Showing 27001 words to 30000 words out of 70697 words

Chapter 10 - Yan Abuja Compelet Book by HAERMEEBRAERH--.pdf

27 Apr 2025

4570

brush ya wanke bakinnan fes,sai ga Talle an yi shar,
shima kar ba yai ya mata wankan ta wanke bakin ta, ta fara leqawa taga ba yaran maza ta fito,
daga baya shima ya biyo ta dakin, shirya shi tai tace yai alwala ya je masjid" ka ji min yarinya da
ke kk sani nai sallar? To banga dama ba hadawa zan da isha'i" " Aa Allah ya baka hakuri, ni so
nake dama kayi da wuri saboda in na zo maka tausar nan bana son abinda zai sa na tsaya"
cikin yauqi da kwarkwasa take maganar,tini ya washe baki kamar dolo, miqewa yai zai tafi
masjid, yajiyo maganar ta," Babe in kaje ka jira sui isha'i kawai ka ga in ka shigo sai asuba
zamu sarara ko ya kace" ta na kashe mai ido daya, " maganar ki duce sweety na" ai ko ana idar
da isha'i sai gashi ya shigo fakam fakam, yana shigowa ya tadda ta tai gayu sosai da yan kayan
da take da su, ta dan fesa turaren ta da ya kusa qarewa dan kale ma take yi, yana shiga daga
ta sama yai yana juyi da ita,ita ko dai dariya take tana sakewa, kisses ya fara aika mata da shi
tana mayat mashi, suna tsaka da wasannin su ya katse ta da "ni fa yunwa nake ji, mu fara cin
abinci kannan yarannan sun yi bacci sai mu dora daga inda muka tsaya, dan yau sai na saki

kiran sunan tsohuwar ki" dariya ta ke sosai a haka ta dakko masu abinci suna ci suna hira, "
Babe me yasa ka amshen waya ta ne, tinda naxo yanzu kusan wata bakwai da wasu kwanaki
ban ji muryar kowa nawa ba" wani mugun kallo ya buga mata daya sa cikin ta kadawa, dan dai
Tallen Tallen ne fa, sunkuyar da kai tai tace" ka yi hakuri ba zan sake zancen ba" wasu hawaye
masu zafi suna sauka a fuskar ta, hannu tasa ta share su kamar ba ita tai kuka ba, ta dakko
cokalin abincin ta kai bakin shi, amsa yai ya dan sake rai kadan, a haka har suka gama,
Huwaila da Jummala kamar yanda suka saba sun fita zance amma zancen da su Badamasi ne,
ana can ana latse2 da tabe2 da tsotse2, ita kuma Marka sun gama shirya duk abinda ya
kamata cikin duhun nan ita da Yayan Talle, da zata wuce ne ya daki duwais din ta ta baya, juyo
wa tai ta hau masifa" kaifa yayan nan jarababbe ne, kwana dayan nan da akai ba ai abun ba
duk ka zama kamar ka dauke ni mu gudu, to ina sanar da kai ka iya takun ka, kasan Talle ya
fika wayo ko dan ba soko bane kamar ka, zai iya gane wa" kada mata kai yai alamar zai kiyaye,
shigewa tai, Salma amarya ana can ana soyewa ita da me gida, Sun yi nisa ba sa jin kira,
komai ya kankama, har ya fara aiki, suna cikin yi ne sukaji motsi ana sanda, gaba daya Talle ya
cika wajen na su da gurnanin shi, Marka kamar ta mutu dan kishi, ga wani irin feelings da take
ji, sai matse qafa take ta kai ta dawo, ta kuma kaiwa ta dawo, tana jin motsin tace," Alhamdu
lilLAAH" ai ko ta manna kan ta a jikin qofa taji ya za a kaya, " Salame bude qofar mana na iso,
me kk yi ne baki riga kin bude ba sai na zo ina bugawa sun ji kamar rannan, so kk wannan
shegiyar kishiyar taki mai baqin tsiya taji ta leqo irin na rannan, Salame ya dai naji ki shiru, dan
Allah ki sauri mana ki bude muyi mu gama na tafi a matse na zo yau" Talle da ya gama jin
komai wani shaqa yai ma Salma da idon ta ya firfito waje, amma da sauri ya sake ta ya sauka ,
ya saka wando jin da yai ba a daina taba qofar ba,kuma ba a daina kiran Salma ba, ai ko mai
maganar da ya leqa ta bular da yake hango su yaga yana ta howa da gudu ya kwasa yai waje,
ya fito da hanzari yaga an gilma da gudun tsiya komawa yai dakin, dan ya san laifin ta ne koma
wane, kan yaje ta zura rigat ta tana ta kukan wannan masifa da ake neman jefa ta, " Marka"
shine abin da ta furta,dafe kan ta tai, da ta sani da bata tsuye ta ba ta bat su da halin su, gashi
yanzu ta jawa kanta,dukan ta ya fara ko ta ina tana ihu tana ya tsaya yaji me ya faru, ba ta da
laifi, inaaa dukan ta yake tin tana kuka tana bashi hakuri sai da ta koma ajiyar zuciya, sai da ya
tabbatar ta kasa motsa ko da ya tsan ta ne sannan ya futa dakin Marka, tana bude qofar ta wani
azababben mari ya maka mata, " Dan uban ki kin san hakan na faruwa ashe kk munafurcen
baki gayan ba ko da ta wayar yarannan ne? Ga shi kwarton na ta ya ce kin gansu" kuma ta fara
dan marin ya matuqar shigar ta" inna fada maka ba yarda za kai ba cewa zakai kishi ne,
shiyasa nace Allah ya nuna maka da kan ka ka gani" kwafa yai yace zata ci uban ta na san
maganin ta ai,komawa yai ya kwanta, a dakin markan, nan take jarabar ta ta motsa, musamman
d ta gan shi ba riga,matsawa tai da zummar kwanciya gefen shi, da dabara ta goga qirjin ta a
bayanshi, wata ajiyar zuciya ya sake ya finciko ta, da zafi zafiya ya fara aika mata saqonnin shi
cikin huce haushi, marka tun ana na dadi tana kukan dadi, sai da ta fara kukan wuya, roqon shi
ta ke Allah Anna bi ya kyale ta amma inaaa yai nisa, sai da ta gwammace ba tau wa Salma
mugunta ba ranar, fadi yake yana" duk sai kunci uban ku, zan maganin kowa a cikin ku, ki min
shiru abin da kk so nake baki ko na farfasa maki baki" ya kaiwa bakin ta duka, dip tai bata qara
kokawa ba sai kukan zuci, da sassafe ya shirya ya daukar wa Salma kayan ta suka wuce cikin
garin Abuja, Marka kamar ta mutu dan haushi, ita da ta so a barta ta zauna da su amma shine
aka tafi da ita, kai wannan abin haushi da yawa yake.

Sun isa Cikin garin Abuja da rana wajen 12pm, gidan Alhjn shi ya kaita, sun qara yin tafiya,
amma wannan karon dakin shi na gidan nan ya kaita, ya aje ta , yai ficewar shi, miqewa tai
fuska ta kumbura sintim da kyar take gani, ta jingina da ginj ta rungume guiwowin ta tana kuka
mai bam tausayi, nadamar zuwan ta ABUJA kam ta yi ta ba iyaka, wato in baka iya kama
barawo ba ya kama ka, wannan shine ya faru tsakanin ta da su Marka.









Jabeer ne yai sallama ya shigo fuskar shi cike da fara'a kamar wanda yai tsintuwar
dimond...........[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 'YAN ABUJA




BY HAERMEEBRAERH




Hey guys thank you so very much for everything. Na ji dadi sosai da kulawa da nuna damuwar
ku, na ji sauqi sosai. Alhamdu lilLAAH. Love u da yawa❤




Page 16:

Shiga yai hannun shi buyu boye a bayan shi, ita kuma ta sowa tai da niyyar mishi sannu da
zuwa yanda suka saba, sai taga ya maqale a jikin gini yana mata dariya, daga girar ta daya tai
tare da lumshe cikin wani salon daukar hankali" me kk boyewa baka son na ganiiii" " matso
kusa ki gani to" matsawa tai, kusa da shi sosai, in ta matsa yace ta qara, haka har saida jikin ta
ya zama gaba daya a nashi, sannan ya fidda hanneyen shi ta bayan ta, ya rungume, yai kissing
din ta sosai, sannan ya kama ta suka zauna, miqa mata leda yai ya tallabe fuskar shi yana
kallon ta da murmushi, bude ledar tai itama tana murmushi tana kallon shi tana kuma kallon
ledar, tana budewa taga wayar da zatai dubu sha biyar, bude baki tai cikin murna da tsalle, ta
dane shi tana mai kisses ko ta ina, kama ta yai ya riqe kafadun ta, " My princess ki nutsu kina
girgiza mana bby, so kk kuji ciwo?" " Kaiiii amma mine na gode, na gode , na gode, Allah ya
saka maka da alkairi, Allah ya sama dukiyar ka albarka da rayuwar ka gaba daya, Allah ya jiqan
iyayen ka ya sa su cika da imani" " Shhhhhhh wai wannan godiya haka kamar na sai maki
mota?" " hmmmm kai ka ga bai kai ai.wannan godiyar ba, kai ma kasan ina da son waya, a
matsayina na wacce ba ta taba riqewa ba yau na samu ai sai godiya ko, beside macen kwarai
dole ne ko tsinke mijin ta ya kawo ya bata ta nuna mai godiya da murnar ta, in ba haka ba taiwa
kanta baqin ciki dan gaba ba zai ci qwarin guiwar kawo wa ba" " wannan haka yake macen
kwarai, mace daga cikin matan aljanna, Juwairah in dai ta dalilin miji ake shiga aljanna na maki
alqawarin na yarje maki" wani irin hawaye mai dumi ne ya ke bin fuskar ta na tsantsanr farin ciki
da nishadi, ga wani son shi da ke ratsa shi, " Yah Jabeer, na gode sosai Allah ya bar mu tare ,
mu je aljannar tare, domin kaima ka shiga cikin alqawarin Allah duk mai kyautata wa iyalin shi
zai shiga aljanna, kana daya daga cikin mazan da suke koyi da halayen Annabin rahama da
sahabbai" haka sukai tai ma junan su dadadan kalamai, ( abinda aka rasa a wannan zamani
kenan, saurayi zai tai ma budurwar shi daddadan zance kan aure, amma da anyi kwanaki ya
daina kenan, itama haka, sai a dawo kowa na dana sanin auren dan uwan shi, auren duk da
muke ganin yana dadewa wallahi ba sa dai na neman junan su kamar ranar suka fara haduwa,
kowa a kullum yana son ya fidda sabon salon da zai faran ta ran dan uwan shi ne, dan haka mu
ci gaba da nemawa juna farin ciki sai auren mu yai qarko).




Bayan an kwana biyu Suwaiba da Saudat sun fara sabawa da wannan mummunan labarin da
suka juyo wa kansu, Saudat ta fara neman dalilin da zai sa ta san me ne ne silar rashin
haihuwar su, watarana Alhj Kalla zasu tafi meeting gidan Oga Zaks , domin a wannan yana yin
da ake ciki ta fuskanci ko su su waye, sai dai ta qi gayawa Suwaiba dan ita akwai wauta, da ta
sani zata fasa kowa ya san sun sani, ta ko jawo masu masifa, sai da ta gama jin komai wani
member suka samu da zai shiga qungiyar tasu amma bai san location ba, take Alhj Kalla ya
fara bashi address, Saudat na kwafewa, tana gamawa zata tura riga Alhj Kalla ya fito, gaban ta
ya fadi amma ta dake, ta ci gaba kamar tana gyaran rigat ne," Ohhh mata kenan, daga kwalliya
sai saka kayan ado, sai gyare2 kawai kar dai aga munin ku" dariya sukai gaba dayan su," ina ta
kiran ki ina palo banji kin amsa ba" take ta gane wayo yake son mata," ai ban jiba Alhj na, ni da

nake nan kana can,wataqila ma da ka daga murya dana jiyo ka, tinda kai ba zakai amfani da
waya kana kirana ba , sai kai ta kira in ban ji ba kace nai laifi" murmushi yai a ranshi ya tabbatar
bata ji komai ba, "k shikenan je ku dakkon ruwa na sha anjima kadan zan fita" tashi tai tana
kada jiki tana yauqi tana isa kitchen ta qarasa da hanzari ta ciro takardar ta wulla a bayan fridge
din dan ya fi kusa, motsin shi ta ji ya biyo ta, budewa tai kan ya qaraso ta dakko ruwan da cup,
yana isowa tace" hmmmm Alhj na kana sona da yawa na kula 'yan kwanakin nan kamar ka
maidani rigar sawa ko ina zaka sai dani" murmushi yai yace" ai ke kk koma haka shiyasa na
koma hakan" ya karbi cup din ya hade da hannun ta, ya matse saida tai qara, ya zaro mata idon
shi jajaye yace" ki kiyayi bincike domin yana kai maiyin shi ga halaka" " Bannnn......ban
ganee...baaa" " dalla malama rufen baki, ji kk ban san kina bin waya ta ba? Ko in da na fita, ki
gani? Ina nake zuwa me nake yi? Me kk son sani yau na sanar dake? Dan ba tsoron ku muke ji
ba? Auren kwadayi auren kudi kukai, kuma kuna samu, to meye na sai kun ji kwakwaf?" Jikin
Saudat sai rawa yake wani ruwa2 taji na tsattsafo mata ta qafart ta batai aune ba taji ya kwada
mata bari" Dan uban ki fitsari kikai a tsaye? Ji yanda kk batan takalmi ni da zan fita? Me kk sani
game da mu?" " Alhj ban san komai ba, sai dai zargi da nake" aje cup din yai ya zaunar da ita a
kujerar dinning dake kitchen din " ehen ina jin ki zargin me kk?" " dama ina zarkin ko ku yan
damfara ne, kai da Alhj Salihu" " kin tabbata zargin da kk kenan?" "Allah shine" " to bari kiji,
zargin ki ya tabbata, amma idan na ji wannan maganar ko a wajen waccan doluwar yayar taki
da ba abinda ta sani sai barin zance, da soj kudi, kin mutu, kinji ko baki ji ba" cikin tsawa ya
qarasa zancen," Nnnnaaajii..."" Good,ni na fita, miqon takardar da kk boye kan na karya ki"
tashi tai ta dakko ta miqa mai, ficewa yai ya barta ta durqushe tana ta kuka, lallai yau data gaya
mai abin da ta gano game da shi da fa shikenan kashe ta zasui, yanzu ta gudu ma nan ma har
gidan su zashi wataqila ma ta jawa uwar su a hada da ita a kashe, ta zauna tai shiru sui ta cin
kudin haram kudin jini, "kaiiiiii wannan Abuja ba tai ba, inaaaa" ni dana sani a Damaturu nai
aure na ma" ta fada tana share majina.




Salma ido ya kumbure dga zaunen tai baccin wuya ba shi ya dawo ba sai wajen la'asar, riqe da
koko da qosai dan yamman nan da ake yi, sai wata leda mai kaya a ciki kala uku da takalmi
kala biyu sai jaka daya, da yan kayan kwalliya da ba a rasa ba, miqa mata yai, ta tashi ta isa ta
karba, leqawa tai ta yamutsa fuska, " baki daku ba kenan ko, gar da zan baki abun da ban sai
wa Marka a shekara goma ba, ke kin samu ma kk kyabe baki ko" a tsorace tace" na gode" ta
tashi ta shiga dan bandakin dake maqale a dakin tai wanka ta canja kayan ta fito, koko da
qosan ta dauka ta ci ta sha, sannan ta koma ta zauna, " kin iya cewa wani yai sallah amma ke
bata dame ki ba, ji kk ban gane ki ba, wa'azi a baki amma ke baki aiki da shi munafuka, irin
kune kuna da yara kuna sa su sallah su qi, to basu ga kuna yi ba" miqewa tai zalo zalo taje tai
alwala tai sallar ta koma ta zauna," zuwa gobe ogana zai dawo shi kadai yake zama anan,
matan shi suna maiduguri, aiki ke kawo shi nan, dan haka in ya dawo da yamma ki shirya muje
mu gaida shi, in muka dawo na gan ki a waje ko kusa da wajen dakinnan kin mutu ranar, dan na
san ki idon ki idon kudi, kice zaki maqale ma bawan Allahn da bai san neman mata ba, na kula
akan kudi komai yi zaki, tinda an iya bin qattin qauye masu bada dari da hamsin" hawaye take

sosai sunqi tsayawa, haushin ta bai wuce yanda yama qi ya saurare ta ba sam, ya tsaya ta mai
baya ni yaqi, kawai sai ta maida kanta ta kwanta, bata qara furta komai ba har ya shirya ya fice,
kuka take mai ban tausayi" Oh ni Salma na saiwa kaina wahala daga yar shawarma da motar
dana gani duk na rude ga inda na kawo kaina, Abuja ko wahala?"



Da kyar Marka ta miqe ta je ta hada wuta ta shiga ruwan dumi ta gasa jikin ta, komawa tai ta ci
gaba da kwanciya, wani qaramin yaro ne shafi'u daya daga cikin yaran da Talle ke auri saki ya
shigo zai kai shekara goma, baya jurar yunwa shi, dan ko da su Huwaila na baccin gajiyar
iskancin su da suka sheqewa da dare, ita Marka takan tashi tai abin kari da wuri, to yau sunji
shiru kowa dif a gidan, tura kai yai ta ware qafafu tana ta firfita da mafici," Marka yunwa muke ji"
da sauri ta sake zanin ta juyo kan shi," me kace?" " cewa nai yunwa muke ji" habaaa ina wuta
na saka wannan yaron, inji Marka, kiran shi tai tace zo ka karba, yana isa data damqe shi ta
hau duka, tana" sai na fashe dukana akan ka, dan uban ka, banda wannan ta'annutin da uban
ka ya min, har abinci kk tambaya? Ga shi tinda ya dauke waccan jaja amaren sai da na gan shi
kuma, to ko xaka ci abinci har ka qoshi, amma na duka" dim dim dim kk ji" Marka lfy me ya miki
haka" cewar Haule kenan, tana qoqarin kar bar shi, wani mari itana ta karba, kai na taqaice
maku duk wanda ya shiga sai ta saki wani ta kama wani haka tai tayi kamar mahaukaciya, sai
da ta gaji jikin ta yau laushi sannan ta kwanta tana kuka, ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login