Showing 102001 words to 105000 words out of 113548 words
Jin tattausan hannun ta abakinsa, zubawa Zara zaran gashin idonsa ido
nayi ina kallo, na shagala a kallan sa, ahankli yabude idonsa daya fara sauya launi shima yana
kallo nah
Juna muka zubawa ido muna kallo, kowa da abinda yake saqawa acikin ransa
Jiyake kamar ya janyo ta jikinsa ya rungume ta, yaji dadin rarrashin ta, yayinda takejin wani irin
yanayi atare da ita mai wuyar fassaruwa, meyasa ahmad ya karbi abinda take tattalinsa fiye d
komai a duniya? Meyasa bayan ta yafe masa takejin har yanzu zuciyar ta, taqi sake wa dashi
kamar da? Meyasa?
Sallama mama ta doka atsakar gidan, hakan ne yafargar dasu daga duniyar dasuka Lula
Cikin sauri yasaki hannun nata ya zauna, yayinda feenah take takawa ahankli Takoma wata
kujerar daban nesa dashi tazauna,
Hannun baby yana cikin na mama suka shigo falon, tana ganin feenah tafara buya a bayan
mama
, mama tace "kekuma me aka miki kamar hawaye a idonki?"
Murmushi ahmad yasaki, baice komai ba
baby tace "mama wai danna cijeta da wasa shine tace saita Rama"
Mama tace "aikinfita hankali baby, Allah ya miki albarka kinji?" Baby tace "amin mama"
Kiran sallar da aka fara ne yasa ahmad yafita sallah, Ana idar wa kuwa sukaiwa mama sallama
zasu tafi inda mama tabasu abubuwan girki dayawa dasu kayan qamshi na girki tace sukaiwa
hajia, feenah kuwa daga Allah yakiyaye bata qara cewa komai ba ahmad yaso yasamu Abba
agida Amma hakan bai iyuba
** *** **
Next day
"Daddy dama inaso ne ka nema min auren nafeesa awajan abbanta, munriga da mungama
dedetawa da ita,"
daddy yasaki murmushi yace "eh naji su hajia sunce anfasa bikin nata ko?"
Ahmad kansa aqasa yace "eh daddy"
Daddy yace "Toshiknn babu damuwa, insha Allah zanje zarian da kaina,"
dahaka ahmad yafice daga falon ransa fari tass, gara ayi auren, koma menene yabata hakuri,
Dan yasan zaiyi laifi, tunda shide basu mayi wata maganar kirki shida itaba
Ba'ayi sati dayaba kuwa daddy da tahir da abokan daddy na kusa sukaje zaria, Abba kawai
ganinsu yayi, nan yashiga kaikawo wajan yi musu hidima, bayan komai yalafa sunci sunsha ne
suke yimasa maganar abinda yakawo su, Abba yace ai ahmad dinma yafadamin sunga ma
daidai tawa ajunansu, saboda haka ni ina ganin babu wata damuwa, dama matsalar ai daga
wajansu ne kuma sun dedeta, Dan haka nabaku nafeesa, nan take aka sanya ranar biki nanda
wata daya cif
Tahir shine yafita yasiyo su alawa da duk abinda ake buqata nasaka rana, suka bawa Abba,
nan suka tafi cike da farin-ciki
** *** **
Mama tanata murna, taje har dakina takirani tace inzo abbanmu yana kirana, ina Zuwa nagansu
afalo da kayaiyaki
Waya Abban yake Dan haka na nemi waje nazauna, da alama da Ammu yake magana, sai farin
ciki yake, Yau de Abba duk yanda akai yana cikin annashuwa inajinsa yana fadawa Ammu yace
yanzun nan suka tafi, banyi zatan da wannan maganar zasu zoba, aida kazo tunda safe Dan
akarbesu dakyau, eh, eh hakane kam, to Babu damuwa, saika zo din, Allah yakaimu, Allah
yakaimu, nan sukai sallama
Yajuyo ya fuskanceni yace "uwa ta ga kayan saka ranar ki nan, ahmad yafadamin kun Gama
dedetawa atsakanin ku, harma ya turo I yayansa dazu, mungama magana dasu, Dan haka mun
tsaida ranar bikin nanda wata daya insha Allah"
Arazane nadago kaina nakalli su Abba
Mrs Usman ce í ½í¶Š[5/3, 9:56 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: í ½í¶Ší ¼í¼±DANA SANI í ¼í¼±
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to my family
61
Nace "Abba sa ranar me? Ni wallahi bamuyi haka dashiba"
Mama ce ta juyo ta kalleni da mamaki tace
" kina nufin wai duk zuwannan dayake yana zarya awajanki kullum kina nufin har yanzu Baku
daidai ta tsakanin kuba?"
Kaina na daga alamar eh
Mama cikin fishi tace
" Tome yake Zuwa yi?"í ¾í´”
nayi shiru, tasake cewa
" nace miki me yake Zuwa yi?"
Abba yace "a a maman nafeesa karki Mata fada mana,"
yadubeni yace "ke uwata
Kalleni nan, banasan maganar wasa kinji ko?
Kifada mana gaskiya"
Mama tace "ai Abban husna daka barni da ita ranta yabaci, yarinyar nan nalura wasu ne da ita
agefe wanda suke zugata"
Ganin ran mama yabaci akaina, abinda sai mutum yadade bai ganiba, nan da nan nafara kuka
Cikin kuka nace "mama kiyi hakuri, Abba kuyafemin Amma ni wallahi bamuyi maganar komai
dashi ba"
Mama ce " tace to yanzu dakika ce bakuyi maganar komai dashi ba, so kike mahaifinki yakoma
yafada musu Baku daidaitaba afasa maganar biki, inyaso saiya koma mutumin banza ko?
Ai haka kikeso ko?
Toshiknn tunda haka kikeso kije kiyi tayi, na tabbatar shima ahmad din gajiya yayi da halinki na
masifar riqo, yagaji da bibiyar ki shiyasa yayi miki hakan, to wallahi bari kiji babu inda Abban
husna zashi, saide ke dayake marar mutunci ce, kije kice musu anqara fasa auranki akaro na
biyu,
Daga nan kuma duk layin dakikabi sai a dinga nunaki Ana zundenki, tashi kiban waje kafin
nadora hannu na ajikinki"
Kuka nake Sosai, yanda mai karatu baya zato, bantaba tunanin Akan ahmad mama Zata dauki
fishi har haka ba
Tashi nayi zan tafi daki, Abba yace "zonan mamana
Zauna anan,"
ya nunamin waje, nazauna ina sharar hawaye da gefen dankwali na wanda yayi bankwana da
kaina tun dazu
Abba yace "meyasa koda yaushe kikeso ki ganmu a hakane nafeesa?"
Dago kai nayi na kalleshi Jin yakira wannan sunan kai tsaye, shida yafi kowa boye sunan,
kasancewar sunan mahaifiyarsa ne
Nide narasa bakin magana Dan haka nace
" kayi hakuri Abba"
Yaci gaba da fadin "nafeesa kowanne iyaye na gari burinsu suga sun aurar da yayansu, Babu
uban da hankalin sa zai kwanta yanada yaya Mata agabansa
Menene laifin yaron nan?"
Kaina na girgiza cikin kuka nace "babu komai Abba"
Yace "yanzu ke ba rufin asirinki bane dana yarku idan ahmad ya aureki?
Yaron nan yazo nan agaban kowa ya nemi yafiyarki, atake kuma ya nuna yanaso ya aure ki
saboda yasan ya lalata miki rayuwa
Alokacin muka nuna masa munyi miki miji, yanzu kuma Babu miji, so kike nakoma nace musu
anfasa inyaso insaki agaba ina kallanki? "
Kaina naqara girgizawa
Abba yace" to Dan haka nafeesa, amatsayina na mahaifinki narokeki gafara ki yafewa wannan
yaron,"
Dasauri nadago na kalli Abba
Yace" eh, nafeesa banaso naci Gaba da ganinki a gabana, nafiso naganki adakin mijin ki,
kamar yar'uwarki, nasan ko bayan raina, nagama daku tunda nacika alkawarin dana daukarwa
Allah na kula daku a matsayin yayana
Kiyafe masa, kidena tuna baya koda wasa, yin hakan shine zaisa ki dinga zama cikin bacin rai
Ki dinga addu'ah Allah yasa hakanne yafi alkhairi kinji? "
Hawayen idona nagoge duka nace" to Abba insha Allah nayi muku alkawari ranku bazai qara
baci adalili naba
Zanyi abinda kuka umarceni insha Allah "
Abba yace" yauwa haka nakeso uwa ta, Allah yayi miki albarka "
Nace" amin Abba "
Tashi nayi da dankwali na ahannuna nace" mama me za'a dora abinci? "
Shiru tayimin
Abba yace" tana miki magana fa"
Mama tace "najita ai
Taje tayi abinda tayi niyya" í ¾í´£
Kamar wata qaramar yarinya nafara bubbuga kafata akasa nace "Abba kajifa abinda tace"
Murmushi Abba yasaki aransa yace auta kenan har yanzu de a autar take ganin kanta
Mama batasan lokacin data saki murmushi ba tace "naji, jeki dora mana duk abinda kikeso
auta"
Jin wannan furucin ne yasa tatafi kitchen din dadan gudunta
** *** **
Yayi kyau Sosai cikin qananun kaya, farar riga, farin wando, Jan takalmi Cambus, sai rigar
sama itama ja, yayi mugun kyau, yana ta zagaye falon, yakasa zama, daddy yadawo yayi
masa sannu da Zuwa, Amma yayi masa shiru, baiji yaya suka qare da iyayen feenah ba, "Allah
sarki ni" í ¾í´£
Yafadi haka afili, yanzu haka Kiran nafeesa akayi tatonamin asiri, tace ni bamu daidai ta da
itaba, Dan haka bazata iya aure naba, oh nikam wanne irin so nakewa yarinyar nan ne?
Toni yanxu wajan wa zanje inji yaya sukayi? Idan nakira feenah ma bazata saurareniba, abinda
zanyi kawai bari inje in lallaba tahir, inji yaya aka qare
Kamar wani zararre haka yake ta magana shi kadai
Key din motar sa yadauka yafice, su daddy da Momy suna zaune afalo, saijin tashin motar sa
sukayi, mamy hakima tace "nikam alhaji ka dawo kayi shiru yaya kukayi da iyayen yarinyar nan
ne?"
Daddy yace "ai mun gama magana dasu hajia, harma ansa ranar nanda wata daya"
Gaba dayansu itada Momy suka saki murmushi
Mamy hakima tace "a a alhaji kace babu zama yanzu zamu fara shirye shirye"
Momy tace "gaskya kam"
Daddy ya kalleta yace "au Yau kema harda ke?" Yana murmushi yace to ai shikkenan
Mamy tace "alhaji Amma ahmad baisaniba ko?"
Daddy yace " ban fada masaba, dazun nan yagama sussunkuyar da kansa yagama yatashi
yatafi, yanzu kunji fitar sa may be wajan abokinsa zaije ya tambaye shi"
Mamy tace "um Yau my son babu zaman lafiya agidan nan"
** *** **
"Wash wallahi nagaji sosai, da mukaje ma ban zauna ba nine nan nine can,"
husna tace "to sannu my husband"
Yace "ina yaran nan suke ne?"
"Suna wajan ummi"
"OK sweet hrt bar tausar nan kije kikawo min ruwa"
, bayan tadawo ne ta bashi yasha, tace "ya kamata ka kwanta kahuta ko? Waima meya kaika
zaria? Kuma dasu daddyn ahmad"
Tahir yace "munje ne ansa masa ranar auren sa,"
cikin mamaki husna tace
" ahmad de ahmad namu aka sawa rana?"
Tahir yace " shide, tare da feenanmu"
Husna tace "wai Dan Allah da gaske?
Wayyo!"
Tahir yace "wallahi, ahmad din yace sungama daidaitawa shida ita, Amma nasan bahaka bane,
zanyi magana dashi de latter"
Husna tace "kace akwai daru"
Tahir yace "saje can su qarata, su suka sani"
Husna ce tadauki waya ta kira feenah
Hakan yayi daidai da shigowar ahmad falon
Tahir yace "a a kaga na feenah angon gobe"
Waje ahmad yasamu ya zauna akujera, husna ta katse wayar tadawo suka gaisa, yace "anty
husna yayara?"
Murmushi tayi batace masa komaiba, tashige daki, tana so tayi waya da feenah
"Man yagarin, ya hanya? Please tahir ya kukayi? Hankali na yakasa kwanciya"
Da murmushi tahir yajuyo ya dubeshi yace "angama komai mutumina, sauran yaqin yana
wajanka"
Ahmad yace "kamar yaya?"
Tahir yace "zaka zama ango nanda wata daya, saide kace bakuyi magana da itaba, saide
kadage ka lallabata,"
wata daria yasaki, har tahir yana mamakin wannan daria,yaushe rabon dayaga ahmad yana irin
wannan dariyar?
"Shine daddy yayita wahalar Dani bai fadamin Ba? Alhmdlh tun yanzu nafara jina ango tahir,
bansan yaya zanyi mataba, tahir nabata hakurin nanemi yafiyar Amma taqi kulani, shiyasa nace
kawai mun dedeta kanmu, idan akai auren a hankali Zata ware, wallahi har tausayin kaina nake
yanda nake zarya agarin nan, ina kaunar ta, ina Zuwa gidansu zamu zauna gani gata, jikina da
jini tahir, bazan iya jurewaba tun kafin tasa inyi abin kunya agaban surukaina gara inmata dole
ayi auren koma menene zai faru saiya faru anamu gidan "
Ajiyar zuciya tahir yasauke, yace" hakane kayi gaskya kuma,"
ahmad yace" yanzu mu tsara komai medame kake ganin za'a yi lokacin bikin "
Cikin sauri tahir ya kalleshi yace" haba gaye, haba, yaufa saura kwana talatin "
Ahmad yace" Naka wasa ne, bari kaga in nemi paper a fara tsara komai yanda zai kasance "
** *** **
"Amarsu ta ango, ashe ashe kuma"
Feenah tace "ashe ashe me?
Ni wallahi sister badan Abba yamin fadaba, Babu abinda zanyi dashi"
Husna tace "hakanma de Mungo de, feenah ahmad yana sanki, nima kuma na tabbatar dahaka,
tun kafin aure na da tahir, mutum yazama shiru shiru duk a dalilin soyaiya,"
"sister damafa haka yake baya magana, in kinga maganar sa toda mijin ki ne, ni narasa ma ya
akayi nakasa mantawa dashi"
Husna tace "tayaya zaki manta dashi kuwa, ai bazai iyuba"
Nace "saboda me?"
Tace "saboda da jininsa kike rayuwa feenah"
Nace "kamar yaya, me kike nufi?"
Tace "tabbas feenah da jikin ahmad ajikinki, lokacin dazaki haifi baby su tahir sun tabbatar
bazaki iya ba saboda bakida isasshan jini ajikinki, alokacin ahmad yana asbitin baisan wacce
marar lafiya ce take buqatar jini ba, batare dayaganki ba yace adiba a nasa asaka miki, kuma
aka gwada jinin yayi daidai danaki
Ki fadamin tayaya zaki iya mantawa dashi, bnda dunbin soyaiyar da kukayi abaya?
Sister ahmad yamana komai, batare da yasan Ammu qanin mahaifinmu bane yadauke shi aiki a
company sa, yabashi manaja
Batare da yasan baby yarsa bace, yasota, yajata ajikinsa, harma yanemi abashi ita aka bashi
Sanadin haka gidan damuke ciki yasauya masa fasali daga tsoho Zuwa sabo
Ahakan duk baisan kinada alaqa da wadannan mutanan ba yayi wannan aikin alkhairin ko
tanan yaci ace kin qara gane ahmad mutum ne nagari, mai taimakon mutane, najikinsa da
wanda ma bai sansu ba
Kiyi tunani feenah, yakamata ki ajiye duk wani fishi a gefe, ki rungumi ahmad, kuyi rayuwar ku
kamar kowa"
Mrs Usman ce âœï¸
[5/3, 10:54 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: í ¼í¼±DANA SANI í ¼í¼±
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to my family
62
Nace sister kina nufin shine yabani jini?
Husna tace qwarai kuwa haka tahir yafadamin
Kaina na dafe da hannu na, nace Amma de kinsan irin halin daya sanyani aciki, na fuskanci
abubuwa dayawa, ciki harda korata da mahaifina yayi, ninaci wahala ta ni kadai, sannan
andauki yarinyar anbashi, kuma hakan bai isheshiba saiya hada dani
Husna tace duk wani bawa mumini da yafiya aka sanshi feenah
Jinake keda bakinki ki kace Abba ma da kansa shiyace kiyafewa ahmad din, to kinga shima
mutumin daya koreki agidan kenan, zuciyarsa tayi sanyi, harya manta da baya yake so kiyi aure
Menene ribarki idan baki aure Shiba, banasan naga kina zaune agida haka kawai a matsayin ki
na yar'uwata, bayan kin Riga da kingama karatun ki, kiyi hakuri feenah, kidauka haka
qaddararki take
Ajiyar zuciya nasauke nace toshkn sister insha Allah komai ya wuce, zamu dawo kamar da
Murmushi tasaki tace yauwa qanwata kokefa
Yanzu abinda nakeso dake kawai kihado kayanki kidawo kano muci Gaba daga inda muka
tsaya
Nace kai anty husna ni banasan wannan abin wallahi, wancan gyaran ma ai ya isa, husna tace
bakida hankali feenah,ke a tunanin ki yanda yake wannan rawar kafar akanki, ke a tunanin ki
qyaleki zaiyi? To wallahi garama ki farka, in kanada kyau toka qara da wanka,gyaraki zanyi tsaf
ta yanda zaidinga tambayar kansa cewa anya kuwa nafeesan daya sani ce abaya? Daria zancan nata yabani, tace Toshiknn tsaya daria, kede kawai kitaho, nace zanzo sister
Amma gaskya agidan kaka zan zauna, tace babu wani gidan kaka, anan zaki zauna, nace to
naji shikkenan sai nazo, dahaka muka kashe wayar
Ajiyar zuciya mama tasauke ta tabbatar wannan dadewar da feenah tayi tana waya da husna
take magana, alhmdlh ta godewa Allah daya bata yaya masu hadin kai, Allah yasa dukkanin
zuri'arta su kasance haka
Husna nafita daga daki, falo Takoma, su ahmad suna nan yanda tabar su, tahir yace my heart
irin wannan dadewar haka, kinbarni ni kadai, nasan keda amarya kuke waya, Amma ni kinbarni
da yunwa, husna tace toyi hakuri mana, bari akawo muku abinci, ahmad yace ai anty husna ni
wucewa ma zanyi, husna tace bazaka tsaya kaci abincin ba? Yace aina qoshi, ina su mama?
Tace suna can wajan ummi
Ahmad yace yakamata de Yau kibani su suje wajan baby, husna tace kadauke su acan, Allah
yakai ku lafiya
Tahir yace wallahi kuwa
Murmushi husna tayi tajuya tayi kitchen
Ahmad ya kalli tahir yace saboda Xaka zauna daga kai sai itaba, ai dole kace atafi dasu
Tahir yace nabaka suma kyauta, har bayan aure, kai har bayan amarci ma, idan kun Gama
amarcin saisu dawo
Kasa magana ahmad yayi kawai ya girgiza kansa yafita, tahir kuwa yabishi da daria
Bai bata lokaci ba awajan ummi yadauke su tareda kayan su suka tafi
** *** **
"Ina kika bar wayar inata kiranki tun dazu zan baki labari mai dadi"
Saudat tace "Momy wallahi munje asbiti ne"
Gaban Momy yayanke yafadi, tace "waye ba lafiya acikin ku?" Daria saudat tayi tace "wallahi
Momy Akan rashin haihuwar nan ne de mukaje aka dubamu , Amma likitan yace lafiyar mu
kalau, kawai Allah ne bai kawo ba,"
Momy tace" to alhmdlh
Muma ai muna nan muna muku adduah Allah yakawo nagari, shima wannan naga ta auren sa
kawai yake kwata kwata babu maganar neman magani agabansa "
" wai yaya?"
Momy tace" shide,"
" to wanne irin aure kuma