Showing 108001 words to 111000 words out of 113548 words

Chapter 37 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

03 Apr 2025

9396


Nace" nayima my Ahmad"

Ahankali yaturo bakinsa daidai nawa ganin abinda yake shirin yi yasa na lumshe idona

Gyaran muryar da mukaji ne yasa cikin sauri muka kalli kofa

Yaya Tahir!!! Nafadi haka cikin zuciyata, aikuwa da gudu nayi cikin gida

Ahmad kuwa Sosa qeyarsa yayi, Yakalli agogon sa qirar Gucci dake daure a tsintsiyar
hannunsa yace "ashe Har lokaci yaja haka
Bari intafi"

Tahir yace "Dan renin wayo, kazo kasamin qanwa agaba kana so kakoya Mata rashin kunya,
wannan kuwa idan mukai muku auren zamu Iya zuwa gidanku?"

Ahmad yace "besty saida safe"

Tahir yace "ai baka isa ka tankaba, oh ni Tahir qarshan duniya yazo," 🤣

Ahmad yace "Tahir ya isheka haka Dan Allah"

Tahir yace "au Har kanada bakin Magana?"

Sunkuyar da kansa yayi Yana murmushi zai fice, Tahir yace " to Sai yaushe?"

Yace "ba Rana abokina, bazan dawoba, saboda idan nacika zuwa za'a samu matsala,"
Yana fadar haka yayi wuf yafice

Tahir yace "daka tsaya ai"

yanunashi da hannu yace wannan, wannan mutumin Ina tausayawa wannan yarinyar

Ina zuwa dakin danake nafada Kan gado, na lumshe idona, afili Nace "I luv u Ahmad"
Dakin husna naje tana shirin tafiya wajan mijinta Nace mata "saida safe," tace "to Sai Allah
yakaimu," futowar dazanyi nahadu da Yaya Tahir, aikuwa kaina aqasa nawuceshi, ban yarda
munhada idoba, shine de Yace "amarya saida safe," nikam babu bakin Magana

Har bacci yafara daukana naji qaran wayata, Ina dubawa Naga number Ahmad, cikin muryar
bacci nadauka Yace "natasheki kina bacci kiyi hakuri," Nace "babu komai"

"Dama Kira nayi ince Miki I luv u kafin nakwanta," 🤣

Nace "to ngd"
Yace "me kikace? Ai baki isaba saikin fadamin Nima"
Cikin muryar shagwaba Nace "Kai Yaya Dan Allah, kanasani Jin kunya fa, gashi Nan Kasa Sai
kunyar Yaya Tahir nakeji,"

Ina jiyo murmushin sa Yace "tokiyi hakuri, shikuma Tahir Ai nayi masa Magana babu abinda
zaice Miki kinji?
Amma kiyi hakuri bazan sakeba"

Nace "toshikkenan, saida safe," Yace "um um nide Sai kin fadamin"

Ahankali Nace " I luv u too"
Dif nakashe wayar

** *** **

Gyara sosai nakesha, Ciki da waje, banda magunguna danake amfani dasu, na tsugunno
daban na wanka daban, fatata tasauya duka, naqara fari, nayi kyau sosai, jikina banda laushi
da tashin qamshi babu abinda yake, gashin Kaina kansa qamshin dayake na dabanne, babu
abinda zance da husna Saide Allah yabiyata,
biki yarage saura Kwana hudu muka taho nida husna da Zahra, Amma su anty za maimuna su
Kala su kaka sundade Azaria

** *** **
Rana Bata qarya

Ayaune dubban jama'ah suka shaida daurin auren Ahmad muhd marzuq Tare da nafeesa mu'az
Akan sadaki nera dubu tamanin lakadan ba ajalan ba, Wanda manya manyan Yan siyasa suka
halarta, cikinsu harda gwamnonin wasu jihohin

bakin Ahmad Kamar gonar auduga, yayinda suka hade cikin farar shadda, tareda babbar Riga,
agogo fari qirar Rolex, farar hula me sirkin ash, sunyi mugu mugun kyau irin na qarshe din Nan

Kawai pictures suke tayi shida abokansa, banda masu video dasuke nasu, cikin su harda Yan
gidan TV, domin sunaso su haska bikin akafafen Yada labarai

Mrs usman ce🖊
[5/4, 6:08 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

Second to the last page


64


Abba gaba daya Yama rasa inda zaisa baqi wasu daga kusa wasu daga nesa
Tahir Yana fama danasa jama'ar Ahmad haka
Ana gama daurin aure, jama'ah suka fara raguwa
Kansa ne yafara sarawa saboda hayaniyar datayi yawa
Nan da Nan yace "muhd yakamata mudau hanya kokuwa?
Ina su wadannan yaran suke?"
Marzuq ne ke wannan maganar, tsoho Mai ran karfe
Daddy yace "to abbey, Bari akirasu"
Awannan lokcin suna cikin gidan tareda abokansu, suna gaida mama da danginta, duk inda
sukayi Sai an kallesu, saide idan Kun gaisa ne, zakaji Ana cewa Ina angonne, shikuwa banda
waige babu abinda yake Wai kozai danga matar tasa
Suna futowa daddy yahango Tahir

Dan haka yayi masa Magana Akan yakamata su tafi Tahir yace "daddy Bari inkirashi"
Wajan Ahmad yatafi Wanda yatsaya ake tayi musu pictures shida mutane, babbar Riga Sai
tashi Sama take,🤣 Tahir yace " Kai to wallahi mutafi, daddy da wancan tsohon suna jira"
Ahmad yace" yaza'ai natafi Tahir Bayan banga matata ba "
Tahir yace" yau munga ta kanmu, daga daura auren,?" Yace" Tahir bafa zan tafi ba saina ganta"

Nikuwa Ina zaune tareda qawayena dasu aysha, Zahra, dawasu daga cikin Yan unguwa,
wayata ce tadau qara, Ina dubawa Naga Ahmad ne, Kai tsaye Ina picking cewa yayi zasu tafi
infuto mu gaisa
Aikuwa nazaro mayafina nafuto, Ina zuwa kofa muka hadu da husna tace "Ina zakije," nayi Mata
bayani, tace babu inda zakije, kikirashi kifada masa yayi hakuri

Nikuwa ba musu najuya, "feenah "
Takira sunana, Ina juyawa tayimin nuni da dakin Abba tace kije can dakin kikirashi
Saida taga nashige dakin sannan tatafi cikin ranta tana fadin badai mutanan su Tahir bane,

tasan Sarai ba hakuri,🤣 musanman ma Ahmad yanda yake wannan rawar kafar
Nikuwa Ina kiranshi yafara fadin, "kina dede Ina?" 🤣

Nace "Yaya anty husna tace bazan zoba, kayi hakuri Yaya tunda ai anjima zamu hadu ko"

, 🤦🏻â€â™‚dafe kansa yayi da hannunsa yace " my feenah yanzu kowama haka yake ganina ko?"
Nace "kamarya?"

"To my feenah gashinan Bana Iya boye soyaiyar danake Miki agaban mutane, ai duk laifinki ne
kekika maidani haka"

Nace "Yaya kabani Daria" , yace "tobani abata"

"Yaushe zaku tafi?"

"Yanzu zamu tafi tunda anhanani ganinki" , Tahir yaduba yace " muje Tahir"

Tacikin wayar naji Yana masa Magana, Nace "Wai tare kuke,"

Yace "emana, menene?" Nace "kaiiii"
tare da zare Ido, dif nakashe wayar
Wayar ya kallah Yana murmushi yace "su Tahir manya Wai Kai akejin kunya"
Tahir yace "to menene kana mamaki?"
Yace "no bawani mamaki kawai de Naga kunyar marar kunya ai bata lokaci ne" 🤣

"Kacika baki dayawa yaro"
Inji Tahir
Ahmad yace "yaro Kuma? Yaro de? Yanzu nine yaro? Zakayi mamaki na"

Tahir yace "kamarya?" Shima Ahmad din yace " a a abar zancen"

"Ina kuka tsayane tun dazu ku ake jira,"

"kayi hakuri daddy" inji Ahmad
Mota suka shiga inda su daddy suka sake yin sallama da Abba dasu ammu sannan suka tafi

Mukuwa muka ci gaba da hidimar biki, photuna de anyi su selfie kuwa ba'a Magana
Inyi wannan shiga incire asake wannan, ko Ina zani Ina tare da Zahra
Anyi kidan qwarya, inda su Kala suka taka tasu rawar

Da magrib aka fara shirin kaini kano, kuka de Kam nashashi dakyar aka rabani da jikin mama
Shikansa Abba saida yayi qwallah
Ammu ne yadaukemu

Har mukaje kano
Gidansu Ahmad mukaje nide kaina Yana qasa, dazamu shiga yace inshiga da Bismillah haka
kuwa a kayi

Saida ammu yakaini Har dakina Wanda yaji furnitures na gasken gaske, sannan yaqaramin
fada Shima yatafi

Ina hawaye husna dasu aysha da Zahra ne suketa ban baki
Kala ce tareda wasu Mata tace nataso muje part din su hajia
Aikuwa haka akayi
Muna zuwa su momy suka karbemu hannu biyu, mamy hakima kuwa janyoni tayi jikinta, Sai
Nan Nan take Dani
Saudat kuwa takama hannu na tariqe, su kalatynmu suna ganin wannan tarbar da aka mana,
sukace tosu zasu tafi, saikuma gobe idan sunzo dinner insha Allah
Dahaka suka tafi gaba dayansu, Ina riqo Zahra tana fizgewa

Dagani saisu momy saikuma baqi Wanda sukazo bikin dasuke ta tururuwar zuwa wajena
Dansu ganni
Mamy hakima tace "hajia inaga wannan suje daki ko, Kota samu tahuta"

Momy tace "eh Hakanma yayi," tadubi Saudat tace
" sauda kuje daki tayi wanka taci abinci saita kwanta tahuta"
Saudat tace" to momy "
Kaina aqasa muka tafi, Wai nice a cikin Gidansu Ahmad, amatsayin matarsa, babu nacin da
saudat batamin ba, Akan nazo tun muna diploma naqi zuwa, Amma yanzu gashi nazo
amatsayin surukarsu

Husna nafita harabar gidan takira Tahir tace
" sweety kazo kadaukeni," alokcin suna tare da Ahmad Yana masa naci su tashi su rakashi
wajan matarsa

Tahir yaceda husna "wai harkun gama ne?"

"Eh mungama"

"Amma kina ganin babu damuwa kubarta ita kadai?"
"No ba ita kadai bace, tana wajansu momy," Tahir Yace" eh hakanma yayi, gani nan zuwa "

Yadubi Ahmad Yace" to ango muje nakaika gida, Nima zan dauko maman twins"
Ahmad Yace " yauwa dama namatsu naje wajan matata," Tahir Yace "tome mata, ai tana
wajansu momy, saide kabita can,"
Ahmad Yace "kamarya bangane ba? Menene amfanin namu part din?"
Tahir Yace " to saide Nakai ka katambayi su momyn" 🤣

"Dan Allah Tahir Kadena batamin Raina, haba Dame zanji, danaka ko danasu"
Kafadarsa yadafa Yace
" man kayi hakuri
Matarka cefa, nasan cewa koma menene yafaru yanzu tana matsayin matarka ne, kawai idan
munje kaje kadauketa saiku koma part dinku ai shikkenan"
Ajiyar zuciya yasauke Yace "shikkenan"

Suna zuwa gidan Tahir yarakashi ciki, daganan yadauki Husna, shikuma yayi part dinsa
Yana zuwa kuwa yanda yazata din hakane, Bata nan, Amma da alamun anshigo part din, koma
menene zaije wajansu momyn ai yanzu
Kan gadon yadafa yarufe idonsa, daga bisani yatashi yashige toilet domin watsa ruwa

Saudat tace "sister gaskya wannan kunyar ta isa haka, kunaso Kuna wani noqewa," mayafin
kaina nayaye nace
" jarababbiya, Ina ruwanki,"
kaina tafado tace "sister amarya,"

"wash Saudat Zaki karyawa mijina ni"
Tace "lalle amarya, yaude gaki a gidan nan, sister Kinga yanda kika koma kuwa? Wallahi kin
qara kyau," nace "kema haka ai, kin girma"


"Eh lalle ma feenah nice nagirma ko ''
Nace" Ina farouq," tace
" Yana nan wallahi, ai zaku gaisa kafin mutafi "

Wanka nashiga, nashirya cikin kayan bacci nakwanta, nan da nan bacci yayi awon gaba Dani
, Saudat taja bargo tarufeni, sannan itama tafice

Wajan 11:30 yashigo part din, duk baqi sun kwanta, kasancewar sanyin da akeyi
Momy yagani afalo tana bawa ma'aikata umarni, domin su gyara gidan sosai kafin safiya

Da mamaki ta kalleshi tace "bakayi bacci bane dama?" Kansa ya Sosa Yace cam momy dama
inajin yunwa ne, ko Zaki sa akawomin abinci? "
Tace" OK,"
Mai aiki ta qwalawa Kira, Yace"a a Barta momy kawai Bari in kwanta," tace "kace yunwa kakeji
ka tsaya mana takawoma abincin," 🤣

Yace "to momy Ina Saudat, ko yaran gidan, kokuma...."
Tace "kokuma me? Kaga walady banasan shirme, wuce kaje ka kwanta dare yayi"

cikin shagwaba

Yace "momy Ina nafeesa?"
Kai tsaye tace "tajima da bacci, tace afadama saida safe" 🤣

Babu yanda ya Iya, haka yajuya Yana shafa qeyarsa, Yana waiwayen falon yayi part dinsa
Cikin bacin rai yake fadin mutum da matarsa Amma ahanashi ganinta, wannan wacce irin
rayuwa ce
Yana tafiya Yana mita dahaka yaqarasa part dinsa, a wannan dare dakyar bacci barawo yasace
Ahmad


** *** **

Yana zaune adakinsa yaharde Yana kallon tashar arewa 24 Kamar wasa yaga photon ta
Tuni yatashi zaune, abin Bai qara daure masa Kai ba saida yaganta tare da mijinta Ahmad
muhd marzuq
Mekenan? Meyake shirin faruwa ne? Yaushe haka tafaru? Feenah ta auri Dan gidan Dan
siyasa, Kenan dana Rabata da mukhtar masu qasar ta aura
Ato masu qasar mana Dan gidan deputy governor, gobe Kuma ai Dan gidan governor ne, gashi
Yaron yaji Ana shi Kansa Mai kudi ne, Bayan babansa, ga kakansa dayake ji dashi

Lalle kuwa Idan hakane ya zalunci mukhtar, gashi yanzu yarabashi da feenah, shi yahanashi
aurenta, Shima Kuma Bai same taba
Gashin Kansa ya hargitsa, ya ilahi, yayi zatan tunda yarabata da mukhtar dole zata hakura idan
yakoma wajanta ta saurareshi, ashe shi cutarsu yayi gaba daya
Lalle dole yanemi yafiyar mukhtar


** *** **

Washe Gari
Ina tashi Wanka nayi, Ina futowa Naga Mai kwalliya tana jirana, zama nayi aka tsaramin
kwalliya tagani tafada, sosai nayi kyau acikin material Mai shegen kyau launin ash color
Mamy hakima ce dakanta tazo tatafi Dani wani falo, tsararre, daddy da momy da marzuq suna
zaune kaina aqasa nagaida su, kowa Sai Jana yake da fira, nide cikin kunya nake amsa musu
maganarsu

Marzuq Yace "Toya kwanan baqunta" nace
" alhmdlh,"
Yace "kinajin dadi ai babu wata damuwa ko?" Nace "babu komai wallahi"

"Amma baki ganeniba?" Nace "ehh,"
"to nine marzuq" 🤣

Kallansa nayi da mamaki yanda naji hausa radau abakinsa, murmushi nasaki batare danace
komai ba
Yace " to alhmdlh, Zaki tashi kuje unguwa yanzu zaku dawo"
Babu musu natashi muka tafi, bamu zame ko inaba Sai wajan passport muna tsaye yafuto aka
bamu, wajan visa aka wuce Dani dayake Abu ne nakudi Yace zuwa anjima za'a kawo Har gida

Yayi mamakin lokcin daya dauka Yana bacci, ahanzarce yashirya yafuto yayi kyau cikin manyan
Kaya
Sai sauri yake yazo yaga feenah, Yana futowa directly Dakin daddy yayi domin su gaisa, Yana
zuwa kuwa yagansu gaba dayansu, suna gaisawa yakoma wajan marzuq
Daddy Yace "my son abeey yasa akai nafeesa wajan passport, yanaso gobe kushirya ku tafi
sharil'asal (honeymoon)"

"To daddy itadawa suka tafi,* daddy Yace" itada Saudat da driver "
Cikin ransa Yace" driver"

Wato dawani qato aka hada amaryarsa suka fita, Bayan shi jiya babu yanda baiyi ba aka
hanashi ganinta

Baiyi musu maganaba, Har suka qari firarsu suka gama

Da yamma aka shirya kowa yafara haramar tafiya wajan dinner
Nayi kyau sosai cikin yadi Mai tsada launin pink
Nasha kwalliya sosai nayi kyau, Ina Bayan Mota Ina jiran Ahmad yafuto, Yana shigowa driver
yaja motor muka tafi, Har mukai Nisa baicemin komai ba, nice nayi qarfin halin cewa
" Yaya Ina yini?"
"lafiya"
Shine kawai abinda Yace
Cikin Raina nace tooo yau abin yazo
Ban daddara ba nasa hannu na naruqo nasa, shiru Yamin Yana Jina,
Taushin hannun ta neyake ingizashi Akan yadan murza hannun
Amma haka ya dake, yaqi kulata
😀
Har sukaje wajan dinner, Prince and Princess dake rijiyar zaki
Sosai an qawata wajan
Duk abinda kake buqata da kanka zakaje kazuba sosai abin ya qayatar da mutant sosai
Washe Gari akayi wata dinner a country mall, Iya qawayan amarya dana ango, daganan Kuma
jama'ah suka fara watsewa


** *** **

"Mukhtar kaji de abinda nayima, Amma naroqeka kayafemin," aqasa ya zuba gwiwoyinsa Yace"

kayafemin mukhtar badan halinaba, saidan Allah "
" Kb hakika kacutar Dani, Amma babu komai nayafema, koba komai nasan kayi DANA SANI
Akan abinda ka aikata, Amma hakika baka kyau tamin ba, babu komai, komai yawuce"
yasa hannu ya tashi Kb yarungumeshi
Shima Kb rungume mukhtar din yayi Yana kuka
, Kb Yace "mukhtar Dan Allah na roqeka Kasa feenah tayafemin itama," mukhtar Yace "karka
damu insha Allah zanyi mata Bayani "


** *** **

"To daddy insha Allah zanyi mata Bayani," Yace "yauwa gobe Shima abeey zai wuce, saiku tafi
tare, Bayan Kaga likita yadoraka Akan maganin saikuje ko dubai ne kusha iska, daga nan kuje
kuyi umara kayi addu'ah sosai Akan Allah yabaka lafiya
Amma idan kun tashi dawowa kufara biyawa ta masar idan kunyi sallama dasu saiku taho gida
ko
Sannan munyi Magana da Saudat tace tanasan tafiya Da baby tayi mata hutu, na Bata damar
daukar ta "

Ahmad Yace" to daddy hakanma yayi nagoge "
Daddy Yace" zaka Iya tafiya "


** *** **

Nagama komai nayi Wanka nashafa humra, da turare iri iri
Nasa kayan bacci na Mai kyau black color
Kasancewar da farina saiyayi min kyau sosai

Hijabi na nake nema zansa naji anturo kofar Dakin, kallan kofar nayi, Ahmad ne, ido yazubamin
yakasa dauke idonsa akaina
Hakan yasa nasan ya hijab dina
Dakin yaqaraso nace "sannu dazuwa"
Ataqaice Yace "yauwa"

Dakin yayi shiru daga baya Yace "me yasa jiya kikabi driver kuka fita"

Dasauri na kalleshi nace "ai daddy ne..." Katseni yayi Yace " saboda sune suke iko dake ko?
Ace matata ahadata dawani qato amota"

Kafin nabashi amsa Yace
" yayi kyau"
Kishirya mana kayanmu gobe zamu wuce masar insha Allah

Nace "to"
Tashi yayi zai fita yaji wayata tana ringing, dubawa yayi
Sunan daya ganine yabashi mamaki
Afili yafurta

"mukhtar "
Ga wayarki Ana kiranki
Yayi wulli da ita Kan gado yafita yabar Dakin😀

Zama nayi aqasa jagab Kamar yar bori nace "nikam yau Naga ta kaina, meyasa mukhtar zai
kirani"

Awannan dare masoyan basu rintsa ba kowa da abinda yake saqawa aransa

Washe Gari kuwa sukai sallama da kowa, suka Lula qasar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login