Showing 81001 words to 84000 words out of 113548 words

Chapter 28 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

03 Apr 2025

9289

kun karbi
haihuwar ta a sbitin ka, har kace ahmd ne yabata jini, auta ce tahir

Alokacin data haihu lokacin yayi daidai da haihuwar mama, ta haifi namiji, Amma ya rasu,
hakan ne yasa Abba ya karbi baby daga wajan auta, yabawa mama ita, saboda rufin asirin ta "

Tahir daya mutu da mamaki yace"yanzu kina nufin baby dama ba 'yar mama bace?" Husna
tasake goge hawayen ta, tace "hakane, bamusan yar waye ba, tunda tun lokacin anyi Mata
tambayar duniya tace wallahi batasan wanda yayi mataba, inda ace tasanshi, nasan cewa Sai
inda karfin Abba yaqare"
Gaban tahir ya dinga faduwa yace "kuma kikace raping akayi Mata?"

Husna tace "eh"
Cikin ransa yace " to ai kuma ita wannan tace batasan waye yayi Mata ba, bare yayi tunanin
wani Abu"
Janyota yayi jikinsa yafara rarrashinta, yace
" Allah yasaka Mata, kiyi hakuri kinji,"

kanta ta dora Akan kirjinsa


** *** **


Next day

"Wallahi alhaji gabana har faduwa yake idan na tuna yarinyar nan jibi Zata dawo"

Abba yace "menene abin faduwar Gaba kuma maman nafeesa?
Saikace ba kece kika karfafamin gwiwa Akan abinda mukai ba
Nafeesa de mune muke iko da ita, dan munbada wannan yarinyar ni aganina kamar rufin
asirinta ne
Saikiga anyi Abu, kana tunanin babu wanda yasani, Amma daga baya sai kiji maganar awaje

To kinga inde ubane, izdihar tasamu, bana tunanin ko mutumin dayayiwa nafeesa wannan abun
yakai ahmad son izdihar
Dan haka ga uba nan tasamu, mamanta kuma nafeesa

Koda tayi aure zaman baby awajan ahmad yafi sauqi
Dan haka tana dawowa zanyi Mata bayani da kaina "
Mama tace" to shikkenan Allah yakaimu alhaji "


** *** **


"Kinga ni kawai kiyimin baqin lallan, banasan Jan"
Zahra tace " meyasa feenah,? Kawai ayi mana, duka, baqi da Jan"

Nace "Zahra Jan lalle yana dadewa ahannu na bai fitaba, Amma baqin baya wuce sati daya"

Zahra tace " ok, kumafa hakane, to kawai ayi mana baqin, kar muje ayi mana Jan yaqi fita da
wuri
Kuma ga biki yana matsowa"
Feenah tace "emana, nima shi nagani"

Zahra tace "Amma de ai a kano za'a yi miki dilka dasu qunshi ko, kinga sai Amana Gaba daya"
Nace "emana insha Allah"

Mai qunshi takama hannun Zahra tafara yi Mata, saida aka Gama musu, su kabar unguwar

Da daddare sunyi wanka, kowa yana kwalliya, Zahra takira mukhtar tace "ango, to anjima din
zaka turo mana motar dazata kaimu airport ne kokuma kawai mutafi?"

Mukhtar yace "a a ku zauna nima sai nazo gidan naku, daga nan saimu kira Tirhal kawai
takaimu Airport din Gaba daya"

Zahra tace "a a yanzun kai kana ina?" Yace "ni ina unguwar Salamah yanzu ina sallama da
friends dina, kuma daga nanma
Meenal barri zanje daganan inje hilla soba,"
Zahra tace "am mukhtar naga al'amarin Naka bana qare bane kawai sai kazo anjima din" 🤣

Ta dubi feenah datake kokarin saka Riga doguwa abaya mai kyau, tace "wannan angon naki
yacika zirga zirga"

Feenah tace "toya za'ai kinsan shi mutum ne na mutane"

Zahra tace "to waye bana mutanan ba, me kike nufi?"
Feenah tace "ahmad mana, tunda nake dashi bai taba nunamin daya daga cikin abokansa ba,
kullum saide yacemin yaso yazo da abokinsa Amma abokin nasa bashida lokaci
Dayake abin nasa bana gaskiya bane, Amma inda ba yaudara ce takawoshi wajenaba mezai
hana yanunamin wani nasa"

Zahra tace "aikuwa inkina neman mutum na mutane ma kika samu ahmad kinga ma yarinya
Ke shaida cede, kingani da idonki lokacin da mukaje masar
Kinga yanda mutane suke rububinsa"

Feenah tace "um aikam nagani, zahra'u Ahmad muha marzuk" 🤣

Zahra tace "edin kiyi ta fada
Yauwa kin kira saudat kuwa?" Feenah tace "gara dakika tunamin namanta"

Wayarta ta dauko, tasa number saudat, tasa wayar a handfree
Zahra tadena kwalliyar datake tazauna zataji ya zasuyi

Kiran farko a kace call end, feenah tace "Zahra kode tadena amfani da layinne?"
Zahra tace "sake gwadawa muji"
Sake kira tayi, aikuwa bugu uku Ana hudun aka daga

Feenah tace "sister saudat, yar'uwata takaina, amaryar farouq maman baby"

Har abada bazata taba mantawa da mamallakiyar wannan muryar ba

Saudat tace "Dan Allah mafarki nakeyi ko a gaske ne?
Feenah kece? Sister feenah
Kiyi magana mana,"

Tuni kuka yazomin, nace "nice saudat, kwana dayawa yagida, yayaranki?"
Saudat itama kukan take tace "feenah ina kika shiga? Neman duniya muke tayi miki nida yaya"

Nace "saudat ina nan," tace "to kina wanne qasa, naga number bata Nigeria bace"
Nace "eh ina Sudan saudat
Gobe zan dawo Nigeria, inaso zamuyi wata muhimmiyar magana dake, idan nazo insha Allah
inasaka wani layin awayata zan kiraki"

Saudat tace " to feenah Dan Allah kikirani, Allah inasan ganinki sosai,"

nace "saudat zankiraki, ina yaranki, sai tambayarki nake kinyi shiru?"

Saudat tace "ban haihu ba feenah, ina fatan de nasamu cikin"
Nace "Allah sarki yar'uwa, nima to zan dinga yi miki addu'ah Allah yabaki," tace "amin"

"Dan Allah feenah ina kika shiga Tsawon wannan lokacin?"


Nace "saudat zamuyi magana idan na dawo kasar"
Tace "to shikkenan, I miss you sosai"

Nace "wallahi nima haka, sai anjima, sai munyi wayar"

Saudat tace "feenah banji kin tambayeni yaya ba, ko akwai abinda yake faruwa ne?"

Nace "saudat babu komai karki damu"
Tace "To shiknn" , nan mukai sallama

Saudat tace wannan daddadan labari ai dole in fadawa yaya, nan take takirashi, saide baya
kusa bai dagaba

Sai wajan 11:30 pm yaga Kiran nata, yace gobe ya kirata yasan yanzu tana tare da mijin ta

Ajiyar zuciya nasauke me nauyi, nakalli Zahra ba tare danace komai ba, Zahra tace " to yanzu

ke bakifijin dadi Bama"

, nace "wallahi naji dadi Zahra,
Nayi missing saudat
Tana sona sosai
Zahra tace mukuma banda mu ba,

nace nina isa nace haka
Aike ce first lady

Karfe uku na dare muka tafi airport, bamuyi awa dayaba muka tashi


Bye bye Sudan

dayake jirgin Ethiopian mukahau

Saida mukayi transit a Adis-ababa, na Tsawon awa biyu, sannan mukahau wani jirgin Zuwa
Nigeria, karfe 11 nasafe, cikin Airport din Malam aminu kano tayi mana








Mrs Usman ce 🖊[5/6, 3:32 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub

Dedicated to my family

51


Bayan mun futo, nayi sallama da Zahra Akan sai munyi waya, mukhtar yace "wai yanzu bazaki
bari azo daukan naki ba?"
Nace "emana dakaina zanje,"

Dan haka yaje yanemomin taxi
Shiya bashi kudin, nan mukai sallama dashi nikuma na shiga sai zaria

Muna sauka a kofar gida, naga gidan ya canja, na futo da mamaki Akan fuska ta, Abba naganin
motar mu ta tsaya yaqara so da sauri, yace
" sannu mamana "
Nace "yauwa Abba,"
Nafadi haka hankali na nakan gidan
Muna qarasawa gate mama tazo ta rungume ni, tana "sannu autata," nace "sannu mama"

Afalo muka zube, nadora kaina Akan cinyar mama inata kallan falon da tsananin mamaki

Mama tace "taso kici abinci kiyi wanka kihuta,"

nace " kai mama barni nagama Jin duminki tukunna," 🤣

saida nahuta Abba yashigo yanamin sannu
Yace " yarinya ki dage ke kadai zaki taho basai munje ba,"

nace "Abba banaso kusha wahala, ai gashi nazo," yace "hakane to Allah yasa angama a sa'ah"
nace

"amin Abba"

Mama na kallah nace
" mama ni banga baby ba, tana ina ne?"
Abba da mama ne suka hada ido lokaci daya


** *** **


Yana juyi Akan kujerar office dinsa, wayarsa na hannun sa yana kallan pictures din baby

Wata folder yabude saida yasa security sannan naga yashiga, pictures dinta ne rututu aciki,
wani da saudat wani ita kadai
Murmushi yasaki yace
" my feenah I luv u"

Hada pic din yayi dana baby, yace afili, " narasa banbanci tsakanin su,
Allah kenan mai hada kama
Saikaga mutum bakasan Shiba baisanka ba, Amma kaga suna mugun kama"
Pic din yashafa yace "ina sanku dukanku"
Ganin pictures din saudat ne yatuna masa da kiranta da baiyi ba
Fita yayi daga cikin folder ya kirata
Bugu daya ta dauka tace

" yaya!!!"
Ahmad yace "sauda karki kashemin kunne Dan Allah"
tana daria tace "yi hakuri yaya, munyi waya da feenah jiya
Shine nakiraka zan fadama Amma ban same kaba"
Ahmad daya tsinci zancan kamar a mafarki yace " me kika ce?" Tace
" yaya serious nayi magana da ita jiya"
Yace "please turomin Number,"

tace "yaya bazaka sametaba,"

"Kituromin nace," yakatse Kiran, ita kuwa batayi musu ba, tatura masa, yana ganin number
yakira
Taqi shiga, yasake kira taqi shiga, haka yayita gwadawa
Daga karshe de yakira saudat yace "meyasa bata shiga ne?"


"Yaya dama fa nafadama bazaka sametaba
nima jiyan tacemin ne tana Sudan kuma Yau Zata dawo Nigeria, Amma idan tasa sim card din
Nigeria Zata kirani"
Cikin mamaki yace
" Sudan kuma?"
Saudat tace "eh haka tacemin, wai tana karatu ne"
Cikin ransa yace "Tome ya kaita Egypt?"

Yace "to shikkenan idan ta kiraki please Kituromin Number,"

sauda tace "wallahi yaya nima na matsu takiranin saboda tacemin wai zamuyi wata muhinmiyar
magana," gaban ahmad yayanke yafadi, bade abinda yafaru Zata fadawa sauda ba

Zancan nata ya katse da cewa " Amma bata yi miki magana taba?"
Sauda cikin murmushi tace "a a batamin ba, da zamuyi sallama nede nace bata tambayeni yaya
ba ko akwai abinda yake faruwa?
Saitacemin karna damu Babu komai"

Wata nannauyar ajiyar zuciya yasauke, yace
" Toshiknn, Amma de tana kiranki Kituromin number karki manta,"

Tace " insha Allah yaya"
Sallama yayi Mata, yafada duniyar tunani, Sudan, Egypt, tana karatu a Sudan, tome ya kaita
Egypt? Duk wannan tambayoyin yana wajan feenah
Muhinmiyar magana, tome Zata fada Mata?
Innalillahi
Gara tunda wuri yadamu saudat Akan tabashi number nan, yabawa feenah hakuri, tayafe masa,

tunma kafin suyi maganar, duk da bashida tabbacin wannan maganar zasuyi


** *** **


"Yanzu mamana menene abun kuka, saboda mun dauki yarinyar nan mun bayar da ita? Nayi
tunanin zamu iya iko dake da abinda yake naki ne
Sannan karki manta duk daran dadewa akwai ranar da zatazo wannan yarinyar tagane ba
mune iyayanta ba
To wannan bawan Allah yana kaunar yarki kamar shine ya haifeta, nafeesa bana tunanin kema
kina Santa kamar yanda yake Santa
Izdihar de tana kano, tana wajan uban gidan ammun ku, idan kinasan ganinta ne kya iya Zuwa
ki ganta 🙆🏻
Kokuma ayi masa waya idan yasamu dama yakawo miki ita ki ganta "

Hawayen idonta ta share tace" Toshiknn Abba Nagode Allah yasa hakane yafi alkhairi"

Abba yace "yauwa mamana, haka nakeso naji, yaron yanada hankali, duk mutumin daya nuna
yanasan Naka ba qaramin masoyinka bane, to nide abinda nakeso dake shine ko bayan raina,
inde ba mahaifin wannan yarinyar ne ya baiyanaba to banaso naji kince ahmad bashine ya haifi
Izdihar ba " Cikin sauri tadago kanta Jin sunan da Abba ya ambata

Ahmad!
Sunan da bazata taba mantawa dashi ba, kuma mutumin dayaci amanarta karshe yaje ya auri
wata, me sunansa ne zasu dauki yarta su bashi

Abba yace" mude mun yarda dashi, Dan haka kema inaso kisawa zuciyar ki salama, kinji ko? "
Nace" to shikkenan Abba,"
Yace" yauwa Allah ya miki albarka," nace" amin "

Daki na shiga, ina kuka ni kadai, Amma abayar da yarinya kyauta, aka sa kirana a fadamin,
Amma aiko husna yaci ace takirani tafadamin
Wayata nadauko zan kirata, kawai ma nafasa

Wanka na shiga, adakin da aka nunamin a matsayin nawa, duk abubuwana suna ciki

Ina futowa awanka, na kwanta da niyyar hutawa nan bacci ya daukeni

Wayar da mama takeyi ne ya tasheni, tace
" gatanan bacci take,"
juyi nayi, nace "mama wace?"

Wayar tabani tayi waje
Nace " hello,"

tace "Allah sarki sis, kina bacci nasa antasheki ko?
Na matsu naji ya kikazo ne"
Nace " anty husna ai fishi nake dake"
Tace "subhanallah, me yake faruwa,"

nace "yanzu har abada baby Amma koki sanar Dani?"
Husna tace " sister bahaka bane, nasan abin da ciwo, tunda nima inada yaran, nasan yin hakan
babu dadi, wallahi shiyasa ma naji tsoron fadamiki"

Nace "to ai shikkenan, Abba yafadamin," tace "kiyi hakuri
, komai mai wucewa ne, kuma hakan shine yafi, idan kikai tunani"
Nace "hakane, aina hakura ma
Ina twins?"

Tace "suna wajan ummi, ga tahir"

Wayar tabashi muka gaisa, yace "irin wannan qin zumunci haka auta, memakon ko kwana biyu
ne ki tsaya kiyi mana"

Nace "kuyi hakuri yaya tahir, wallahi na matsu nazo naga mama ne da baby"
Yace "to ai muma gobe zamuzo ko jibi, kar muyi laifi," nace "a a yaya tahir, kawai ku zauna nima
zanzo, inaso naje naga baby, this week insha Allah zan shigo,"

tahir yace "to shikkenan, da fatan de Babu matsala ko?
Karfa kisa tunanin abin aranki," murmushi nayi nace "babu komai yaya tahir, sai anjima,"

yace "toshkn ki huta lafiya"

Baccin daban komaba kenan, sai kirana suke ta layin mama suna min sannu da Zuwa, daga
karshe ma a cinyar mama na kwanta muka kafa sabuwar fira, sai zance muke munata daria,
kamar babu abinda yake damuna,
Nace "mama wai nikam yaushe Abba yasake mana sabon gina ne?"

Mama tace" ba abbanki ne yayi ba, baban Izdihar ne yayi mana "
Cikin raina nace wai baban Izdihar, ga babanta acan wani waje ga nan Ana liqawa wani ita,
nace" Allah sarki, Allah yasaka da alkhairi"
Abba ma daya shigo yaga nasaki raina saiyaji dadi


** *** **

Awannan rana saida saudat tayi DANA SANI Akan Kiran ahmad datayi, domin kuwa damunta
yayi da jarabar Kiran waya, Ajima kadan yakira ta yace har yanzu bata kiraba?
Saudat tace wlh yaya bata kiraba, nima jira nake, ai tana kira zan turoma insha Allah
Allah Allah yake yasamu number ya kirata, ya matsu yaji muryar ta, lumshe idonsa yayi yace my
feenah, please kikira mana


** *** **


"Momy albishir inkin"
", goro sauda, menene?"
Tanada fara'ah tace
" Momy Yau sis takirani," Momy cikin rashin fahimta tace "wacce sister?"
Saudat cikin shagwaba tace "kai Momy sister feenah fa, budurwar yaya"

Momy cikin mamaki tace "wai wannan qawar taki dakukai karatu?"
Saudat tace " emana" , Momy tace " um Amma nayi miki murna, yanda kika shiga damuwa
dakika rasa number ta,"
Saudat tace "Momy muka shiga de nida yaya" 🤣

Momy cikin mamaki tace "wai kina nufin itace yarinyar dayake so, yace yanemeta yarasa?"
Sauda tace "emana, itace fa Momy"
Momy tace "to ina tashige kuwa duk dadewar nan?"
Saudat tace" wallahi Momy bata qasar ne, karatu takeyi a Sudan," Momy tace" kai alhmdlh
Allah Nagode ma,
Yanzu shi ahmad din yasamu labari? Sunyi magana da ita? "
Saudat tace" ai bamuyi waya da itaba a Nigeria, jiyane fa takirani, tace Yau Zata dawo qasar,
idan tazo Zata kirani inga number ta", Momy tace

"Kai Amma naji dadi wallahi, Allah ya karbi addu'armu Yau

Kice mutumin naki, sai murna," saudat tace "ai Momy Yau kadai ma yakirani yakai sau biyar,
wai takirani? Nace har yanzu de nima jira nake"
Momy tace "to Allah yasa ta kira" , nan sukai sallama


** *** **

Daddare Ammu yakirani awayar mama, yayimin sannu da Zuwa, yace yakira number ta taqi
shiga, nace wallahi ban dora layin bane
Yace to insa zai turo min kati yanzu, godia nayi masa gamida saka sim card din nawa

Aikuwa ya turo katin 1k, nakira shi nayi masa godia

Ina kwance adakina, da daddare, nakira layin Zahra, Allah yatemakeni nasameta, tace shine
tun dadewa kikaqi dora sim card dinki, sai nemanki nake, nace "yi hakuri Zahra, wallahi bana
cikin kwanciyar hankali nane"
Zahra tace "subhanallah me yake faruwa?"
Nan take nabata labarin abinda yafaru game da baby
Tace "anbada ita, abun kamar almara, Amma nikam banji dadi ba, saide ta wani Fannin kuma
sunada gaskya," nace " hakane"
Tace "to kiyi hakuri feenah, haka Allah ya tsara mana, yanzu yaushe zakizo kiga babyn?"
Nace "cikin satin nan zanzo Zahra"
Tace to saikin zo, Allah yakawo ki lafiya, nace "amin Zahra Nagode ''


** *** **

Da asuba mama tajira taji shiru shiru bataji motsin tashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login