Showing 30001 words to 33000 words out of 113548 words
** *** **
" Salamu Alaikum,"
" wa'alaikumus Salam, "
" a a adamu kaine agidan namu Yau, "
" eh wlh nine mama, yagida, "
" lafiya kalau adamu, ya su aisha mutanan Uganda,"
"wallahi aisha tana can karatu yafara nisa,"
"to Allah ya temaka,"
"amin mama,"
Daga murya tayi tace" nafi, nafi, "
" Na'am kaka, gani nan,"
" zoki karbo wa adamu ruwa yi sauri, "
futo wa nayi da hijabi a hannu na, nace" baba ina wuni "
yace" lafiya kalau nafeesa ya karatu,"
" alhmdlh baba jibi ma zamu fara jarabawar karshe, "
" to Allah ya temaka,"
" amin baba "
Kaka tace" yi sauri mana nafi, "
" Ka ganta nan batajin dadi ne kwana biyu, "
baba adamu yace" kaiya, haba mama aida kin kyaleta, dawo ki zauna nafeesa Allah yasawaqe"
" amin baba,"
nakoma daki
Baba adamu yace "mama dama munyi magana da baban husna ne, Akan zamanki agidan nan,
da yace kikoma can zaria kokuma ki dawo gida na da zama, muna so zamuyi wa gidan naki
gyara,"
Kaka tace "gyara kuma adamu me yasamu gidan nawa,"
baba adamu yace "mama ai muna so ne a maida miki shi na zamani"
Kaka ta fashe da kuka tace "adamu Allah yasaka muku da alkhairi, na gode na gode adamu,
shima mu'azun zanyi masa godiya,"
baba adamu yace "haba mama ai mun daukeki tamkar mahaifiyar mu, Babu komai," tace "to
ngd kawai zan dawo gidan Naka, basai naje zaria ba," yace "to nima hakan Naso dama, to Dan
inji ra'ayinki shiyasa nabaki zabi," haka
kaka ta dinga godiya ga surukan nata, mutanan kwarai
** *** **
Gumi ne yagama wanke masa fuska ganin irin illar da maganin yake dashi, sosai ansa maganin
dayawa acikin just din, kuma ko waye yayi hakan da mugunta, domin kuwa Babu marar imanin
dazai aika ta haka, dama yasan wannan al'amarin akwai sa hannun wani aciki, sannan bayan
haka qwayar tanada hatsari sosai, Amma bazai tabbatar da shin ahmad din yasamu abinda
yake tunanin ba, saide idan yayi aure ne zai tabbatar, zubar da lemon yayi, Yabar asbitin yayi
gidansu ahmad din
** *** **
Duk suna zaune inda suke da, saide saudat da hand out ahannunta tana dubawa, tahir yayi
sallama yashigo, shi kanshi sun bashi tausayi, gaskya suna kaunar ahmad dayawa, wai nan
zazzabi ma kenan an zauna anyi jugum inaga sun San gaskiyar abinda yafaru kuma.
Abinci yagama ci dama, Dan haka yabashi magunguna da qarin ruwa,sannan su Momy suka
fita suka barshi ya huta,
Ahmad ya kalli tahir yace" kai Malam nifa na warke kawai idan na tuna abinda yafaru ne banajin
duniyar tanamin dadi "
Tahir yace" dole kacire abin nan aranka, kar hawan jini ya kamaka,"
ahmad yace" hakane insha Allah zan kiyaye dahiru, "
harararsa tahir yayi
Ahmad yace" toba dahirun bane, dahirun ummi "
Tahir kallansa yayi, yana murmushi yace" nawan har naji dadi wallahi daka warware "
Ahmad yace" toya zanyi tahir Allah yadoramin abinda dole saide inyi hakuri in karbi kaddarata,
Amma kuma fa yarinyar tayi, tayi, ba karya akwai zaqi, í ½í¹ˆwallahi tana kukan nan banma San
me take fadaba, "
tahir ne yakai masa duka, yace" Allah mutumina,"
ahmad yana murmushi gamida hawaye yace" serious tahir, gaskya yanayin akwai dadi "
Tahir yace" muma de zamu dage mu yi auren muji yaya akeji, "
ahmad yace" gaskya kam, nima zan nemi yafiyar nafeesa ne kawai inta amince ayi mana auren
mu, "
tahir yace" why not"
Ahmad yace "yauwa ya mgnr abin nan,"
anan tahir yafada masa komai ahmad yace" acikin gidan nan ina zaune ake wannan qulla qullar
lalle kuwa zan bincika, akwai rikici "
Tahir yace" kaide kabi komai a sannu insha Allah komai zai warware, "
" Hakane, "
inji ahmad
" Yawwaa Tahir ya maganar babyn ka din nan, dakake tunani, "
Tahir yace" ina tunani ahmad kana jinya, so nake ka warke saina kirata infada Mata "
Ahmad yace" no kakira ta Yau inka koma gida, ka tsarata sosai yanda bazata qi amincewa ba,"
" Toshiknn" inji Tahir
Ahmad wayarsa ya janyo gabansa na faduwa, yayi dialing number feenah, gara yakirata inma
zaginsa zatayi kawai tayi inzata huce
Saide kuma wayar akashe, dole saide idan ruwan yakare yaje ya nemeta agida, Allah sarki
rayuwa su kuma haka tasu kaddarar take
Wayar ya cillar gefe, Tahir yayi masa allurar bacci yace yakamata ya huta, shikuma yakoma
bakin aikinsa
Saudat ce tanata shiri Zata je wajan feenah, tunda batazo Dan ziyara ba aitazo Dan jinyar yaya,
Momy ce tashigo Dakin tace "kekuma ina zaki,"
saudat tace "Momy nayi ta Kiran wayar sister feenah ne, inasan magana da ita Amma wayar
akashe shine nakeso inje inga ko lafiya,"
Momy tace "saudat rigima, banda abinki ai jibi zaku shiga exam
Dole zaku hadu, kiyi hakuri nasan insha Allah tana lafiya, kiyi karatu dakyau, idan Baku haduba
Zuwa jibin daga school dinma saiki wuce, Amma yanzu de kije ki kula da brother dinki,"
"Toshiknn Momy"
** *** **
Bayan kwana biyu ahmad ya warke sosai, saide Gaba day ba shida walwala, Gaba dayansa ya
canja, shiru shiru Babu magana, yayinda feenah sun Dade da fara exam, inda tabawa saudat
uzurin cewa batada lafiya ne, shiyasa kuma ga exam agabansu ta karshe shiyasa ta kashe
Wayarta, haka saudat ta hakura badan ranta ya soba, a bangaren feenah kuwa ita kanta saudat
din haushinta takeji í ½í¹Ší ¾í´£
Ahmad yashiga Hali na wahala kullum cikin tunani ga tafiyarsa Cairo na matsowa ga shi yana
so ya gyara tsakanin sa da feenah, Amma taqi bashi damar hakan
Kullum saiyaje kofar gidansu, haka kullum sai ance masa bata nan, kaka tayi tambayar duniya
Akan su waye suke kiranta tace kawai samarin unguwa ne, wanda ita feenah tasan ahmad ne,
Akwai lokacin da kaka tace Mata taje ta duba ko yayan saudat ne, Amma qememe feenah tace
ai suna waya dashi bashi bane haka kaka ta hakura
** *** **
Gidan yashigo ransa abace yayi part din Momy tadaga kai ta kalleshi tace "waladeey lafiya
kuwa?"
Yace "Momy lokacin danayi rashin lafiyar nan waye yashiga part dinane?" Tace "gaskya Babu,
kasan saudat tana karatun exam so bata shiga mabaruka kuma kasan dama akwai kasala
saudat tafi ta gyaran, bana tunanin tashiga,"
"OK" kawai yace yatashi yafuta fuuuu
Momy tabishi da kallan mamaki, tome aka masa?
Main falo yadawo yana kwalawa walaya kira," walaya! Walaya!! Walaya!!!"
Yasan cewa tana aiki afalo sosai may be zatasan wayashiga
Kai tsaye yace "Mata wakika ga yashiga part dina kwanaki acikin yaran gidan nan?"
Lokaci daya ta firgita da Jin furucin sa, har ahmad yaso yayi tunanin wani Abu, cikin duburcewa
tace "wal..... Walla... Wallahi bansaniba ba," baice komai ba yajuya yayi wajan baba maigadi, ai
walaya tana ganin yatafi wajan baba maigadi damm gabanta yayi wani irin faduwa, nan take ta
dora hannun ta aka í ½í¹†í ¼í¿»
Mrs Usman ce í ½í¶Š
[5/6, 3:32 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: í ¼í¼±DANA SANI í ¼í¼±
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to my family
25
Tana shiga gida Dakin ta ta wuce ta dinga kuka, Bama wannan ne abin damuwar ba, yanda
takasa cireshi acikin ranta, gaskiya so masifa ne, ta tabbata yanzu shi yana cikin kwanciyar
hankali, kaka ce take Jin sauti kamar na kuka, ta futo, tana daga labulan Dakin tace "ah nafi
ashe kin dawo, menene kuma abin kuka? Dama rabuwa da abokai ai tazama dole, nima haka zaki tafi ki barni nafi nasaba dake agidan
nan" kaka takarashe maganar tana kuka
Haka suka rungume Juna suna kuka itada kaka Babu mai rarrashin wani
Kwanana uku a kano, nayi shirin tafiya zaria, banajin kuma zan qara waiwaitar wannan Garin,
danma na taya kaka hada kayanta dazata koma gidansu aysha
** *** **
"Husna najima ina bin kanki Akan ki bani dama na shiga cikin zuciyarki, Amma hakan yaqi
samuwa ko?"
Husna tace "bahaka bane doctor kawai nayi tunani ne" yace "to me tunanin naki yabaki?"
Tace "nabaka"
Tahir yace "mefa?"
Tace "zuciyata" dif taka she wayar
Wayarsa yarike ahannunsa yana murmushi shi kadai
** *** **
"Wlh khadijaty haka mukai dashi,"
khadija tace "gaskya mutumin nan ya yanke mu, ashe dama yana ciki shine yake ta wani cin
magani," husna tace" aini abin yabani mamaki da farko, Amma bakiji yanda yake min magiya ba
Akan na aure shi," khadijaty tace" wlh ki amince, "
nace" ai nafada masa na amince, "daria suka saki Gaba dayansu suka tafa
** *** **
Aguje nafada kan mama ina mamaaaa! Da karfi, kai ta dafe tace" auta bansan yaushe zakiyi
hankali ba, "
baki naturo nace" kai nayi missing dinku fa," tace" to dagani banajin dadi, "
tashi nayi nahau cire kayana agabanta
Tace" wai nikam haka kikewa maman ma acan kano din? "
Nace" kai mama ai kaka Babu ruwanta Dani, abinda nakeso nake yi wlh, bana aiki sosai, "
tace" to shige daki ki shirya "
Nace" wai sister bata dawo ba har yanzu," mama tace" ai sai wajan yamma,"
jakata naja nayi daki, bayan nagama shiryawa nayi wanka na futo falo na kwanta Akan kujera
nadora kaina Akan cinyar mama
Tace" to ya karatun"
" nace wlh mama karatu mun barshi sai jiran results dinmu kuma,"
tace "to Allah yasa a dace" nace "amin"
Mungama cin abinci kenan husna ta dawo aikuwa da ihun murna muka dane Juna, mama
kawai kallanmu take tace" Allah ya shiryeku," aifa nan aka baje sabuwar hira, ina bata labari
tana bani anan take fadamin labarin ta da doctor tahir, nace" wlh ki amince" tace "ai na yarda
muna gaisawa de kadan kadan, ta waya," nace "to sister nunamin pic dinsa" tace "bai turomin
ba saboda Bama chting Amma zanyi mai magana ya turomin saina tura miki," nace "to"
** *** **
"Guy kaje ka zauna, please ka dawo mana,"
ahmad yace "wlh wannan tsohon ne yarikeni tahir, Amma jibi zan dawo,"
Doctor tahir yace "yauwa kokaifa, munyi missing Naka," ahmad yace "wlh nima haka, ga kuma
feenah datake raina inaso inzo in bata hakuri Akan abinda yafaru"
Tahir yace "eh gaskya ne nima maje Gaba dayanmu in tayaka bata hakuri," ahmad yace.
"Amma naji dadi sosai nawan," tahir yace "karka damu,"
"Friend ya maganar babynka ne?"
Murmushi tahir yayi yace" husna, tana nan acikin zuciyata, dazu muka Gama waya," ahmad
yace" harka gyaro ta kenan, "suka sa daria Gaba dayansu, ahmad ne ya kwaikwayi maganar
tahir yace"
Ahmad iklima, iklima tabarni ahmad wlh ina sonki iklima, "í ¾í´£ katse wayar tahir yayi
** *** **
" Mamana, "
" na'am daddy, "
" nasan ke mai biyayya ce, kuma nasan duk abinda zan fada miki bazaki qi yimin biyayya ba,"
tace" hakane daddy,"
" to munyi magana da Dan abokina, muna so mu hadaku aure nanda 3 months,"
gaban saudat ne yafadi cikin rawar murya tace" to daddy,". yace " yauwa, Allah ya miki albarka
Zaizo ku daidai ta sunansa farouq, "
" to daddy nagode,"
yace" tashi ki tafi "
Daki Takoma ta dinga kuka, Wayarta ta janyo ta kira feenah saide wayar akashe, tun lokacin da
abin nan yafaru kwata kwata ma wayar tafita daga ranta
Momy ce ta shigo tace " sauda, haba kiyi hakuri mana, idan yazo inbai miki ba kawai kiyi
rejecting dinsa ni sai nayiwa daddynku bayani, a hankali, shi dama abinda yake so shine ayi
bikin kafin su fara zabe,"
"to Momy nagode,"
tafada jikinta tana kuka
** *** ***
One month later
"Feenah, feenah, tashi kiyi sallah mana,"
"kai anty husna ke akwai damu,"
nayi juyi naci Gaba da bacci na, kyaleni tayi taje tayi alwala tayi sallah, da taga de banda niyyar
tashi, ta dakamin duka, na tashi ina goge idona, tace "ke miye haka, tun dazu ina tashin ki
sallah sai wani magagin bacci kike min,"
baki naturo Gaba, na tashi nayi toilet
Bayan sati daya, su husna sun Gama school, haka soyaiyar su da doctor sai abinda yaqaru
koda yaushe suna cikin waya, suna kaunar junansu sosai harma da alkawarin aure atsakani
** *** **
Farouq yazo yaga saudat, baida matsala, haka kuma yanada hakuri, hakanne ma yasa ta
amince, yana zaune a Abuja, Dan haka aka ci Gaba da shirin biki, ya rage saura 2 month's
** *** **
Yayi zurfi cikin tunanin mafita, Gaba daya bayajin dadin wannan aikin dama Garin baki daya,
yaje yaje yaje harba adadi, karshe ma ance masa kaka tabar gidan, wayar feenah akashe tun
lokacin da wannan matsalar tafaru, Gaba daya yadawo wani shiru shiru
Saudat ce tafado masa arai,
Daga murya yayi yana kiranta, ta futo "
Yaya gani,"
wayarsa ya miqa Mata, tace "yaya bangane ba,"
Yace "sakamin Num feenah, kokuma number da kikasan zan same ta idan naje zaria"
Saudat tace "wallahi yaya bansaniba,"
mamaki shinfide kan fuskar sa yace "bangane ba, kamarya baki sani ba?"
Tace "wlh yaya nima kaina nema nake,"
yace "toko zamuje zaria din mu dubata,"
saudat tace "yaya to zaria ina?
Ina zamu nufa? Sannan ko jiya nadau mota naje gidan kaka an tabbatar min tariga da tatashi
agidan, ni maganar bikinama nakeso nasanar Mata,"
alama yamata da hannu Akan tatafi, karta qara masa wata damuwar
** *** **
"Mama ga maganin naki fa da doctor yabayar nasan baki shaba,"
"wlh husna banasan maganin qarin jinin nan banajin dadinsa,"
"to mama kiyi hakuri kisha,"
"to bani nasha, tashi kiramin autata tazo ta dora abinci,"
"yanzu mama saura 7 months ki haihu,Amma kina ce Mata auta,"
mama tace "husna gidanku, kunji yarinya ke har wani lissafi ma kike, tashi kiramin ita"
Daki tashiga zaton ta, karatun novel nake, Amma sai taga sabanin haka, bacci na nake
shararawa haiqam, kallo na tayi da mamaki, aranta tace Tome yake damun yarinyar nan, tashi
na tashiga yi, dakyar na tashi, ina tashi na shaqi qamshin turaren ta, aikuwa da gudu nayi toilet
na dinga shara amai, husna tabini da kallo gabanta yana faduwa Ina futowa tabini da kallo, nace "sister wannan turaren naki bana sansa, Dan Allah fita daga
Dakin nan,"
husna tace "yar renin wayo dagani har ke dashi muke amfani kafin kitafi school......
Kafin tagama magana nasake yin toilet da gudu nayi wani aman, aikuwa ina futowa tajani, ta
duba idona, takama hannu na, ta duba, cikin loka ta dauko pt strip, tace" jeki iyo min fitsari
anan"
tabata wata roba, aikuwa ba musu feenah taje tayi, jikinta duk yayi sanyi, ta futo tabawa husna
Jikin husna ne yadauki rawa ganin layi guda biyu Ajikin pt din, wato kenan abinda take tunani
ne yake San tabbata, lokaci daya hawaye yasilalo daga idanunta tana hawaye tace "feenah"
Nakalleta da mamakin meyasa ta kuka, tasake cewa "feenah wayayi miki ciki?"
Kuka nafasa da karfi, nadora hannu na akaina, hakan yasanya mama dataji shiru daga kiramin
auta itama tayo Dakin cikin sauri
Abinda kunnuwanta suka jiye Mata ne yahanata qarasawa Dakin
Mrs Usman ce í ½í¶Š
[5/6, 3:32 PM] â£ï¸DANGI DAYAâ£ï¸: í ¼í¼±DANA SANI í ¼í¼±
Writing by Amnah el yaqoub
Dedicated to my family
29
Ganin yaqi bata wayar yasa tasa hannu ta karba, "hello yata yagida?"
Husna cikin ladabi tace "mama ina wuni?"
Ummi cikin Jin dadi ta nemi wajan zama tace "alhmdlh ummin tahir ce"
Husna zare ido tayi tace "ummi ina yini ai ban ganekiba"
Ummi Ana murmushi a kace "a a ai ba komai yarinya, yaya sunan kine?"
Tace "husna"
Ummi tace "masha Allah, yaushe zakizo naganki?"
Husna tace "ai da nisa, saide wani lkcin idan munzo kano sai nazo"
Ummi tace "a a ba'a nan Garin kikeba?"
Husna tace "eh wlh muna zaria"
Ummi tace "Toshiknn yata Babu komai kinji, ki gaida ummanku,"
"to Ummi