Showing 39001 words to 42000 words out of 113548 words
ciki tun dazu "
OK kawai yace, yasamu waje ya zauna yace" kiramin shi, kice masa maganar takardun
sababbin motocin nan ne"
Takira 2 time's Amma bai dagaba, Dan haka tace kawai yashiga may be, wayar bata kusa dashi
ne
Ahankli ya tura kofar office din yashiga, gaskya office din ya tsaru, ga photon sa nan yasa
manyan kaya farare yana murmushi amanne Ajikin bango,
Nishin dayaji ne yadawo dashi daga tunanin daya tafi
. "Subhanallah yallabai, Garin yayi haka?"
Kamashi yayi, ya kwantar dashi Akan doguwar kujera wayar office din yadanna, nan da man
likita yazo,
Yayi Dan dube dubensa yadago yace "gaskya oga saide muje asbiti" "Ok" kawai Ammu yace
Ya cicciboshi, sai mota, shawara kawai yasake yajuya kan motar sai asbitin doctor tahir
Dayake ahmad sananne ne, nan da nan aka karbeshi aka kai shi wani daki
Office din tahir yanufa, yamiqa masa hannu suka gaisa, tahir yayaba da kamala irin ta Ammu,
haka shima Ammu nan take yaji tahir ya kwanta masa arai, bayanin abinda yakawo su yayi wa
tahir, ai cikin second da basu wuce biyar ba yanayin tahir yasauya, cikin hanzari yayi Dakin da
ahmad din yake
** *** **
Naci abinci dakyar, inajin wani daci amaqogarona, dakyar de nadan caccakali abincin, nayi
wanka na kwanta, kala ce ta shigo, tace "idan na huta saina tashi nakoma bangaren ta"
Ai kaka najin haka tace" a a Babu inda nafi Zata ina nan tare da ita,"橙提
ba yanda kala ta iya haka tahakura,
Ina kwance ina tunanin duniya na shafa cikina araina nace kome zan haifa? Ko idan ya
tambayeni mahaifinsa yaya zance?
Wai nice da ciki, cikin ma na shege
Hawaye naji ya ziraro min nasa hannu na goge wallahi banasan cikin nan, tunda de shima jinin
ahmad dinne
"wallahi bana sanka"
nafada afili hannu na nadauke daga kan cikin, nasake cewa "nikam bana sanka," 橙提
wani motsi naji cikin yayi, nace "shikkenan qarasa ni ma kamar yanda shima yanemi kashe ni,
ranar nan"
** *** **
Tahir yace "haba ahmad, meyasa kake San saka kanka cikin matsala ne?"
Ba tare daya kalleshi ba, yace "tahir najima acikin matsala ai, har Zuwa Yau dana same ta"
Tahir yace "bangane ba," ahmad tiryan tiryan yabawa tahir labarin komai
Tahir yace "gaskya tadau zafi dayawa, yanzu yaya za'ai?"
Ahmad yace "wannan mgnr da fadamin itace takemin yawo akaina tahir ta tsaneni, nafeesa ta
tsaneni," sai hawaye
Tahir jikinsa yayi sanyi yace "ahmad kasan Mata, zafi ta dauka dayawa, nanda wani lokacin
Zata huce komai ya wuce ka kwantar da hankalin ka, muci Gaba da addu'ah kaji, kaga yanzu
jinin ka yahau, kuma sosai ma hawan jinin dole saika rage tunani, kayi hakuri abokina haka
tamu qaddarar take, "
ahmad baice komai ba, ya lumshe idonsa
Turo kofar Ammu yayi, yace" doctor yajikin yallaban? "
Tahir yace" alhmdlh jikin da sauqi, dan Allah abokina ka dinga kula dashi nabaka amanar amini
na,"橙提
Ammu yace" Babu komai insha Allah "
Bude idonsa yayi a hankali ya cewa Ammu," kaje kaci Gaba da kula da komai, zan wuce gida ta
nan,"
Ammu yace" to Amma yallabai dakazo namaida ka gidan aiko? "
Ahmad ya girgiza kansa yace" karka damu tahir zai maidani"
" Toshiknn yallabai Allah yasawaqe,"
gyada kansa kawai yayi
Bayan ya fita tahir yace" Amma wannan mutumin yanada kirki, "
ahmad yace" eh wlh nima tun ganina dashi na farko naji y kwanta min, shiyasa bana shakkar
bashi kowanne aiki daya shafi company" tahir yace "gaskya ne"
** *** **
Bayan sati uku, companyn su ahmad sun bawa ma'aikatansu wajan zama wadanda suke Zuwa
daga nesa, cikinsu kuwa harda Ammu
Yakira waya gida yafada musu, anty maimuna murna kamar me Zata koma kusa da yan'uwan
ta
Dakuma mijinta
** *** **
Baba adamu yayi duk wani zirga zirga Akan maganar gidan kaka, an sai Mata wani gida sabo
gwanin sha'awa anan bompai saide fa sun kashe Mata kudi, shida Abba, ita kanta tana godia
tana kuka, haka muka koma sabon gidan kaka nida ita, nikaina nafijin dadin zama agidan nafi
sake wa, Dan haka dakaina nafita waje naje nasiyo sabon sim card, kuma alhmdlh naji dadin
tafiyar danayi, tunda Babu inda nake Zuwa kullum muna gida amanne, nakira kowa na nuna
masa sabon layina, banda mutum biyu, saudat da ahmad, a wannan lokacin cikina watansa
shida, yayinda na mama yake wata bakwai
** *** **
"Ahmad! Ahmad!!
Ahmad!!!"
Tafada da karfi, cikin sauri yaduro daga kujerar daya kwanta akai,
" na.. Na... Na'am momy"
"Waladeey na me kake tunani hakane, tun dazu inata kiranka?"
"Momy kawai ina tunanin office ne,"
badan ta yarda ba, tace "kuma office kamar Yau kafara Zuwa Waladeey?" Shiru yayi
Saide ita aranta tasan karya yayi Mata, wani abun ma da sakacinta, bata fiya kula dashi ba,
yakamata ta janyo shi jikinta harya sanar da ita damuwar sa,
Tace "munyi waya ne da hajia bilki tana min maganar kaya, tace tazubamin ido tayi zuru tayi
zuru bataga kayaba, nace nikuma aina manta ma dana baka wannan kayan kuma nasan ka kai
Mata,"
Ahmad yace " Momy wanne kaya kuma?"
Tace "lesuna dana baka kwanaki,"
ahmad yace "tab ni wallahi Momy nama manta dasu, suna can adakina, mabaruka taje tadauka
takai Mata" , yana fadar haka yayi hanyar waje, tabishi da ido, tabbas akwai abinda yake damun
yaron nan, shikuma yayi hakane Dan karma tace yaje yakai kayan, saboda bayasan ganin
kayan kokadan, DAYA SANI ma tun farko bai karba bare wannan sabanin yashiga tsakaninsa
da feenarsa
** *** **
"Gaskiya baby nide nagaji yakamata ki barni nazo na ganki hakanan, haba husna Allah nide ki
barni kokuma inyi miki kuka," husna tace "haba doctor kuka kuma kamar ba namiji ba," yace
"inde Akan kine zan iyayin komai ma husna, zaki haifamin twins idan mukai aure?"
Husna cikin mamaki tace "yan biyu de, a a bazan iyaba," tahir yasake gyara kwanciya Akan
doguwar kujerar dake shinfide afalon nasu yace" aikuwa ke, danni inasan yan biyu, "tace" toka
dena, danni kam banaso akwai wahala fa doctor, tafadi haka cike da shagwaba,"
nan danan mutumin ku ya rikice yace" to to naji baby ni karki min kuka shikkenan? "
Kafin husna tayi magana can cikin wayar taji Ana cewa" Dan ummi da yar tawa kake waya ne?
"橙提
Dagowar da tahir zaiyi yaga ummi a tsaye akansa, haba qasa Bude tahir yashige, yaji kunya ta
Kamashi, Allah yasa de bataji zancan duka ba
Husna taji shiru har Zata kashe saita qarajin ance bani ita mu gaisa
Tahir ya daskare da waya akunnan sa
Mrs Usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicatedg to my family
30
"Kinyi shiru nafi,"
nace "kaka ai baya nan, yatafi misra,"
" au to shiyasa naji shi shiru, nasan da yasan inda nake aida tuni ya zo"
Nace "um" 踫
Natashi nayi daki
** *** **
Akwana atashi Babu wuya awajan Allah, har cikina yacika wata tara, duk kafafuna sun
kumbura, nayi wani fari, kaka bata barina inyi aikin komai, ina kwance kokuma in tashi inta
zagaya gidan
** *** **
Baba adamu shine yayi shige da ficensa ya karbo min takarduna, yahada dana wajena yatafi
dasu gidansa bansan me zaiyi dasu ba
** *** **
"Maman nafeesa anya kuwa ba zamuje asbiti ba aduba lafiyarki?
Tunda kika samu cikin nan bakida lafiya Yau fari gobe tsumma, gashi naga watan naki ma ya
haura, ga kuma bikin husna dayake ta matsowa saura wata daya da sati daya"
Mama tace "Babu komai Abban husna, aidama Ana samun hakan, yanzu Babu abinda nakeji,"
Abba yace "Toshiknn"
** *** **
Su ahmad tunda bikin nan ya matso ake ta zirga zirga kai kace bikinsa ne za'a yi,橙提 baya zama
Yau shine can gobe shine can
Kullum suna shirya yanda bikin zai kasance,
Haka a bangaren su mama ma, basu zaune basu tsaye, Ammu yayi kokari sosai wajan ganin
ya qawatawa yar tasa gidanta, sosai yayi Mata siyaiya ta gani ta fada Babu abinda su mama
zasuce sai godiya
** *** **
"Kaka ni banajin dadin jikina, tun jiya wani irin ruwa nake zubarwa,"
kaka tace "a a nafi to haihuwar ce ta matso inaga zaqi ne, shiyasa banasan wannan ciye ciyan
naki,"
tunda kaka ta ambaci haihuwa gabana yafadi, gaskya ina tsoro, qila ma Garin haihuwar na
mutu, sai hawaye, kaka ta kalleni tace "to nafi ki adana kukan ki ba yanzu橙提橙提 ba akwai
lokacin da zakiyi mai dalili,"
maya finta taja, tace "bari inje in karbo miki rubutu kyasha," bata jira amsa taba tayi waje, na
zauna ni kadai na rafka uban tagumi, tashi nayi naje nayi alwala domin gabatar da sallar la'asar
** *** **
"Wash Allah Abban husna mu tafi asbiti, ina tunanin haihuwa zanyi,"
Abba Gaba daya yarikice, Yama rasa yaya zaiyi
Husna yakira ta futo da sauri, suka hada duk wani abin buqata sai wani asibitin kudi
Suna Zuwa kuwa likitoci suka karbeta sai labour room, husna sai kuka take, Abu tun la'asar sai
gashi mama takai kusan isha'i bata haihu ba, duk nurse din data futo amsar daya ce bata haihu
ba tukunna
** *** **
Ina zaune kan sallaya na idar da sallah kenan da carbi ahannu na, naji wayar kaka na kuka, kira
na qwala Mata, nace " kaka Abba yana kiranki,"
ta futo daga daki ta amsa wayar, sai ji nayi kaka tana salati,
"ma'azu to anya kuwa Babu wata matsalar ka boye min?"
"Mama Babu komai wallahi kawai de dama Dan in fada miki ne kisan halin da ake ciki,"
kaka cikin sanyi jiki tace" to Allah yarabasu lafiya"
" amin" Abba yace
Ta zauna akujera nace " kaka lafiya kuwa,?"
Cikin jimami tafadamin abinda yake faruwa gabana naji yabada dam, araina nace nima fa
inakan hanya, bayana naji ya riqe da sauri nasa hannu na awajan, nace " wash Allah, kaka
bayana,"
ina yi ina yarfe hannu, kaka tace "subhanallah nafi karde kema haihuwar ce?"
"Wayyo kaka marata ciwo, zan mutu kaka,"
kaka tace " tsaya nafi bazaki mutu ba insha Allah,"
Wayarta ta dauko tafadawa baba adamu abinda yake faruwa, yace gashinan Zuwa
Kala taso ta biyo shi yace ta zauna tunda kaka tana nan, sai ihun kuka nake Mata ina yarfe
hannu, yana Zuwa muka shiga bayan motar nida kaka, sai ihun kuka nake musu
Kaka tanaban hakuri, asibitin gwamnati muka fara Zuwa, saide sun shaida mana sun tafi yajin
aiki, haka baba adamu yajuya kan motar sai wani asibitin kudi shi kansa ya rikice, yana tausayi
na, ga halin danake ciki gani yarinya
Inata kaina banma kula da sunan asibitin ba nide nasan muna Zuwa wasu Mata suka karbeni
aka dorani Akan gado, suka turani Zuwa labor room
** *** **
10:30 na dare, wata doctor tazo tace "alhaji saide fa kasa hannu anan, dole aiki za'a yi mata,
Dan gaskya karfin ta yaqare, bazata iya haihuwa ba, sannan gashi ta manyanta,"
Abba cikin rawar jiki yasa hannu, anzo tura gadon za'a maida ta Dakin operation Allah cikin
ikonsa ta sauka, ta samu danta namiji
Nurse dince ta futo, Abba da husna har rige rigen Zuwa gareta suke, tace musu " ta sauka,"
hamdala Abba yayi, yace" meta haifa,? "
Tace" tasamu danta namiji, Amma saide kayi hakuri yaron yarigamu gidan gaskya, sakamakon
wahalar da babyn yasha, "
Abba yace" yanzu a wanne Hali take?"
Nurse din tace" alhmdlh munkai ta Dakin hutu, Amma kafin nan kaje wancan office din likita ya
nasan ganinka, "
Abba ya wuce, yasamu doctor, anan doctor din yake masa bayani Akan abarta ta huta haka,
yakamata ace a shekarun ta, tadaina haihuwa ma, yanzu ma Allah ne yatsare da saide ayi biyu,
Amma sunyi iya kokarin su ganin kare lafiyarsu Gaba daya, shide yaron Allah yayi hukuncin sa,
Abba yace " Babu komai likita, insha Allah za'a kiyaye"
Daga nan suka wuce Dakin da mama take ciki shida husna
** *** **
11:56 ahmad yace "to man ni zan wuce gida, kaga dare yayi, wannan de shine tsarin yanda
dinner din zai kasance
, kaga har lokaci yaja ban tafi gida ba duk ka wani hanani sakat saboda wannan auren,"
Kafin tahir yayi magana, wata nurse ta shigo afirgice, tace "doctor ankawo wata Mata tana
naquda, munyi iya yin mu Amma takasa haihuwa, batada jini tana buqatar jini, ko zakazo asan
yanda za'a yi?"
Tahir yace "nawane group din jinin nata?"
Nurse din tace "wallahi bamu dashi doctor group O negative gareta"
Tahir yace " to ina yan'uwanta?"
gaskya suma mun gwada baiyi daidai ba
Tahir ya miqe da sauri, zai fita, ahmad ya tareshi yace " kaga muje kawai na bata nawa, ainima
shine Dani,"
tahir yace "a a ahmad kaima fa bakajin dadi sosai," ahmad yace
"kaga da Allah muje," lab sukaje aka gwada jininsa, yayi daidai, haka kuma ba shida matsalar
komai
Dan haka gado Aka bashi ya kwanta aka dibi jinin
Doctor tahir da kansa yasa mata jinin, kaka tana waje banda kuka Babu abinda take yi
Saida yasa Mata jinin sannan yaje, wajan ahmad,
"man mungode fa," ahmad yace "Babu komai, bari in wuce," tahir yace " no kabari na kaika,
jini aka diba ajikinka kada kayi wani abin wahala yanzu,"
haka ahmad y hakura, suka fita shida tahir yasaukeshi agida, shikuma tahir din yadawo
12:30 daidai na haihu, nahaifi 'yata mace, muna Dakin hutu nida ita, tana kwance a gabana
ansa Mata kaya farare masu shegen kyau, gata bul bul da ita yarinyar, masha Allah wannan
yarinya badai kyau ba, na zuba Mata ido ina kallanta, Babu abinda ta dauko na uban ta, komai
nawa tayi, Daga farin har hancin hatta yan yatsun ma irin nawa ne, idonta kar Akan glof din wutar Dakin
Na shagala ina kallanta kaka ta shigo Dakin, maganar tace tadawo Dani da duniyar tunanin
dana afka
"Um yaran zaman, su nafi ko kunya Babu anzubawa ya ido" 橙提
, kallanta nayi, ni banma San tana kainaba, tunawa nayi da yarinyar nanfa bata hanyar aure
nasameta ba, sai wani baqin ciki ya to kare ni, nan take na juya Mata baya
Kaka tace '' zancen yaushe kuma nafi, 橙提"
Wata nurse ta shigo tabani magani nasha da tea mai kauri, baba adamu ma yazo yaga yar
sosai yarinyar ta shiga ransa, yarinya kamar wata yar baby 橙提
** *** **
Karfe goma nasafe nayi wanka, naci abinci na shirya tsaf Dani, ga jaririyar dana haifa nan a
gefe na, kaka sai magana takemin Akan na bata nono tasha naqi bata,
Wayar tace tadau qara, ta daga kawai ji nayi tace
"to Allah yaji kanshi ita kuma tunda de Allah Yabar mana ita to Allah yabata lafiya"
Can naji tayi shiru, bansan me take jiba, sai tace "eh hakan ma yayi ma'azu, insha Allah gobe
zan taho, sai nabar nafin awajan kalatynsu to, to sai nazo,"
ta juyo tafadamin komai, nace "kash dama yaro maman ta haifa, to Allah yabata lafiya,"
kaka tace " amin,"
Amma batamin zancan tafiyar ta taba goben
Rarrashi na tashiga yi, Akan nabawa yarinya nono, dakyar de na dauketa nasa Mata aikuwa
cikin sauri takama tanasha
I nayi ina rintse ido
Kofar Dakin dr Tahir ya turo yashigo,kaka tashiga toilet, saini kadai, sai muka birgeshi a yanda
ya ganmu, ina shayar da yarinyar, sannu d jiki yayimin, ya tambayeni ko akwai abinda yake
damuna nace a a, yarinyar yadauka yaji dama abashi ita yarinya saikace yar turawa, wasa yayi
Mata gamida yimin sannu yafice daga Dakin
Mundawo gida da yamma yin duniya kaka tamin yar nan tana kuka in bata tasha, nayi mirsisi
nahana, araina nace kyayi kya Gama kaka Amma bazasu zubar min nono ba itada ubanta
Haka kaka ta