuskata dukan wasa Nakai masa a kirjinsa, nace "kaiko? Meyasa?
Meyasa zakasa murabu?"
Shima cikin kukan Yace
" kiyi hakuri kinji nadena Bazan sakeba"
Sake rungumeshi nayi, babu gardama Shima ya rungume abarsa 橙提
Tsawon minti biyar suka dauka ahaka, itace tafara kokarin janye jikinta, cikin rada yaqara
rungume ta Yace "please!!!"
Tsayawa tayi, tareda lumshe idonta, Shima Hakan yake awajansa, jinsa yake Kamar ba'a
duniyar ba, baiqi ace sun dauwama ahakaba
Dataga Abin nasa ba sarki Sai Allah 橙提Hakan yasa taqwace kanta cikin sauri
Sakinta yayi, Amma still hannunta Yana cikin nasa, Yace "my feenah thank you"
Murmushi nayi masa kawai, yace "mekuke shiryawa ne? Medame kukesanyi Kuma nawa kike
ganin zai isheku?" Nace "katambayi Zahra, zansa takiraka," yace "Ok"
Shiru ne yabiyo baya kawai muna kallan junanmu Kamar za'a sace dayanmu, Hakan yasa Nace
"My Ahmad"
na'am "my feenah,"
"kayimin alqawarin bazaka sake gudunaba"
Cikin rada Yace "Har abada
Bazan sake tunanin aikata abinda zai rabamu ba,"
kema kiyimin
Babu kunya nace "nayima"
Hannu na yakama yasanya min zobe Mai kyau da harafin A'N ajiki
Hannun nakalla yayi kyau sosai
Wani zobe yasake bani tareda miqomin hannun sa
Sanya masa nayi, yayi masa kyau sosai, shikuma ansa Harafin N'A ajiki
"Kiyi alqawarin barina acikin zuciyarki, Nima nayi alqawarin haka"
Daga masa Kai nayi alamar nayi masa
Matso da fuskarsa yayi dab da tawa, cikin rada Yace "kinyi alqawari?"