Showing 24001 words to 27000 words out of 113548 words

Chapter 9 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

03 Apr 2025

9263

Toshiknn zanyi ta jira kaima yashafeka,橙提
wallahi a kudin ka,"

musa yace "a a hajiya baza'ayi haka ba, bari nasake tuntubar hanyar gidan matar, tunda yar

aikin tayimin bayanin komai,"
ba tare datace masa komai ba, ta katse wayar



** *** **



Ahmad bai tashi dawowa daga duniyar daya Lula ba ta dadin kowa, sai bayan kusan 46
minutes
Awannan lokacin feenah batasan inda kanta yake ba, Babu alamun numfashi atare da ita
Jikinsa yazare daga nata, daga baya kuma ya rungume ta gam ajikinsa, kukan ma Gaba daya
yaqi Zuwa, kawai kallan ta yake
Yau shi ahmad shine da yiwa wata yarinya fyade,踫葉 raping dinma yarinyar dayake mutuwar
so,踫葉 Gaba daya sai tausayin ta ya kamashi

" feenah, feenah, feenah!!!"

Yafada da karfi, saide Babu alamun Zata iya tashi,
Sai Awannan lokacin kuka mai karfi da cin rai yazo masa, tana rike ajikinsa yana buga kansa
Ajikin glass din motar, har hakan ya haifar da tsagewarsa



"Nafeesa Dan girman Allah ki yafemin, nafeesa na yaudareki, tabbas nacika mayaudari, kiyimin
ko wanne irin hukunci nafeesa

DANA SANI daban daukoki ba, saida zaki fita nahanaki nafeesa, kiyi hakuri,"

yafada yana kuka tamkar, mace, tunda yake arayuwarsa bai taba kuka irin haka ba, yaci
amanar wadda ta yarda dashi fiye da kowa da komai

Jijjigata yayi, yaga de tabbas idan baiyi da gske ba zai iya rasata, hakan yasa yatashi yagyara
wandonsa
Futowa yayi da ita a hannun sa, kamar matacciya, yabude bayan motar yasaka ta aciki yarufe
Hawaye shabe shabe Akan fuskarsa yazago yajasu aguje, sai wani private hospital dayake
kusa

Yana parking ko kofar motar bai rufe ba yabude yadauko ta, Babu alamun rai atare da ita,
mantawa yayi da hijab dinta yakoma yadauko yarufa Mata, yayi cikin hospital din aguje

"Malam baka rufe motar ba,"

wani mutum dayake gefe yayi masa magana,
Ahmad yace" Dan Allah bawan Allah rufemin"

bai jira amsarsa ba, yayi ciki

"Nurse!"
Yake fada cikin daga murya
Wasu Mata biyu suka karbeta ahannun sa, wani daki sukayi da ita Akan gadon tura marasa
lafiya,
Dafe kansa yayi kawai yana hawaye, har yanzu ganin abun yake kamar amafarki, Ajikin bango
yadora kansa yana kuka 踫葉




** *** **



"Oni rabi'atu wannan wacce irin fira ce haka, yarinya tun dazu tafita Babu alamun ta, to kode
wani wajan sukayi, bari nakirata"

Wayarta me torch light ta dauko ta kira har sau uku, ba'a dagaba Awannan lokacin wayar
nacikin aljihun ahmad, yakasa dagawa, tome zaice Mata, irin wannan cin Amana
Kaka taja hijabi tayi kofar gida, taga Babu kowa, sai gida ta dawo tace
"bari Ajima nasake kira, Allah yasa de lafiya



** *** **



8:56 pm, ahmad yana Dakin da feenah take, ansa Mata ruwa, fuskar ta tayi wani iri, kawai
kallanta yake yana hawaye, Awannan halin nurse tashigo tace" masa doctor yana kiransa a
office "

Jiki asabule yatashi yabita, yana tafiya yana waiwayen feenah

Yazauna akujera a gaban doctor, doctor yagama rubuce rubuce yadago kansa yace,

" haba abokina, irin wannan barna haka kamar ba amaryarka ba, ai yakamata kabita a hankali,"

Hawaye ne ya zirarowa ahmad yace "doctor kayi hakuri, tsautsayi aka samu, insha Allah hakan
bazata qara faruwa ba,"

Doctor yayi ajiyar zuciya yace "ok, yanzu de Dan Allah kabarta ta huta Tsawon sati daya,
sannan munyi Mata dinki, munyi Mata allurar dazata kashe Mata zafin ciwon, da abinda
yakamata
ga wannan, yabashi takarda kaje kasiyo Mata magungunan nan, dole Zata buqacesu"

Karbar takardar ahmad yayi, yafuto
Maigadin ne yanuna masa inda zai samu magungunan

9:8pm wayar dake gefen gadon ta dauki qara, itace ta taimaka Mata wajan farkawarta
Bude idonta tayi wanda yayi ja, saboda kuka, ta kalli Dakin, sannan takai hankalinta kan wayar,
gani nayi ansa kaka, Akan screen din wayar, kashe wayar tayi gaba daya, ta yunqura ta tashi,
ruwan dake hannun ta ta cire, tasauko, zafi taji agabanta nan tasaki qara, tana yarfe hannu,
Kamar me tafiyar ta ta ta, haka ta futo daga Dakin, Babu wanda yakula da ita, haka ta zare jiki
tafuto harabar hospital din,
Dakyar taje gate din asbitin, baba mai gadi harda ce Mata sannu yarinya ganin yanda take
tafiya yasan Babu lafiya
Kawai daga masa kai tayi, ta wuce
Gaban titi ta tsaya ta tsaida mai adaidaita, tayi masa kwatancen inda take so yakaita, dari biyu
yace Mata, Babu musu tace masa Amma sai sunje Zata shiga gida ta dauko masa, yace.
"ba damuwa"


Tashige suka tafi




** *** **



Laila nagani tana waya, tace "Malam musa bazai zoba kawai zan hakura Yau din inci Gaba da
bibiyarsa, kokuma mu sake wa dabarar,"

"Toshiknn hajiya ngd"

** *** **



Kaka nagani ta rafka uban tagumi a kofar gida, tun dazu take Kira wayar nafi akashe, acan
kuwa feenah kukan zuci kawai take, tana kuma share hawayen ta, kasa danne zuciyar ta tayi,
tasaki kuka mai sauti, mai "raksha" (adedeta) yace

" hajiya kiyi hakuri, cuta ba mutuwa bace, Allah yabaki lafiya, saboda naga daga asbiti na dauko
ki," 橙提

qyaleshi tayi taci Gaba da share hawayen ta, har sukazo kofar gidansu, kaka tagani atsaye
itada wani saurayi da alama cikiyarta ta take bayarwa
橙提



** *** **



" Abban husna, nifa Gaba daya banajin dadin jikina,"

Abba yayi murmushi yace "to maman nafeesa me yake damunki,"

tace "haka kasala kasala nakeji, bakina banajin dadin sa,"

Abba yace "to kiyi hakuri Zuwa gobe sai muje asbiti,"

mama tace "haba alhaji wanne irin asbiti kuma,"


Abba yace "a a banasan musu,"
hannu yasa yashafa wuyanta, aikuwa zafi kamar gidan biredi, yace

" subhanallah maman nafeesa me yake damunki haka?"

Mama tace "alhaji ni kalau nake,"

Abba yace "a a Babu wannan maganr kawai de kice bakyasan fadamin abinda yake damunki
Dan kada hankali na yatashi, narasa yaushe zaki dena wannan halaiyar taki,"

"to alhaji kayi hakuri,"

"Kinga tashi, tashi maza muje ki kwanta ki huta gobe insha Allah sai muje asbiti kiga likita,"

mama tace "to Allah yakaimu"



** *** **



Futowa nayi daga adedeta dakyar nake dingisa kafata ina hawaye, badan kaka tana cikin tashin
hankali ba, Babu abinda zai hana ta fahinci halin danake ciki,
Dasauri ta qara so gareni, "sannu nafi, sannu daga ina kike naga kina tafiya a hankali kamar
marar lafiya bayan nasan kalau kika fita,"

kafin na bata amsa me adedeta yace "mama, ai asbiti na dauko ta, batajin dadi,"

salati kaka tasa, ta janyoni jikinta,
Gaba daya tausayin kaka yakamani yanda ta damu Dani, take kaffa kaffa Dani, ga abinda naje
na aikata, mema ya kaini bin saurayi unguwa, nayi DANA SANIN Sanin ka arayuwa ta ahmad,
Cikin kuka nace" kaka ki bashi dari biyu kudin sa, "


Kaka tace" yaro yi hakuri bari nadauko ma kudin,"

me adedeta yace" a a mama ki barshi, ai jinya ce tana kan kowa, "

kaka tace" to Mungo de Allah yasaka da alkhairi, kafin tajuyo kaina tana fadin nafi meyasameki?
Ina shi amadun?
Ya akai kuka rabu? "

Nikam nama rasa amsar dazan bata, kawai sai wani tunanin yazo min, nace" kaka hatsari
mukayi, "

Salati kaka rafka" hatsari nafi
Innalillahi wa inna ilaihir raju'un
Garin yaya? "

Nide da nake ji ajikina nace" kaka muje, "

kamani tayi mukayi ciki,

Anan nafada Mata me mota ne yabuga mana motarsa shine motar mu tayi gefen titi, anan aka
taimakemu, shi yana asbiti ma yakarye, nice de nasamu targade aqafafuna
Hawaye kaka ta share tace" sannu nafi, bari nahada miki ruwa kiyi wanka, "

bayan tatafi awajan na kwanta kan tabarma ina tunanin rayuwa ta
Zancen kakane yadawo Dani daga tunanin dana fada, tace" nafi na dora miki ruwan dumi, saiki
gasa kafar, bari inje in kira me gyara,"

nace" a a kaka ai an gyara min a asbiti shiyasa nataho, "

kaka tayi tagumi tace," to waidaku ina zaku je ma?"

Nace" kaka wajan qawar mamansa zamuje zaikai Mata kaya,"

kaka tace" dama da kunyi shawara Dani bazakuje yanzu ba, saida safe,"

nide Bama najin me take fada
ruwan tajuyemin tace inje in sirka yanda zaimin saina watsa kozanji karfi ajikina, haka natashi
nayi "hammam" (toilet)



** *** **



Gudu gudu sauri sauri ya qarasa office din doctor din, yabashi magungunan, doctor ya duba
yace "eh sune sunyi, yanzu muje Dakin idan ruwan yaqare sai abata maganin, kokuma idan
kunje gida sai kabata,"

Doctor na Gaba ahmad na binsa abaya, Gaba daya kunyar hada ido yake ita, 橙提

suna Bude kofar Dakin sukaga wayam Babu feenah Babu alamar ta, gaban ahmad yayanke
yafadi, duhu yafara ziyartar idanunsa, nan take ganinsa ya dauke





((to Malam amadi daukacin makaranta wannan novel suna Maka fatan farfadowa lafiya))

Mrs usman ce 踫
[5/6, 3:32 PM] 儭DANGI DAYA儭: 潤摹DANA SANI 潤摹



Writing by Amnah el yaqoub



Dedicated to my brother Abdulmumin Muhammad El Yaqoub Happy birthday 潤



22



Da taimakon doctor aka daukeshi aka maida shi gadon da feenah ta tashi, doctor yafara duba
shi




** *** **




Ruwan da kaka takaimin a bucket na raba biyu, daya najuye acikin bahon wanka, nadan sirka,
kasan cewar ina karance karancen littafi shiyasa nabi duk hanyoyin dana karanta wajan gyara
kaina, ina shiga cikin ruwan namike nasaki qara
Kaka datake zaune tadaga murya tace "sannu nafi yi a hankali"


Maganar kaka ce tasa na rufe bakina da hannu na, nadaure na shiga ruwan, saida zafin yaragu
sannan nasake Zuba wani ruwan zafin, na shiga, shikuma sauran nayi wanka dashi, ba laifi naji
dadin jikina
A hankali nazo na wuce kaka, tana zaune atsakar gida, badan wankan danayi ba, Babu abinda

zai hana taga hawayan fuskata
Daki naje na zauna nasauya kayan jikina, ina zaune da humra a hannu na, nakasa shafawa,
kaka ta shigo tace "sannu nafi,"

nace" yauwa kaka, "

tace" me yake miki ciwo yanzu bayan kafar,"

nace" kaina,"

tace" to ina Zuwa "


Bayan jimawa kadan tashigo da pure water da maganin ta bani nasha na kwanta, tace " to ki
huta yaude karkiyi wannan jarababban karatun naki, ki huta,"

saida tayi maganar karatu natuna da exam din datake gabana, wutar Dakin ta kashe min ta
rage fanka kadan sannan tafita
Tana fita nakafa sabon kuka, yanzu shikkenan ahmad ya cuceni, duk mutumin dana aura bazai
ga mutunci naba, nayi DANA SANIN haduwa ta dakai Ahmad, wallahi bazan yafe maba, dama
ashe yaudara ta kake akwai abinda kake so ajikina, saudat DANA SANI tun farko daban karbi
qawancen dakika zomin dashi ba, wanda shine silar haduwa ta da wannan azzalumin saida
nace yayi hakuri, idan wani laifi nayi masa yayafemin Amma shine ya nunamin ba shida imani,
afili na furta "insha Allah saika yi DANA SANI ahmad"



** *** **





11:00 yana zaune gaban ummi suna kallo afalo dagashi sai jallabiya yana shan iska, tunani
yake shin yakira doctor Bashir Akan maganar yarinyar nan kokuwa? Kawai wata zuciyar tace
yakirashi Dan shine kawai mafita
Ummi tun dazu tana kallansa taga Gaba daya hankalinsa bayama kan abinda suke kallo daga
gani cikin tunani yake, Amma zataga gudun ruwasa ai
Gani tayi yadauki waya yana dannawa hakan yasa ta kawar da kanta daga kallansa
Bugu daya doctor Bashir yadauka, "abokina ya fama da jama'ah,"

tahir yace "wallahi gasunan alhmdlh kullum muna fama,"

tahir yace "yauwa Bashir nikuwa Yama sunan yarinyar nan daka nunamin rannan,"

aikuwa karaf akunnan ummi tayi murmushi aranta tace ai nasan arina wai ansaci zanin
mahaukaciya
Doctor Bashir yace. "yarinya kuma wacce iri,?" Tahir yace "yarinyar nan daka nunamin har
sukazo suka gaida kai muna tsaye menene ma naji kace sunanta?"

Bashir sarai yaganeshi Amma da niyya yake Jan maganar, yace "kai ban gane taba gaskya ko
tayi ma wani laifi ne?"

Tahir dayaji kansa yawani sara yace
"a a kaida baka gane taba tayaya kasan ko tayimin laifi, wai nazo office dinka ina fadama
abinda yarinyar tayi, har na hanata shiga aji," 橙提

doctor Bashir yace "oh abokina sorry sai yanzu nagane ta husna kake nufi" 橙提

, tahir yace husna aransa suna me dadi, afili kuma yace "no bande saniba,"

Bashir yace "to me kake so,"
tahir yatashi daga falon yayi daki yana waya yace" number ta nakeso ka nemomin kokuma
kabata tawa number kace ta nememi yanzu,踫董"

ummi
murmushi tayi akaro na biyu ta daga hannuwanta sama tace" alhmdlh addu'ah ta ta karbu Allah
yasa wannan yarinya a dace kar a kuma irin ta baya, "
Bashir aransa yace lalle tahir wato shide bazai futo fili yace inasan yarinyar nanba, gara ya
dinga wannan kwana kwanar 橙提
Yanzu banda abinsu wacce budurwa ce mai hankali kawai za'a bata number ace ta kira, kuma
ma Abu kamar umarni ta kira yanzu yanzu 橙提
Bashir yace "a a bari inturo ma kawai ka kirata, Dan nikam bazan iya wannan karfin halin ba,"

"OK" kawai tahir yace, ya kashe wayar

Yana zama agadonsa yaji shigowar text yana dubawa kuwa yaga Num yarinyar, yawwa yafada
a fili,橙提 yaude za'a yi ta takare, wannan labari dole yafadawa ahmad, a wannan lokacin kuma
ahmad yana kwance baima farfadoba, doctor din daya duba shi, yana shirin fita daga falon yaji
wayar ahmad din tana qara hannu yasa ya dauko wayar best friend yagani, doctor kai tsaye ya
daga yayi masa bayanin halin da ahmad din yake ciki, tahir baisan lokacin daya tashi ba yace
"wanne asbitin?"
Nan doctor yayi masa kwatance
Falo ya futo cikin sauri ummi tana tambayarsa ina zaije yace Mata ahmad ne baida lafiya zaije
wajansa, cikin alhini tace to Allah yabawa wannan yaro de lafiya, hankalinsa yayi Gaba baima ji
abinda take fadaba, mota yashiga aguje maigadi yabude masa yadau hanya

** *** **



Yana Zuwa yafaka motarsa yashiga ciki cikin sauri,ahmad yagani a kwance ga doctor a gefe,
anan doctor din yace kawai tashin hankali ne yayi masa yawa, ganin yazo Dakin matarsa bata
nan kuma muma bamusan inda tayi ba, sannan mai gadi yace yaga fitar ta, da nasa aka
tambayeshi Tahir yace "matarsa kuma?"
Doctor yace "eh aishi da ita sukazo shiya kawo tama,"
tahir ya nemi waje ya zauna, yace "doctor in bazaka damuba kabani shi mutafi zan kula dashi
dan'uwana ne," ID card dinsa ya nuna masa nan take yace Babu damuwa yafita, tahir hannun
ahmad yakama yarike, yace ahmad cikin mamaki, tome yakawo ku asbiti bayan nasan sallama
zakuyi
Yakai kusan minti talatin a zaune sannan ahmad yafarka, bai Bude idonsa ba, yafara magana

" feenah karki barni wallahi ba laifi na bane, please feenah ki yafemin,"

tahir ne yace "ahmad, ahmad, ahmad tashi, ba feenah bace nine"

Bude idonsa yayi, yana ganin tahir ya rungume shi yana kuka,

" tahir feenah bazata yafemin ba, wallahi nayi mata laifi"

Kamashi tahir yayi suka fita daha hospital din

Amota ahmad banda kuka babu abinda yake, tahir bai hana shi ba, yasan akwai abinda yake
faruwa babba, suna Zuwa gate din gidansu ahmad tahir yabawa driver gidan key din ahmad din
yayi masa kwatance yace yaje yadauko masa motarsa

Suka shiga ciki, maryam tafuto da gudu tana musu oyoyo, ahmad bai kula taba, sai tahir ne
yace "auta me kike bakiyi bacci ba?"

"Tace banga yaya ba shine naqi yin bacci,"

tahir yace "to yaya bayajin dadi jeki kwanta ki huta kema"

Tatafi da gudun ta,
Bangaren ahmad din suka nufa, ahmad ya zauna a qasa yajingina da bangon Dakin, hawaye

suka ziraro masa, tahir yace "ahmad me yake faruwa ne?"

"Tahir na ha'inci feenah, yarinyar tana sona dayawa, Amma na yaudareta,"

kansa yafara bugawa da bango, tahir yatashi da sauri ya rikeshi, "haba ahmad, meyake
damunka haka wai meke faruwa ne,"

ahmad ya rike tahir yace" tahir meyasa baka bini ba?
Meyasa tahir?
Kasan me hakan yajamin? Tahir nayi abinda ban taba tunanin ko amafarki zanyi ba, wallahi
inasan feenah nasan duk abinda zan fada Mata ayanxu bazata yarda daniba, "

Tahir ne yarike shi, suka zauna abakin gado, tahir yace" ahmad fadamin meyake faruwa? "
Nan ahmad yafada masa komai
Salati kawai tahir yakeyi, yace" ahmad Amma ina tunanin ka yatafi? Tun muna yara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login