Showing 96001 words to 99000 words out of 113548 words

Chapter 33 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

03 Apr 2025

9321


Tashi kitafi "

Daki na shige da gudu ina kuka,
Wayata ce tafara kuka, ina dubawa naga husna ce, cikin kuka nayi Mata bayanin komai, husna
tasaki salati tace" yanzu yaya zamuyi da mutanan da muka gaiyata?" Nace

" kede bari sister nide inaga banda sa'ah a abangaren maza "

Husna cikin sanyin jiki tace
"Dan bakisan burin danaci Akan wannan auren bane,"
Bamu Gama magana ba takashe wayar, saboda batasan wanne kalma Zatayi amfani da itaba
wajan rarrashin yar'uwar tata, wannan yarinya tana ganin rayuwa 踫葉橙

Nikuwa ina daga kwance naturawa saudat da Zahra text Akan cewa anfasa bikina da mukhtar,
aikuwa ko minti biyu ba'ayi ba, saudat takirani, tace "me nakeji haka feenah babu dadin ji?"

Nace "wallahi sister abinda yafaru kenan"

tace "Tome yasa?"

Nan nabata labarin komai, tace "wallahi infada miki, dazu fa nake fadawa farouq yadaure
yabarni inzo bikin ki, harfa su Momy nafadawa ina nan tafe,"

nace "wallahi kiyi zaman ki anfasa saudat,"
Cikin jimami tace "to kiyi hakuri feenah, Allah yasa hakane yafi alkhaairi"

nace "amin, kinga Zahra ma tana kirana bari in daga,"

nan mukai sallama da ita, ina amsa wayar Zahra tace "sister kiyi hakuri, Allah yasa hakane yafi
alkhairi"

nace "amin Zahra,"

tace "kinyi magana da mukhtar dinne?"

Nace "ban kira shi ba," tace "toki kirashi kiji, halin dayake ciki,"

nace

" to Zahra sai anjima "

** *** **

"Oga angama komai, nasa yara sungama abinda ka umarceni,"

murmushi yasaki yace "gaskya ne, haka nakeso, zakaji alert din sauran kudinka,"

"to Oga muna jiranka," sake duban yaron yayi yace "kofisto, yanzu yaya suke ciki itada yaron,"

kofisto yace "ai Oga ayanda mukai bincike ma maganar auren tafasaya, Iyayansa sun janye"

Murmushi kb yasaki yace "zaka iya tafiya kofisto,"

Kofi yana tafiya afili yace
" mukhtar kenan, kaida kana tunanin idan bansamu feenah ba kaima zaka sameta ne? Ai bana
neman Abu narasa, idan narasa kuwa dole shima wanda yasamu yarasa, kekuma feenah kinyi
biyu Babu, Babu nidin babu mukhtar din, Babu Dan Malam babu Dan gidan Dan siyasa, kinga
yanzu saiki auri Dan gidan Dan kasuwa,橙提"
yana qarasa fadar haka, ya bushe da daria

** *** **

After 2 days

Karfe sha biyun dare tana dakinta tana waya da mukhtar, tace
" Mukhtar meyasa ka kashe wayarka, tun shekaran jiya nake faman nemanka," mukhtar da
idanunsa yayi jajir yace "feenah tah kiyi hakuri, bansan kalmar dazanyi amfani da itaba wajan
neman yafiyarki, Amma inaso kimin adalci ke kanki kinsan cewa ina kaunar ki feenah tah,
wallahi ki yarda Dani bansan baba zaizo gidanku Akan wannan mgnr ba, dana hanashi, saboda
da farko yacemin inhakura, nace bazan iyaba, saiya nunamin maganar ta wuce, ashe shi bai
hakura ba, feenah tah ina son ki, zan iya jure komai komin wahalarsa inde akanki ne, ki yarda
Dani, "

Ajiyar zuciya nasauke nace"nayarda dakai mukhtar, kuma kokadan bakayimin komai ba,"

yace "Nagode feenah"

Nace "yanzu shikkenan mun rabu mukhtar? Duk soyaiyar damuka Dade muna ginawa taqare
kenan? Wallahi mukhtar bazan yafewa duk mutumin dayamin katanga dakai ba,"

yace "kiyi hakuri feenah tah, dole zamu rabu, tunda iyayen mu sun Riga dasun tsaida magana"

,nan yafara kuka shima kamar ba namiji ba yaci gaba cewa "Amma inaso kisa aranki, nimai
kaunar kine har gobe feenah," yana Gama fadar haka yakashe wayar
wani kuka ne yazomin mai ciwo, bansan haka zafin rabuwa yake da masoyi kai tsaye ba sai
Yau, hakika mukhtar yamin komai, yasoni alokacin dayaji ni wacece, yatemakeni alokacin dana
rasa waye zai temakeni, tabbas mukhtar yacika masoyina, bansan ina kaunar saba sai Yau,
haqiqa nayi DANA SANI Karo na biyu Akan soyaiya, kuma bazan yi na uku ba insha Allah

** *** **

Yana kishingide Akan kujerar office dinsa, sai juyi yake yana aikin rarrashin matar tasa, dataqi
sakin jikinta tadawo normal kamar da, duk saboda abinda yafaru d yar'uwar ta, gaskya zai jima
baiga yan'uwa wadanda suke kaunar junan su ba kamar husna da feenah

Yace "kiyi hakuri kinji baby nah, nasan itama autar yanzu ta kwantar da hankalin ta ai"

husna tace "Amma doctor naci buri dayawa Akan wannan auren nata, meyasa Iyayansa zasuyi
mana haka?"
Tahir yace "shine abinda nake so kigane, haka kaddararta tazo,

Dole hakuri zamuyi dukanmu"

Turo kofar office din yayi ahankli yashigo, yayi kyau cikin qananan kaya, baqar Riga, baqin
wando, yadora rigar yar sama fara, hula fara, sai farin kombos, yayi masifar kyau Sosai
Waje yanema ya zauna, yana jiran tahir yagama wayar,
Shikuwa tahir sai qara kashe murya yake da niyya yana fadin "to baby tunda bazaki hakura ba,
kawai zanzo gidan yanzu na lallashi babyna" 橙提

Tsaki yasaki yana daga gefe yace " Malam kaji Dani Dan Allah"

Tahir ya mannawa matarsa kiss ta wayar tare dayi Mata sallama
ya kalli ahmad yace

" kaga saurayi mijin yanmata, wannan wankanfa? Da alama sai zaria"
Ahmad yace " tahir banasan wasa naga alama kai kuma wasa kakeji, ni nasan ba kyau neman
aure Akan aure, haramun ne ko a muslinci, Dan haka bazan yi ba, Amma inaso kasani inda ace
hakan yanada kyau da tuni na qwace feenah ahannun wannan yaron"

Tahir yasaki murmushi yace "ah ah, kaga na feenah
To ai yanzu ma lokaci bai quremaba,"

cikin mamaki ahmad yace "me kake nufi tahir?"
Cikin jimami tahir yace
" wallahi iyayen mukhtar sunce sun janye maganar auren nan, saboda matsalar nan de ta
kwanaki itace tasake faruwa
Kaima kuma....."

Kafin tahir yagama magana, yaji ahmad yakai masa wani wawan rungume cikin ihun murna
yace
" yes! yes!! "

Saikuma yasaki tahir ya tsugunna yayi sujud shukr, yana"Allah Nagode ma, alhmdlh gobe gobe
azaria zan wuni" 橙提

Tahir daya zama Dan kallo yace "ahmad wannan auran bazai iyuba, bazan baka qanwata ba
kaje ka kashe ta, Dan yanda kake wannan rawar kan naga alama ba sauqi" 橙提

Ahmad yace "yaya tahir, yaya tahir nawa"

Cikin murmushi tahir yace " bawani yaya tahir"

Wayarsa ya dauko daga aljihun sa, yana ta faman sakin murmushi

Wajan massage yashiga, nan yafara tura Mata da saqo

"ina miki jaje "

Abinda yafara tura Mata kenan

Saiya sake tura Mata

" ina tayaki murnar dawowar tsohon boyfriend dinki kuma baban yarki gareki "





Mrs Usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

58


(afwan afwan afwan fan's, 踫潤蕃踫banda bakin magana saide in rufe ido saboda kunyarku, Amma
ina muku albishir da insha Allah zaku dinga jina kullum kamar da insha Allah, ni kaina inaso
nagama nahuta, ga fire na siyan baki潤撕潤撕�)


** *** **

Ina zaune afalo ni kadai, abin duniya yataru yamin yawa, kamar wata yar tsana Asa ranar bikina
afasa, Kodan kowanne bawa ai baya wuce qaddararsa, dole indauki qaddara ta mai kyau ko
akasin haka, qaran text naji yashigo min wayata, ina dubawa naga new Num. Tattara hankali na
nayi waje daya, na Bude text din "ina miki jaje "
Abinda nagani kenan, qaran wani text din nasake ji, bayan na karanta na duba number, number
da bazan taba mantawa da itaba arayuwata
Fita nayi daga wajan massage din, ina sakin wani matsiyacin tsaki
Mama data futo daga falo ta kalleni, tasake kallona, ta girgiza kai gamida fadin Allah yabaki
lafiya, 橙提inba haka ba mutum yayi ta tsaki shi kadai
Kallanta nayi cikin raina nace mama kenan bazaki ganeba
Nima daki nakoma nazauna agefen gado, naci Gaba da tagumi abina, ni abinda yafi damunama

yanda nake Jin jikina wani iri, saboda magungunan dasu husna sukai ta dirkamin kamar ba
gobe, Gaba daya jina nake cikin wani irin yanayi, Babu abinda nake buqata idan ba mijinaba,
gashi kuma al'amari ya banje �
Oh ya Allah gani gareka kayimin zabi na alkhairi ya ilahi!


** *** **

"Man yanaga Kanata murmushi kana typing ne?"

"Nida matata ne," inji ahmad kenan
Tahir yace "ok au wai tsohuwar matarka laila?"

Ahmad yayi masa kallan tara saura kwata, yace
" inada wata Mata ne data wuce nafeesa?"

Tahir yace "au Yau kuma Babu feenah, sai nafeesa kai tsaye?"
Ahmad yace "a a wai Dan kafi ganewa shiyasa nafadama sunanta na gaskya,
Nafada Mata ne, ta shirya karbar sabon ango, tunda wancan ya kasa"

Tahir yace "ahmad, wallahi de ka kiyaye dakyau, Dan kaima idan aka saceka, Babu ruwanmu"
Ahmad yasaki murmushi yace "sata! Saikace a film, kai nifa yanda nakejina yanzu, gani nake
kawai kamar ma andaura, Dan wallahi ina Santa tahir, ina kaunar feenah, shekara da shekaru
tamin nisa yanzu tadawo gareni, to saboda me zanyi sanya?"

Tahir yace "hakane, gaskya kunyi kokari dukanku,"

ahmad yace "kamarya dukanmu?"

Tahir yace "kasan abinda yafi bani mamaki Dan gane da yarinyar nan, ace namiji boyfriend
dinka yayima haka, Amma saboda tsabar soyaiyar datake ma takasa fadawa iyayen ta, kaine
kayi Mata laifi, ai kaima kasan ba duk matane zasuyi wannan jajircewar ba, soyaiyar ma dayaya
akeyi, "
ahmad yace" to ai tahir ni feenance yanda take iya tsaya wa ta kalli idona tafadamin magana sai
al'amarin nata ya dinga bani tsoro kamar tafi kowa tsana ta wallahi tahir "
Tahir hararar wasa yayi masa yace" to saika tsaya ai ta renaka," ahmad yace
" Allah mutumina,"

tahir yace" to tsaya wasa"

** *** **

Abin duniya ya yiwa laila yawa, kullum tana gida, bata Zuwa ko'ina, bata isa takai qarar dad
dinta wajan hajia salaha ba, sai tace tayi hakuri, to hakuri har yaushe zai qare, daganan bata
wuce ko'ina ba, kai tsaye sai wajan mahaifinta, inda ta bashi hakuri, Akan abubuwan dasuka
faru, takuma nuna tayi DANA SANI Dan haka nan da nan alhaji bukhar yahadata da wani
abokinsa, Dan Garin misau, alhaji Bala, yanada Mata biyu, laila Zata je ata uku, a hakanma
shine yaga zai iya, yace yaji yagani zai aure ta, saboda shi mutum ne maisan haihuwa ita kuma
Babu halin hakan
Allah yakaremu duniya da lahira yarabamu da sharrin zuciya


** *** **

Next day
Tana zaune awani wajan shan iska, ita kadai, tana tunanin rayuwar ta, oh yanzu shekarunta sai
qara Gaba suke Amma Babu wani mashin shini
Sallamar da akayi ne yakatse Mata tunanin data Lula, daga kanta tayi tare da amsa masa
sallama, babban mutum ne kamili, aqalla shekarun sa zasu kai hamsin da wani abu, yace
"sannu fa yanmata," tace "yauwa fa"
Yace "tun dazu nake ta kallanki kina zaune ke kadai, idan Babu damuwa maizai hana inrage
miki tunani," murmushi tasaki tace "babu damuwa bissmilla," tafadi hakan tare da nuna masa
wajan zama, zama yayi tare da daukan lemon dake gabanta ya tsiyaya a cup yasha, yadubeta
yace " kiyi hakuri fa nasha miki kayanki batare dana nemi izni ba," murmushi tasaki akaro na biyu,
tace
" karka damu Babu komai "
Yace "ok, thank you, ni sunana honorable sani Abdul qadir, ni mutumin kano ne, Amma nafi
zama a Abuja, inada Mata daya da yarana hudu, yanzu haka nazo nan wajan ne Akan wani
taronmu na siyasa

Maganar gaskya tunda na dora idona akanki naji kinyimin idan bazaki damu ba, zan so ki
kasance Mata agareni, idan har banyi miki tsufa ba "

Cikin ranta tace" to wanne tsufa ma, nima dana Dade agidanmu ai gara ma amince tun kafin
nima na tsufan, Allah sarki rayuwa, ni iklima naga ta kaina, inda ace tun farko na amincewa
tahir da tuni na auri yaro kusan sa'a nah, Amma nabi Rudin duniya ninan sai governor, gashi
yanzu zan bige a honorable Nan take tayi DANA SANI yafi cikin carbi, batare da bata lokaci ba ta amince masa


** *** **

Yayi kyau Sosai cikin manyan kaya, yadi ne Dan uban su mai tsadar gaske, kalar golden, sai
zuba qamshi yake

Cikin sauri sauri yake saukowa qasa, yana Zuwa falo yaga sauran yan gidan suna break,
agurguje yaqarasa suka gaisa
Mamy tace "yauwa my son qaraso ga break dinka nan yana jiranka Yau harda mutumin Naka
akai kunun gyada"

Yatsina fuska yayi, gamida dafe cikinsa yace "mamy wallahi inaso Amma kuma ina sauri ne"
, Momy ce ta dago babu alamar wasa tace " kai zauna!"
Babu musu ya zauna yana shafa qeyarsa, shikam yanzu Momy bata sansa, tun Akan abinda
yafaru shida feenah
Amma aishima bayin kansa bane ko
Kofi daya yasha agurguje, bukhari yace

" yaya zaka qone fa idan kana sha da zafi,"
ko kula shi baiyi ba, yakafa kai babu wani yanga yashanye Gaba daya 踫

Tissue yaja yagoge bakinsa ya miqe yace

" Momy, mamy, naje zaria saina dawo"

Baby tace "uncle nima zani please"
Kallanta yayi yace "next time zanje dake kinji, Amma banda yanzu,"
Yaci gaba da tafiya

Mamy hakima tayi karaf tace, "zaria kuma? To Allah yasa de lafiya Dan naga Kanata sauri"

Kafin yabata amsa Momy tace "ina kuwa lafiya hajia zaije ya kashewa yar mutane de aure
yadawo" 橙提

Cikin sauri yakai kallansa gareta
Baice komai ba ya girgiza kai yafice cikin sauri
(nikuwa cikin raina nace ina ruwan kanku akeji �)

Bai Dade da tafiyaba saudat takira su Momy suna gaisawa, kowa saida aka bashi suka gaisa,
baby kuwa saida aka qwace wayar,橙提 saboda surutun nata bana qare bane

Zasu yi sallama ne, Momy tace "ya maganar zuwan naki? Zakizo bikin ne da wuri kokuma sai
abin ya matso?"

Ajiyar zuciya saudat tayi, tace "hmm wanne biki Momy da anfasa"
Momy tace "bangane ba, kamar yaya?"
Saudat tace "wallahi munyi waya da ita rannan tacemin anfasa bikin nata, daga bangaren
angonne aka samu matsala,"
nan de ta basu labarin komai

Momy tasa salati tare da kashe waya

Ta dubi mamy hakima tace "hajia ashe shiyasa danki yake ta rawar kafa zashi zaria" 橙提

Mamy tace "me yake faruwa hajia?"
Momy tace "ashe wai kinji anfasa bikin yarinyar nan ne, shine dagajin labari yadebi kafa yatafi,
banda rashin hankali irin na ahmad daga faruwar Abu yadiba kaje musu gida salon suce dama
murna kake da hakan?" 橙提


Guda mamy hakima tasaka tace "alhmdlh
A a hajia banga laifinsa ba, gara yaje tun kafin wani Yarigashi"
Murmushi kawai Momy tayi
Dan ita kanta tana yiwa danta fatan samun feenah


** *** **

Yana faka motarsa a kofar gidan, yashiga ciki, batare da tunanin komai ba, saide idan yatunada
abinda yafaru abaya sai yaga da wanne ido zai kalli wadannan bayin Allah
Kawai shahada yayi yashiga
Mama tana tsakar gida tanashan hantsi
Sallama yayi, ta amsa masa da mamaki, tace
" a a ahmad ashe kaine atafe"

Kansa aqasa bai yarda sun hada idoba yace " eh wlh mama, dama zan wuce ne nace bari in
qaraso mu gaisa daku tukunna" �

Mama tace "ahhh aikam ka kyauta, ya wajansu hajia da izdihar din,"

ahmad yace "sunanan kalau, daddy ma yace a gaishe ku, Yama bani saqo yace akawo muku"

Bai jima da rufe bakinsa ba, samarin dayace su taimaka su shigo masa da kaya suka fara
shigowa dasu doya ne, taliya, macaroni, jarkokin mai, su indomie,yasan idan yace shine yasiyo
fada Zata masa

Mama tacika da mamaki, shida yace Akan hanya yake me kuma yahadashi da kaya?橙提 Tasan
sarai aikinsa ne
Dan haka tace "kaide kullum baka gajia ahmad"

Shiru yayi tare da Sosa qeyarsa

Abba ne yafuto daga falo yaci binjimar Riga, saboda yanayin sanyi, nan yagansu a tsakar gida

Mama tace "Abban husna ai yanzu nake shirin kiranka ku gaisa da ahmad"
Abba yace "kice baqi mukayi"
Hannu yamiqawa ahmad, ahmad yaqi bashi hannun yakoma ya tsugunna yagaida shi har qasa
Hakan dayayi saiya birge Abba

Abba yace "kace Yau da safe kake take, kuma ahmad baka gajia da wahala haka"

Murmushi kawai yayi Baice komai ba, dama kuma shima Abban baisa ran Jin amsar sa ba,橙提
saboda yasan Hali
Dan haka yaci gaba da cewa, "wannan nasan ai ko break fast ma bakayi ba

Shigo falon azuba mana abinci"
Babu musu sukai cikin falon dukansu harda mama

Mama ce tafara hada musu,abincin Abba yace "a a kekuma bazaki hutaba, kira yarinyar nan
tazo tahada mana"
Daga murya mama tace
"nafeesa!"
Gogan naku cikin ransa yace "alhmdlh" 橙提

Da sauri na futo daga daki kaina ko dankwali babu,kasancewar nasan Babu kowa agidan,
dagamu saimu rigar jikina robace, Dan haka shafe dina yabaiyana acikinta, yan madaidaitan
breast dina dasuke a tsaye, sai suka qaramin kyau
Ina futowa falon dashi nafara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login