Showing 72001 words to 75000 words out of 113548 words
Chapter 25 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf
dace
Hannu ahmad yaqara bashi sannan suka futo
Baby tace uncle nan school din aka dawo Dani? Ahmad yace eh gobe zaki fara Zuwa, tace to
kaine zakai dinga kawo ni?
Ahmad yace a a baby akwai driver zai dinga kawoki, kinga nima akwai office
Turo Dan qaramin bakinta tayi gaba, tayi shiru
ya kalleta yace to menene kuma? Tsugunna wa yayi, yace toyi murmushi mana, zan dinga
kawoki shikkenan?
Amma baby banasan rigima ba kullum zan dinga kawoki ba, kinga ne?
dahaka har suka koma gida
** *** **
Dad aure nakeso, kuma cikin sauri nake buqata kuyimin, alhaji yasaki murmushi dansa dayake
ji dashi ne Yau shine dakansa yace yana son aure, lalle kuwa za'a yi bikin da ba'a tabayiba
Yace A'ina take? Wacce mai sa'ar ce wannan? Kabeer yace dad a zaria take, inaso Asa mana
rana nida ita da wuri, nafisan namata surprise, kawai saide taji bikinmu
Alhaji yasake sakin murmushi, yace kungama daidai tawa da ita yarinyar ne? Kb yace sosai ma
dad, kawai kayi komai yanda ya dace,
Dad yace karka damu dana, inde kudi na aiki, mulki na aiki kasamu yarinyar kagama
da murna Kb yatashi yayi dakinsa yana ayyana irin rayuwar dazasuyi da feenah
** ** **
Akwance yake dagashi sai kayan baccinsa, yana sakin murmushi shi kadai, my feenah, ina kika
shiga ne inata nemanki? Kinsan yanda hakan yake azabtar da zuciya ta kuwa? Murmushi
yasake saki tareda janyo fillo ya rungume shi sosai akirjinsa, yanajin kamar itace atare dashi
Lumshe ido yayi, yaci gaba da tunanin ta, bai tsammani ba yaji anfado kansa da karfi tace
uncle!!
Ahmad yace baby bakyajin magana ko, nahanaki shigowa ba tare da kinyi sallama ba
Tace sorry uncle
Yace naji, banasan uncle din nan, sauya wani sunan, tace Tome zance uncle yace abbey
Daria tasaki tace to zanfada
Tace Un.... Au namanta tasa hannu abakinta da sauri, abbeey yimin tatsuniya
Cikin mamaki yace baby me kika ce?
Tace tatsuniya
Murmushin dabai shiryaba yasaki, yace niban tabayiba, tace nima sabuwar anty tataba min
Yace toki yimin naji koda dadi
Tana farawa, auta tashigo Dakin itama tariketa tana cewa Wana kama?
Ahmad yace maryam lafiya? Auta tace yaya kagafa tsokanata tayi tagudo wajanka
Ahmad yace toyi hakuri aikinga kece babba, baby tayi kalar tausayi tace bazan sakeba
Ahmad yace kinji ba? Itama tace bazata sakeba, shikkenan zance ya wuce ku tashi ku tafi kuje
ku kwanta
Baby tace a a uncle nide anan zan kwana, ahmad yace no ga maryam nan tashi kuje, banaso
naji kinsake min magana
Hakan kuwa akayi, batace komai ba suka fita
** *** **
Baby na rokeki kibar wannan babyn agida, inba haka ba kuwa Babu inda zaki bini, babyn ta
kalla tace to ai uncle idan nabarta kuka zatayi, ahmad yace a a ga momy nan, Zata rarrashe ta,
izdihar tace to momy ga yata nan, suka kama hanyar fita, harsun fara tafiya tadawo tayiwa
babyn kiss sannan suka tafi
Momy tana zaune kamar gunki tana ganin wannan salo
, yana fita yakira saudat awaya yace yaushe zaku shigo ne? Tace yaya meyafaru? Yace kizo
kiga yata, nayi yarinya
Saudat tace yaya kamarya?
Girgiza kai yayi, kawai ya kashe wayarsa
Wayar ta kallah tana hello hello taji shiru
Momy takira danta samu qarin bayani, cikin mamaki momy tace au ashe kema anfada miki,
tana nan wata yarinya yaje aka bashi, tana nan kamar yar buzuwa
Tunda aka bashi ita yakasa zaune, yakasa tsaye
Saudat tasaki daria tace lalle yaya, nima fa yanzu kirana yayi wai inzo naganta, momy tace
aikuwa kizo inba so kike yayi fishi ba
** *** **
Tariqe hannun sa nadama, haka suka qarasa company, yayi abinda zaiyi, suna zaune a office
baby tataba wannan, yayi magana ta janyo wannan yahanata, cikin ransa yace bari de mu tafi,
tun kafin narasa wata takardar
Ammu yakira, yashigo office din, baby na ganinsa taje ta rungume shi, Ammu yace a a izdihar,
manyan kasa, yagida? Tace lafiya, Ammu ina Abba?
Ammu yace Abba yana gida izdihar, ya school kina Zuwa ko? Tace eh
Ahmad yace Ammu wallahi tafiya takama mu nida baby, zandan kwana biyu ban shigo ba,
please inaso ka kula da komai, Ammu yayi murmushi Jin sunan da ahmad yakirashi
Yace to yallabai babu damuwa Allah ya tsare
Tare suka futo, kowa sai kallan izdihar yake, wasu kuwa har wajansu suke Zuwa, daga nan
wajan passport ya wuce akayi Mata, suka wuce wajan visa suka bada passport din
Daganan sukayi wajan yawo, ya kaita nan ya kaita nan, da sukaje Park ne yaga hankalin ta ya
karkata waje daya, yajuyo ya kalleta yace baby me kike gani ne? Tace nan mukazo da sabuwar
anty rannan, murmushi yayi yace kede baby bakida dama, abinda akai jiyama saikice rannan
Kinga taho mu tafi
Tayi wasa sosai sannan suka kama hanyar gida
** *** **
Wato alhaji abinda yake faruwa, shine, ita wannan yarinyar dakukazo magana Akan ta, ni kwata
kwata ma, bata min maganar wannan yaron ba, sannan Bama wannan ba, ai anriga ansa Mata
rana itada wani yaro, daddy cikin rashin walwala yace to Mungo de, mun gode sosai, Abba yace
babu damuwa, suka sake musabaha suka tafi
Yana Zuwa gida mahaifinsa yafada masa wannan maganar atake ya haukace musu, shi wallahi
yana Santa kuma bazai iya hakura da itaba, dad yace Kabeer kabi komai asannu mana, Kb
yace daddy wallahi idan yarinyar nan bata aure niba sai tayi DANA SANI
** *** **
Cikin sati biyu aka Gama musu komai, dukansu suna falo anata fira kasancewar saudat tazo
ganin baby, tana ganin yarinyar taji tashiga ranta, duk motsin da baby zatayi, idan saudat na
kanta, har ahmad yafahinci halin datake ciki
Saida yatafi daki, yana shirya kaya ajaka, saudat tashigo tace yaya, yanaga kana hada kaya,
yace sauda jibi zamu wuce misra ne, zan kai baby wajan tsohon can taganshi yaganta, saudat
tace yaya wallahi wannan yarinyar kama suke da feenah sosai
Ahmad ya kalleta da mamaki, yace cikin ransa ashe bashi kadai ne yake wannan tunanin ba,
Yace kama ce kawai saudat
Dahaka tayi shiru dataga kamar bayasan maganar, tajuya ta fita, yana ganin fitar ta, yagoge
qwallar idonsa
Bayan kwana daya sukai
sallama dakowa, inda suka Lula Egypt shida baby
Kakanninsa sunyi murna sosai da ganin baby, inda marzuk yasake masa fada Akan Dan Allah
koda yayi aure yadaure ya riqe matar dakyau kada yasake tunanin rabuwa da mace, koma
menene hakuri akeyi da Juna
Ahmad yaji shawarar kakan nasa Sosai, kuma yayi alkawari zai kiyaye Gaba
Tunda sukaje yake kaita wajan yawo kala kala, pictures kuwa harda na banza, duk inda sukaje
sai yayi musu pictures, ahaka suka dauki Tsawon sati biyu, har yana shirin dawowarsu Nigeria
Bai cika dora pictures dinsa a Facebook ba, Amma Yau saboda baby yahau danya do rasu,
abinda yagani ne yabashi mamaki, pictures din bikinsa shida laila
Babu wanda yafado masa arai sai tahir, yasan shine zai aikata
"zamu hadu ne "
Yafadi haka afili, pictures dinsa yasa shida baby yasauka, duk tarin massages din da aka turo
babu wanda ya bude
** *** **
After 4 months
Feenah sun kammala karatun su itada mukhtar, soyaiyar su kuwa sai qara gaba take yi, sunaji
da junan su sosai, saura wata uku su dawo gida, abinda ya rage Mata yanzu project ne kawai,
data gama sai gida, shiyasa tabaro madani, tadawo Khartoum kusa da Zahra, tunda rubutu ne
kawai
Itama tagama karatun ta kawai jiran result dinta take, sosai nake rubutu na, danna matsu na
dawo gida, baby tana raina, kullum nakira waya nace abata akwai abinda ake fadamin, nasan
akwai abinda yake faruwa, Dan haka koda yaushe nake Allah Allah nazo naga halin da yata
take ciki,
Muna falo nida Zahra, munacin abinci, su salma suka shigo nan suma suka zauna mukaci Gaba
daya,
Muna gamawa aka fara firar duniya, salma ce tahau chting tafara daria ita kadai
Alamar a chting dinne ake bata daria
Tashi nayi nashiga daki danna kwanta in huta, Zahra ma tabiyoni, salma tace "laaa! Ku tsaya
kuga pictures din ahmad Dan gidan deputy governor , shida wata yarinya wai yarsa" 橙提
Nide nace "a a kede kigani," 橙提
nayi daki, Zahra ma tace
" salma kyaban labari daga baya," itama tashigo Dakin
Ina shiga na tsaya ni kadai adakin ina tunani, kenan ma har ya haihu, mayaudari kawai
A a feenah, kimanta dashi kawai, kidena zancan yaudara ki barshi da halinsa, juyawa nayi na
kalleta sai a sannan nasan maganar danayi ashe afili nayi
Zahra tace " kiyi hakuri, ki rungumi mukhtar dinki, tunda kinga har salma nacewa wai ya haihu,"
Nace "insha Allah zanyi yanda kika ce"
Zahra tace "yauwa kokefa, ni wallahi salma ma tabani haushi, shiyasa nace latter tabani labari"
橙提
Nace "aike kin kulatama ni bazan iya controlling kaina ba, gara nabar wajan,ni yar iska ce zan
tsaya kallan pic din wata yarsa ina ruwana da ita" 踫潤蕃
Zahra tace "wallahi kuwa" 橙提
Mrs Usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to my family
47
Mama Jin wannan tambayar yasa jikinta yayi sanyi, tace "auta baby tana kano,"
feenah bata kawo komai aranta ba, tunda tasan de baby bazata wuce gidan kaka ko kalatinsu,
ko gidan husna ko Ammu ba, Dan haka tace
" Toshiknn, mama wannan satin iyayen mukhtar zasuzo,"
mama cikin farin ciki tace " to alhmdlh, Allah yakawo su lafiya auta, Allah ya nunamin bikin ki,"
feenah cikin murmushi tace "amin mama,"
nan sukai sallama,
Mama falo ta futo taga Abba a zaune tace "Abban husna yanaga Kanata farinciki haka,"
anan ya nuna Mata text din da nafeesa taturo masa, mama tace
" yanzun nan nima take fadamin awaya," Abba yace "to Allah yakawo su lafiya,wannan karon
insha Allah bazamuyi DANA SANI ba"
** *** **
momy tazauna jiki asanyaye, mamy hakima itama tazauna tace "hajia me yake faruwa ne naga
jikinki yayi sanyi?" Momy tace "hajia yaron nan yasaki yarinyar nan," mamy hakima ta rafka
salati, tace "saki hajiya?" momy tace "saki har uku,ahmad bashida hankali," mamy tace "a a
hajiya kina ganifa ita dakanta tace bazata iya zama dashi ba," momy tace "Amma kuma sai yayi
Mata saki har uku?"
Mamy tace " gaskiya de ahmad bai kyauta ba, kuma ni narasa me yake damunta? Kidubafa
kiga abinda take," momy tace
" akwai abinda yake faruwa hajiya, dole akwai abinda yamata, zaizo yasameni," waya ta dauka
ta kira ahmad Amma wayar akashe, tajuyo ta cewa mamy "wayar tasa akashe"
mamy tace "bari inkira alhaji hajia, yasan abinda yake faruwa yakira mahaifin yarinyar nan,"
momy tace "kirashi to," idonta yakada yayi Ja, mamy tace " haba hajia kiyi hakuri mana," momy
tace "yanzu ace hajia duk wata matsala datake bullowa agidan nan, shine yake haddasa ta,
haba hajia dole nashiga damuwa," mamy tace "kiyi hakuri mana hajiya" tafadi haka muryarta na
rawa itama
Mamy takira alhaji tayi masa bayanin komai, yace "gashinan Zuwa gidan"
** *** **
Hajia salaha tana ta zirga zirga agaban office din doctor, wata nurse ce tazo tace doctor yace
Zata iya shiga taga yarta, idan ta futo taje ta sameshi a office
Dakin tashiga, laila tana kwance tana bacci, hajia salaha tace cikin ranta duk abinda yasamu
yarta, wallahi bashi suka dauka, Dan saita qwatowa yarta yanci, duk ahalin marzuk sai sunyi
DANA SANI Akan taba yarta, office din doctor ta nufa
Kujera taja tazauna tana fuskantar shi, doctor yace " wato hajia gaskya sai kinyi hakuri, yarki
tasha qwaya, har tayi Mata shan hauka, wannan dalilin ne yasa Tafita ahayyacinta,"
Hajia salaha tace " to yanzu me ake ciki doctor?"
Yadubeta da kyau yace "maganar gaskya yarki bazata iya haihuwa ba, tasamu matsala a
mahaifarta dalilin wannan qwayar,
Kuma barin mahaifar haka zaisa ta dinga kumbura
Saide ayi dayan biyu ko adaure mahaifar kokuma acireta" 踫潤蕃
Hajia salaha cikin kuka tace "nashiga uku, laila ta kalau take likita, karya kake,"
doctor ya dubeta yace "kinga hajia banasan hayaniya, idan bazaki nutsu kiyimin bayanin abinda
za'a Mata ba, to kofa abude take"
File yabude yafara rubuce rubucensa
Hajia salaha kamar mahaukaciya tace
" wallahi bazai iyu ba, bazai iyuba,"
Tafita daga office din tana" bazai iyuba!! "
Bata wuce ko ina ba sai gidansu ahmad
Su momy suna nan, inda suke da, ko sallama hajia salaha batayiba, tafado falon tafara nunasu
da hannu," wallahi daya bayan dayanku sai kunyi DANA SANI "
Daddy da shigowarsa kenan yace" hajia me yake faruwa ne? "
Su momy sukai shiru,
Hajia salaha tace" Danku yasaki yata saki uku, sannan ya dirka Mata magani tasha har hakan
yasan mahaifar ta ta lalace, "
salati su momy suka sa, daddy kuwa waje yanema ya zauna yace
" hajia kiyi hakuri zanyi magana da alhajin "
Hajia salaha ba tare datace komai ba tajuya ta fice
Daddy yajuya ya kalli momy tada fara kuka, al'amarin ahmad ma kadai ta isheta, kosu Muslim
baza suyi abinda yake ba
Mamy ce tayi karfin halin yimasa bayani, daddy yace" to Allah yarufa asiri, idan yadawo
nazauna muyi magana dashi," yatashi yayi sama, mamy ta juya taci Gaba dabawa momy hakuri
Hajia salaha na fita, asbiti Takoma, alokacin laila tafarka, nan tafada Mata abinda likita yace,
laila tace" wallahi ahmad ne yabani lemo nasha, tabbas shine yasamin magani aciki "
Hajia salaha tace
" kwantar da hankalin ki, dole alhaji yadau mataki Akan haka, tunda dama can shine ya qulla "
Waya tadauka takira alhaji bukhar, tafada masa abinda yake faruwa, alhaji yace" to Allah
yakiyaye hanya "橙提
Hajia tace" kamarya Allah yakiyaye hanya,? Bangane ba "
Yace" kidauketa kiwuce gidanku, karki dawomin gida, tunda kin kashe Mata auren ai shikkenan
Amma idan kika kuskura kika dawomin gida abakin auren ki, "
yana Gama fada Mata ya kashe wayarsa
Hajia salaha ta rafka uban tagumi
** *** **
Juyi tayi tabu de idonta, cikin muryar bacci tace
" uncle munzo ko?"
Yace" baby munzo ga gidan can "
Tashi tayi dakyau tafara kalle kalle, har sukazo gidan tace " uncle,"
yace" na'am baby"
Tace "gidanku yanada kyau, yafi namu kyau,"
ahmad yayi murmushi yace "ai yanzu kema kin dawo nan, nan shine gidanku, kowa ya
tambayeki inane gidan Abban ki kice masa nan"
, cikin murmushi tace " to uncle"
Parking yagyara, yazo yabudewa baby kofa tafuto, yace " kinga wancan hanyar?"
Ya nuna Mata wani kofa, tace "eh,"
yace "to kije kishiga tanan, gani nan Zuwa, zan dauko kayanki,"
tace "to uncle"
da babyn ta a hannunta tabi hanyar, a hankali taturo tashiga falon, Gaba dayansu suna zaune
Ana jiran Ahmad 橙提banda daddy dayake dakinsa
Tana shiga falon taja ta tsaya abakin kofar, su momy suka zuba Mata ido, mamy hakima tace
" to ina muka samu baqi kuma? 橙提
Yarinya shigo"
Ahankli baby tashigo, mamy hakima tace
" wakike nema?"
Baby tace "Uncle"
Mamy tace " uncle kuma?" Cike da mamaki
Baby ta daga kai, alamun eh
momy cikin ranta tace
" masha Allah wannan yarinya kamar ba bahaushiya ba,"
Momy tace "zonan, menene sunanki?"
Izdihar tace sunana "baby"
Momy ta juya ta cewa mamy nifa da farko jinake batajin hausa" 橙提
Mamy tayi daria tace
" hajia ai shiyasa nace ina muka samu baqi"
Ahmad suka gani yashigo da jaka ahannun sa, baby tatafi da gudu wajansa
Su mamy da sauran yara suka zama yan kallo
Mamy tace "ahmad baqi mukayi ne?"
Ahmad yana murmushi yace " mamy yarinya aka bani, kyauta" 橙提
Kallansa suke da mamaki
Yace " mamy serious, bani ita akai, nima nayi 'ya yanzu"
Momy ce tace "kai yimana bayani yanda zamu gane" 橙提
Anan ahmad yafada musu komai
Momy nan da nan taji tana kaunar yarinyar, ta janyo ta tace "zonan baby sannu kinji"
Izdihar tace "yauwa," ta kalli ahmad tace "uncle ina maryam din dazamuna wasa?"
Ahmad yace "baby bakya mantuwa ko?"
Mabaruka tashi kije kibata abinci, kiyi Mata wanka ki kaita Dakin auta, mabaruka cikin murna
tace "to zomuje," takama hannun ta suka tafi
Shiru sukai dukansu, sannan daga baya momy tace "ahmad me yake faruwa, tsakanin ka da
laila?"
Shi sai sannan ma yatuna da ita, shaf ya manta ta wallahi
Ahmad yace "babu komai momy"
Momy tace "hajia kinji ba, kinji abinda nake fada miki ko? Zurfin cikin tsiya
Bari nakira mahaifin ka,