Showing 66001 words to 69000 words out of 113548 words

Chapter 23 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

03 Apr 2025

9287

su,
Tahir inajin kaunar izdihar sosai araina, banajin iyayen dasuka haifeta ma, zasu kaini sonta ν ½νΉ†ν ΌνΏ»
ni idan aka bani itama ta isheni rayuwa
Katayani da adduah tahir Allah yasa iyayenta su amince da buqatata "

Tahir yayi ajiyar zuciya, yace" ahmad karka damu inde Akan wannan ne, idan ma basu yarda
ba, nima zan shiga cikin maganar insha Allah zasu bamu ita,"

yaqarashe maganar yana murmushi, ahmad yayi masa wani irin kallo, yace" abamu ko abani?
Aiku kun nema anhanaku, yanzu lokaci nane, "
tahir yace

" to hammad baban izdihar, "
ahmad yasaki daria kamar bashida damuwa yace" kai Amma tahir naji dadi wallahi, idan aka

bani izdihar wannan uncle din datake kirana dashi denawa zatayi, takirani da.... ''

Cikin sauri Tahir ya katse shi, yace "daddy?"
Ahmad yace "no banasan daddy
Nafisan takirani da Abeey," tahir yace "um kun koma larabawa kenan,"

ahmad yace "ka manta da jikansa kake tare, Dan renin hankali kawai,"

tahir yace " naji,"
Ahmad yaci gaba da fadin " idan kuma na auri my feenah, nasan itama inde taga baby Zata
sota, kaga ita kuma saita dinga kiranta da ummi"

Tahir ya harare shi cikin wasa yace "wannan ai sata ce, da gasa" ν Ύν΄£


Ahmad yace "edin mun sata,"

tahir yazuba masa ido yana kallansa cikin ransa yace Allah yabaka feenah ahmad, wato har
yanzu de tana nan aransa, ahmad yace "gaye kallanfa?"
Tahir yace "kawai so nake naga yaushe zaka haihu, bansan wanne irin so zakayi wa yaranka
ba, wannan yarinyar izdihar ma kana Mata irin wannan son"

Ahmad yabata fuska yace "oh tahir naroqeka kadena banbanta izdihar da yaran dazan haifa,
itama yata ce"

Tahir yazuba masa ido yana ganin karfin Hali, yace "Toshiknn daddyn izdihar, magana yaqare"

Ahmad yayi shiru, sai can yace "tahir nikuwa kunada irin qwayar da aka sakamin nasha?"
Tahir ya kalleshi da mamaki, yace "eh akwai mana me zakai dashi?"

Ahmad yace "nikuwa me zanyi dashi tahir kawai ganinta zanyi"
, waya tahir yadauka, yabada umarni, nan da nan aka kawo masa ita,tahir yace "kaganta nan
idan mutum yasha ta wuce guda biyu, shine take yi masa illah,"

ahmad yakarba ya karanta, yace "shikkenan nagani ungo abinka

Nizan wuce gida,"

tahir yace "Amma ahmad bamuyi magana Akan magungunan dazaka dinga shaba,"
Ahmad yace "no karka damu tahir, nafadama nifa izdihar ta isheni, kabar maganin kawai, latter
mayi magana,"

tahir yace "ok,"

yafuto domin rakashi wajan mota, anan yajashi yafara nuna masa yanda yakeso ya maida
fasalin hospital din


** *** **


"Mom wallahi bazan iyaba, dama nafada miki, ai wannan zaman danayi ma nayi hakuri, kinga
kuwa yanzu tunda bazai iya haihuwa ba, mezan zauna inyi agidansa,"

hajiya salaha tace
" gaskya kam tayaya ma zaki zauna da mutum fanko, ai gara kibar masa gidan, wannan jaraba
har ina, Allah yabaki wani kawai,"

laila taka she wayar ba tare datace amin ba, mai taxi din tabawa umarni yaqara sauri, tagaji da
wannan tafiyar dayake kamar bayaso
Tana Zuwa gida batayi bangaren taba, Part din su mamy tanufa, suna zaune dukansu mabruka,
yan biyu Muslim da bukhari, da auta maryam, laila tashigo duk bata hayyacinta
Mamy hakima tace "laila lafiya?"

Laila tace "mamy da momy zanyi magana bada keba" ν ½νΈ³

Mamy hakima najin haka aranta tace babu lafiya, mom tace "inajin ki laila meya faru?"
Laila ta kwashe komai tafada musu, tace
" nikuma bazan iya zama da juya ba, Dan haka ku fada masa yasakeni, bazan iya zama babu
yara ba, ashe ma Dan naku Dan shaye shaye ne, inba Dan qwaya ba, meya hadashi da shan
qwaya har takai shi ga samun matsala, to nide bazan iyaba,"

tana fadar haka tajuya tayi gaba

Mabruka dayake itace babba maidan hankali, nan da nan tafara kuka, momy tace" innalillahi wa
inna ilaihir raju'un"
Mamy hakima kuwa itama kuka tasa, tace
" mun shiga uku, wannan wacce irin masifa ce Zata shigo mana gida, gaskya nikam ban yarda
ba"
Mamy tace "hajiya ba'a shedar Dan Yau, Muslim dauko min wayata"
Yana kawo Mata wayar, ta kira ahmad tace
" waladee kazo gida yanzu inasan ganinka,"

ahmad najin haka yace cikin ransa sun samu labari kenan ν Ύν΄£


** *** **

"Haba Abban husna, wacce irin magana ce wannan? Ahmad fa yayi mana komai, nikam yaron
ya kwanta min araina, nayarda da tarbiyar shi, Dan haka inde nice babu damuwa na bashi
baby," ν ½νΉ†ν ΌνΏ»

Abba yace "to shikkenan alhmdlh, yanzu zamu fadawa ita nafeesa ne kokuwa?"

Mama tace "haba alhaji ita take iko damu kokuma mune muke iko da ita, idan aka bada baby
kamar qarin rufin asirinta ne ai, Akan abin kunyar data janyo mana, Dan haka ni aganina kawai
aqyaleta,"

Abba yace "to insha Allah idan tadawo sai nayi Mata bayani dakaina," mama tace "hakan yayi,"

Abba Ammu yakira awaya, yafada masa shawarar dasuka yanke Akan maganar ahmad, Ammu
cikin ransa yace gaskya ahmad yasamu karbuwa sosai awajan yaya
Shima kai tsaye yace " ai Babu komai, ahmad kowa yana masa shaidar kirki,"
Mama tace "to ai kaji alhaji, nikam wallahi banji dadi Bama daka bashi sati dayan nan, sai yaga
kamar bamu yarda dashi ba, Dan haka kirashi kafada masa gobe yazo yadauke ta su tafi, tunda
itama kanta yarinyar tana sanshi,"

Abba yace "hakane, Amma kinsan komai yana buqatar shawara, shiyasa na bashi sati dayan,"
sake daukar wayar yayi, yakira ahmad, alokacin yana kan hanyar sa ta Zuwa gida, Abba yana
fada masa, ahmad ya dinga kwarara godiya, kuma yace insha Allah gobe zaizo gidan, dahaka
sukai sallama, parking yayi agefen titi, yafuto daga motar yayi sujud shukur, yanata farin ciki,
sannan yakama hanyar gida


** *** **


Yana Zuwa gidan,tun kafin yagama gyara parking din motar sa laila ta taho da sauri tace,
" dama jiran ka nake, ahmad inaso kasani zamana dakai yaqare, kasakeni kawai shine abinda
nake buqata,"

ahmad yace " laila kanki daya kuwa? Meya kawo wannan maganar? Kinga kije ciki, ina Zuwa
zanzo sai muyi magana,"
tana huci tayi part dinta

mabruka naganin ahmad yashigo falon tahada kan qannanta sukai daki, momy tatashi cikin fishi
tace" ahmad mai nakeji? "
Ahmad yace cikin rashin damuwa" momy me yake faruwa naganku haka?"

Momy ta dauke shi da mari, cikin sauri ya riqe kumatunsa, cikin mamaki yace"momy?"
Mamy hakima tace "my son, meya kaika shaye shaye har hakan yahaifar ma da rashin
haihuwa?" Ahmad yace "shaye shaye mamy, ni ban taba shaye shaye ba" ,
momy cikin fishi tayi kansa tace "laila karya Zata ma ne?
Kokuma mune zamuyi Maka karya?"
Ahmad zuciyar sa takarye, nan da nan yafara kuka, yace "momy ki yarda Dani mana, wannan
bahali na bane,"

mamy hakima tace "munji Ahmad Amma me yake faruwa,"

cikin hawaye ahmad yace "momy, mamy, kuyi hakuri, ni ban taba shan qwaya ba, wannan
dalilin ne yasa nakori walaya daga cikin gidan nan, wani yabata magani da kudi Akan ta
sakamin acikin lemo nasha, kuma tayi nasara akaina, nasha, nasha momy"

ya qarasa yana kuka ν ½νΈ­

Yace "wannan qwayar datasamun itace dalilin dayasa likita yace bazan iya haihuwa ba, saboda
nasha dayawa, sannan... zaici gaba da magana wani irin Baqin ciki yatokare masa maqoshi,
har gobe idan yatuna abinda yayiwa feenah abun yana qona masa rai

Momy tayi jagwab ta zauna Akan kujera, mamy hakima tace "mun shiga uku, meyasa baka
fadaba ahmad? Aida an tambayeta waye yasa ta aikata hakan"


Ahmad yace "mamy na tambayeta harma tabani number datake magana da mutumin, Amma
alokacin ina cikin fishi, saina fasa wayar"

Mamy hakima tace
" innalillahi, kaga tashi kaje kabawa matar ka hakuri, zamuyi magana anjima"
Ahmad ya share hawayen sa, yatashi yafita

Yana Zuwa part din, yaga laila bata nan, Dan haka yabita daki, tura kofar yayi a hankali yashiga,
Amma kuma waya take bataji shigowarsa ba, taci Gaba da waya tana fadin

"Wallahi sofy kede bari, ai nake fada miki, qwayar dana bayar asaka masa ne kwanaki,
ν ½νΈ³ν ½νΉ†ν ΌνΏ»toya zanyi sofy, nakira shi nayi nayi dashi tawaya ina kaunar sa, yabani dama inbaiyana
masa son danake masa, Amma yaqi, shiyasa kin sanni ba jira nabawa musa aikin, Naso kawai
dana dandani zumar sa in wullar dashi, Amma bansamu hakan ba, Dan haka nayi amfani da
yar aikinsu kawai, kuma still shima abun yaci tura, kinga kuwa dana sameshi yanzu sama taka,
ai kinga saina kyaleshi kawai, yasakeni kawai, akwai alhazan dasuke jirana "

Idonsa ne ya rufe ruf, yadena gani, kamar makaho haka yajuyo baisan inda yake jefa kafarsa
ba, yanabin bango ahaka ya qarasa falo, kan kujera yafada, yana ambaton

" innalillahi wa inna ilaihir raju'un ν ½νΈ­ "







Mrs Usman ce ν ½νΆŠ
[5/6, 3:32 PM] ❣️DANGI DAYA❣️: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my lovely sis golden girl

44

Tsugunna wa yayi daidai tsawon ta, yafara kallanta, itama zuba masa ido tayi, tana aikin
kallonsa, ahmad yace "ya sunanki? Kuma keda waye kike gudu haka?"

Tace "sunana Baby" , ahmad yace "baby kuma?"


Acan cikin gida kuwa, mama ce tanemi husna tace "yi sauri, naga su baby sun fita da gudu,
nasan fada suke jeki kirasu"

Ahmad yace " nace keda waye kike gudu haka?"

Tace "nida qannai nane, gasu can,''
su mima ne suma suka taho da gudu, suka riqe ta suna" mun kamaki,"

mama tace" laaa uncle,"

nan da nan dayake su sun sanshi suka riqe shi, ahmad yace " kunga muje kushiga gida
kudena guje guje,"

Ammu ne yahango shi tare da yara, yaqaraso da sauri, yace

"yallabai fada suke ko? Bari nakai su gida,"

cikin sauri ahmad yace "a a hassan bari in kaisu, kasan wannan yarinyar ne?"

Yafada yana nuna baby, Ammu yace "eh nasanta," ahmad yace "ok bari in kaisu,"

nan kuwa yafadi hakanne danya sake samun damar kallan yarinyar

Saida yakawo su har bakin kofar gidan, Amma hankalin sa yanakan wannan yarinyar, nan sukai
kicibis da husna, cikin sakin fuska tace
"a a kaga angon lailah,"

ahmad yace "gwauruwa"
Husna aranta tace um Yau kuma yan wasanne akansa,
Gaisawa sukai, yace
" Mata nima nazo daurin aure ne, saikuma naqare arabon fada,"

husna tace "ai inde izdihar ce har ka gaji, haka take bataji, kuma fadan ma da qannanta ,"

ahmad yace "au haka sunan ta?" Tace "eh"

Cikin ransa yace "izdihar"
Suna mai dadi
Sallama ya yiwa husna, yajuya yana kallan baby yatafi

Husna tace "sarakan rigima saiku juya mutafi aiko,"

tayi gaba su mama suna bayanta, juyowa tayi kawai sai ganin baby tayi ta tsaya tanata kallan
ahmad dayake tafiya, husna tace "wannan yarinya bataji,"
ta daga murya tace "baby taho mana,"

da gudu izdihar ta taho


** *** **


Gida yakoma cike da gajiya, kasancewar yatsaya gaishe gaishe duk yagaji, dining ya kallah,
aransa yace " tofa Yau yaushe"
Daki yashige yayi wanka yafuto da kayan shan iska ajikinsa, afalo ya zauna ya kunna kallo,
Amma Gaba daya tunanin sa baya tare dashi, yana tare da yarinyar nan, murmushi yasaki daya
tuno ta, aransa yace meyasa nakejinta araina ne haka?
Allah sarki my feenah, bayan rabona dake Yau naga photo copynki,ya Allah!
Meyasa nakasa cire yarinyar araina, laila ce takatse masa tunanin sa, tace " Majnunun lailah,
ga abinci a dining fa naga ko budewa bakayi ba,"
ahmad yace "ok aiji nake wani kika hadawa, tunda naga bayi kikeba, sannan laila naroqeki Dan
Allah kidena fadamin sunan nan, banajin dadin sa," ν Ύν΄£

laila ta harzuqa cikin fishi tace "ok bakajin dadin wannan sunan, saide feenah ko?"

Ahmad ya kalleta da mamaki, "ya akai kikasan wannan sunan?"
Laila tace. "ai dole kayimin wannan tambayar, kullum bakada aiki sai Kiran sunanta da daddare,
wallahi zan nemi wannan yarinyar sai jikinta yagaya Mata" ,

Ahmad baisan lokacin daya saki daria ba, ya kalleta yace, "da gaske? Amma wallahi Dakin
taimaka min, ni kaina nemanta nake, laila da kinyi babban jihadi idan kika shiga duniya kika
nemota, ni kaina dana soki" ν Ύν΄£


Zuciya tazowa laila wuya, cikin takaici tajuya tayi daki, wato Yama maidata mahaukaciya, itace
Zataje yawon duniya ta Nemo masa mace, lalle ν Ύν΄£


** *** **


After 2 months
"Uncle, idan nayi tsokana zaka dinga taremin?"

"To meyasa zakiyi tsokana? Bakya Jin magana ko?"
"To uncle kenan kai baka sona ko? Nikam ina sanka"
Cikin sauri ahmad yace
" izdihar ina sanki mana," turo Dan qaramin bakinta tayi, tace "nide um um, natafi tunda baka
sona, bakasan ka taremin tsokana,"
ahmad yace "ina sanki mana, tsaya kiji,"

"a a uncle natafi baka sona,"
kawai tasa gudu, yana "baby! Baby!!"

Amma ina tatafi

Cikin baccinta taji yana fadin "Baby ! Baby!! Baby!!!"
Takaici ya isheta, fillon dayayi matashi dashi tajanye, cikin sauri yafarka daga baccin dayake,
yace "laila, lafiya ina bacci zaki tasheni?"

Laila tace "wato abin Naka kullum qara ta'azzara yake,ν Ύν΄£
da kaine feenah, yanzu kuma ka dawo Kiran wata baby
Wacce shegiya ce baby kafadamin?"

Ahmad yace "Allah yabaki lafiya," 😏

yadauki fillonsa yakoma falo
Daga murya tayi yanda zai jiyota, tace "saide yabamu lafiya Gaba daya, bazan iya zaman
wannan jarababban auren ba,"
tayi juyi gamida rufe idonta


** *** **


Ita kadai ta qyalqyale da daria, tana zaune afalo, da teddy ahannun ta, mama datake linke
kayan Abba tajuyo ta kalleta da mamaki, tace
" izdihar kedawa haka yarinya kamar me aljanu? "

Baby tace" mama rannan na tuno, naqwace abin wasan su mima nagudu, ingaya miki ko mama
ina fadawa wani mutum yaqi karbe abin daga wajena, kuma yake ta kallo na, shine nima naketa
kallansa, kuma kullum kullum saina tunashi mama "

Mama tace" yaushe kika ce? "ν Ύν΄£


Baby tace" mama nace miki rannan "
Mama tasake kallanta cikin mamaki tace" toko amafarki kika hadu dasu? "ν Ύν΄£

Baby tace" mama rannan fa da mukaje auren anty aysha"
Mama tace "kekiji shirme, Abu kusan wata biyu,amma kicemin rannan"
Izdihar tasa daria, tace "to mama kema zakina taremin idan nayi tsokanar?"
Mama tace "ban fada miki ba, shima kuma bai kyau tamin ba, dabai dakekiba, tunda ke kullum
kunnan qashi ne dake"
Mama tana wannan fadan Wayarta tadau qara, feenah ce ta kirata, bayan sun gaisa mama
tabawa baby wayar, Ana bata wayar tayi daki da gudu, tana cewa, sabuwar anty, infada miki
rannan nahadu da wani ya taremin tsokanar danayi ν Ύν΄£


Mama aranta tace ai Yau kuma mun shiga uku 🤔�

** *** **


Wayarsa yadauka yakira hassan, cikin sauri Ammu yasameshi a office dinsa, ahmad yace
" yauwa dama inasan inma wata tambaya ne, yarinyar dana gani kwanaki, shine nace Dan Allah
inane gidansu, inaso inje inganta"

Ammu ya kalli ahmad da mamaki, yace "wai izdihar?"

Ahmad yace "eh itafa, wato hassan inajin kaunar yarinyar ne acikin raina, yanda baka zato, tun
lokacin dana ganta, naji inasan kasancewa da ita, please a wacce unguwa suke?" ν ½νΉ†ν ΌνΏ»

Ammu yayi murmushi yace "ai yallabai a zaria take,"

gabansa ne yafadi, cikin ransa yace zaria, garinsu feenah fa kenan

Ammu yaci gaba da fadin "ai yarinyar yaya nace, itace qaramar yarsa,"

ahmad yace cikin "mamaki yayanka?kenan kanaso kacemin sister husna ce?"

Ammu yana murmushi yace "hakane yallabai,"

ahmad yace ikon Allah, to bani address din gidansu please, saboda bazan gane ba, rabona da
naje Tun bikin su Husna "

Babu bata lokaci Ammu yabashi, ahmad baiyi wata Wataba washe gari yatafi zaria,ν Ύν΄”
da rana ya isa gidan, yafaka motarsa a gefe, manyan kaya ne ajikinsa, yatsaya awaje, yarasa
wazai aika ayi masa sallama damai gidan
Kamar anjefota saigata da gudu tazo Zata shiga gida, aransa yace yar halak, wato itade
da'iman tana cikin gudu, daga murya yayi yace "baby!!"

Juyowar dazatai ta ganshi, wajanshi ta qaraso da sauri, ahmad yace "daga ina kike da gudu
haka ?"

Tace "daga school"
Saida tafadi haka sannan ya lura da uniform din jikinta, da kuma lokaci, yasan yanzu ne ake
tashin yara a school, yace "to zo nan"
Matsawa tayi kusa dashi, ahmad ya tsugunna daidai tsawon ta, yace
" kin gane ni?"
Baby tace "emana, kullum saina tunaka, jiyama nabaiwa sabuwar anty labarin ka" ν ½νΈ³

Ahmad cikin ransa yace kullum saita tunani, tome yake shirin faruwa ne? Yace "nazo ne nima
naganki,"
washe baki tayi tace
" Allah?"
Kafin yabata amsa tace
" ina sonka,"

tafada jikinsa, ahmad yayi saroro, baiyi wata Wataba shima ya rungume ta ν Ύν΄£
Tsayuwar motar dasuka jine ya ankarar dasu, baby tatafi da gudu wajan Abba, tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login