Showing 93001 words to 96000 words out of 113548 words

Chapter 32 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

03 Apr 2025

9288

Allah ya tabbatar da abinda yake alkhairi,"

ahmad yace "amin
Wai wayema wannan yaron ne? Dan waye?"


Murmushi tahir yayi, yace "kai mukhtar ma yaga takansa, badan kowa bane, kawai de Allah ne
yahada soyaiyar su
Kwanaki ma bawan Allah saceshi akayi akanta, wai saiya rabu da ita 橙提
Suma auren nasu ai sai sunyi taka tsantsan Dan may be akwai abinda yake faruwa wanda mu
bamu saniba, Amma inba haka ba satar ango guda? "

Ahmad yace" to ai gara asace shin, "踫董踫潤蕃

tahir yace"ahmad kalau kake kuwa?" 橙提
Ahmad yace " a a totaya zaisa mutane dayawa cikin tunani Akan shi kadai?"
Tahir yace "a a karka ce haka, kasani wanda yasa asaceshin ko shima Santa yake?" 橙提

Ahmad yadagawa tahir hannu yace "tahir please kadena cewa Ana sonta"

Tahir yace "shikkenan nayi shiru"

Acan falo kuwa saudat tace " gaskya Momy abun kamar almara," Momy tace "wallahi sauda,
kede al'amarin sai adduah shine fa mukaje bada hakuri d neman yafiya"
Saudat tace hakane, "bari nakira yaya tahir din ince masa ya turomin Number ita feenah
Nasan bazai rasaba," Momy tace "eh hakane kikirashi"


** *** **

After one week
"Zahra wallahi de kinji abinda ya faruwa,"

"to feenah yanzu yana Kiran kine?"
Nace "bai kirani ba Zahra kuma nima bana fatan hakan,"
Zahra tace "hakane kam
Gara zauna lafiya,"

Wayarta ce tayi ringing
Tana dubawa ta daga, tace "hello"
Sauda tace "sis feenah kin kirani Nagode"

Daria nasaki nace " sis kiyafemin Dan Allah"

Saudat tace "a a wlh Babu komai karki damu
Sis feenah naji abinda yake faruwa, nima ina qara baki hakuri Akan abinda yaya yayi miki ni
nasan ba laifinsa bane, Amma haka kawai bazai miki komai danya cutar dake ba"

Nace "babu komai Saudat
Ai komai ya wuce, saide Allah yayafe mana,"
Tace " amin"
Nace "ina garinkufa, wallahi Yau na shigo," saudat tace "wayyo sis inama ina kano, me akeyi?"
nace "wallahi gani na dawo nida baby, zankaita gidanku, sannan kuma..." Sai tayi shiru
Zahra ce ta qwace wayar tace "saudat Zahra ce sabuwar qawar feenah, wallahi tazo gyara ne
na bikinta, kinsan yarage saura sati uku"

Saudat tace" bata wayar," saida sauda tayi Mata tatas, wato da saide aji bikin ko, anan de
feenah tabata hakuri, tace kuma zatazo bikin insha Allah, nan sukai sallama,
Zahra tajima sannan tayi musu sallama tatafi gida itama

Washe gari da safe, na shirya, nayiwa baby wanka, nace "to sai muje nakaiki wajan uncle ko?
Tunda ni bakya sona," nafadi haka cikin bacin fuska, baby tace " to anty kema ki zauna agidan
mana ai zai ishemu"

Banza nayi da ita, yaya tahir ne yafuto zaije wajan aiki, yace " wannan bari nakira ahmad yazo
yatafi da ita," nace
" wallahi daka hutar Dani yaya tahir"
Wayarsa yadauka yakirashi, aikuwa ahmad yace gashinan Zuwa
Tanaji ance ahmad zaizo tashige daki
Tahir bai Dade da fita ba, ahmad yashigo, husna tana falo itada yara, suka gaisa, baby ta
rungume shi, tafara qwalawa feenah kira
"Anty! Anty!! Anty!!"
Da gudu feenah ta futo, tayi zatan wani abinne yafaru da ita, tana Zuwa tayi turus, ganinta tare
da ahmad
Juyawa zatayi, husna taja yaran sukai daki tace "ki tsaya ku gaisa mana, ko baki ganshi ba?"
Tsaya wa nayi, batare dana ce masa komai ba, shima ido ya zubamin yayi kyau sosai cikin
baqin wando farar Riga, sai yar sama kalar ruwan toka, takowa yake wajena ina matsawa,
dahaka har mukaje bangon falon


** *** **

Suna wullar dashi a kofar gidan sukaja motar suka tafi

Dagudu baba yafuto daga gidansa binjimar sa sai tashi take, dakyar aka kama mukhtar da
jikinsa yayi jina jina saboda duka

Bayan komai yalafa yana kwance atsakar gida, inna tana masa firfita, baba yace "wato mukhtar
abinda nake tunani shine kawai karabu da yarinyar nan"
Dasauri mukhtar ya kalleshi




Mrs Usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

56


"Amma baba ina sonta, ina kaunar zama da ita, Dan Allah baba karka rabani da nafeesa wallahi
inasan ta, munyi alqawarin aure nida ita"

Baba da inna suka zubawa mukhtar ido suna kallanshi, wato shi duk wannan dukan da aka
masa bai isheshi ba, ahaka yake maganar kar arabasu
Baba cikin ransa yace mukhtar ba a hayyacinsa yake ba,橙提 Dan haka yace masa "Toshiknn,
bazan rabaku ba"
Mukhtar yasaki murmushi kamar babu abinda yake masa ciwo, yace "Nagode baba"


** *** **


"Yanzu de alhaji abinda yakawo ni kenan, hajiya salaha taje har gida ta roqeni Akan muzo itada
wannan yarinyar, yayi maganar yana kallan lailah
Tace muzo mutaru mu baka hakuri"

Alhaji bukar yace "alhaji musa dande sunje wajanka ne, Amma da tsakanina da wannan matar
saide alahira
Gaba daya alhaji musa ta lalatamin tarbiyar yarinya, ban isa inyi magana Akan haka ba saitace
min yarinyar datake guda daya jal awajanmu
Toni idan ta shirya zama Dani saide tatsuke bakinta Akan abinda zan yiwa yata, kar inji kar
ingani
Sannan ke lailah, daga Yau nakafa miki doka karki sake naqara ganin qafarki awaje
Bake ba fita, ki zauna agida, idan kuma bahaka ba wallahi hukuncin dazan yanke miki bazai
miki dadi ba daga ke har uwar taki, "

hajia salaha dataji jiki tace" babu abinda zai faru ma "
Ta dubi alhaji musa abokinsa tace" Mungo de alhaji "
Alhaji bukar yace"kwa iya tafiya,"
hannun laila taja suka yi ciki, laila sai kumburi take ita ala dole anyanke Mata hukuncin dabai
mataba


** *** **

Cikin tsoro da faduwar Gaba nake kallansa nace "Malam miye haka?"

Tsareta yayi da ido, kawai yana murmushi yana kallanta, kokarin kaucewa nake in gudu daki,
Dan gaskya ba qaramin kwarjini yamin ba
Ganin zan tafi ne yasa shi saka hannunsa yadafe bangon
Cikin qasa qasa da murya kamar mai rada yace "meyasa bazaki kai baby da kanki ba, saide
akirani inzo indauketa?"

Cikin takaici nace " naga yarka ce, ai dole kazo ka dauketa,"

murmushin dabai shirya ba yasaki yace "ashe kin yarda yanzu yata ce, da kuwa kika mareni
kika ce nabaki yarki,
My feenahhh
Yakirani tare da Jan sunan,
Yaci gaba da fadin" my feenah ina sanki, meyasa kika tsaneni? "
Cikin fishi nace" ahmad Dan Allah matsa na wuce"

Kallo na yayi da mamaki yace "please maimaita sunan Dan Allah"

Bansan ya akai ba kawai naji hawaye yacika idona, kafin in furta masa komai naji duminsu a
kumatuna, shikam gogan naku murmushi yake saki yana kallanta, shi kawai koda ace Zata
zageshi ne inde zai kasance tare da ita to Babu komai
Yanzu haka wani mugun dadi yakeji kasancewar sa tare shida ita
Banyi aune ba naji tafin hannunsa mai mutukar taushi Akan fuska ta, zaro idona nayi cikin
mamaki, wani qarfi naji yazomin na tureshi nayi ciki da gudu,
Shi kuwa murmushi yasaka, cikin ransa yace matsoraciya kawai,
Kujera ya zauna, yana jiran baby

Feenah kuwa tana shida daki husna taganta tana goge hawaye, Tabe baki husna tayi tace
"hakade kika iya, ai sai ki dinga yimasa kuka yaji dadin rainaki"
Kama hannun baby tayi suka fita, saida sukaje kofa baby ta juyo tace anty bye bye saikinzo
kema"橙提 ,
Dan haushi ko kulata banyi ba

Suna Zuwa falon, ya karbi baby suka tafi, tanata yiwa husna bye bye

Husna na komawa ciki, ta cewa feenah, "idan kina zama kina masa kuka ya dinga miki abinda
yagadama kenan, toma menene abin kuka,?
Abinda yafaru fa ya Riga yafaru, kawai ki manta, shima da yarinyar take wajansa ya manta ya
fuskanci abinda yake gabansa bare keda kike shirin shiga gidan wani, kawai kema ki manta da
komai, kiyi tunanin rayuwar da zaki gina nan Gaba "
Nace" to anty husna"
Janyoni tayi jikinta tace "yauwa kokefa"
Wayar husna ce tadau qara tana dubawa kuwa taga sunan kalatynmu yafuto baro baro, bayan
sun gaisa ne, kala tace a turo Mata nafeesa, yanzu yanzu, to husna tace tare da kashe wayar
Ta juyo ta dubeni tace kala tace kije yanzu, dama already a shirye nake, Dan haka kai tsaye na
miqe natafi
Ina Zuwa gidan kuwa, bayan mun gaisa, tabani wasu magunguna hadeda madara tace na
shanye
Babu bata lokaci nasha, tace to najirata Zuwa anjima, ganin haka yasa na kwanta afalo nida
sultan qanin aysha muna ta kallo,
Danaga tashiga kitchen ne naje da niyyar in karbi abinda zatayi inyi Mata, Amma fur tace bazan
yi ba

Dole sai falon na dawo nazauna, bata dauki lokaci mai tsawo ba naganta da naman kaza, taji
romo, takawomin tace gashinan incinye duka
Tunanina zanji da dinta kamar farfesun kaza, saide ina fara ci nafara yatsina fuska, kala tace
kiyi abinki kigama tas saikin cinye
Ina ci ina kawar da fuska ahaka na cinye, sannan tace tonatafi kar dare yayi tunda ni kadai ce
Karfe hudu da rabi natafi gida


** *** **

Suna zaune aharabar gidan Akan mota shida tahir
Tahir ya dubeshi yace
" man narasa dalilin wannan ziyara taka, kazo da safe kazo da yamma gida gidan
magidanci,橙提"
ahmad yace "to magidanci zageni Akan banda Mata, nima ai nakusa kwana nawane," tahir yace
"to gara de kasamu wata ka aura, komaji dadi,"

Jikin ahmad ne yayi sanyi daya tuna matar dayake mutuqar so wani Zata aura
Can ya cewa tahir "aidama ina Zuwa,"

tahir yace "a a kaide fadi gaskya man"

Suna wannan musun nashi go gidan, ina tafiya ta cikin nutsuwa, kaina aqasa nace "yaya tahir
barka da hutawa," yace
" yauwa autarmu"
Shi kuwa mutumin basarwa yayi kamar bai ganta ba, tahir ya kalleshi da mamaki yace "man, ga
feenah can fa,"

ahmad ya yatsina fuska yace "naganta ai, to menene?
Bahaushe ma yace So mai sonka"
Tahir ya girgiza kai yana kallansa cike da mamaki,
Wayar tahir aka kira yajuya suna magana shida wata nurse datake tambayarsa wasu
magunguna
Yana Gama wayar yajuyo zai nunawa ahmad wani Abu awayar, yace
" ahmad kaga abin.... Wayam yaga wajan ba ahmad ba alamarsa
Yana daga kai yaga ahmad yana bin feenah abaya,橙提 tana dauke kafa yana mayarwa

Sai abinma yabawa tahir daria, lalle ma mutumin nan nizai rainawa hankali, lalle ai zai dawo ne

Yana Zuwa wajanta yakama hand back dinta yariqe saboda ya kirata ya kirata ta share shi,
Da tayi niyyar rabuwa dashi, Amma data tuna da shawarar husna saita dake ta juyo tace
"cikamin jaka"
Ahmad yace "muje ciki"

Nace "babu inda zanje, kabani jakata"
Yace "wallahi idan baki jeba cimak zan dagaki"
Yafada yana gyara hannun rigar sa

da mamaki na kalleshi nace "wa? Ai wannan jikin yafi karfin ka wallahi, na adanashi ne ga
mukhtar"
Cikin tsawa yace
" nafeesa!!!!"
gabanane yafadi dajin wannan tsawar tashi, Amma nadake nace "to bani jakata," nafada ina
miqa masa hannu na
Yace "zan baki, Amma karki sake kikara kiramin sunan wannan mutumin a gabana"
Nace "mijinane fa
Lokacin dakai Naka auren nahakana ne?Kokuma nayima magana lokacin daka dora a
Facebook?"

Da mamaki ya kalleta kenan feenah tana bibiyarsa
Nace " kaga ahmad kana batawa kanka lokaci ba auren ka zanyi ba, koda ace babu mukhtar
babu abinda zanyi da sauran wata "
Cikin bacin rai yace
" Amma ai sauran ki ne, kuma insha Allahu saina aure ki innuna miki kece zakiso sauran watan"

Baki kasan abinda zaka fada, bakasan mai za'a maidamaba, maganar sa Gaba daya tasata Jin
kunya
Jakarta ta fizge tayi ciki
Ahmad yakama qugunsa yariqe da hannu biyu, ya furzar da iska mai zafi, afili yace "akwai aiki a
gabana" 橙提


** *** **

"Alhaji ashe kaine, haba shigo daga ciki mana ''

Baba ya kalli Abba yace" a a alhaji basai na shiga ciki ba, magana ce zamuyi guda daya
Alhaji ni inaga maganar auren yaran nan akwai matsala, saboda kwanaki yaron wajena, ansace
shi, yanzu haka maganar da nakema, jiya jiya aka kamashi akayi masa Dan iskan duka,
Yanzu haka yana kwance agida rai ahannun Allah, to shine naga idan akai aure kuma menene
zai biyo baya?
Alhaji kayi hakuri mukhtar shi kadai ne awajena, kuma bana fatan narasa dana
Dan haka maganar auren nan mude mun janye "

Gumi ne ya wanke ilahirin jikin Abba, yadubi baban mukhtar yace
" Amma alhaji duka duka auren baifi sati biyu da kwana biyar ba,"
baba yace "shiyasa natako da kaina alhaji, ban turo wani ba, kayi hakuri Alhaji kayafe mana"

Yana Gama fadar haka yayi Gaba

Abba yajuya cikin gida salalo salalo
Kamar wanda qwai yafashewa







Mrs Usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

57

Yana shiga cikin gida yanemi waje ya zauna, babbar rigar sa yake kokarin cirewa
Mama ta futo daga daki ta zauna tana cewa "wallahi alhaji wannan hidimar bikin duk taqi
qarewa, kullum ragewa ake Amma kamar babu abinda ake ragewa" 橙提

Shide Abba shiru yayi yana jinta, mama ta dubeshi tace "haba alhaji yaka naji ina magana
Amma kamar ba dakai nake ba kayi shiru"

Abba yace "wallahi maman nafeesa, al'amarin yarinyar nan yafara dauremin kai,"

cikin mamaki mama tace "wacce yarinya kenan alhaji"
Abba yace "nafeesa, wato halin da ake ciki yanzu gidan iyayen yaron nan sunce sun janye
maganar auren nan"

nan da nan mama tafara salati, tace "to alhaji kakira mahaifin yaron mana kuyi magana,"

Abba yace "ai shida kansa nema yazo yasameni da maganar"

Mama ta rafka uban tagumi tace "yanzu abinda mutanan sukai sun kyauta kenan? Saida Abu
yazo kusa anriga da ansanar da kowa
Yanzu fisabilillahi yaya sukeso muyi?"

Abba kasa magana yayi, wayarsa ya dauko yakira husna, suna gaisawa Abba yace tabawa
nafeesa wayar, ina karbar wayar Abba yace"duk abinda kike kibari kikamo hanya kitaho gida

yanzu,"

gabana ne yafadi nace
" Abba lafiya kuwa?"

Yace "babu komai kawai kiyi abinda nace" , jiki asanyaye nace "to Abba"
Husna ce ta kalleni tace "me yace?"

Nace "Abba ne yace intafi gida yanzu yanzu,"

husna tace "to Allah yasa lafiya,"

nace "amin,"

magani ne a kofi ta meqomin tace "gashi kisha wannan din saiki tafi,"

bata fuska nayi nace
" anty husna Dan Allah kidena duramin wadannan abubuwan haka,"

husna tace "yarinya bakida hankali, wannan din shine gatanki, nafisan mukhtar yakasa gane
kedin maman baby ce kokuma yayarta" 橙提

Murmushi nayi nakarba nasha
Ina Gama shanyewa na shiga toilet nayi wanka, cikin sauri na shirya, nayi sallama da ummi
sannan na dawo part din husna tarakani har gate sannan tadawo gida nikuma natafi
Ina Zuwa gida nafada jikin mama nace "mama wallahi nagaji,"

cikin sanyin jiki mama tace "ke dagani, kede kullum cikin San jiki"

, kallanta nayi nace
" mama kalau kike kuwa?"
Tace "kalau nake auta ta,"

nace "naga duk jikinki yayi sanyi"

Kafin tabani amsa nace "mama nima tun jia gabana yake ta faduwa, kawai de addu'ah nake
Allah yasa lafiya"
Mama tace "ai kin kyauta dama hakan akesan bawa," 橙提

Abba ne yashigo da alama daga masallaci yake
Saukowa nayi kasa na gaida shi, ya amsa tare da neman wajan zama, nima komawa nayi kan
kujera nazauna kusa da mama, Abba yace
" mamana dawo nan zamuyi magana"

Ina Saukowa Abba yace "nafeesa duk abinda kikaga yasami bawa toya dauka kaddararsa ce
tazo masa haka,
Kuma Allah yayi hakanne domin ya jarraba imaninsa,"

nace "hakane Abba, me yake faruwa ne?"

Abba yace "jiya ne mutanan da suka kama mukhtar kwana ki, jiyama suka kamashi sukayi
masa duka harda lahani, to...

Cikin kuka natare Abba nace" na shiga uku, shikkenan Abba sun kashe shiko?"

Abba yace" to ai baki bari na qarasa ba uwa ta, basu kashe yaron ba, kawai de sunji masa
ciwuka ne, Dan haka nema mahaifinsa yazo har gida yace sun janye maganar auren ku

Dan haka kema inaso kisawa zuciyarki salama, kidauka hakan shine mafi alkhairi "

Kuka nane ya tsananta nace" Abba wallahi ina sanshi "

Abba yace" shima yaron yana sonki, Babu yanda zasuyi ne shiyasa suka dauki wannan hanyar
tun kafin abin yakai ga rasa rayuwar sa,
Kowanne iyaye suna San yayansu nafeesa, ni kaina da akanki abin yake faruwa bazan juri
ganinki kullum cikin tashin hankali ba, saboda sude mutanan nan ba'a San kosu wayeba, idan
kashe shi sukai ma ba'a San suba
Dan haka keda mukhtar dole zakuyi hakuri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login