Showing 12001 words to 15000 words out of 113548 words

Chapter 5 - DANA SANI BY AMNAH EL YAQOUB .pdf

Advertisement

03 Apr 2025

9423

akansa,"

"Da gaske kike farin cikina?"

"Serious abin alfahrina"

"Gaskiya naji dadi nagode, zanyiwa yaya magana Yau, duk yanda mukai dashi zakiji,"
haka sukaci Gaba da firarsu ta masoya.

Asuba tagari maimunan Ammu.

** *** **

Dif takashe datar ta, Ahmad yana jiran amsa yaji shirun yayi yawa, kawai yana dubawa yaga
wayam Babu feenah Babu alamarta, kansa ne yasara, badai yarinyar nan bata sansa ba,
innalillahi, yanzu ya zaiyi, dama hakane yanzu shida yake qin wasu shine, shima ake gudunsa,
bai Gama tunanin saba yaji dumi akumatunsa, hannunsa yakai wajan
"hawaye?"

Shine abinda ya furta da bakinsa, shi wallahi ko durqusa mata sai yayi, inde Zata so shin,
Agogo yakalla yaga 12:45 bai tsaya shawara da zuciyarsa ba, kawai ya kirata, saide kuma harta
gama ringing bata amsaba,
Shikkenan hasashe na yazama Gaskiya,

"Nafeesa bata sona,"

yafada abaiyane,
Dama nasan tana kulani ne saboda qawarta saudat
Kwallar idonsa ya share,

"wallahi saina sake kira"🤣
yasake fada abaiyane, shi kadai adaki sai sunbatu yake

Acan bangarenta kuwa duk ta rikice, tayaya wannan Dan gayun zaice yana Santa ta yarda,
anya kuwa ahmad ba yaudarar ta yake ba? Amma ace mutum mai aji, da kudi da gayu kamarsa
har yana kiranta bayan kuma taga abinda yace, yanzu menene mafita, yaya zatayi dashi?
Wani bangare na zuciyarta yana masa kwadayinsa sbd ahmad yayi Babu qarya, saide wani
sashen kuma yana fada Mata yafi karfinta karta jawa kanta abinda yafi karfinta itada iyayenta
Saide maganar da saudat tafada Mata data tuna da ita sai taji bazata iya kyale ahmad dinba
Amma dole zai bata lokaci tayi tunani

Wayar tasa aqasan fillo, tayi addu'ah ta kwanta, saide tana rufe idonta qarar wayarta yasake
tashin ta
Hannu tasa ta dauko, tana dubawa kuwa ahmad ne, samun kanta tayi da amsawa tunda tariga
ta yankewa kanta mafita,

"feenaaah"

ya kirata gamida Jan sunan nata

"Na'am yaya,"
kayi hakuri naga kiranka bana kusa da wayar ne

"a a feenah, ban yarda ba"

"feenah "
yasake Kiran sunana, na amsa

" feenah bakya sonako? "
Nace "a a"

" to meyasa kika sauka a chatting Babu amsa Babu sallama bayan ba haka kika sabar min ba?"

Nide nayi shiru inajinsa yana magana a hankali cikin nutsuwa badan dare neba nima nasan ba
lalle naji komai ba
Nace "yaya bahaka bane kayi hakuri"

"Shikkenan anyi miki afwa, Amma pls yanzu fadamin yaya kike jina a zuciyarki?"

Saida nayi Jim sannan nace "kamar yanda nakejin saudat mana,"

yace "um um, niba wannan nake nufi ba, kema kinsan me nake nufi,
"Feenaaah" yasake Kiran sunana
"Na'am yaya,"

"Feenah kinaso namiki kuka?"
Nace "kuka kuma yaya,?"

"Emana tunda bakya sonaba, nafeesa tunda nake bantajin nakamu dasan wata yarinya lokaci
dayaba sai akanki, pls kisoni feenah Dan Allah kinji
Yaqarasa maganar cike da shagwaba ni sai yabani mamaki ma," ganin yanda yake magana
cike da shagwaba
Nace "yaya to kabani lokaci zanyi tunani,"
Yace" nide um um yanzu nakeso naji, "

nace" yaya.....

Yayi saurin tarar numfashi na "pls karki ce komai haba feenah ki yarda Dani, kinji, zan kasance
mai rike miki amanar soyaiyar mu, "alaikillah quli anti tuhibbuni" (Dan Allah kice kina sona) "

Kinji feenah ta pls, yafada kamar zaiyi kuka, nace masa" Shikkenan yaya na amince, "

" Alhmdlh to fadamin"

"ina sonka"

Lokacin datace tana sansa baisan lokacin daya lumshe idonsa ba, "nima ina sanki matata

Murmushi nayi kawai," yaushe zaki kwanta?"
Nace" yanzu"

, "to da fatan de kinyi addu'ah muradina,"

“nayi mana, "

" Toshiknn nikam banyi ba, ko zakizo kimin, "

rufe idona nayi da hannu na, nace" Toshiknn kasa aranka nice nake yima yaya "

" OK baby toki kulamin da kanki kinji "

" Insha Allah yaya."

" Oya to rufe idonki pls karki kashe, "

" Narufe yaya"

saukar kiss naji Akan kunne na Dif ya kashe wayar
Yabarni da waya a hannu, wayar nabi da kallo tamkar yana gabana karshe na rufe idona cikeda
nishadi, sai alokacin na farga da lokaci 1:28, tuni nasake addu'ah na kwanta.

"Oh ni rabi'atu yaran zamani saiku kwanta da wuta qwal akanku bazaku kashe ba, ke nafi nafi,
dake nakefa, inajinta nayi shiru, cande nayi juyi nace" kaka menene kuma,"
" sallah zanyi naga wutar taki akunne, ke bakya tsoron kwana da jinnu ne", nace "haba kaka
fadi alkhairi kokai shiru, haka a kace,"

"to naji kinga tafiyata, gara inyi sallah indanyi lazimi tun karfe tara inata zuba bacci," nima wutar
na kashe na kwanta

** *** **

Bayan sati daya, kwance suke adaki suna firar duniya, ya kalleta yace" maman yara yakamata
fa a yiwa auta qani, ko qanwa, "
Murmushi tayi" haba Abban husna, yanzu duk tsawon wannan shekarun ai yakamata ace mun
hakura "

" A a maman nafeesa karki sake fadar haka, ai bawa baya yankewa kansa rahmar Allah, nide
har gobe inde yara daga wajanki ne to ina maraba dasu, saide inkece bakya maraba Dani "

" Haba Abban husna kaimafa cewa kayi auta, to tayaya za'a yi Mata qani "

" Kinga wannan duk maganr ku ce hausawa nide nariga nafada miki inason yara "







Mrs usman ce🖊
[5/6, 3:32 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: 🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family



15





"To kayi hakuri Abban husna, ai abin bana zafi bane, duk ka daga hankalin ka"

" to ai kedin ce naga alama nema kike ki sande,"
"to alhaji Allah yabamu nagari,"

"yauwa kokefa."



** *** **


After 2 months, a wannan lkcin soyaiyar ahmad tayimin mugun kamu, har banajin zan iya auren
wani bayan shi, banga abinda zai nema in hanashi ba inde ban sabawa addini naba, koda
yaushe muna liqe awaya, haka a chting dinma ba banza ba, sosai ya koyamin yanda zan soshi,
ta yanda bazan iya mai musu ba, haka shima idan muna waya tamkar bawana yake zama.

** *** **



Wayarta ce tayi ringing, tana kallan wayar, wannan ne kira na hudu, dakyar de ta amsa, tana
wani yauqi, iklima Kenan 'ya awajan mai bawa gwamnan katsina shawara🤣, kai tsaye tace
"doctor ya akayi,"

"Haba iklima sau nawa ina kiranki, baki amsaba, meyasa ke bakya bani time dinane, kamar kin
manta da soyaiyar da mukayi, iklima kema kinsan irin soyaiyar danake miki, a school fa har
sha'awarmu ake"

" dakata doctor tahir, yanzu menene laifi na saboda ban amsa wayarka ba,? So kake infatse
abubuwan dasuke gabana inqare akanka?
Sannan Bama wannan ba, iklimar da daban ta yanzu daban, a yanda nake jina kam, na wuce
ajin doctor, saide matar governor, rayuwar school dakake magana, kawai nasoka ne saboda ka
taimakamin kuma kagama, Dan haka banda case dakai, dif takashe wayar ta"

Daskarewa doctor tahir yayi awajan, baisan lokacin da wayar ta fadi qasa ba, nan take ta
tarwatse.



** *** **


"My feenah yaushe zaki bani dama inzo inga wannan kyakykyawar fuskar taki ne?"

"Karka damu my ahmad nabaka dama koda yaushe zaka iya Zuwa"

"serious?"

"My ahmad kenan da gske nake"

"Toshikkenan zaki ganni very soon,"
sukai sallama

Number tahir yake kira Amma akashe, to me yake damun wannan gayen shida baya rufe waya,
cigaba yayi da nemansa ganin yakasa samun sa saiya yanke shawarar Zuwa office din nasa,
domin yafada masa yazama ready zai kai shi su gaisa da gimbiyarsa feenah.

Asbitin tahir din yanufa, dayake yanada hospital nasa nakansa, halinda yatarar da abokin nasa
aciki yayi bala'in daga masa hankali, tahir yagani kwance shame shame Babu alamar numfashi
atare dashi
Acan cikin asbitin kuwa marasa lafiya suna ta jiransa wanda shi zai dubasu da kansa
duk suna tunanin yana wani uzirinne, shiyasa bai futo ba, ahmad Gaba daya ya rude Yama rasa
ya zaiyi, fita yayi daga office din, saura kadan suyi Karo shida wata nurse, anan yayi Mata
bayani ta kira wani likitan aka kai shi wani Dakin, aka fara bashi temakon gaggawa

Bayan wani lokaci ya farfado, ruwan da aka qara masa ya kallah, yajuya ya kalli ahmad dake
zaune agefensa, ya share qwallar idonsa, "ahmad shikkenan iklima ta gujeni bansan Mena
mataba ta gujeni, iklima tacemin bazata iya aure naba, shikkenan yanzu burin hajiya bazai
cikaba, bazata ga jikokinta ba, Haba, haba iklima Mena miki meyasa zaki gujeni alokacin da ni nafi buqatar ki a kusa Dani,
Mena miki iklima,"
yana magana yana hawaye abin tausayi

Ganin abin nasa zai zama kamar sambatu ahmad yatashi yakira wani doctor yazo yayi masa
allurar bacci, yana fita daga Dakin, office din tahir ya nufa, Yau saide ayi abinda za'a yi, Amma
saiyaci mutuncin iklima, saita gane kuranta, saide yana Zuwa office din yaga wayar a tarwatse,
haka ya hakura Dan kansa yace Allah yasaka Maka abokina, insha Allah, Ubangiji zaiyima zabi
da mafi alkhairi wadda tafi iklima

Dakin yakoma ya zauna yana jiran farfadowar tahir
Yakusa awa daya yana zaman jiransa, sannan yafarka, saide ba magana yana kallan silin
Dakin, yayi shiru, ahmad ne ya dinga kwantar masa da hankali da dadadan kalamai,
"man bazaka ganeba, ni tun farko nayi tunanin wannan Zata kasance, dole nasan iklima akwai
abinda ta taka shiyasa take wulakanta ni, Amma Babu komai Dan kanta, rayuwa ce, ba
governor ba, ta auri shugaban qasa ma,🤣 ahmad baisan sanda ya kwashe da dariya ba yace"
baba buhari fa kenan"
"yes" inji tahir

"Ahmad kaga idan bazaka bani hakuri ba Dan Allah ka tashi katafi kabarni da abinda nakeji
araina," ganin serious yake maganar hakan yasa ahmad ya daina dariyar yace," yanzu menene
mafita?"

Tahir yace" damuwa ta dayace ahmad ummi ta matsa insami mace inyi aure, Sanin kanka ne ni
kadai suka mallaka, yanzu haka jiyan suka zaunar Dani Akan inyiwa yarinyar danace musu
inaso magana, zasu tura ayi maganar auren mu, yanzu ya zanyi? Yaya take so nayi Dan Allah,
meyasa tun farko bazata fadamin Ba? "
"Ahmad yaja dogon numfashi yace" karka damu abokina nasan yanda za'a yi, matso kaji, "

Tahir ya matsa, ahmad yayi masa rada akunne, dagowa yayi,
" Kana ganin hakan zai iyu?"

" Mai zai hana, ta so muje wajan ummin ni zanyi Mata bayanin komai. "





Mrs Usman ce 🖊





🌱DANA SANI 🌱

Writing by Amnah el yaqoub


Dedicated to my family



16




"Oh ni rabi'atu, yar nan tun dazu kike ta kwalliya kamar zakije wajan zabar sarauniya,"

"hmm kaka kenan, ai wannan ba kwalliya nakeba, kawai gyaran fuska nake,"

kaka tace "ahakan?" "Emana kaka,"

"To yanzu nafi ina zakije,"
"Kaka baqi fa zanyi,"

"au to to to, to jikanane ne zaizo?"
"Kai kaka yan makarantar mu nefa zasuzo,"
"Bawani nan munafuka, ai zanji zan gani, kinga mayafina ma nadauka zani unguwa, Amma
nafasa sai naga qwaqwaf," 🤣

"Ke kaka ashe kin koma sa'ido bansaniba?"

"Tun yaushe, tun yaushe nafi, ainajima a wannan halin
Tunda ki kazo gidan nan baki taba irin wannan caba adoba, tayaya Yau zakiyi, sannan kicemin
wai qawanki ne zasuzo nayarda, kema kinsan ba wannan mgnr nafi"

Fari nayi da idona, nace" to kaka zauna wallahi, inkin gaji da kanki zaki tafi, zakice nabaki
labari"


"Aiba inda zanima nafi"


** *** **


Ahmad na hango ya rike tahir suna tafiya dakyar, tahir ya dora kansa Akan kafadar ahmad suna
tafe dakyar, me gadi yana ganinsu, ya matso "sannu alhaji, sannu, ba shida lafiya ne?"

"Eh"
kawai ahmad yace suka qaraso cikin qayataccen falon gidan, wanda yaji kujeru na alfarma,
ummi na hango a zaune ta zubawa TV ido tana kallah hankalinta kwance

Bayan sunje wajan ummi ahmad ne yayi Mata bayani, da yanda yasa meshi a office dinsa, da
kuma dokar likita na adena takura masa Akan tunani, (duk wannan shirin ahmad ne) haka ta
dinga sababi, wai wata shegiya zatayi Mata sanadin ran danta, daga karshe de tace zatayi
masa addu'ah Allah yabashi mace ta gari, ta San da iklima dinma ya aura bazata haifi da mai
idoba, shi tahir kawai yana jinta ne Amma baya tunanin zai qara San wata yarinya kamar yanda
yaso iklima

Daga karshe tace "to Allah yasawaqe kamashi, ahmad kuje daki,"
tahir kuwa sake langabewa yayi, saida tataso da kanta ta rike hannu a kaje da kinsa aka
kwantar dashi
Dakin yayi kyau komai neat, black and white komai, sosai Dakin ya yi kyau
Saida ahmad yaqara Jan kunnansa Akan yarage tunani sannan yatafi

Tafiya yake yana so yaje gida ya shirya, yana so yaje yaga babynsa tunda shide tahir Zuwa
bazai iyu dashi ba
Wani super market yashiga yana so ya siya Mata koda ice-cream da chocolate ne
Shigarsa keda wuya kawai daga siyan chocolate saiya wuce wajan perfumes

Wani turare yagani mai kyau na Mata aqallah kudin sa zaiyi 50k yakai hannu zai dauka itama ta
dora nata hannun, dasauri ya janye hannun sa, ya kalleta, mace ce aqallah zatayi 28 year's,

murmushi tayi masa tace "sorry fa,"

"no problem" yace
Yabar Mata turaren aikuwa tasa hannu tadau ka, memakon taga yadauki yadauki wani irinsa
kawai sai taga yadauki Dan 95k yasa akwando yayi Gaba ko a jikinsa

Murmushi tasaki tabbas nasamu wanda ya dace da rayuwa ta, yana gama abinda yake yaje
yabada ATM dinsa suka cire kudin su yayi gaba
Motorsa yashiga ya dau hanyar gida

Har gate man ya Bude masa, tana kallansa harya shige sannan tasake sakin wani murmushin
tayi rebus Takoma gida

Wanka yadauka yayi shigar manyan kaya, yadi yasaka fari mai ratsin ash color, sosai yayi kyau
bema shiga ta wajan su momy ba kawai wucewa yayi

Yana tafiya amota suna waya, shida ita, saida yazo har kofar gidan sannan yace ta futo, mayafi
ta yafa ta fice, kaka ta bita da kallo, tun kafin taqaraso ya zuba Mata shanyaiyun idanunsa, yana
cikin mota,
Saida ta qaraso sannan yabude ya futo wani qamshi ya bugeta, ta lumshe idonta, shikuwa
yasamu abin kallo yayi shiru yana kallanta, firgigit ta dago kanta aikuwa suka hada ido
Tayi murmushi ta sunkuyar da idonta
"my feenah yakike ya missing dina?"

"Bayan tun dazu inata jiran ka shine ka shanyani,"
"sorry feenah abokinane baida lafiya, aina fada miki da tare dashi zamuzo tahir, Amma kuma
hakan bai samu ba,"
nace" ayya to Allah ya bashi lafiya "
Yace" amin
Danma likita ne yasan yanda zai kula da kansa," nace" au doctor ne?"

Yace" babba ma kuwa,"

" Allah yabashi lpy, "

" amin my feenah"

"Muje kimin iso na gaida kakarmu ko"

"ok"

kawai nace
Gaba nashiga, yana Bina abaya, Gaba daya ya shagala da kallan yanda nake tafiya, duk natafi

da imaninsa
Kawar da wannan tunanin yayi sbd agaskiya baida burin daya wuce suyi aure ba tare da komai
ya gifta ta tsakanin suba, yaqi jinin zina haka yana Allah wadai da masu aikatata

Kaka Ana zaune akujera yar tsugunno sai ganinsu tayi, kallan mamaki take masa, saida ya
tsugunna har qasa ya gaisheta sannan tace" Dan nan ban wayekaba,"
yayi murmushi baice komai ba, kasancewarsa bamai yawan maganaba
Feenah ce tace" kaka yayan saudat nefa, "

Sannan kaka a kace" au to, yanzu naji batu,yasu sauden yaro? "

Oh ya Allah feenah tafada da karfi tare da dafe kanta 🤦🏻â€â™€


" to menene zaki fara iyayin naki, menene laifi dannace saude yaro,".

ahmad yayi murmushi yace" Babu komai kaka,"
" Yauwa kokaifa, yaya sunanka ne?"
" Sunana Ahmad Muhd marzuq kaka, "

" Oh Allah sarki amadu, (kawai sai kaka tafara kuka) amadu anacan karkashin qasa
Yaro ai sunan majina kaci, shima haka yake akwai shi da fara'ah
Allah yaji kanka amadu tafada tana goge hawaye, "
ahmad yace" amin kaka Allah yaji kansa, "

Dago kai tayi ta kalli feenah tace" nafi ko shine wanda kika cemin kwanaki yanada kyau?"🤣 🤣

" Wayyo kaka bashi bane "
Tabe baki kaka tayi," ke kika sani "

Tashi yayi zai fita Yabar wa kaka kudi masu yawa, feenah tabi bayansa suka tafi
Ajikin mota sukai ta firarsu daga karshe yace yagaji dole sai ciki suka koma, Gaba daya
yagama kashe Mata jiki da sanyaiyar muryarsa

" Nafeesa tah"

yakira sunan ta, kafin ta amsa yaci Gaba da cewa "nafeesa ina kaunar ki, inaso Allah ya
mallakamin ke ki dinga haifa min yara masu matukar kama dake,"

"Nafeesa," yasake Kiran sunana, kafin in amsa yaci Gaba da fadin" a koda yaushe idan na
daga kai na kalli sama sai inganta cike take da taurari masu matukar haske, Amma haske mafi
mafi haskaka kyawun fuska da yaye duhun zuciyata yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login